KULSOOM

TWENTY EIGHT

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

            P28

FREE BOOK

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

Marubuciyar:

ZAYTOONAH

ABARWA RAI

KIBIYAR SO

GUDUN WUCE SA'A

SABABI PAID

Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:

@Ummu-ameer

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

   Maimu

Tunda suka haɗu da Kulsum hankalinta ya ƙara matuƙar ɗaguwa domin ganin ta ba ƙaramin firgitata yayi ba. Ta wani canja gaba ɗaya, Daman ga yadda kalar fatar ta take to kuma sai gashi ta game da sanyin AC da hutu da jindaɗi ta koma wata balarabiya ta daban.

Wallahi da bata san cewa ita ɗin ƙawar Azima Shu'aibu ba ce da zata rantse da Allah ba Kulsum ba ce mai kama da ita ce.

Haka ta dinga kuka wiwiwi kamar anyi mata mutuwa. Wuraren ƙarfe goma na dare ko wane mahaluƙi da ya zo bukin yasan in da dare ya masa Maimu ce kawai bata tafi gida ba.

Daga ita sai sauran en uwa Azima na gidan suka rage.

Azima na cire kayan jikinta Maimu ta shigo ɗakin ta ce.

“Azima ta ya Kulsum ta san cewa kin haihu har ta zo suna? Wai kin san duk yadda muke da Kulsum da naje gidanta hanani shiga aka yi kuma ta aiko mai gadi cewa wai bata san wace ni ba tsabar wulakanci da samun wuri. Waye silar auren ta da Khaldun Zurmi idan ba ni ba? Amma yau ni ce Kulsum zata gani ta wuce ni tamkar taga kashi.....”

“Amma ko Maimu ke kika iya ƙarfin hali! With all the bad things that you have done to her Har kina da wani guts ɗin cewa Kulsum ta ƙi ta kulaki. Ke dan Allah baki ji kunya ba? Tsabar son zuciya da cin amana a lokacin bandits suka yi attacking na su kika cewa iyayen ta wai duk en gidan mu basa nan suna Zaria. Na rasa wannan ƙiyayyar wace iri ce, da kika ce saboda Ex ɗin ki kike ƙiyayya da ita gaskiya daga baya i doubt. Saboda abin is worse more than expectation. Amma na gaya miki ai tun a baya sharri ɗan aike ne to gashi nan ya fara dawo miki tun ba'a je ko ina ba, saboda ko yadda Sadeeq ke miki kaɗai ya isa ki gane kin koma baya ya ƙi auren ki ya je ya auri wacce ya ke so kullum yana miki ƙarya ke kuma kina yarda saboda baki da hankali. To Kulsum kam ta riga da tayi miki nisan da ba zaki taɓa iya kamo ta ba...”

Cike da jin zafin kalaman Azima tace.

“Wallahi ƙarya ne. Sai na nuna miki ni ke Saman Kulsum ba ita ke sama na ba. Kuma da kike zancen Sadeeq wai ya yaudare ni wannan kuma ƙarya ne domin....”

“Ni dai ina gargadin ki kashe wutar ƙiyayya da hassadar da kika kunnawa zuciyar ki akan Kulsum, domin kullum ƙara sama take ke kuma kina yin ƙasa. Hassadarki taki ce a gare ta.....”

Jakarta ta rataya ta wuce alamar bata ma son jin zancen Azima. Tun ba yau ba ta gane cewa yanzu Azima ta dawo goyon bayan Kulsum saboda ta ga tana auren mai kuɗi yanzu.

Itama Azima mamakin rayuwar Maimu ta ke, ta rasa wace irin zuciya ce Allah ya yi mata. Zuciyar ta bata da kyau ko kaɗan. Tana yi mata Addu'ar Allah ya shiryeta ya ganar da ita gaskiya.

**********

Har yanzu bata yarda cewa Sadeeq yaudarar ta ya ke, domin yadda ya ke mata daɗin baki da nuna mata shi kwata-kwata baya son auren Hafsa dole aka yi masa.

An yi buki wanda ya amsa sunan sa buki, babu abinda basu yi na event, yasha kyau shi da Amaryar sa har sun gaji. Ga iyayen sa ga iyayen ta anyi haraka ta manyan mutane.

Tana ɗaki tana kwance saman katifar ta tana kallon pictures da vedios ɗin bukin tana darza kuka. Ita kaɗai tasan yadda ta ke ji, ta tuna wai Sadeeq yana can yana tarayya da wata a matsayin matarsa sai taji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu saboda baƙin ciki.

Sai an gama event ya samu ya zo yayi ta yi mata rantsuwa wai dole aka mishi.

Kullum sai ya ce mata ta kwantar da hankalinta ita ka ɗai ya ke so musamman idan ya na so su haɗu ta sakar masa jiki.

Wutar ƙiyayyar gabar Kulsum da ta ƙara ruruwa a zuciyar ta yasa ta hasa wuta gidan su dole sai an raba gadon su an bata haƙƙinta. Kuka sosai mahaifiyarta keyi tana roƙon akan ta daina wannan maganar, domin shagun nan da babansu ya bari ne kaɗai hanyar cin abincin su, da kuɗin hayar ne suke samu suna gurgura rayuwarsu da ta ƙannenta ta yau da kullum ba su da komai su ne rufin asirinsu. Ga shi ba su da wasu maza manya a gidan duk ƙananune kwanyami ita ce babba a ciki.

Allah yasa iyayen nata duk da suna su huɗu suna da haɗin kai babu wadda ta ɗaga kai da sunan tana son Gado domin sun san ba wani abin ya bari ba. En sana'o'in hannun su suke suna rufawa kan su asiri.

Sai ita marar kunya zata zo tace wai tana son Gado.

A dangin babansu babu wanda bai yi mata magana ba amma ta dage ita lallai Gadon ta ta ke so, uwar ta tayi kuka kamar ba gobe.

Ƙarshe dole aka sayar da shagunan guda biyu aka sayar da gidan da suke ciki a ka game kuɗin wuri ɗaya aka yayyaga musu daidai da haƙƙin kowa.

Iyayen kowa ya kama gaban sa da yaran su. Mahaifiyarta kuma ta koma 'yan doto ita da sauran yaranta ta ce ta cire Maimu daga cikin yaran ta taje ta nemi wata uwar ba ita ba.

Abinda ta samu kwata kwata bai tasarwa dubu ɗari biyu ba. A unguwa duk wanda yaji abinda tayi sai ya tsine mata. Ta sha surutu har ta gode Allah.

Wata ta samu ta kai ta gidan wani malami tashin farko dubu ɗari da hamsin ya karɓa. Sauran kuma idan aiki yayi yadda ta ke so zata ci kasa. Ta zauna ta karanta masa matsalar ta ta farko akan Kulsum. Sannan matsala ta biyu kuma akan Sadeeq da matar sa Hafsa so ta ke duka a raba ma'auratan a sanya musu ƙiyayyar juna. Kulsum ta wulakanta a duniya shi kuma Sadeeq ya dawo a tafin hannunta Sai yadda tayi da shi.

Ya ɗauko magani ya bata yace duk yadda za'a yi tasan yadda zata samu ta shiga gidan Kulsum ɗin ta binne wannan layar kuma ba tare da kowa ya ganta ba. Bayan ta gama tayi ƙoƙari su haɗa ido da Kulsum ɗin sannan da zaran sun haɗa to ta bushe da mahaukaciyar dariya. Muddin tayi wannan to shi kenan an gama aiki. Idan kuma har ta bari wani ya ganta yayin binne layar da zaran sun haɗu ido da Kulsum to aikin kanta zai dawo.

Ita ma Hafsa ɗin tayi mata yadda zata yiwa Kulsum shikenan an gama da ita. Shi kuma Sadeeq garin magani ne ya bata yace ta wanke gabanta, da tafin ƙafafunta da hannuwan ta da hammatar ta ta zuba a garin maganin sai ta saka mishi a abinci ko abin sha ta bashi shike nan ta gama da shi, ko uwarsa ba zai saurara yadda zai riƙa saurarar ta ba.

Cikin farin ciki ta dawo gidan ƙawar ta ta. Sai kusan magariba ta fara tunanin ina zata je ta kwana don matar ta gaya mata mijin ta yana nan kuma ba zai bari ta kwanar musu a gida ba zai yi faɗa.

Sadeeq ta kira akan tana so ya kama mata haya kafin auren su don gidan su ya matse ta yanzu. Ce mata yayi ta bari sai da safe tace a'a ba zata iya bari ba domin yanzu haka ta baro gida.

Dole ya fito ya zo ya kama mata ɗaki hotel yace tayi squatting a nan kafin a samu gida.

To a nan fa ta fara rayuwa a hotel. ta mayar da hankali akan plan ɗin ya zatayi ta shiga gidan Kulsum daga baya bayan tayi bincike ta gane ashe bata ma ƙasar.

Shi kuma Sadeeq saboda Rhamadan ne yasa shi yankewa da Ita. Sai dai waya idan tana son kuɗi sai ya tura mata. Ko da zai zo bayan ansha ruwa ne kuma bai wuce minti goma ya wuce to tana tsoro kada ta haɗa mi shi abinsha yace mata cikin shi a cike yake. Ga magani amma ko ɗaya bata samu damar aiwatarwa domin ko gidan Sadeeq ɗin bata san yadda zatayi ta shiga ba domin akwai masu gadi, ga kuma yadda suka shirya da Sadeeq ɗin cewa ana gama azumi da sati biyu za'a ɗaura musu aure amma ya gindaya mata sharaɗoɗa daman tun can yace mata kada ta taɓa mafarkin zuwa gidan ko da wasa bai yarda ta taka masa gida ba. Ta bari idan sunyi aure sai a kawo ta, ɓangarenta na nan yana jiran ta ba kowa a ciki. To shi yasa bata san yadda zatayi ta shiga gidan ba kada ya ganta ya fasa auren nata.

Da tayi mishi maganar cewa hotel ya ishe ta ita tafi son gida, shine ya hauta da bala'i yana faɗin auren kwata kwata saura kwana nawa, shi bai damu da biya mata kuɗin daki ba duk kwanan duniya sai itace zata ce ta gaji.

Azumi na kwana ashirin ya kira ta da rana tsaka yace mata ta hau abin hawa tazo gidan shi yanzu. Hafsa bata nan sun tafi Mafara wurin gaisuwar rasuwar da aka yi musu sai gobe zata dawo. So yana so ta zo ta haɗa mi shi abin buɗa baki.

Cikin farin ciki babu ɓata lokaci ta shirya ta zo, Daman ta gaji da hotel ɗin nan don kawai bata da yadda zatayi ne.

Ko da ta zo gidan ma baya nan. Ganin ƙarfe huɗu tayi bai zo ba yasa ta tashi ta shiga Kitchen ta hau shirya abinci.

Tana gamawa gab da kiran magariba ta shige wanka kamar wata matar gida. Ji take kamar zata taka rawa saboda farin ciki.

Bai dawo gidan ba sai da aka yi Isha. Har ta gaji da jiran sa, taci abincin ta.

Tana kallon sa ta ɓata rai tace.

“Da kasan cewa wannan wulakancin ka shirya min ai da baka gayyatoni ba.in zo da azumi na a baki in sha wahala in shirya maka abinci amma ka ƙi zuwa ka ci”

Murmushi yayi yace.

“Sorry Baby,wallahi Ina office ƙarfe uku Hajiyata kirani wai tunda mata ta bata nan in zo gida in yi buɗa baki, kinga ba zan iya yi mata musu ba kuma bani da wata hujja tunda bata san ina wata matar ba....”

“To ni dai duk naji. Yanzu muje kaci abincin gashi can na shirya maka....”

With pleading tone yace.

“Eyyah! Sorry to say, Kema kinsan Idan na riga na ƙoshi ba zan iya cin wani abinci ba kuma...”

Kamar zatayi kuka tace.

“To wai tsakani da Allah Sadeeq don hajiya ta kira ka shine zaka buɗe cikin ka kaje ka kwashi abinci, to wannan da nayi ayi yaya da shi Ken.....”

Maganar maƙale mata tayi jin ana knocking ƙofar bedroom ɗin....

Bata gama tsurewa ba sai da taga an turo ƙofar kai tsaye matar ta shigo.

Yadda ƙirjinta ya ɗau lugude ji take tamkar zai tsage gida biyu tsabar tsoro.

Shi ma cikin tsananin shock ya tashi daga jikin Maimu ya miƙe tsaye da tsantsar mamaki a idanunsa.

“Hafsah...!”

Abinda ya iya furta wa kenan.

Ita kuma Hafsa kasa ma magana tayi kawai ta ringa kallon su ɗaya bayan ɗaya tana girgiza kai. Ta ke wani matsanancin kuka ya ƙwace mata. With so much pain in her voice ta fara magana.

“Sadeeq....! Abinda zaka saka min da shi kenan. Ina can Ina tausaya maka cewa na barka kai kaɗai har sai da na kasa jurewa na biyo Baban mu ya dawo dani saboda kai, ashe kana nan kana cin amana ta. Ba ka ji kunya ba baka ji tsoron Allah ba,a wannan wata na Rhamdan Sadeeq! Watan kusanci da Allah da neman yafiyar zunubai kai shi ka zaɓa ya zama abin saɓon Allah da cin amanar aure? Cikin gida na, cikin ɗaki na, Saman gadona na sunna Sadeeq zaka kawo min mace..”

Cike da nadama ya fara mata magiya.

“Dan Allah Hafsa, Dan darajar Iyayenmu kiyi haƙuri ki rufamin asiri...don soyayyar da ke tsakanin ku Hafsa....”

Cikin matsanancin kuka tace.

“Wace Soyayya Sadeeq? Ai ka riga kaci amanar so......”

Maimuna da ke ƙoƙarin barin ɗakin ta yi saurin cafkewa tare da gaura mata wani mummunan marin da ya hadda sa mata ganin wasu taurari tana huci tace.

“Wallahi sai kin yi nadamar zuwa gidana da kika yi, er iska, karuwa, fasiƙa, er wuta....”

Da sauri ya matso yana roƙon ta da.

“Dan Allah Hafsa kiyi haƙuri ki barta ta tafi na roƙeki...”

“Wallahi Sadeeq sai mahaifiyarka ta zo gidan nan kaji na rantse maka da Allah, Daman kasan ba son ka nike ba don anfi ƙarfi na ne yasa na aure ka. To sai Hajiya ta zo..... Mai gadi! Nura mai gadi..”

Murya ta ɗaga haiƙan tana kiran mai gadi akan ya saka wa ƙofar gida lock ta samu ta kira gida su zo.

Ganin cewa da gaske ta ke yasa Maimu ta shiga kokawa da ita domin ta samu ta ƙwace kafin Mai gadin yazo.

Shi kuma yana nan sai faman roƙar ta yake amma tayi kunnen uwar shegu da shi.

Cikin wani ƙarfin tsiya da bata san inda ta same shi ba tayi nasarar tunkuɗa Hafsah ta faɗa ƙum! Kanta ya bugi katakon gadon ta ƙeyar ta, cikin zafin nama ta sake yunƙurin miƙewa santsin tyles ya ɗibeta ta yi muguwar faɗuwa still ta bayan ƙeyar kanta. Faɗuwar bata sake motsi ko na second ɗaya ba.

Ganin jini yasa hankalin Sadeeq yayi matuƙar tashi da sauri yayi kanta yana kiran.

“Hafsah! Hafsah... Hafsaahhhh.....”

Wani mugun mari ya tashi ya kife Maimu da shi yana faɗin

“ wallahi duk wani abu ya samu Matata kin shiga uku kin lalace.....”

Mai gadi ne ya shigo afjajan jin yadda Hafsah ke ihun kiran sunan sa bai jira izini ba kawai ya shigo ɗakin.

Nuna Maimu Sadeeq ya shiga yi yana faɗin

“kada ka barta ta fita gidan nan... Je ka ka rufe ko ina kada ta fita, ta kashe min Matata, ita ta kashe ta,wallahi Ita ce ta kashe ta”

Tashin hankalinda Maimu take ciki baya ko misaltuwa, kuka ta ke sosai tamkar ranta zai bar jikinta. Ja baya ta fara yi tana girgiza kai kamar wata zararriya tana faɗin.

“A'a... A'a! Wallahi a'a kada ka min haka dan Allah Sadeeqqqq! Wallahi ni ban mata komai ba”

Jijjigata yake yana kiran sunan ta, yana roƙon ta akan ta tashi amma ba wani alamar numfashi tare da ita.

“Ka tashi mu kai ta asibiti don Allah...kada fa ta mutummm...”

Shaƙar da ya kaiwa wuyan ta ne yasa sauran maganar maƙalewa a cikin maƙonshi ta, cikin zafin rai ya shiga zagin ta.

“Ina zaman zamana da Matata lafiya, faɗa bai taɓa haɗamu ba ko na wuni ɗaya yau kin zo kin tarwatsa min farin ciki, ina sonta fiye da yadda nike son kaina ma...”

A gigice mai gadi yace.

“Mai gida a fara kai Hajiya Asibiti tukun a san a wanne take ciki”

“Kuma fa kayi gaskiya Nura. Amma dai kasan ba tare muka shigo gidan nan da wannan matar ba, ni ban ma san tana cikin gidan nan, kai ne shaida...”

Maimu tana kuka cike da mamaki tace.

“Yanzu Sadeeq abinda zaka ce kenan? Haka kayi min adalci kenan? Kai ne fa ka gayyatoni.....”

Wani marin ya sake ɗauke ta da shi yana faɗin.

“Ki roƙi Allah ba abinda ya samu Hafsah Maimuna ”

Daga haka ya cicciɓi Hafsah ya kai ta mota ya sanya lock a main entrance na gidan baki ɗaya ta yanda ba zata iya fita ba.

Da gudu ya ja mota zuwa asibiti, kafin kace mi duk en uwa sun cika asibiti ana ta kuka, Sai faɗin yake shi bai san ko wacece ita ba kawai ya dawo ya tarad suna ta kokawa da Hafsah.

Ya faɗa musu haka ne kawai don bashi da wata mafita, daga baya kuma idan Hafsah ɗin ta farfaɗo sai ya roƙeta da ta rufa masa asiri ta yi haƙuri ta yafe mai.

Bai san cewa ƙaddara ta riga fata ba domin Hafsah rai ya riga da yayi halin sa.

Likitan bai gama yi musu bayani ba Sadeeq ya yanke jiki ya faɗi akan tsananin shock. Hafsah ɗin ce ta mutu? Hafsah dai,. Matar sa?

************

“Watan Azumi, watan alfarma, ranar Juma'a cikin gidan ki, da cikin wata uku wannan tsinanniyar yarinya ta kashe ki Hafsah. Allah ya isar miki Hafsah. Shikenan Hafsah Allah yayi miki Rahma ya gafarta miki yasa kin tafi a sa'a. Kina tare damu kika ce lallai ke ba zaki kwana ba, mijin ki na can kin baro shi kaɗai, ashe ajalin ki ne ke kiran Ki, Allah ya yafe miki Hafsah, ni na yafe miki duniya da lahira, ke kowa ya yafe miki Hafsah kiyi kwancin ki da alheri........”

Mahaifiyar Hafsah ke wannan maganar kwana uku bayan har an gama binciken gawar an je an binne ta suna zaman makoki ne.

Kowa kuka ya ke babu wanda ke iya rarrashin wani,domin mutuwar Hafsah ba ƙaramin gigita su ta yi ba.

Shi ma Sadeeq duk ya birkice ya haukace kamar ba Sadeeq ba. Sai sabbatu ya ke yana faɗin matar shi bata mutu ba ƙarya likita ya ke.

Maimu na can rufe a cell babu wanda ya koma kanta, sauro da zafi da wahala duk sun sauya mata kamanni.

Sai da aka share sati ɗaya sannan suka waiwayo kanta. Ga Sadeeq ya kafe kai da fata ya ce shi ko mai kama da Maimu bai taɓa sani ba, ko da yazo gidan bai san tana ciki ba sai da ya shigo ya cimma ta tana kokawa da Hafsah.

Sai yanzu ta gane cewa Sadeeq ya riga ya gama da ita. Domin waɗan nan da take gani sune asalin iyayen sa waɗan can da ya turo gidan su ba iyayen sa ba ne hayo su yayi. Duk haukar da ta ke ashe babu wanda yasan da zaman ta Kab! Dangin sa.

An je an nemi dangin ta tun daga na uwa har na uba domin a samu wanda zai zo ya tsaya mata hatta mahaifiyarta ta ce babu ruwanta ko zuwa ba zatayi ba, a barta ta ci gaba da ji da en marayunta, aka yi a kayi kowa ya ce ba zai zo ba. Su kuma dangin Hafsah da shi kanshi Sadeeq ɗin sun ƙagu a yanke mata hukunci.

***********

Ko a can Saudiyya ɗaki ɗaya muka zauna dani da Meerah har muka gama ibadah. Yana nan dai hotel ɗin mu ɗaya ko ina zamu je muna tare da shi. Ina mamaki idan naga yana dariya da Meerah in suna fira.

Sai dai in yi murmushi ina ji a raina nima akwai irin wannan lokacin a tsakanin mu in dai na yi haƙuri.

Ban damu ba ibada ta na mayarwa hankali domin ita ta kaini, na yi ta roƙon Allah zaman lafiya da Zuriya ɗayyaba tare da mijina, uban 'ya' yana haske kuma madubin rayuwa ta. Na yi mishi addu'a Allah ya ci gaba da tsare shi a duk inda yake ya ƙarawa neman sa Albarka, na kuma roƙar mana Aljanna da ni da shi da iyayenmu da sauran musulmi baki ɗaya. Iyayena nayi musu addu'a suma yadda suka zaɓa min abokin rayuwa na gari suka yi sanadiyyar kasancewa ta a yadda nike yanzu Allah ya basu aljanna maɗaukakiya ya raba su da duniya lafiya.

Nayi kuka har na gode Allah akan irin wannan ni'ima da yayi zuwa gare ni, ba don nafi kowa ba sai dai ya ƙaddara min a cikin littafina cewa wannan yana daga cikin ayyukan rayuwa ta.

Wata ɗaya muka shafe, munje duk inda ya kamata muje na ibada sannan munje wani wuri kuma don ziyara da tarihi. Ni ce baƙuwar abin shiyasa nayi ta kwasar kaya kamar hauka, Meerah sai dariya ta ke min, wai idan na zama er gari sai anyi lokacin da ba abinda zance in siya, suma haka suka fara.

Sallah da sati ɗaya muka dawo ƙasar mu ta Nigeria, lokacin har Ramlah ta shigo sati na uku da haihuwa.

Har ƙofar gidan mu ya je ya ajiyeni da dukkan kaya na suka wuce gidan Ayaa shi da Meerah da Sa'adu.

Kowa kamar zai haɗiye ni tsabar yadda suke ta murnar ganina, ni kuma ba su san na fisu farin ciki ba domin ba ƙaramin kewar su nayi ba.

Innani harda kukan ta. Yah Naziru mun daɗe muna fira muna dariya kamar ba shi ne yake min mugun ta ba. Khadija ma ta kasa matsawa daga inda nike Mama kuma farin cikinta ya kasa ɓoyuwa.

Ina nan bayan na gama sallar la'asar sai ga mutanen unguwa tuɗuɗuɗu!, Sai shigowa suke, wai Innani ta je gida gida tana faɗin su zo ga kursume ta dawo daga Saudiyya kowa faɗawa ta ke watana ɗaya a can har da sati biyu.

Da en gulma da masu zuwa da zuciya ɗaya kowa sai shigowa ya ke har da Hajiyarsu Idirisa ta zo muka gaisa kamar wani abu bai faru ba.

Muna can ɗakin Innani Khadija kuma tana nan ta watse min jakunkuna na saboda rashin haƙuri, bayan ta ɗauki abinda ranta ke so sannan ta je ta kirani tana dariya.

Da wasa na Harare ta Ina faɗin.

“Kin aike ni ne da zaki taɓamin kayana?”

Dariya tayi tace.

“Anty Kulsum kada ki yi min gori, Mudassir ya ce in sha Allah dani za'a je aikin Hajjin bana, to ki bari idan lokaci yayi a rama taƙwarƙwara”

Cikin mamaki na ce.

“Waye kuma Mudassir Khadija,? Kada fa ki zama mai ruwan ido...”

“Kai Anty! Yanzu tsabar wulakanci wato baki ma san sunan tsohon saurayin ki ba, to Maina ni ke nufi”

Tsaki na ja tare da zaunawa na cire wa kowa tsabar kayan da nayo musu. Sannan na shiga ɗakin Mama daga ni sai ita mukayi ta fira har sai da Baba ya dawo sannan na je ɗakin sa.

Na zuba hijab kenan da nufin tayar da Sallar Isha sai ga ya Naziru ya shigo wai in fito ga Yayanmu ya zo.

Yana shigowa suka gaisa sama sama da su Innani muka fito wai jiran sa ake.

Sai da na shiga motar na Kalle sa na ce.

“Yayanmu ina wuni....”

Kafeni yayi da ido sannan yace.

“Ban san in da yabi ya wuce ba. Shi kenan kin manta da mijin ki ko?”

Dafe ƙirji nayi na ce.

“Wace ni! Kawai dai naga yau muka dawo”

Banza ya min kamar ba shi ne yayi maganar ba. Ganin haka nima sai nayi shiru kawai muka ci gaba da tafiya.

Wurin Ayaa ya kaini tana gani na ta rungume ni tana ta yi min barka da zuwa har sai da kunya ta hanani magana.

Kallona Ayusha tayi tana da dariya ta ce.

“Anty Kulsum barka da zuwa, Allah ya karɓi ibadah, shi ne kika tsere gida ba? To wannan abin cin da na kawo gaskiya sai kinci kema, ko yayanmu sai da na mishi ɗuren sa saura ke, don haka kar ma ki fara cemin wai kin ƙoshi”

Dariya duk muka saka na ce.

“Maman Muhammad zan ci ayi haƙuri. Ina Muhammad?”

“Yana wurin Meerah, ina ga Nasir ɗin bai tafi ba”

Bamu wani daɗe ba muka wuce koda muka je gida Jodan na can na jiran mu. Bayan ya mana sannu da zuwa mun gaisa ya hau yiwa Yayanmu tsiya ni dai shigewa ta nayi na bar su nan don a mugun gajiye nike, ina yin wanka ban jima ba bacci ya ɗauke ni.

Kwanan mu biyu da dawowa muna cin Breakfast ya ce min wai in duba littafaina in yi revision gobe Monday zan koma Islamiyya. Ajiye cup ɗin hannu na nayi tare da marairece fuska ina kallonsa nace.

“Yayanmu saura kwana biyar a fara bikin Meerah fa. Dan Allah ka bari a gama bikin please....”

“Ai kinyi hutu mai tsawo, ana can anata karatu bada ke ba, ki koma daga gobe zuwa Wednesday idan monday ta dawo sai ki koma”

“To shi kenan, Allah ya kaimu”

Daga haka ya tashi Ya wuce, ni kuma na hau aikace aikace na.

*********

Maimu.

Shari'ar ta ba tayi wahala ba domin bata da wata hujjar kare kanta, Sadeeq ya tsaya akan bakar shi cewa bai san taba, a gaban idon shi ta kashe Hafsah. Bisa ga bincike da zaman da aka yi ta yi a kotu an yankewa Maimu hukuncin Kisa ta hanyar rataya bi sa ga kashe Hafsah da taje har gidan aurenta ta iske ta ta kashe ta ba tare da wani dalili ba.

Muna wurin shirye shiryen walimar Meerah Khadija ta kira ni hankali tashe tana faɗamin mummunan labarin wai an yankewa Maimu hukuncin kisa. A gigice na ce.

“Na'am khadija! Mi kika ce? Banji da kyau ba...”

“Aunty ki nutsu fa, Aunty Maimuna an yanke mata hukuncin kisa, ta kashe matar saurayinta”

“Innalilahi wa inna ilaihi raji'un! Innalilahi wa inna ilaihi raji'un! La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzhalumin! Na shiga uku ni Kulsum...”

Jin na fashe da kuka yasa khadija ta kashe wayar ta. Nan ta ke kowa yayo kaina yana tambaya ta lafiya. Fadi nike ina kuka ba lafiya ba, Maimuna an yanke mata hukuncin kisa, wallahi ba lafiya.. Jiki na rawa na kamo Layin yayanmu, jin yadda ni ke ta kuka yasa shi kashe kiran kawai yayowa gidan tsinke. Koda ya zo ina ɗakin Ayaa dani da ita da Ayusha sai aikin rarrashi na suke.

Ina ganin shi ba kunya na je na faɗa jikin sa da gudu ina ƙara rushewa da wani sabon kukan ina magiya na ce.

“Dan Allah Yayanmu, da darajar Allah kayi haƙuri ka kaini naga Maimuna ko da ace shine ƙarshen alfarmar da zaka yi min ne a rayuwata..... dan Allah ina roƙonka”

“Miye ya samu ita Maimunar?”

Yanda khadija ta sanar min haka na sanar mai, ni ko kaɗan banji wannan labarin ba sai yau, ashe shi yaji tun muna Saudiyya.

Sai yanzu ma kowa ke cemin ai sunji tun cikin Ramadhan abin ya faru.

Ganin ya nufi hanyar waje yasa na saka hijab ɗin da niƙab da gudu na bi bayansa na faɗa Mota.

Ni dai naji yana magana a waya amma ban san mi yake cewa ba, domin hankalina gaba ɗaya baya wurin.

Ba mufi 30minute ba sai gamu a kotun, wanda har angama rubuce rubucen komai an je za'a sakata a mota, domin tace buƙatar ɗauka ka ƙara kawai ta amsa ta kuma amince da hukuncin kotu.

Liƙab ɗina na yaye da mugun gudu na nufe ta ina ta darza kukan fitar rai, ƙoƙarin hanani suke amma sai gunjin kuka nake ina roƙonsu akan dan Allah su bar ni in yi magana da ita.

Ganin yadda nike ta kuka itama sai ta fashe da kuka. Girgiza kai nayi nace.

“Ki daina kuka Maimu in sha Allah mijina zai fitar da ke, Dan Allah ki bari a ɗauka ka ƙara in sha Allah zaki fita....”

Murmushi ta dinga yi haɗe da kuka tana faɗin.

“Hakan kaɗai ya tabbatar min ke kaɗai ki ke ƙaunata a duniya sai Kamal har uwata ma ta guje ni. Na gode Kulsum, amma ƙarshe na ya riga da yazo, ina roƙon ki da ki yafemin duk abinda nayi miki wanda kika sani dama wanda baki sani ba, kuma dan Allah ki roƙar min afuwa a wurin mahaifiyata da ta yi haƙuri ta yafe min....”

Kallon ƙanenta Kamal tayi tana ɗaga mishi hannu wanda babu abinda yake in ba kuka ba tace.

“Na gode ƙanena Kamal da ƙaunar ka a gare ni, Allah ya sadamu a darussalam cikin aminci..”

Wani kukan kura nayi na zabura kamar mai wasu mahaukatan Aljanu na dumfari in da take zan kamo ta amma ina! Har ta shige mota. Ihu na dinga yi ina miƙa mata hannu ina faɗin.

"“Wayyo Maimu... Maimu dan Allah.... Dan Allah Maimu ki dawo, ki dawo dan Allah Yayanmu zai ɗauka ka ƙara.... A'a...”

Rungume ni Yayanmu yayi gam, yana bani haƙuri. komai rashin imaninka sai ka tausaya mini yadda na dinga ihu shima ƙanenta Kamal sai kuka yake yana ɗaga mata hannu.

Da ƙyar ya iya sakani a mota, gida ya wuce dani direct.

Zaunawa yayi ya rungume ni yana ta bani haƙuri. Domin yadda na haukace na gigice na fita hayyacina bama gaskiya ba ne.

Shi kan shi ya sha jinin jikinsa ganin yadda na dawo lokaci guda kamar ba ni ba.

           OUM AMEER