TWENTY NINE
💝 KULSUM 💝
P29
FREE BOOK
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
Marubuciyar:
ZAYTOONAH
ABARWA RAI
KIBIYAR SO
GUDUN WUCE SA'A
SABABI PAID
Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:
@Ummu-ameer
SOPHIE INCENSE
SOPHIE'S INCENSE
SOPHIE INCENSE
Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa
Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi
Muna da turaren wuta kamar haka
💞 Dorot
💞 kajiji
💞 Sandal banger
💞 Gab-gab
💞 Sandal flakes
Da dai sauran su..
Sai kuma Humrah munada:
💞 Sandal Humrah
💞 White Humrah
💞 Soul malting Humrah
💞 Oil Humrah Da dai sauransu
Akwai kuma
💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida
💞 Turaren mopping
💞 Air freshener
Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku
Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa
Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa
Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria
Delivery Nation Wide 🔮
Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye
Sai kunzo muna maraba da customers 💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕 muna matuƙar godiya
Ban ƙara firgicewa ba sai da akace an gama zartar da hukuncin Maimuna nayi kuka nayi alhini.
Duk na zabge na fige na fita a hayyacina da ko uwata ce ta mutu sai haka, Yayanmu yayi ta rarrashi na har ya gaji ya ƙyaleni da ya ga abin bamai ƙarewa ba ne sai da ya kai ni har gida wurin Mama tayi ta min faɗa sannan na sassautawa kai na.
Naji al'amarin Maimuna a raina ba kaɗan ba, kullum sai na yi mata addu'a Allah ya ji ƙanta ya gafarta mata.
Bukin Meerah duk yadda naci buri akan shi har aka yi aka gama gani nan dai tamkar mutum mutumi. Su ma kuma basu tsawwala min ba saboda ganin yadda na koma.
Ayaa itama ba'a barta a baya ba wurin ganin ta janyo ni a jiki sosai tana ƙara kwantar min da hankali tare da jan hankali na akan duk wanda ya rasa wani abu kuma ya ɗabbaɗa haƙuri, haƙuri mai kyau to Allah zai yi masa sakayya akan wannan hakurin.
Wannan abun da ya faru kuma sai ya ƙara mini matuƙar kusanci da Yayanmu domin ko bacci yanzu tare muke yi a ɗakin sa, Sai dai kowa da ɓangaren sa kamar an yi mana dole ko ince kamar wanda ya ke tsoro na.
Wanda ni a yanzu na riga da na gama yankewa cewa kawai ba shi da Lafiya ne.
Domin biri ya yi kama da mutum, ace namiji har namiji amma bai taɓa neman ko wace mace ba tun ƙurciya har yanzu da yakai matakin shekara kusan Hamsin sai dai aka masa auren dole. Haba! Abin akwai Mama ki.
Shi yasa yanzu na cire komai a raina kawai Ina addu'ar mafi alheri a cikin rayuwata.
Sai da na koma Islamiyya sannan na ƙara warwarewa na mayar da hankali ga karatuna da kuma kula da mijina.
Shirye shiryen auren Khadija kuma ya kankama wanda ya rage saura sati biyu cif!
**********
Khaldun
Tafiya suke a mota tare da jodan kan hanyar su ta dawowa daga ƙaura wurin ɗaurin auren wani abokin su da ya cika mata ta uku.
Duk labarin da Jodan ke basa gaba ɗaya hankalin sa baya wurin. Tunanin sa ya tafi wani wuri na daban. Duk yadda ya ke so ya yaƙi zuciyar sa akan Kulsum ya kasa. Shi yasan baya mata adalci domin tana da haƙƙi a kansa. Shi yanzu tausayi ma take bashi, yarinya ƙarama kamar ita tayi haƙuri duk tsawon lokacin nan bata taɓa complain ba ko ta kai ƙararsa, ga tsantsar biyayya, ga ilimin addini ya lura sosai bata wasa da ibada, sannan tana matuƙar son mahaifiyarsa da girmama ta. shi kuma a yanzu baya jin haushin ta ko wani abu yasan cewa yana sonta har cikin zuciyar shi yana matuƙar jinta a ransa. Amma rayuwar ta ta baya ta kasa goguwa a cikin kansa. A duk lokacin da ya tuna sai ya ji kwata kwata baya mararinta kuma, idan zai tuna sau dubu sai yaji kamar ya haɗiye zuciya ya mutu. A farkon auren na su yake ganin ba komai ba a kowane irin lokaci za su iya rabuwa, to amma yanzu da ta kasance wani ɓare daga cikin rayuwar sa sai ya ke jin ba zai iya yin nisa da ita ba balle rabuwa saboda haka yanzu dole ya samu mafitar yadda zai gyara al'amura tsakanin sa da ita........
“Zurmi magana fa na ke”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli jodan ya ce.
“Jodan please park the car”
Ba musu Jodan ya samu gefen hanya yayi parking yana kallon sa yace.
“I'm all ears”
A baibai Ya fara ma Jodan bayani da cewa.
“Jodan something is wrong. So I.... I need some one to shade some light about... About..”
With good attention Jodan ya kallesa ya ce.
“And what's that?”
Frankly yace.
“Something I can't tell Jodan. But sincerely Ina buƙatar Nasiha”
Murmushi Jodan yayi tare da girgiza kai ya ce.
“Zurmi, mun kwashe shekaru ashirin da wani abu muna tare, atleast ko ban sanka ba baki ɗaya ba nasan 50%. While ba komai”
Daga haka ya tayar da motar suka ci gaba da tafiya, ba wanda ya sake magana a cikin su, Sai dai kowa da abinda ya ke saƙawa a cikin ransa.
Shi a tunanin sa ya ɗauka zai iya discussing problem ɗin da Jodan walla Allah zai iya samun mafita, sai dai a yayin da suka yi ido huɗu da sunan maganar gaba ɗaya yaji ba zai iya fallasa sirrin sa ba duk yadda suke da Jodan ɗin kuwa, ya san waye Jodan, aboki ne na amana tun ana gwagwarmaya ake tare har aka zama wani abu, yana da assurance cewa ko wani ya kashe Jodan ba zai iya faɗawa kowa ba shi ma haka. Amma duk da haka he's not feeling safe akan wannan maganar.
Suna isowa Gusau Jodan ya ɗauke wata hanyar da shi.
“Where are we heading to?”
Bai ce masa uffan ba sai da ya kawo sa ƙofar wani gida. sauka yayi ya bar shi a motar ya sallama gidan sai wani mutumin ya fito. Bayan ya gama yi masa bayani sai ya shiga gidan ya ba su izini akan su shigo.
Motar ya koma ya tsaya ta waje ganin haka Khaldun ɗin sai ya sauke glass ɗin yace.
“What are we doing here Jodan?”
“Ba nasiha kake buƙata ba?......Sauka,sauka kaje wurin Malam ne na kawo ka, in sha Allah everything will fall apart”
Sauka yayi ba musu ya shiga gidan wani yaro yayi mishi iso har cikin Babban farlourn baƙin Malam. Shi kuma Jodan ya zauna a mota.
Bayan sun gaisa ya shiga zayyana masa duk irin da zaman da suka yi da Kulsum da kuma irin rayuwar ta da ya sani a baya, amma sai ya sakaya gaurayar da su kayi da ita bai faɗa mishi ba, wannan wani sirri ne wanda ya binne a zuciyar sa har ya kwanta damansa.
“Innalilahi wa inna ilaihi raji'un! Malam Abdul Rahim yanzu kana zargin matar ka ne?”
Da sauri ya girgiza kansa ya ce.
“Malam tun da na aure ta ban taɓa zargin ta ba, bata ma taɓa yin wani abu da zai sanya zargi a tsakanin mu ba. Kawai dai al'amarin rayuwar ta ta baya ne yake yi min ƙaiƙayi a cikin zuciya ta, bana samun nutsuwa da sukuni a duk lokacin da na tuna, hankali na ya kan tashi in ji bana ra'ayi da ita kuma bazan iya ma kusantar ta ba”
“Abdul Rahim da farko ina jan hankalinki da kaji tsoron Allah, haƙiƙa haƙoƙan aure da shi auren karan kansa ba abin wasa ba ne. Muddin matarka ta kiyaye maka kanta da dukiyarka kuma ka amince ka yarda da cewa ita matarka ce to bai kamata ka riƙa kallon ta ta wannan fuskar ba. Duk girman saɓon da Bawa ke yi Allah yace idan yayi tuba mai kyau zai yafe masa matuƙar bai kai gargara ba. Abdul Rahim tsakanin bawa da ubangijinsa kenan fa! Ballantana mu a tsakanin mu. Mutum nawa ne Allah ke jarabtar su da son karuwa kuma tana a gidan karuwan ma, idan Allah ya shiryar da ita sai kaga ta tuba sunyi aure kuma an zauna lafiya har an hayayyafa.
Kuma wani abu da baka sani ba Abdul Rahim shine; Kaga bin iyaye! Bin zaɓin iyaye matuƙar sun yi shi ne saboda Allah to akwai babban Alheri a ciki. Akwai sahabin manzon Allah tsira da aminci su ƙara tabbata a gare shi da wata mata tazo ta same shi tace wane na haɗaka da girman Allah ka aureni, shi kuma yace saboda girman Allah da tace sai yaji ba zai iya haƙura ba saboda haka yaje ya nemi aurenta. Sai bayan ta tare sai ya ga kamanninta da tsarin halittar ta kwata-kwata ba su dace da ra'ayinsa ba, ga shi kuma ya riga da ya aure ta, Sai yace ya riga yanzu ya aure ta saboda haka tana da haƙƙi akansa da kafin ya aure ta ne ya ganta da kyau da ba zai aure ta ba, amma yanzu dole ya sauke mata duk wani haƙƙinta da Allah ya ɗora masa. Ya ce idan zai fita haka zatayi ta kuka bata so ya fita shi kuma haka zai zauna tayi ta kallon sa tana farin ciki, wallahi yace bai taɓa tauye mata haƙƙi ko sau ɗaya ba kuma bai ƙara aure ba har sai da ta rasu, domin ya na jin tsoron ya ƙara aure ya zama yafi fifita wannan a kanta. Saboda haka shaiɗan ne ke yi maka waswasi ka tashi tsaye ka yaƙe sa da gaske domin ka zauna lafiya......”
Haka ya yi ta yi masa nasihohi da jan hankali tare da janyo masa ayoyi da hadisai masu umarni da hani akan abinda ya shafi rayuwar aure har sai da yaji ya gamsu da kuma ɗaukar alƙawarin gyarawa.
Bayan ya dawo mota shiru kawai yayi shi kuma Jodan sauka yayi ya shiga yayi wa malamin godiya sannan ya zo suka tafi.
A madadin ya sauka office sai ya cewa Jodan ya ajiye sa a gidan Hajiyar sa,ba musu ya kawo sa ya tafi.
************
Tun zai fita da safe ya ce kada in ajiye masa Lunch ba zai samu damar dawowa ba, na so in tambaye sa dalili amma ganin ban samu fuska ba kawai na ce mishi to domin ko Breakfast ɗin bai ci wani abin kirki ba. Shiyasa na yi aiki na da wuri na gama daman yau ba Islamiyya na zauna nayi ta kallo ina chart ta what'sapp. Ina kitchen wurin dafa indomie naji wayata ta hau ɓurari.
Ina zuwa naga Azima shu'aibu ce ta kira ni wadda a yanzu bani da wata ƙawa da ta wuce ta, duk wasu ƙawaye na manta da su na kama kai na.
Kiran ta nayi back ta ɗauka duk da mun kwana biyu bamu gaisa ba, ke koda Ruɗanin Maimu ya faru ba muyi magana ba.
“Kulsum”
“Azima kwana biyu, ina Imtihal? Ya gida”
“Lafiya lau Alhamdulillah! Imtihal tana bacci. Ya gida ya mai gida da fatan komai lafiya”
“Komai lafiya lau Azima, ya ƙarin haƙurin mu kuma?”
“Haƙuri Alhamdulillah! Maimu sai dai mu ce Allah ya sanyaya ya haskaka makwancinta, abubuwa sun zo ta yadda ba muyi tsammani ba, ina gida sai na ji mugun labari, wallahi ban iya zuwa ba, Sai dai naje na yi wa maman su gaisuwa daga baya”
Hawayen suka ziraro min na share ina girgiza kaina kamar tana gaba na nace.
“Hmmmm Sadeeq...! Sadeeq zai girbi abinda ya shuka da ikon Allah, yadda yayi mata sai Allah ya bi mata haƙƙinta. Duka su biyun ma har Hafsat ɗin sai Allah ya saka musu zaluncin da ya musu.....”
“Kulsum ai Allah ya nuna mu su aya daga shi har iyayen nasa. Yanzu haka yana asibitin kware Sokoto ya haukace tuburan ina gayamiki. Sun zauna nan asibiti ana tunanin zafin mutuwar matar sa ke taɓa shi yana saka shi sabbatu, ashe ba haka ba ne. Ihu ya ke da ƙarfin gaske idan ya kira sunan Hafsat ya kira sunan Maimuna yana faɗin ga su nan zasu kashe sa...”
“Allah ya kyauta yasa mu cika da kyau da imani, Allah ya gafarta musu ya sa aljanna firdausi ta zamo makoma a gare su damu baki ɗaya”
“Amin. Yawwa na ce wai Auren khadija yaushe ne ma?”
Wani ihun murna na buga ina faɗin.
“Zaki zo ne?”
“Ke dai ki faɗamin date”
“8days remain”
“OK, Daman muma auren Yah Halifahn mu ne next week shine nike tunanin ko date ɗaya, in sha Allah Friday zan shigo”
“Kai! Gaskiya naji daɗi, ubangiji Allah ya kawo ki lafiya”
“Amin. Bye”
Daga haka munka tsinke wayar. Ina nan ina ta shiriri ta ta sai da 6pm tayi sannan na tashi na je na yi masa tuwon semo miyan kuɓewa bushashshe ni kuma na haɗa dambun cous-cous ka ɗan.
Sai da na gama sallar isha sannan na je na jera masa warmers ɗin abincin a kan dining table sannan na wuce na yi wanka. Abaya baƙa na zuba domin na gane duk wasu sexy dress ɗin da zan saka aikin banza ne ba shi da wani amfani, shi yasa na raba kaina duk wasu kayan ma khadija ta kwashe.
Ina nan zaune har kusan 10pm bai dawo ba naje na nikam naci cous-cous ɗina na kwashe kayan na kai Kitchen na dawo na ci gaba da kallo
Ganin har na fara gyangyaɗi don har 11pm ta gota da mintuna yasa na tashi da nufin zuwa in kwanta amma a raina na damu sosai domin tunda na san lokacin dawowar sa bai taɓa wuce 9pm ba.
Har na miƙe tsaye da nufin tafiya Sai ga shi yayi sallama ya shigo.
“Sannu da zuwa Yayanmu. Duk na damu baka taɓa kaiwa haka ba”
Wucewa yayi ya zauna yana faɗin.
“Uzuri ne ya ɗan riƙe, Na gode”
Kallon sa nayi ta gefen ido domin naji yana yin maganar sa tamkar wani marar lafiya na ce.
“Abinci... Ga abincin ka a kan dining ko zan kai maka ne ɗaki?”
“A'a, Ki sanyo a filet ɗaya ki kawo min nan”
Sanyo masa nayi kamar yadda ya umurceni na kawo masa tare da sanya masa spoon.
Ɗayan cushion na samu na zauna, na mayar da hankali na a TV ina kallo.
Bai ci abincin da yawa ba ya umurceni da na kwashe kayan.
Kasa daurewa nayi cikin nuna damuwa na Kalle sa nace.
“Yayanmu ba kada lafiya ne?”
Kai tsaye yace.
“I'm fine”
“OK... Allah ya bamu alkairi, I'm going to the bed”
Har na kai ƙofar bakin ɗakina naji amon muryar sa da cewa.
“Ummu Kulsum”
Kusan dasƙarewa nayi a in da nike tsaye domin a bazata kalmomin sunana suka ziyarci masarrafar sauraro na. Sake maimaita sunan yayi may be a tunaninsa banji sa ba ne.
U-turn kawai nayi Ina mai ƙuresa da fitilun ganina domin na kasa motsawa ma.
“Kin dai na kwana a ɗakina kwana biyun nan ko me yasa?”
Da ƙyar na samu harshe na ya bani haɗin kai wurin tattaro kalmomi na ce.
“Baa... Ba komai...”
“Zo nan Ummu Kulsum”
Ba musu na je da nufin zaunawa a gefen sa sai ya janyo ni zuwa cinyarsa yayi min masauki. with feeling guilt in his voice ya ce.
“Ummu Kulsum wane ne ni a gare ki?”
“Kai Mijina ne wanda Aljanna ta take a tafin ƙafarsa. Kai farin ciki ne, haske a cikin rayuwata kuma garkuwa ta...”
“Kin yarda mu zamo abu ɗaya kenan? Kin amince wa wannan tsohon ya zamo abokin rayuwar ki na har abada?”
Shiru nayi, a raina na kasa tantance ma a wanne yanayi na ke....
“Ummu Kulsum....”
Hannuna na sanya a cikin nasa tare da jimƙewa sosai alamar eh.
Miƙewa yayi tare da kallon fuskata wadda ta mamaye da wani yalwataccen murmushi yace.
“Ɗaki na zamu kwana ko a naki?”
Nan ma shiru na nayi tare da sunkuyarda kaina a ƙasa.
Jan hannuna yayi zuwa ɗakin sa, ya ɗauko kayan da yake tunanin zai buƙata muka ranƙayo muka dawo ɗakina. A nan yayi wanka ya fito, a gabana ya shirya sannan ya zira jallabiya yace mu yi nafila.
Komai ganin sa na ke tamkar a mafarki. Sai da ya sake maimaita kansa sannan na je nayo alwala tare da yin brush na fito.
Raka'a biyu muka gabatar ta nafila sannan ya dafa kaina ya yi addu'ar da manzo Allah S.A.W ya koyar bisa sunna sannan ya tashi ya sake fita sai gashi ya dawo da system ni kuma ta shi nayi na gabatar da shaf'i da wutri sannan na cire rigar jikina na saka wata lallausar Sleeping dress na je gaban dressing mirror na bulbula kayan ƙamshi na sannan na ɗan Kalle sa ta wutsiyar ido, hankalinsa ma ba a kai na yake ba ya duƙufa sosai da alama akwai abinda yake mai muhimmanci.
Ina kwantawa ban fi 10minute ba sai gashi ya kashe System ɗin ya hawo gadon ya mirgino har inda nake ya janyo ni zuwa jikin sa.
Bai tsaya wata wata ba kai tsaye ya fara kai min farmaki a hankali... Wani irin ciri jikina ya ɗauka ko ina sai da ya amsa, kamar wata wadda aka jona a shocking haka nikeji.
Ganin yadda na rikice gaba ɗaya yasa a hankali ya furta min a kunne na.
“Ummu Kulsum kina jin tsoro ne in dai na?”
Hawayenda suka silalo min na sharce da faffaɗan ƙirjinsa da yayi min rumfa da shi na girgiza kai na kamar yana ganina murya cike da ƙwarin guiwa na ce.
“A'a Yayanmu, zan jure...”
Jin yadda ƙafafuna ke mazari akan tsoro ta ina kuka mai tsuma zuciya yayi matuƙar sanya mishi tausayi na, amma kuma a yadda jikin sa ya gama amsar dukkan saƙonni masu wuyar fassaruwa ba zai iya jurewa ba.
OUM AMEER