KULSOOM

TWENTY SEVEN

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

            P27

FREE BOOK

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

Marubuciyar:

ZAYTOONAH

ABARWA RAI

KIBIYAR SO

GUDUN WUCE SA'A

SABABI PAID

Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:

@Ummu-ameer

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

   

   Mamakinta ya kasa ɓoyuwa har ta samu wuri ta zauna ta kasa ɗauke idonta a kaina kamar yadda ni ma na kasa daina kallon ta.

“Kulsum kin ganki kuwa? Masha Allah tubarakallah!”

Dariya nayi Nima na ce.

"Ke ma kuwa kina kallon kanki a mirror? Wallahi kin yi muni sosai, ji yadda hancin ki ya wani buɗe, ciki bai miki kyau ba duk ya canza miki halitta”

Dariya Azima tayi har tana dafe ƙatoton cikinta da ya turo sosai daga ƙasa tace.

“Muguwa kawai. Wallahi kamar kin sani tunda na dawo garin nan liƙab nike sakawa idan zan fita, na koma wata horror. Kafin in dawo kuma Idan ya tashi mugunta ya sakani gaba yayi ta min dariya har sai ya ga raina ya ɓaci tukunna sannan ya bari”

“Amma dai baki da kirki wallahi, Tun yaushe kika shigo garin nan?”

“Yau two weeks Kenan. Wallahi nayi takaicin abinda ya faru, ga shi su su Hajiya ba Susan Wai da ke a motar su Lukman ba, ance Ummu amma ba su gane ke bace, ni kuma tun ranar kin san muna isowa ya karɓi wayata ko da ya dawo da ita ya canjamin har simcard ɗin aikin ƙaddara kuma ya karya wancan maimakon ya fara bani in yi copy. To abinda ya ƙara ɓata al'amari Maimu sai ta ce musu wai bata san ina kike ba, kuma 'yan gidanmu duk basa garin suma suna zariya tsabar mugunta da rashin tausayi, ni ban san mi yasa tayi haka ba?.....”

Murmushi nayi na ce.

“Azima duk wannan ya wuce, Alhamdulillah! Sai an rasa wani abin an sha wahala ake samun wani abin. Allah ya ƙaddaro sai hakan ta faru da ni ta sanadiyyar wannan ne har Allah ya kawo ni wannan matsayin, saboda haka ko kaɗan ban riƙe ki a rai ba wallahi. Itama Maimu na yanke duk wata alaƙa da ita amma na yafe mata duk abinda tayi min wallahi har cikin zuciya ta. Ya gida? To amma cemin zakiyi tunda aka kai ki baki zo gusau ba?”

“Wallahi Kulsum ban zo ba idan kin yarda. Ai ko sati bamu cika ba muka wuce portacourt, sai yanzu da cikina ya shiga watan haihuwa ya kawo ni gida”

“To ya akayi kika san nayi aure yanzu?”

“Ina isowa ko minti ashirin banyi ba naje gidan ku, shine ake faɗamin kinyi aure, na ce idan na shirya zanzo, to yau ban fito da wuri na je khadija ta kawo ni...”

Cikin mamaki nace.

“Khadijah! Where is she?”

“Da ƙyar fa ta amince, wai saurayin ta zai zo kada in shiga haƙƙin shi. Shi ne nace ta kawo ni kawai idan muka zo sai ta koma, to shi ne ko gidan bata shigo ba mai napep ya Juya da Ita.”

“Lallai Khadijah....”

Dariya Azima ta fashe da ita tace.

“Abincin wani gubar wani, wato Maina zata aura?”

Miƙewa nayi Ina faɗin.

“Wallahi kuwa kedai... Nima sai daga baya na san suna tare.... Bari in kawo miki ruwa na tsaya sai cika ki da surutu ni ke”

Bayan na dawo muka yi ta firar duniya itama tayi mamakin auren Khaldun da nayi, nima na bata labarin yadda abubuwa suka kasance min.

Kallo na tayi tana murmushi ta ce.

“Idan ciki na saka wasu muni ke kyau kikayi, duk da dai may be sabo ne sai ya tsufa mu gani”

Taɓe baki nayi nace.

“Cab! Wallahi ko mai ba ni da...”

Cikin mamaki Azima ta ce.

“I don't understand. Planning kukeyi Ko kuma Allah ne bai kawo ba? Gaskiya da baku yi tunani idan har kuka fara Family planning baku ga ƙwan ku ba....”

Dariya na fashe da ita na ce.

“To Uwa Azima dan Allah kiyi haƙuri na tuba. Mutumin da ko hannuna bai taɓa riƙewa ba taya zakiyi tunanin ciki balle har in kai ga yin wani planning”

Tamkar wadda mummunan saƙo ya isarwa ta dafe ƙirji tana mai zaro ido waje ta ce.

“What?? Kulsum are you kidding me?”

With a serious tone na ce.

"Wallahi I'm serious Azima. Farkon kawo ni ma na sai in fi wata ban sanyan shi a ido na ba, Sai daga baya ne da ya sakani a Islamiyya, kullum shi ya ke kai ni ya kuma dawo dani, to daga nan ne muka ɗan samu kusanci kaɗan, Sai idan kuma zamu fita ya ce min in shirya lokaci kaza zamu fita. Duk inda zanje yake kai ni ya dawo dani, daidai ku ne driver ke kaini ko shi sai ya fara gayamin a waya idan bai same ni ba sai dai in fasa idan ba ya nan, Sai ni ke ganin kawai rashin yarda ne. Amma gidan su gidanmu, gidan 'yan uwa duk ya kwanta ta ranar da ba islamiyya yana kaini in wuni sai dare ya dawo da ni. Ƙanwar sa kuma idan zanje saloon ko kasuwa tare muke zuwa tana rakani. Dukkan ƙannensa su uku suna daraja ni suna mutuntani sosai tamkar yadda suke masa. Abin takaici abin baƙin ciki Azima kin ko suna na? Ko suna na bai sani ba, duk zai min magana sai dai yace min Ke! Ko kuma Malama....”

“Innalilahi wa inna ilaihi raji'un! Yanzu duk tsawon lokacin nan Kulsum a haka kuke rayuwa?”

Murmushin yaƙe nayi ina gyaɗa mata kai nace.

“That's how we be. But muna girmama juna, idan na gaishe sa yana amsawa cikin mutunci. Kuma yadda yake min kallon tsana da wulaƙanci a baya yanzu duk ya daina. Komai na jin daɗi matuƙar kuɗi na sayen sa babu abinda bai yi min, hatta wayar da ya sayamin kusan 1.5 million ya saye ta. kuma ina farin ciki sosai a haka, Sai dai kawai matsala ta auratayya....”

Hawayen da suka ziraro mata ta share cikin ɓacin rai tace.

“Kulsum you are mad! Ban taɓa sanin cewa ke mahaukaciya ba ce sai yau. Abu kamar ba wayayyiyar mace ba. Taya kika bari abubuwa suka kawo ku har haka?....”

"Mtsw! Azima you won't understand. Mutumin nan ya wuce duk yadda kike tunani.....”

“ What is that that I can't understand? Ina ji tell me? Kin zauna kin zama shashasha, aure almost a year kin zauna kin cutar da kanki kin kuma cutar da mijin ki. Who's at fault now? KE? Because da ace kin koya masa ƙaunar ki da son kasancewa tare da ke da yanzu ya zama ɗan gari. Na yarda baya son ki aura masa ke aka yi dole but the way he's treating you ya kamata ace kin zauna kin saka tunani a cikin kanki, da ace baya son yayi rayuwa da ke ba uwar sa ba ko acikin kundin ƙaddarar rayuwar sa aka ce idan bai zauna da ke ba komai zai iya faruwa da shi wallahi sai ya rabu da ke ɗin duk abinda zai faru sai dai ya faru.....”

Tsaki ta sake ja tana kallona tace.

“To wai ko dai shima bashi da lafiya ne? Idan ba shi ba, ace mace irin ki tsaye da kyau zaune da kyau ga ki sai wani ƙyalli ki ke amma ko sau ɗaya bai taɓa attempting kai miki farmaki ba daga ke sai shi a cikin gida....”

Dariya na fara ƙasasa domin maganar ta bani dariya, amma kuma can wani gefe na zuciyata duk na amshi kalamanta....

Cikin jin haushi ta kalleni tace.

“Au! Dariya abin ya baki kenan ma? Wallahi I'm very serious Kulsum wannan ba abin dariya ba ne, abin takaici ne abin a jajanta. Ji na ke a zuciyata kamar in samo bulala ta mai baki kyau in yi ta zanar ki da ita wallahi. Wallahi ki tashi tsaye ki nemi hanyar da zaki samu kan mijin ki. Aure babu activities ɗin auratayya miye amfanin shi, duk wani jindadi da kike ganin kina ciki aikin banza ne, baki mu'amala da miji, ba ku firar soyayya baku ta yau da kullum baku neman shawarar juna. Jindaɗi bance laifi ba ne amma dai idan akwai mu'amala tsakanin ku zaki fi jindadi amma ba zaki gane abinda nike faɗamiki sai kun zauna da juna tukun”

With so much interest na bata dukkan attention ɗina nace.

“To yanzu ya zanyi?”

“Malama ki yi duk yadda zakiyi zama ya riƙa haɗaku wuri ɗaya, ki riƙa girka masa abinci kina ciyar da shi safe, rana, dare. Sannan kiyi ƙoƙari kiyaye duk wani abinda kika kasan baya so da wanda ya ke so. Idan zakiyi magana ki riƙa sanin abinda zai fito daga bakin ki ba komai zaki riƙa furzowa ba, sannan ki riƙa sanin yadda zakiyi seducing nasa, har sai ya ji a cikin zuciyar sa akwai wani abu a tare da ke wanda ya dace ace ya kasance da shi...”

“To ya zanyi kenan?”

Tsaki ta ja tare da Miƙewa ta ɗauki Jakarta da nufin tafiya, nayi saurin riƙe jakar ina roƙonta dan Allah ta tsaya wallahi har zuciya ta da gaske nayi maganar.

Zaunawa tai tayi ta bani shawarwari, da hanyoyinda zan bi wurin ganin na samo kan mijina. Sosai naji daɗin zuwan Azima daman abubuwan suna damuna sai dai bani da wanda zan tun kara ya bani shawara, duk da Ayusha in mun haɗu tana yawan cemin idan ina da wata damuwa in riƙa neman ta a shirye ta ke ta bani shawara, to gaskiya ba zan iya ba, domin a yadda suke ganin mu dani da shi ba za su taɓa cewa wai mu ɗin ba abu ɗaya ba ne. Mama ma haka ba zan iya tunkarar ta ba domin a yanzu hankalin ta ya kwanta ganin na zauna gidan mijina lafiya auren khadija ta ke dubi yanzu to ba zan iya kai mata wata matsala ba. Maman surayya kuma da muke zama a islamiyya muna girmama juna tana ganin yadda mijina ke ɗawainiya da ni bata taɓa kawo komai ba ni ma kuma na ɗauka kawai islamiyya ce ta haɗa mu saboda haka ba zan iya fayyace mata damuwa ta ba. Sai gashi yau Allah ya kawo min Azima ta bani haske kuma in sha Allah I will try all my possible best in ga mun zama ɗaya.

Katsemin tunani tayi da faɗin.

“Tashi ki kawo min maltina marar sanyi sosai in ta shi dare yayi”

Miƙewa nayi ina faɗin.

“Gaskiya tana da sanyi sosai sai dai ki saka a ruwan ɗumi. EDD ɗin ki yaushe suka ce miki?”

“A lissafi yau saura kwana goma ya cika”

“To Allah ya kawo miki mai sauƙi”

Ina ajiye mata na ce

“Bari in duba idan yana da chance sai ya ajiye ki gida, dare yayi yanzu da wuya a samu abin hawa da wuri”

Kai tsaye na yi knocking ba tare da wata damuwa ba, domin yanzu ni ke so in fara aiki da shawarar da ta bani ba zan tsaya sanya ba.

Sai da nayi kusan almost 2minute a tsaye sannan ya bani go ahead. Sallama nayi na shiga yana zaune yana kallo wayar sa na hannun sa da alama amfani ya ke da ita.

“Sannu da hutawa Yayanmu”

Ido ya zuba min yana kallo na yadda na shigo daga ni sai mini trouser da half vest ɗin da ke jikina kai na ba ɗan kwali.

Sai da ya gama ƙare min kallo sannan a matuƙar mamaki ya ce .

"Ke! What nonsense is this? Kin ɗauka gidana gidan iskanci ne....”

Shagwaɓe fuska nayi tare da turo baki na kwantar da murya ta nace.

“Allah ya huci zuciyar ka Yayanmu, amma ni ban yi don in ɓata maka rai, kayi haƙuri. Amma kada ka manta ni fa matar auren ka ce, babu abinda ya haramta a gareka idan har Kaga jiki na....”

Cikin fushi yace.

“Oh! Ashe kin san da cewa idan wanda ba muharram ɗin ka ba ya ga jikinka ka aikata zunubi, kika yarda har kika nunawa maza jikin ki da nufin bada go ahead ɗin suyi duk abinda suka ga dama da ke......”

Ban san lokacin da na fashe masa da wani mugun kuka ba, because I have already got it, he's referring to our first meeting. Innalilahi wa inna ilaihi raji'un! Abinda na ke ta nanatawa kenan a cikin zuciyata. Tabbas na riga da na baro kyau tun ranar haihuwa ta...wannan wane wace iriyar kalar ƙaddara ce..??

Tsamo tsamo nayi tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi. Ƙyale ni yayi naci kuka na a wurin sai daga ƙarshe murya a dusashe na ce.

“Na rantse da Allah, wannan ranar ita ce ta farko kuma ita ce ta ƙarshe, ban san ko hannuna wani namiji ya taɓa riƙewa ba.....”

“What are you here for?”

Cikin sheshsheka na ce.

“Azima ni ke so mu mayar gida dare yayi, kuma ga tsohon ciki a jikinta”

“Ki jira ni Ina fitowa”

Har ya gama canzawa bai daina ganin ta a idon sa ba. Kukan da tayi yayi matuƙar taɓasa sai dai duk lokacin da ya tuna yana jin tana bashi haushi ne kamar yayi ta dukan ta haka ya ke ji.

Ko da ya fito ya cimmata ta zuba hijab har ƙasa da liƙab kamar yadda ta saba duk zasu fita. Kuma ganin haka yana masa daɗi yasa da suka fita kasuwa ita da Meerah da khadija ta yanko 4-4yrd da sabbin liƙab with socks. Duk in da zasu je a haka suke tafiya.

Gaida shi Azima tayi ya amsa cikin fara'a kamar ba shi ne ya gama gurza mini ba yanzu.

Bayan mun ajiye ta har ƙofar gidan su ta tsaya ta bani digits ɗinta sannan muka wuce. Muna kan hanyar mu ta dawowa Ramlah ta kirani tana shaidamin Ayusha ta haihu amma Sa'ad ya ce ba zata je ba sai gobe.

Wani uban ihu na buga ina tambayarta mi aka samu tace Baby boy ne.

Shi dai ƙala baice min, ina cikin wayar shi ma naji Ayaa ta kira shi tana sanar mai.

Kallon shi nayi bayan ya ajiye wayar na Shagwaɓe murya nace.

“Yayanmu dan Allah muje mana... Ka ji... Please...”

“OK!”

“Thank you”

Nan da nan sai gamu a FMC. Sai murna na ke,da na rungume babyn ji nike tamkar nawa ne, mai kyau da shi. Shima Yayanmu ya daɗe riƙe da babyn ban san mi yake ji a ransa ba amma ya kafe sai kallon sa yake. Sai da Barrister kabir ya shigo sannan ya bawa Meerah shi suka fita suna magana.

Muna nan muna fira da Meerah, ita Ayusha ta dai shiru kawai tana sauraren mu. Sai kusan sha ɗaya muka baro asibitin.

Muna kan hanyar na kalle shi na ce.

“Yayanmu zan sha rufaida please”

Na zata bai ji abinda nace ba ne, domin ko bihim bai ce mini ba ni ma kuma sai na kama kaina.

Muna isowa titin da ke shagon Rufaida yogurt ya tsaya ya siyo sannan muka tafi.

Ina karɓa na shige ɗakina na cire kayan jikina na watsa ruwa na zauna na buɗe ledar, har da gasashiyar kaza a ciki.

Kitchen na je na ɗauko fillet na zuba mishi naman kazar na ɗauki robar Rufaida na je har ɗakin sa.

Har bedroom na samesa, yana zaune akan sallaya da jalabiya a jikin sa yana waya.

Wayar yake amma gaba ɗaya hankalinsa ya dawo kaina.

Wata figaggiyar sleeping dress na saka pink, shara-shara ta ke kuma a bakin guiwa ta tsaya mini, na saka hula mai bakin lace itama pink colour ce.

Tsinke kiran yayi yana mai kafe ni da damuwansa da basa ko ƙyaftawa ya ce.

“Lafiya”

“Yayanmu na kawo maka na ka ne”

“Yaushe na faɗa miki ina buƙata?....”

Shagwaɓe murya nayi tare da langwaɓar da kai na ce.

“But ai tare muka siyo saboda haka tare zamu ci”

Mamaki ne ya cika masa zuciya. Wai yarinyar nan ko dai wasu aljanu ne suka taɓa ta?.....

“Dan Allah mana...”

“Na ji to, ajiye nan ki tafi zan ci idan na gama”

“Thank you. Allah ya tashe mu lafiya”

“Amin, thank you too”

Yana gamawa yaci kaɗan kamar yadda ta Buƙata. Ko a gado ya daɗe bacci bai ɗauke sa ba, Kulsum kawai Yake gani yana tunanin yadda Iya confronting ɗin sa.

**********

Washe gari ko da 7am ta yi clocking na gama haɗa masa break fast, abinda ban taɓa attempting ba.

Ko da na shiga parlounsa har ya gama shiryawa ya ɗauko briefcase ɗin sa da nufin tafiya.

Muka haɗa ido.

“Good morning Yayanmu”

“Good morning!”

“Breakfast ɗinka ne na kawo maka”

Cike da mamaki yace.

“Breakfast fast?”

“Eh. Dan Allah Yayanmu kayi haƙuri kaci”

Ba yabo ba fallasa ya duba agogon wayar sa yace.

“Ana jirana a office ne, but kiyi packaging Sai ki saka min a mota”

“OK...”

Da sauri na koma Kitchen. Ban san wane kalar packaging yake magana ba ni dai na saka mishi a basket na ƙara yawan komai na kai mishi na saka a backseat na ce Allah ya tsare.

Har cikin ransa yaji dadin hakan. Yaci abincin fiye da zato, yana mai jin daɗin ta sauƙaƙa masa neman Breakfast ɗin a waje.

Da ƙarfe biyu ma da ya dawo sai da na introducing masa lunch yaci sannan ya kai ni Islamiyya. Da nai masa zancen zuwa gida wurin Ayusha cewa yayi in bari sai da dare. Idan kuma da rana nike so in jira sai Thursday and Friday.

A whole week haka mukayi. Da ya fahimci ina ajiye masa abincin rana sai ya riƙa isowa gida at 1:30pm. Yayi matuƙar bawa islamiyya ta muhimmanci ban san mi yasa ba. Kullum baya lattin dawowa. Ni kuma da zaran ya fita zan gyara masa part ɗin sa, in yi mana girki, idan na dawo in yi mana abu mai sauƙi a dinner.

Ana gobe sunan Ayusha munci aiki mun gaji, ina kwance ɗakin Ayaa bayan na yi wanka ina jiran Yayanmu ya zo mu tafi sai ga Azima ta kirani tana sanar min cewa ta haihu.

Cikin ihun murna nayi mata bar na bata assurance cewa da zaran mun gama wannan sunan in sha Allah zata ganni, amma ta turomin hoton Baby girl in gani kafin in zo.

Washe gari tun 10:am ya kai ni gidan mukayi ta hidima, har Innani da Khadijah sai da suka zo. Ban manta da mijina ba, ina ganin ƙarfe ɗaya tayi na je na diɓar mishi abincin da aka haɗawa Barrister da lemuka da komai na kira sa a waya nace ga abincin sa.

Shiru yayi sai da yaji ina ta kiran hello sannan yace zai aiko Sa'adu ya zo ya karɓa.

An ci an sha suna yayi masha Allah, yaro ci suna  'Muhammad'. Shi kenan na ce na samu sunan da zan riƙa kiran ta na huta, maman Muhammad.

Ƙarfe goma ya zo na fito ba tare da na yiwa kowa sallama ba, domin abin da 'yan uwansa suka yi min har in mutu ba zan manta shi ba. Da yamma suka iso gidan, Meerah ta rakani mu gaisa suka dinga gasamin maganganu son ran su wanda yasa na kasa daurewa na shige ɗakin Meerah da ba kowa na yi ta kuka, Meerah sai aikin bani haƙuri ta ke tana faɗin sai ta haɗasu da aya ta ɗaukar musu mataki, ni kuma na roƙeta alfarmar dan Allah kada ta faɗa mata kada ma ta faɗawa kowa ta bar shi a haka. Sai da na tabbatar tayi alƙawari sannan na ƙyaleta.

Muna shiga gida na wuce ɗakina na faɗa kan gado na tisa wani sabon kukan kamar zuciyata zata fashe haka nike ji........

Ban san ma ya shigo ɗakin ba sai da naji yana faɗin.

“Ke! Mi ke damun ki?”

Kasa ɗagowa nayi domin ban san mi zan ce masa ba, ni na san ina da zuciya sosai, idan nace zanyi magana a yadda nake ji yanzu tabbas numfashina zai iya ɗauke wa. Shi kuma duk ya ruɗe sai tamabayata ya ke mi ke damuna.

Jin nayi masa banza yasa shi fita ya koma ɗakin sa ya ɗauki waya ya kira Meerah. Tana yin sallama kai tsaye yace.

“Meerah mi ya samu Ummu-Kulsum?”

Zaro ido Meerah tayi tamkar yana gabanta, ta miƙe zaune daga kwancen da ta ke hankali tashe ta ce.

“Yayanmu ta faɗa maka anyi mata wani abin ne?”

“Fuskar ta kaɗai na kalla na fahimci akwai damuwa a tare da ita, kuma lafiya ƙalau tabar gidan nan, and you are with her throughout the day, so tell me the truth what happen?”

Duk da sanyin ACn da ya gauraye ɗakin baccin nata bai hana mata shafkewa da zufa ba. Tattaro courage ɗin ta tayi ta fara magana.

“Lafiya ƙalau muka yini Yayanmu, Sai da yamma matan Baba Hamza suka zo da su Auntyn Hamida, shi ne Ayaa tace in rakata ta gaishe su. To shi ne suka hau zazzaginta wai duk ita ce ta hana auren ka da Hamida, duk alherin da ka ke musu da abincin ka ke aika musu yanzu duk ta tare komai da ita da iyayen ta. Iyayen ta saboda tsabar kwaɗayi sunga kuɗi shi ne suka aura mata tsoho sa'an babanta.....”

“Waye tsohon?”

“Da Kai fa suke Yayanmu. Haka suka sakata a gaba suka yi ta zagin ta, shi ne da nace zan gayawa Ayaa ta hanani wai kada in faɗawa kowa....”

“Matan Baba Hamza! Baba Hamza na tashar Magami dai?”

“Eh..”

Kitt! Ya tsinke wayar, ranshi a mugun ɓace ya kira Sa'adu.

Yana ɗagawa bai jira komai ba ya fara magana.

“Sa'adu, gobe ka je ka faɗawa Baba Hamza ya yiwa matan sa kashedi Matata ba sa'an wasan su ba ce. Billahi idan har hakan ta sake faruwa ba zan ƙyale su ba.....”

Cikin ɗaurewar kai Sa'adu yace.

"Yayanmu ban fahimce ka ba fa, mi ya faru ne?”

“Ask Meerah, she will tell you yanda Suka tozartar min da Matata”

Kashe wayar Sa'adu yayi ya kira Meerah ta sanar mai duk abinda ya faru. Ba Khaldun ka ɗai ba hatta Sa'adu ran shi yayi mugun ɓaci akan wannan abin. Sake kiran Khaldun yayi yace.

“Yayanmu gaskiya basu kyauta ba, nayi matuƙar takaici da jin wannan abin. But ba za'a tunkari Baba Hamza da wannan maganar ba domin nasan cewa shi ba da yawun shi suka aikata hakan ba. Zan samu Ayaa sai muyi magana....”

“To ka sameta ka faɗa mata ta ɗauki mataki akan hakan, kuma kada in sake ganin fuskar su a ko ina ma a cikin gidana.......”

“Yayanmu dan Allah ka yi haƙuri, kasan sha'anin mata sai haƙuri.....”

Ƙitt! Ya kashe wayar sa zuciyar sa na wani irin tuƙuƙi tamkar an ɗora ta akan tuƙubar tsirai.

Ɗakin ya sake komawa still kuka ta ke amma sautin ya rage ba kamar na ɗazu ba.

Zaunawa yayi akan gadon ya janyo ta jikin shi ya rungumeta. So yake ya rarrashe ta amma bai san ta in da zai fara ba.

Sun fi minti goma a haka jin tayi shiru sai ajiyar zuciya ta ke sauke wa yasa a hankali ya furta mata.

“Sorry! Meerah told me everything, I.... I apologized on be hv of them....”

Ɗago rinannun idanuwana nayi waɗan da suka yi ja tsabar kuka na kalle shi Ina ta ƙara ciccika saboda zuciya ta ta gama kaiwa ƙololuwa, murya a dusashe na ce.

“A..bin....daaa yafi ba.... Ni hau.. Uushii shine...wai kaik...kai sa'an babbbana ne....”

“Eh Kice kinji ɗin ni sa'an babanki ne is that Haram? Sannan ai sunji haushi ne saboda sa'an babanki ɗin bai auri ta su 'yar ba”

Girgiza kai na nayi alamar A'a. Sannan ya sake cewa.

“Ai na san duk abinda zasu ce it won't bother you because you love me, or don't you?”

Soke kaina nayi domin maganar ta zo min a lokacin da ban tsammace ta ba....

“Idan ma ke bakya so na ai ni nasan ina son ki, ina ƙaunar ki. So matuƙar dai ni ban sakaki kuka ba wanda ya isa ya sakaki kuka. Ki daina kuka bana son kuka”

Shiru nayi tare da ƙara lafewa a ƙirjinsa, ina jin wata irin sassanyar rahama na ratsa dukkan wani ɓargo na sassan jikina. Haƙiƙa wannan lokacin zai zama wani tarihi madawwami a cikin shafukan kundin rayuwa ta da bazan taɓa mantawa ba.

Ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba, Sai dai na farka da asuba na ganni ni kaɗai baya ɗakin.

Washe gari ina shirin zuwa Islamiyya sai ga Ayaa da kanta ta zo har gida ta same ni wanda wannan shi ne zuwan ta na uku idan zan iya tunawa. Haƙuri tayi ta bani akan abinda ya faru kuma ta roƙeni akan kada in faɗawa iyayena wannan maganar a raina na ce sai kace wata 'yar yarinya.

Bata jima ba ta tafi shi kuma ya zo muka wuce. Bayan na dawo ne ana gama sallar Magrib ya kaini gidan su Azima.

Tun daga ranar muka ɗan ƙara samun kusanci domin har abinci mukan zauna muci Breakfast da dinner sannan kowa ya je makwancinsa.

***********

Zuwa biyu nayi gidan su Azima kuma duk sai da dare yake kai ni.

Sai ranar suna ne na je ƙarfe huɗu na yamma.

Ina shiga muka haɗa ido da Maimu. Ni wallahi har ga Allah na manta ma da wata Maimu a duniya. Sai yau da muka haɗu.

Kallona take ta yi kamar yadda nima na kafe ta da ido.

Sai da naje kusa da ita sannan na ce.

“Hi”

Tsaki ta buga tare da faɗin.

“Aikin banza aikin wofi. In da dai bamu san asalin kolo ba sai yace daga Misra ya fito. Ni wallahi na fi ƙarfin yarinya don uban uwar ta. Ƙaryar arzikin da ba naka ba ko na ubanka ai aikin banza ne. Kowa ya sani da aikin baƙin asiri aka samu aka tura ki gidan Khaldun Zurmi....”

Dariya ce ta ƙwace min har sai da jerarrun haƙora na suka bayyana. Girgiza kai na kawai nayi na wuce domin ban san ma mi zan ce mata ba.

Hakan kuwa ba ƙaramin ƙara tunzura ta yayi ba, ta sa ke hawan bakin ta sai abinda ta mance ta yi ta zage zage tana faɗin ta san sirri na, wanda ni ko a sleepers ɗina ban kawo ta ba. Ina shiga ko minti ashirin ban cika ba na sallameta kawai na kira shi ya zo muka wuce.

Tana ganin na fita ta fashe da kukan baƙin ciki tana faɗawa en buki wai ita aminiyata ce ita ce silar aurena da Zurmi amma yanzu ita ce abar wulaƙanci a gare ni. Azima na can tana ji da mutane ita kuma tana nan ta zube hajarta sai kuka take tana basu labari su kuma sunata aikin bata haƙuri suna zagi na.

***********

Ina zaune bayan Magrib ina bitar harda ta katsam sai ga su Innani, har da Mama da Baba da Yah Naziru.

Abin yayi matuƙar ɗaure min kai, domin ba ƙaramin tsorata nayi ba.

Wai sun zo yi min ban kwana Khaldun yace duk sai sun zo har gida bai ɗauke wa kowa ba. Zamuje Aikin Umrah kuma a can zamuyi azumi ni da shi da Meerah.

Ban san lokacin da na fashe da kukan daɗi ba, itama Innani sai ta biyeni muka yi ta yi, Baba sai addu'a ya ke min. Haka ma Yah Naziru. Basu wani jima ba suka wuce.

Yana shigo gidan ban san lokacin da na je da gudu na rungumeshi ba ina faɗin.

“Thank you, thank you Yayanmu Allah ya saka da alheri na gode matuƙa”

Murmushi kawai yayi ya janye jikin shi ya wuce ɗaki.

Azumi ya rage saura kwana biyar muka yi wa Saudiyya tsinke. Ni da shi da Meerah.

        OUM AMEER