KAWAICI

Episode 2

by @zahraroyal

KAWAICI

©Zahra Royal Star

PAGE 2

Unguwar Dokoki Ramiye, Kankia LGA, Katsina state Nigeria

A hankali ta gyara kan matar dake zaune ƙasa tana mata ƙitso kanta na akan cinyarta, tana yi duban tsakar gidan nasu babu kowa sai ita zaune tana ma wata makwafciyarsu kitso, sauri take ta gama dan tana son tattare gidan yadda duk yayi ƙura kamar wadda aka shekara ba'a share ba.

Makwabciyar ce tayi gyaran murya tana faɗin.

"Ni ko Falmata wannan tsakar gida naku a rasa wadda zai gyara shi sai ke kullum kike ƙoƙarin sharewa?, ai ya kamata yadda gidan nan yake shaƙe da ƴan mata ana zuwa ana iskesa a gyare, gashi duk an kashe gidan da lallai da ake yi"

Falmata ta ɗan kalli tsakiyar kan matar taɗan tsaya da kitson tana sakin tsaki ciki-ciki ta ce.

"Baiwar Allah kitso kika zo yi ko kuwa namen jin gulmar gidanmu?".

"Ah ah daga magana gaskiya fa ce nake faɗa?, ni ai tausayinki nake ji, ace kullum kice ƴar gyara waje ana ɓatawa".

"Ki riƙe gaskiyarki Malama kinji".

"Allah ya baki hakuri".

Tsaki ta kuma, tana ja mata kai danta fara bata haushi, a rayuwarta bata son zaman gulma da mata keyi, amma mudun za'a zo kitso ko ƙunshi a gidan sai an zauna ana ƙananun surutai da gulmace-gulmace, ita kam bata yarda da wannan ba, amma Ma'u ita da ita da ake zama ana buɗe shafin gulmar mutum idan aka zo mata ƙunshi, daga kiji ana zagin waccar sai kiji ana gulmar wannan.

Kamar an korota haka ta fito daga cikin ɗakinsu tana sanye da wasu matsiyatan kaya ƙananu, sai wata riga data ɗora a saman kayan, saida ta dubi inda su Falmata ke zaune suna kitso tun tana cikin ɗaki take jiyo maganar matar dan haka ne yasa ta fito riƙe da key na Mota a hannunta, dan jiya wani Alhaji yayi mata kyautarta.

"Idan mata bazata iya gani tayi shiru ba, to kuwa zata daina shigowa gidan nan, saiki canza wajan zuwa kitson?".

Wani kallon baki isaba Falmata tayi mata zatai magana Shamsiyya ta shigo gidan tana saurin faɗin.

"Aunty Zahariyya kece kika aje Mota a ƙofar gida nan, naji Baba yana ta santin motar?".

"Idan kece maiyi mata kitson sai ki hanata shigowa gidan nan mu gani ai?".

Da wani irin sauri Zahariyya ta waigo inda Falmata take tana binta da wani matsayacin kallo tana ɗaya key na motarta tana nunata dashi ta ce.

"Ke har wuyanki iya isa yankan da zanyi magana kina gaya min ba daɗi?".

Turo baki tayi na zallar rashin kunya itama ta ce.

"To haka kawai tsakani da Allah, baki ji saida naja mata kunne bane?, da Ma'u ce ke tara jama'arta masu ƙunshi ana gulmar jama'a ai ita baku taɓa shiga harkarta, sai ni haka kawai duk salon a kore min mutane".

"Kinga Falmata idasa min kitso na, na wuce na tafi, kiyi hakuri ke kuma baiwar Allah".

Wata uwar harara Zahariyya ta watsama matar data yi magana, tana sake nuna Falmata ta ce.

"Wallahi ki kiyaye ni".

Zatai magana Mama ta ɗaga labule ta fito jiki a sanyaye domin kwana biyun kwata-kwata bata da ƙarfin jiki saboda rashin lafiyar da take fama da ita, ta ciwon ƙirji, dama kuma ɗan kitson da Falmata keyi a gidan suke samu a ɗakinsu ana ɗora sanwa, domin yanzu kowanne ɗaki girkinsa yake, idan kaga anyi girki gidan gaba ɗaya, takar sa'a akai Baba ya bada wani abun aka dafa gaba ɗaya, to sai ayi wata ma bai kawo wani abu ba, cikin kitson da take yi ba kullum ake samun masu kitso ba, gara ma Ma'u wani lokacin anayin biki ko suna kullum tana samun masu ƙunshi, daga nan idan sun zo ƙunshi sai ta samu masu ƙitso, a haka fa ake rayuwar, shi yasa wani lokacin basa samun abun kirki suna ci, shi yasa ma Mamar ciwon ƙirji ke damunta kuma tasan ba abunda yasa mata hakan sai kwana da suke da yinwa wani lokacin.

"Falmata karna sake ji kinyi magana a nan wajan".

Mama ta faɗa tana kallon Falmata.

"Mtsww aikin banza da anyi magana sai a kama faɗa ma mutum wasu maganganun ban hakuri tsabar ace ma mutum na Allah ne shi".

Zahariyya ta faɗa tana yin hanyar waje dan haushin sanyin da Mama ke dashi take.

Wani kalar baƙin ciki ne ya ciyo Falmata tana bin bayan Zahariyya da kallo, wato ma maganar data faɗa da Mama take kenan ba?.

"Amma Mama dan Allah ki duba fa yadda ta gaya miki magana ta wuce sai kace tana magana da sa'arta haba Mama?, ya kike hanani ɗaukar mataki ne?, ni ce dai-dai da uban kowa a cikin gidan nan wallahi".

Ta ƙare maganar tana idasa ma matar kitson, tana ƙare mata ta miƙe tana miƙa mata ɗari biyar ta amsa tana ajeta akan kujerar da matar ta miƙe tsabar ɓacin rai, matar bata tsaya ba tayi saurin ficewa daga gidan.

"Amma Aunty Falmata kamar dai yadda Mama ta ce ki rinƙa masu shiru, shima ai magana ce, saima kinfi ƙunsa ma mutum baƙin ciki idan har baki biye masa ba".

"Ke da'allah kiyi min shiru kema, ba nan kika wani shigo kina tabbayarta wai Mota a ƙofar gida ba ko tata ce?, ko kallonki ma tayi ne?, baki ga key ɗin Motar a hannunta ba, idan banda abunki da shiga abunda babu ruwanki, ai kema kinsan Mota itace zata zo da ita, duk gidan nan waye yake zuwa da irin wa'innan idan ba ita ba, mutunan dake yawo gidajen ƙaruwai miye Maza bazasu basa ba?, wallahi kin ban haushi".

"Yi hakuri Aunty Falmata".

Mama dake ta kallon Falmata na masifa sai kace ta ari baki, idan kaganta saika ɗauka bazata iya magana mai tsawo irin wannan ba.

Girgiza kanta kawai Mama tayi tana komawa ciki.

"Yawwa ƴar albarka yanzu nake cewa kece kika zo da wagga Mota mai shegen kyau haka?".

Duban Baba Zahariyya tayi tana sake matsawa jikin Motar ta danna key ɗin Motar, Motar ta buɗe ta buɗe gidan gaba tana shiga sai kuma ta dawo da dubanta inda Baba yake tsaye sai washe baki yake ta ce.

"Baba ni ce mana, ai kasan duk gidan nan ba mai iya zuwa da mota sai Zahariyya, wake da alfamar wannan ai sai ni ko?".

Washe baki ya daɗayi yana cewa.

"Ahab kware ko dama na faɗa ai kace da wannan aiki, to yanzu ina za'aje, ina ce dai Motar taki ko?".

Ya faɗa yana sake bin Motar da kallo, dan duk ɗaukarsa ko kawai an bata ne ta hau tazo gida da ita.

"Baba tawa ce mana ko wani ya faɗa maka ba tawa bace?".

"Kai Masha Allahu, kice munyi Mota kawai".

Ya faɗa yana shafa motar bakinsa yaƙi rufuwa.

"Baba na daiyi Mota".

Shiru Baba yayi yana sosa kai ya ce.

"Hakane kam kinyi Mota, to yanzu zan iya samun wani abu?, tun safe bansa komai a ciki na ba, gashi naga gidan duk yau babu wani motsi".

Haushi ne ya ɗan kama Zahariyya tana buɗe jakarta ta miƙa ma Baba naira dubu ɗaya, jikinsa na rawa ya amsa hannu biyu ya fara mata kirari da godiya yadda kasan ba uba ne da ƴarsa ba.

"Wai kai Baba dai a haka zaka zauna ƴaƴa ke ɗaukar nauyinka?".

"Zaka bakkani ne ko kuwa sai kin gama cimun fuska?".

"A'a Baba mi yayi zafi Allah ya baka hakurii amshi gama ƙirin ɗari biyar".

Haba ai sai ya ƙara daɗa washe baki yana dariya-dariya ya ce.

"Ko ke fa da haka kikeyi ai ba'a wani jin kanmu dake".

Ɗanja baya yayi yana matsawa ya bata waje zata tayar da motar kawai sai ga Shamsu sun shawo kwana ta wajan gidan da jama'arsa dake take masa baya.

Baba yana dubansu daga nesa ya ɗaga masa hannu yana barin jikin Motar Zahariyya dake neman tayar da motar amma ganin inda Baba ya nufa yasa ta tsaida motar tana buɗewa ta fito, ganin wadda yazo gidan yau yasa ta nufar wajan itama, dan kwata-kwata basa shiri da Baba da Shamsun, domin duk cikin gidan ba mai ɗakko masa magana harta kai wajan ƴan sadda sai Shamsu, shike sawa ana sake zaginsa a cikin gari, gara daɗawa ma bai basa ko asi sai jawo masa maganar da yake yi.

"Miye ya kawo ka gidana yanzu?, ba na ce karna sake ganinka ko hanyar unguwar nan ba?".

Faɗin Baba dai-dai yazo gabansu, ganin haka yasa Shamsu tsaida jama'arsa yana wani ɗaga masu hannu.

Sanye yake da wasu kaya ƙananu ya jifga babbar riga a sama, kayan duk sun yamutse, fuskarsa ko duk tabo ne wani wajan yankan wuƙa ne, sai idonsa dake shafe da kwalli baki, sanye kansa yake da wata hula ta karkace, bakin nan nasa a karkace yana dubansa cikin Muryar ƴan daba ya ce.

"Haba Father ya kake haka ne?, gidanka fa gidana ne".

"Ta gidan uban waye ya zama gidanka iyee?".

"Wai kai Father ya kake yawa ne?, wannan fa yawa kake yi, ya nida gidan ubana nazo ake min haka ne?".

Baba zai sake magana yana nunasa da yatsa Zahariyya ta ƙaraso wajan tana cewa.

"Please Baba barni dashi kayi tafiyarka kawai".

"To ki tabbatar bai shigar min gida ba".

"Shikenan naji".

Tafiya Baba yayi, Shamsu yana binsa da kallo wato dai bazai taɓa canzawa ba?.

"Mi ya kawo ka?".

Zahariyya ta faɗa tana harɗe hannunta a kirji tana kallonsa.

"Ke bana son iskanci fa, wato shi dai wannan Man ɗin ba zai daina son zuciya ba ko?".

"Uban naka kike cewa ma haka?".

"To duk waye silar shigarmu wannan halin bashi bane, wato kema harda wata Mota kika mallaka ba?, kema kin lalace idonki ya buɗe?".

"Zagina kike neman yi, Ya Shamsu miye haka kuma?".

"Ke dalla can ware ni ki ban waje".

Ya faɗa zai raɓata ya wuce cikin gidan nasu, ta tsaida shi da sauri tana faɗin.

"Baka ji abunda Baba ya ce bane karka sake ka shigar masa cikin gida?".

"Ai ko waye yazo bai isa ya hanani kutsawa cikin wannan gidan ba, ke ko shine yazo billahir azim na ɓarar dashi na wuce".

"Innalillahi yanzu Baban zaka ɓarar?".

"Ke kin fara cika ni fa, ki wuce kawai yawon gantalinki".

"Ya Shamsu karfa a fara jinmu da kai, nima fa na iya tashancin nan a'ato, da ne ka sanni a baya amma ina haɗuwa da wa'inda suka fika ɗanyen kai".

Wani kallo yayi mata yana sakin dariya yana sake binta da kallo sama da ƙasa ya ce.

"Kware kuwa gashi shi yasa naga ai har kin mallaki Mota, dole kice kema dai-dai kike da irinmu, to yayi ya isheki haka, zaki wuce ne ko sai na kikkifa miki mari?".

Ya faɗa yana wani matsowa kusa sosai da ita, idon nasa jawur, da sauri ya matsa tana banka masa hararara, itama duk cika baki ne, amma tasan Ya Shamsu ya shallakema tunaninta, domin duk wata rigima ya sani kuma ya iyata, shine har ƴan siyasa yake ma aiki, itama kawai cika baki ne.

Shigewa motar tayi tana barin wajan.

"Mtsww kai gayu ku tsaya yanzu zan fito mu wafce".

"Sai Oga Allah ya fito da kai lafiya".

Suka haɗa baki wajan faɗa......