THIRTY
💝 KULSUM 💝
P30
FREE BOOK
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
Marubuciyar:
ZAYTOONAH
ABARWA RAI
KIBIYAR SO
GUDUN WUCE SA'A
SABABI PAID
Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:
@Ummu-ameer
SOPHIE INCENSE
SOPHIE'S INCENSE
SOPHIE INCENSE
Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa
Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi
Muna da turaren wuta kamar haka
💞 Dorot
💞 kajiji
💞 Sandal banger
💞 Gab-gab
💞 Sandal flakes
Da dai sauran su..
Sai kuma Humrah munada:
💞 Sandal Humrah
💞 White Humrah
💞 Soul malting Humrah
💞 Oil Humrah Da dai sauransu
Akwai kuma
💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida
💞 Turaren mopping
💞 Air freshener
Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku
Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa
Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa
Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria
Delivery Nation Wide 🔮
Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye
Sai kunzo muna maraba da customers 💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕 muna matuƙar godiya
.................
Ƙarfe takwas da kusan minti arba'in ya fito da shirinsa na zuwa office. Dinning area ya riskeni Ina shirya masa break fast kamar yadda na saba, duk da dai yau na makara sosai domin ko da 7am kayi na gama shirya masa, shima kuma 7am ɗin ya ke fitowa. Amma yau sai da muka sha bacci duk da dai ni ɗin ba wani baccin kirki nayi ba. Domin har yanzu murna da ɗoki sun kasa bari na baccin ya ɗaukeni. Ina cikin jikin sa kamar wata mage na lafe ina tunanin rayuwa yadda al'amura suka kasance har suka kawo mu nan. Sai da naji alarm ɗin sa ya buga sannan na zamo a hankali na fito na dawo ɗakina.
Ajiye briefcase ɗin sa yayi akan kujera ya nufo ni yana faɗin.
“Ummu Kulsum ya kamata ki huta....”
Murmushi nayi nace.
“Yayanmu ta ya zan barka ka fita baka karya ba”
“Lokacin da kika raboni da Hajiyata tana tsaka da kula dani, kika barni ba abincin kin taɓa tunin ya nike rayuwa?”
Cike da jin kunya na ce.
“Amma Yayanmu ai wan can time ɗin ba ka sa ke min fuska....”
“Kin taɓa ɗaukar abinci kika bani na ce miki ba zan ci ba?”
Hannayena na harɗe wuri ɗaya tare da marairece murya na langaɓar da kai ina faɗin.
“Na yarda na aikata kuskure a can baya ranka shi daɗe tuba na ke. Yanzu kuma idan har na barka da yunwa ko da ta second ɗaya ce ni kai na ba zan yafewa kai na ba”
Cike da gamsuwa da kalamaina ya ƙara so ya zauna ya ce.
“Godiya ni ke. Yi maza kiyi serving ɗina ana jirana”
Da sauri na zuzzuba masa, ni ma na zauna ina ci. Shap-shap ya ci ya miƙe ya kalle ni yace.
“Ummu Kulsum zan fita, ki kula da kanki kinji ko”
Nima miƙewar nayi ina faɗin. In sha Allah Yayanmu. Sannan na je for the first time na amshi Kayansa na rakasa har bakin mota. Nayi mamakin ganin drivern sa yana jiran sa. Amshe Kayansa yayi murya ƙasa ƙasa wanda ni kadai ni ke jin abinda yake faɗi yace.
“Ummu Kulsum ki koma gida, na gode”
“To Yayanmu, Allah ya tsare ka da tsarewarsa ya kai ka lafiya, ya kuma dawo min da kai lafiya”
Bai shiga motar ba sai da yaga na shige ciki sannan suka tafi, ni kuma ganin kamar baya son na gaisa da drivern naja baki na nayi shiru shima kuma bai gaida ni ba wanda ban san dalili ba.
Ɗakina na koma na cire rigar baccin da ke jikina na shiga wanka, Sai da na tsaya na ƙara gasa jikina da kyau domin ba ƙaramin zafi wurin ke min ba. Bayan na gama na shirya cikin wandon jeans black color mai ratsin stones Sai shining yake,rigar kuma Pink color tana da zane zanen baƙi a gaba da stones ciki, sai hula ta itama pink mai bakin lace.
Ban sha wata wahalar aiki ba, in da ya yi datti kawai na keɓe na gyara sannan na kunna turarukan Wuta na na Sophie incence waɗan da bani taɓa gajiya da ƙamshin su tare da Air freshnar, saboda yana yin jikina sai a hankali. Amma kuma wannan daren da yinin yau suna cikin wasu ranaku na tarihi na da bazan taɓa mantawa da su ba.
Goma da minti hamsin naje ɗaki nayi alwala na gabatar da sallar Duha sannan na shiga Kitchen na ɗora mana white rice and stew with chicken. Sai sauri nike dokawa domin naga Khadija ta ajiyemin saƙo a gidan what'sapp wai tayi ta kirana ban ɗaga ba zasu shigo ita da ƙawayenta. Abincin na kan wuta ina tsaka da yanka Salad naji yo sallamar Yayanmu. Cike da mamaki na fito ina ƙarewa Wall clock ɗin parlourn kallo naga 12:17pm.
“Yayanmu Sannu da zuwa. Allah yasa lafiya?”
Murmushi yayi yace.
“Lafiya lau Ummu Kulsum, ina buƙatar na huta ne”
Ba tare da na kawo komai a raina ba nace ok! Tare da yin sauri na amshi kayan hannun sa na kai masa ɗaki. Zan fito ya riƙe min hannu cike da shauƙi ya ce.
“Ina zaki je kuma?”
Rausayar da kaina nayi gefe nace.
“Na bar abinci akan wuta ne Yayanmu”
Sakin hannuna yayi yace.
“OK! Ki je ki ƙara sa ina jiran ki”
Da sauri na je na ƙarasa komai na kwashe mana a warmers na kai kan dining table sannan na zo na wanke Salad ɗina da kyau na zuba mishi ruwan sanyi na tsanesa a kwando. Sannan na koma ɗaki na ƙara kallon kaina a mudubi, na ƙara sanya shu'umar Humra ta ƙwararriya kuma gwana gidan ƙamshi wato Sophie incence.
Ina shiga parlour naga ban gansa ba na wuce bedroom. Kwance na tarar da shi kawai, bayan ya rage kayan jikinsa ya ɗaura kansa akan pillow yana nazari.
“Zo.....Zo nan Ummu Kulsum”
Nufarsa nayi kamar wata shashasha ya ja ni na faɗa jikinsa tare da faɗin.
“Zo.... Zo muyi fira. Do you know what?”
Girgiza kaina nayi alamar a'a, sannan yace.
“Na ɗaukar miki hutu ne kawai domin mu samu kusanci da juna sosai, mu ƙara sani da fahimtar Juna. Na barwa Jodan da Sa'ad komai, saboda haka fara bani labari ina jinki... ”
“Yayanmu Khadija ta faɗamin cewa za su zo....”
“An shi waya yi maza kira ta kice mata fitar uzuri ta kama ki, bakya nan...”
“To yayanmu da wayar ka kuma..”
“To ai tare kika fita da mijin ki... Yi maza kada fa su zo, idan suka zo zan fita in faɗa musu da kaina cewa bakya nan”
Ba musu na amshi wayar na saka numbern khadija sai gata ta fito ɓaro-ɓaro. Tana ɗagawa ba ɓata lokaci na faɗa mata cikin hikima cewa wata fitar gaggawa ce ta kama mu. Ina jinta tana faɗin kai anty gashi har mun shigo napep fa. Dariya nayi nace to ki ce ya mayar da ku. Daga haka na kashe wayar.
Shiru nayi ina wasa da yatsun hannuna akan screen ɗin wayar sa shi kuma sai aikin kallona ya ke.
“You look beautiful”
Ni dai da Uhm! Kawai na amsa domin ina jina cikin wata duniya ce ta baƙunta.
Hannunsa ya saka ya tallafo fuskata muna kallon juna yace.
“I love this...,”
Ƙara kusanto ni yayi ya shiga bani wasu hot kisses tun daga wuya na har zuwa kan laɓɓana.
Take jikina ya fara kyarma saboda saƙon sai na ke jinsa ya fi ma na jiya shiga jiki. Lokaci ɗaya shima idanuwansa suka ri ne zuwa wata kala mai cike da buƙatuwa da kuma bege.
Yanzu banyi ƙoƙarin hana sa ba, duk da wurin na yimin zafi haka na ɗaure muka sha soyayya mai cike da so da ƙauna tsantsa.
Ko da muka shirya Ƙarfe biyu saura cikin azama ya fita masallaci nima nayi sallah. Bayan ya dawo muka ci abinci sannan muka dawo palour na muka tusa sabuwar fira kamar yau ne muka fara ganin juna. Mafi yawan firar shine yake bani ni kuma sai dai kawai in yi murmushi.
“Murmushi kawai kike Ummu Kulsum. Ki bani labari ina ji”
Kawai wata kalar tambaya ta faɗomin a rai kai tsaye ba tare da wani tunani ba na ce.
“Yayanmu miyasa ka daɗe bakayi aure ba? Kuma sai cewa ake baka soyayya da gaske ne?”
Murmushi yayi yace.
“Duk kin damu ko, ace kamar ki ta auri iri na tsoho kuma a matsayin matar farko....”
“A'a wallahi ko ɗaya. Kawai dai ina mamaki ne”
“To matso nan.... Matso da kyau in baki labarin 'yan mata na”
Ƙara kanainayeni yayi a jikin sa tamkar zan tsere masa ya fara bani labarin da ko a mafarki ba aka faɗamin ba zan karyata ba zan taɓa yarda ba.
“Ummu Kulsum nayi soyayya da kusan mata guda uku, ƙaddara ce duk ta rabani da su wanda labarin ma bana fata ki jisa bashi da daɗin saurare. Tun daga nan na yanke na daina so, duk yadda Iyayena suka so in yi aure na kasa. Amma kuma da na basu zaɓi yanzu Alhamdulillah.....”
Kiran Meerah ne da ya shigo wayata ya katse masa zancen da yake.
Na ɗauka da niyyar in yi picking yayi saurin karɓe wayar tare da kashe ta baki ɗaya.
Cike da mamaki nace.
“Yayanmu kashewa kayi fa?”
“Eh. Ai na faɗa miki yau daga ni sai ke...”
“But Yayanmu ta fa dage Ita lallai tunda banyi participating yadda ya kamata a bikin ta ba dole sai na je wurin rakiyarta Lagos”
“To ke naki mijin fa”
Uhm! Kawai nace domin ban san miye a zuciyar sa ba.
“Yaushe ne tafiyar ta su?”
“Ana gama bukin Khadija da kwana biyu”
“ok. Ta shi muje muyi Asr, ki zo ki bani labarin ki”
Dariya nayi na ce to shikenan yayanmu.
Bayan na mun kambala muka sake zaunawa muka buɗe sabuwar Chapter.
Wannan yinin gaba ɗaya haka muka yi shi har muka shiga bacci cikin farin ciki da annushuwa kamar ba mu ba.
*************
Bukin Khadija ma tunda muka fara shi kullum shi ke kaini ya dawo dani ya daina fita ko ina yace mini ya ɗauki hutu na ɗauka da wasa yake. Idan zan fita zai ajiye ni da kansa ya dawo gida idan kuma muka gama shi dawowa dani, kuma duk yadda buki yakai baya barina na saka gyale sai dai wataran a rangwancemin saka niƙab idan cikin gida ne, ni kuma farin ciki mijina shine nawa ban taɓa jin hijab ɗin ya dame ni ba comportable ni ke ji na.
Da muka haɗu da Meerah ta yi ta mita kamar zatayi kuka wai ita bata yarda cewa rashin caji ba ne da gangan na kashe wayar. Ni kuma sai na bita a haka nayi ta bata haƙuri duk da bani da assurance akan zai barni na tabbatar cewa tare zamu tafi.
Buki yayi buki munsha shagali ranar Asabar aka ɗaura auren Khadija Salman da Mudassir.
Nasha mamakin irin kayan da aka danƙarawa Khadija na ɗaki, domin na san ƙarfin Iyayena. Part biyu ne ta ke dashi ko wane 2 bedroom and parlour with kitchen each. But Ko Ina an saka mata kaya na gani na faɗa.
Sai bayan bukin Innani ke faɗamin wai Yayanmu ne ya sayi kayan ɗakin Khadija, nan nike faɗa mata nima 500k ɗin da nabawa su Baba shi ne ya bani.
Sannan Ayaa ma ta kawo musu 200k,duk don a haɗa a rufawa juna asiri domin shima gidan su Maina ba laifi suna da kuɗi.
Komai ko an yi shi yadda ya kamata Alhamdulillah!
**********
Kwana biyu da kai khadija ina zaune ina azkhar bayan na kambala sallar Subhi sai gashi ya dawo daga masallaci ya shigo ɗakina ya kashe fitila ya haye gadona ya kwanta.
Abinda na fahimta game da Yayanmu shine ya na son Kasancewa dani da bayan sallar asuba. Shiyasa idan na tashi sai na fara yin wanka na shirya masa sannan nayi sallah, idan har yana da buƙata shikenan zan je garesa babu wata fargaba idan ma babu shikenan an Huta.
Ina ganin ya zo ya kwanta na iyarda kambalawa sannan na tashi na cire jalabiya zuwa under skirt kawai na je na kwanta a gefen sa, a hankali na furta gefen kunnen sa.
“Yayanmu good morning....”
Mirginoni yayi na dawo samansa yace.
“Yaushe ne tafiyar ku?”
“Yayanmu ai baka ce komai ba”
“Ki fara bani amsa tukuna”
“Gobe ne zasu tafi”
“To muma gobe zamu tafi, idan kika rakata sai mu wuce in da zamu tafi....”
Cike da zumuɗi na ce.
“Dan Allah Yayanmu da gaske? Ina zamu je?”
“Wurin Soyayya zamu je. Nan duk yadda na ce zan hutu, Sai Sa'adu ya zo har gida yana damu na. Ki shirya anjima zamuje wurin Hajiya da su Innani da wurin Ayusha..”
“Dan Allah da gidan su Azima Yayanmu, don ko da zata tafi bana nan”
“while If time parmit zamu je. A cikin rayuwar ki akwai ƙasa ta da kike so kike burin wata rana ace kin tafi can?”
Rausayarda kai na nayi tare da walwala idanuwana nace.
“Um! To Ina son in je Dubai.. Inje London,. Inje India, in je China, Saudiyya Allah ya nufe ni da zuwa sai dai aikin Hajji idan ya bani ikon zuwa”
“Why did you choose those countries?”
“Saboda 'yan Dubai Larabawa ne kalar su daban, En India daban, China daban...”
“You are not serious..”
“Allah Yayanmu da gaske ni ke”
“Okkkk!”
Daga haka ya Mirginoni ƙasa babu ɓata lokaci muka Lula wata duniyar.
*************
Tunda muka je gidansu Meerah da daren da muka isa Lagos bata sake ganin mu ba, mun kwashe two weeks sannan muka bar ƙasar, ashe Yayanmu da gaske yake.
Duk in da na ce masa sai da muka je har in da ma bance ba, nayi yawo na kashe ƙwarƙwatar ido.
Munsha Soyayya kamar mu cinye Junanmu. Dubai ita ce ƙarshen Ƙasar da muka je a can muka yi Sallah Babba mukayi zaman mu. Sai da muka share wata uku cif a nan sannan muka koma gida Nigeria.
Duk wanda zai ƙyalla ido ya ganni tabbas sai ya sake kallo na domin na canja sosai hutu ya zauna a jikina ba ni da wata damuwa yanzu.
Innani na ganina ta dinga kabbara saboda cikin da ta gani a gare ni har ya fito. Ina ganin ta da haƙoran maka na sake baki ina Kallonta wai Yayanmu ne ya biya mata ita da Mama da Baban mu. Yace musu kada su sanar dani wai, ni kuma ban gane ba duk zamuyi magana da su sai dai ya bani su a wayar sa mu yi magana.
Khadija ma kamar yadda Maina ya alƙawanlata mata tare suka tafi.
Kukan farin ciki na dasa Innani sai tayani ta ke tana ta saka wa Abdul Rahim albarka shi da iyayen sa da yi musu addu'a.
Ayaa ita ma tayi matuƙar farinciki musamman da taga ciki a jikina. Ni kuma kunya ce ta ke kamani idan suna zancen. Yayanmu ya ƙwalla fa rai sosai a cikin nan sai Addu'a yake Allah ya bashi 'yan biyu, domin shi da bibbiyu zai fara, ni kuma sai in yi ta dariya ina faɗin ba ruwan Allah duk wanda yaga dama ya baka sai kayi godiya ka roƙeshi ya sanya albarka.
***********
Ina kitchen ina ɗauraye kayan da muka gama cin abinci ya shigo har Kitchen ɗin ya same ni.
“Ummu Kulsum Matar Jodan ta haihu, yanzu ya kira ni yana sanar min ta haifi twins....”
Hannunshi na riƙe tare da sassauta murya na ce.
“Yayanmu please! Kada ka wuce iyaka fa, komai Allah ya riga ya gama tsara shi, duk abinda zai baka ka zama mai godiya, ƙaddarar Jodan daban ta ka daban. Allah ya bamu rayayye mai albarka. Ni wata alfarma ni ke nema a gareka don Allah”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.
“Allah yayi miki albarka Ummu Kulsum. Ina sauraren ki mene ne?”
“Amin Yayanmu. Dan Allah ina neman yardar ka da amincewar ka ina so in je garin su Maman Maimuna dan Allah”
Cike da mama ki yace.
“Maimuna kuma Ummu Kulsum?”
Hawayen da suka silalo min na share tare da gyaɗa masa kai nace.
“Eh”
“Naji. In sha Allah zan kaiki amma ba yanzu ba, ki gama duk abin da kike bayan magariba sai muje gidan Jodan ɗin”
“To! na gode sosai Allah ubangiji ya bamu aron rai da lafiya amin”
“Kawo min wani abu mai sanyi, ina jiran ki a ɗakina”
Girgiza kai nayi ina murmushi na ce.
“Hmmm! Yayan mu dai. Wanke wanken zan ajiye kenan”
“Eh. Ai nace a kawo mai aiki kince a'a.....”
“Gani nan yanzu faka faka in sha Allah”
*************
Cikina na da cikin watan haihuwa mukayi bikin Yah Naziru da Asma'u. Wata ƙawar Khadija ce tare suka yi candy da ita.
Duk wata shawara yanzu Yah Naziru ya sanya ni a gaba komai sai ya faɗamin yake yi mun samu haɗin kai sosai ba kamar da ba.
Ko shi ya ƙara zama Babban mutum yanzu da NGOs yake aiki a Shinkafi. Yana samun kuɗi Alhamdulillah, duk wasu sana'o'in yanzu Mama ta rage su sosai, duk shi ya Naziru ya so ta daina sana'ar baki ɗaya ita kuma tace ba wanda ya isa ya hana ta.
Tun kafin Bikin Innani ta so na dawo gida Yayanmu ya ce a'a. Bayan biki ma ta matsa akan in dawo gida, ƙarshe free ya fito da kanshi ya faɗawa Ayaa cewa ta sanar gidan mu shifa ba zan koma gida ba tunda ba ibada bace Al'ada ce.
Innani bata fi kwana biyu da zuwa gidan mu, naƙuda ta taso min rigi rigi, Sai da Yayanmu ya je ya taso ta sannan ya fito duk jimawar da mukayi a parlour.
Muna zuwa asibiti suka ce Haihuwa ce amma akwai sauran lokaci. Tun cikin dare ni ke abu ɗaya har ƙarfe biyu na rana. Ƙarshe likita yace ba zan iya haihuwa da kai na ba,sai dai a mini Cs. Ƙarfe biyar na yammacin ranar Juma'a aka shiga da ni Theater bayan an gama shirya komai.
Yayanmu kamar zai haukace tsabar ruɗewa da shiga tashin hankali, Ayaa sai faɗa masa take cewa yayi ta addu'a in sha Allah lafiya lau za'a fito daga ni har abinda yake ciki na.
Ban farkawar da na ji dama dama ba sai da aka wayi gari.
Yayanmu na gani riƙe da baby a hannun sa,Sai Innani, Khadija, Ramlah, Ayusha, da Asma'u.
Muryar Innani na tsinta tana faɗin
“Ayyo! Kulsum kin farka, sannu er nan. Ubangiji Allah ya baki lafiya ya raya miki jaririnki”
Duk suka amsa da amin.
Ruwan lipton khadija ta kawo min kowa sai sannu ya ke min.
Murmushi Ayusha tayi tace.
“Anty Kulsum Meerah ta addabe ni tun jiya take faɗa dani sai na baki waya tunda wayarki na hannun yayanmu”
Murmushi kawai na sakar mata a hankali na ce.
“Ƙyale Meerah maman Muhammad zan kira ta. Ina muhammad?”
“Yana wurin Ayaa na baro shi Yah Sa'adu nace ya wuce da shi, yanzu zai zo ya dame mutane a nan”
Bayan duk mun gaisa suka fita suka bar ni daga ni sai Yayanmu.
Matsowa yayi in da nake ya sanya Hannunshi cikin nawa yace.
“Thank you dear wife. Thank you so much. Thank you for everything. Allah ya yi miki albarka ya baki lafiya ya raya mana Umar Farouk Abdul Rahim”
Wani murmushi nayi masa mai sanyi tare da lumshe idanuwana na ce.
“Amin Yah Allah”
“I love you so much”
Murmushi kawai nayi masa tare da lumshe idanuwana,har zuciya ta naji daɗin yadda ya nuna min matuƙar kulawa kamar zai haɗiye ni da Ɗanmu da ke hannun sa.
Da dare Su mama suka zo har da Baba suka duba ni.
En uwana da en uwansa suka yi ta tururuwar zuwa gani na tamkar biki.
Sai da nayi kwana biyar sannan aka bani sallama.
************
Anyi bukin sunan da ya amsa sunan sa, domin duk garin gusau sai da ya amsa. Meerah akan ƙulafuci sai da tazo ashe itama ciki na nan har yayi soro time kawai ake jira.
Sai da muka cika kwana sittin cif sannan Innani ta koma gida.
Muka buɗa wani sabon shafin soyayya ni da yayanmu. Wata iriyar ƙauna na ke masa wadda ban san ma ya zan kwatanta ta ba. Sai dai Ince Allah ubangiji ya saka masa da gidan Aljanna ya sa har a aljanna mu kasance a tare da juna.
Sai da nayi six month cur! Da haihuwa sannan ya tado min da zancen zuwa gidan su Maimuna.
Tare muka je da shi, ɗan jarida ne ya kai mu har can. Munsha kuka daga ni har mahaifiyarta, daga ƙarshe na yi mata gaisuwa sannan na faɗa mata saƙon Maimuna duk da na san Kamal ya sanar mata akan ta yafe mata. Tana kuka tace ai ta daɗe da yafe mata, tana yi mata addu'a Allah ya kwantashsheta lafiya.
Rayuwar duk ta sauya musu saboda ba su saba da rayuwar ƙauye ba. Ƙanwar ta Surayya da iyakacinta shekara goma na roƙi mamar arxiki akan ta bani ita zan riƙeta.
Shima Kamal Yana kuka ya roƙeni akan dan Allah shima in tafi da shi ko wanki da guga ya riƙa yi mana. Ban da ya furta wa dole sai da na fita naje wurin Yayanmu ban ɓoye masa komai ba, yace miyasa to suka baro gusau suka dawo nan, na ce kawai yanayin rayuwa ne, an raba musu gadon su ne an sayar da gidan na su.
Cikin tausaya wa yace Allah ya sawaƙa ya amince da zuwa da su ɗin.
Abubuwan da na zo mata da sune nasa aka sauke musu sai kuka suke.
Ƙarfe biyu na rana muka baro ƙauyen tare da Kamal da Surayya.
Gida na fara biyawa na kaiwa Mama su tare da yi mata bayani sannan nace tayi mana addu'ar zaman lafiya da su har Allah ya raba mu. Cikin farinciki tayi ta yi mana addu'a tana saka mana albarka.
Ƙarfe biyar muka wuce gidan Ayaa, wannan Yayanmu ne yayi mata bayani da kansa. Bayan ya gama cikin tausaya wa tace ya saya musu gida su dawo nan garin sannan idan akwai wata er matashiya cikin yaran akawo mata. Kuka nayi ta yi ina yiwa Ayaa da yayanmu godiya domin Maimuna wata mutum ce ta daban a rayuwata ina matuƙar ƙaunar ta duk yadda muke da rashin jituwa, wallahi a duk lokacin da zan tuna sai nayi ta kuka ina jin kamar zan mutu akan abinda ya faru da ita.
Nan da nan Yayanmu yasa aka samo musu gida mai ɗaki kusan shida jere da Kitchen da toilet sai filin tsakar. Yace har waɗan can sauran kishiyoyinta idan suna da raayi suma za su iya dawowa ya, Sai gashi nan da nan kowa ya dawo sun cika kamar yadda suke da, daman kowa ta kansa yake idan an mutu an bar maka yara zamannin kai aka barwa.
100k ya bawa kowaccen su yace taja jari suci gaba da kula da yaran su.
Sai da Farouk ya kai shekara ɗaya sannan na koma islamiyya,yayanmu yaso nema min admission na ce masa a'a bana buƙatar boko kuma haka ma ya ishe ni.
Samun Surayya ya yi matuƙar taimaka mini, duk da tana zuwa makaranta. Kamal Kuma shima yana zuwa makaranta amma daga zaran ya dawo ya ke wucewa kasuwa.
Tunda na ce masa ba zan yi karatu ba, ya aika aka saro min kayan laces, atamfa, kayan yara, hand bags da sauran su ina sayarwa a cikin gida, kuma alhmdllh kasuwa tana ja ba laifi. Ni da Yayanmu sai sambarka...........
ALHAMDULILLAH! ❤️ 😘 😍 ❤️ 😘
NAN NA KAWO ƘARSHEN BOOK ƊIN KULSUM, ABIN DA KE CIKI ALLAH YASA AMFANAR DA MUTANE DARASIN DA KE CIKI NA CIWON HASSADA DA BIN ƘAWAYEN DA BA SU DA CE, DA NEMAN ABINDA YA FI ƘARFIN KA. KUSKUREN DA KE CIKI ALLAH YA YAFE MIN AMIN. INA ƘAUNAR KU MASOYA KULSUM. NA GODE SOSAI 🙏😄 😄 😄 LOVE 😍 YOU ALL❤️❤️
MY BOOKS
ZAYTOONAH
ABARWA RAI
GUDUN WUCE SA'A
KIBIYAR SO
KULSUM
BAHIYYA
NUUDARR
KURURUWA A KUNNEN KURMA