Page 19
*KARAGAR MULKI*
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
*YOTA*
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 19
Tamkar matacce, haka su ka rik`a jan shi a k`asa haka su ka wuce da shi sauran fursunoni da ke cikin kurkukun sai faman lek`owa su ke,su na ganin me ke faruwa ,tamkar bola haka su ka yasar da shi a cikin d`akin da saura k`iris ya jefa shi saman Ishmal da ya ke zaune ,ko ta kansu babu wanda ya bi daga cikin Dakarun da su ka kawo sa,ko motsin kirki Yarima Haisam bai yi ba yanda su ka watsar da shi tamkar sharar bola haka ya ke kwance,har sai da ya kwashe sa'a wajen uku a haka ganin halin da ya ke a ciki ne ya sa wanda su ke a d`aki d`aya ya matso kusa da shi ya na yi ma sa magana jin shirun ya yi yawa ya sa ya kai hannunsa jikinsa,ba k`aramin k`aduwa yai ba sakamakon rashin jin motsin da bai yi ba a jikinsa,da sauri ya fara ambaton sunayen ALLAH gami da girgiza shi,sai dai ina domin ko da wasa ko kad`an ya ki motsawa da sauri ya nufi inda k`waryar da ta ke aje ruwan sha ko na alwallarsa ya d`ebo sai da ya tofa wasu addu'o'i kafin ya zo ya yayyafa ma sa,da wasu tagwayen ajiyar zuciya ya farka amma kuma ya kasa iya bud`e idanunsa amma bugun zuciyarsa da fitar numfashin sa duk sun dawo dai-dai, "Sannu ka ji Yaro,ka na dai lafiya ko ?", shiru Yarima Haisam yai da shi ba tare da ya ce da shi komi ba, a karo na biyu ya sa ke cewa da shi,"Ungo ruwa ka sha in ka na da buk`ata ,wata k`ila ko k`ishir ruwa na damun ka", duk da rashin kwarin jiki da kuma k`arfi da ke damun Yarima Sadauki haka ya sa hannunsa ya wancakalar da k`ok`on da ke d`auke da ruwan ya na mai Jan jikinsa ya koma can gefe guda ba tare da ya kalli wannan mutumin da ke da niyar taimakon sa ko sau d`aya ba.
Ko da isowar Boka Dürsäås bai zame ko ina ba sai cikin kurkukun, Sarauniya Junayyah na biye da shi,ba k`aramin k`aduwa gami da mamaki Yarima Ishmal ya shiga ba a sa'adda ya ga Boka Dürsäås da Sarauniya Junayyah a cikin d`akin kurkukun da su ke a ciki shi da Yarima Haisam, ba su yarda sun shigo da kowa ba daga cikin Dakarun da su ka zo da su face Sallama da Shamakin Sarauniya Junayyah su d`in su ne amintattun ko kuma a kira su da na hanin damarta," Kai la'ananne tanbad`ad`e kuma watsatstsen tsoho me ya dawo da kai cikin wannan Masarautar ba na gargad`e ka gami da yi ma ka korar kare a cikinta ba",wata irin shak`iyiyar dariya Boka Dürsäås ya sa ki wanda ya na bud`e bakinsa sai ga wani yauk`i-yauk`i ya na fita saboda tsabar k`azanta gaba ki d`aya bakinsa ya dafe,har wani kalar ruwan d`orawa-d`orawa ya ke,daga wani gefan ma har kore-kore da gansa kuka ya yi,tamkar an bud`e tsohuwar shadda haka wari ke fita daga bakin na sa,hak`oran bakin sa na gaba tuni dama sun dad`e da zubewa,Idan kai duba ya zuwa sturar jikinsa sai ka yi tunanin ko wani Mahaukaci ne wanda rashin gata yai mai katutu kafin ya tsagaita ya ce dashi,"Yarima Ishmal kwana biyu ba mu had`u ba,ta ya akai d`an Sarki jikan Sarki ya k`are da rayuwa a cikin kurkuku ,ko dai rashi gata ne da rashin matsayi ya fara bayyana a tattare da kai?",ya k`are zancen ya na mai matsawa ku sa da shi ya shinshina shi tamkar tsohon maye,"Ta ya ka juri irin wannan rayuwar alhalin ba ka saba da ita ba,ko ni da na ke wulak`antacce a wurin ka ba zan iya zama da yin irin wannan rayuwar da ka ke ba","Rayuwar da na ke anan ba ta da me ka ba ,kawai dai abinda na ke so ka gaggauta barin k`asarnan kafin in fita daga cikin wannan wurin da na ke in ko har kai kuskuren na fito daga cikin kurkukunnan sai na zama silar ajalinka,domin jininka ya dad`e da halarta da a zubar da shi kai ko da".....da sauri ya katse shi da cewa,","Ai ka yi kuskure tun farko domin na yi alk`awari sai na zame ma ka hayak`i fidda na kogo, da sannu zan mallaki abinda kai ka ke tunanin ya fi k`arfina,zan shayar da kai ruwan mamaki game da girman iko da isata","Hhhh ai na dad`e da sanin Mahaukaci ba ya ta`ba warkewa gabad`aya sai dai ya samu sauk`i, don haka wannan zancen na ka ba abin damuwata ba ne,Ga fili ga mai doki ga maciji ba a nuna ja shege ka fasa","oh haka ka ce","Babu tantama domin na san duk lalacewar tsangayar Kura ba a bama kare dilanci ta,hakama ko mage ta tsofe gashin bakinta ya fi k`arfin bakin `bera kuma dole in ana Sara za a tsallake bishiyar tsamiya da ta kuka", "Kai Kai Kai ka cika surutu ga ka da hayaniya mai hawan kai,ba dan kar in wuce makad`i da rawa ba da ne ce ta ya ma akai ku kai kuskuren aje su wuri guda Sarauniya Junayyah ?",ya k`are zancen ya na mai fuskantar saitin inda ta ke, "Banga ne mai ka ke son cewa ba ya kai Mashahuri kuma sannanne Boka ?","Ki gafarce ni ya ke Sarauniya K`asar BAIBAH amma wannan d`an'uwan na ki fitinanne ne ga shi kuma ibilishin gaske,ta ya za ku had`a shi da d`an Sarkin k`asar BIHINAR, ai zai iya k`ulla fiye da abinda zuciyarku za tai tunani ko haikace,idan so samu ne ku canza ma wani daga cikin su masauki", ya k`are zancensa ya na mai duk`ar da kan sa k`asa alamar risinawa.
" Ban san me ka hango ba akan wannan lamarin ba amma za a aikata kamar yanda ka so","Ina Godiya da amsa buk`atata da ki ka yi ya ke wannan Sarauniya mai cike da iko,Isa da MULKI,in ba za ki damu ba me zai sa ki maida d`aya daga cikin su wannan d`akin da da ya ke cikin wannan d`akin",yai nuni da shi,da ya ke d`akin kurkukun kamar guda biyu ne a cikin sa,"In so samu ne ki sa a mai da Yarima Ishmal a cikin wancan d`in kin ga kenan sai dai ya jiyo ya kalle shi daga nesa,ba shi da halin cewa da shi komi balle har ya zuge sa bisa irin buk`atar da za mu bijiro ma sa da ita",da ido Sarauniya Junayyah ta dubi shashin da su Shamaki ke tsaye ba tare da ta ce komi ba,su ka gane nufinta ta k`arfi da yaji su ka sa ka shi cikin d`akin da Boka Dürsäåsai ya ce sai faman shure-shure ya ke tare da cewa,"Ka kuka da kan ka a duk ranar da na samu damata a kan ka ,sai na dasa ma ka munmunan bak`in fentin da ba zai ta`ba goguwa a rai da rayuwarka ba","To a yaushe kuma,wai ance da kuturu je ka ka gani ,a ta ya za ka samu wannan damar kalli a matsayin da ka ke ciki a yanzu,ni d`in dai da ka raina kuma ka ke ma kallon wulak`antacce,kuma yasasshe abin korewa daga `bigiren da ka ke ,ni ne a saman ka na yi ma ka nisa fintinkau sai gani ko hange daga nesa,na zame ma ka tamkar bishiyar mad`aciya lasata ko tauna ta abu ne me matuk`ar wahala,a ta ko ina in ka waiga a rayuwar ka sai ka ganni",",Murmushi mai ciwo Yarima Ishmal ya sa ki wanda ya ke bayyanar da bak`in ciki damuwa gami da halin da ya ke a ciki, da har ya yi shiru ba zai ce da shi Komi ba ,zuciya ta ciyo shi ya lek`o ta k`ofofin da ya ke hangensa ya ce da shi,"Mutane sukan raina Cinaka saboda ganin k`ank`antar shi,amma idan ya cije su ,sukan ji zafin cizon har cikin k`ok`on rai da zuciyarsu,don haka ka da ka ta`ba raina mage a kan kare,itama idan ta ga nama ci take,ka da ka ta`ba raina dama komin k`ank`antarta,da wannan na ke ce ma ka ka jira zuwan lokacin na domin yanzu na ka ne,da gaske ni Yarima ne kuma tamkar ruwan sha haka na ke,idan ba ka sha a yanzu ba za ka neme shi anan gaba, idan kuma ka k`i k`ishir ruwa ce za ta kama ka ta kuma zama ajalinka,ka rik`e wannan kuma ka sa shi a can cikin Ranka inda ba za ka manta ba,inda halima ka rok`i abun bautarka da ka da haka ta kasance"
Boka Dürsäås bai sa ke bi ta kan sa ba sai umarni da yai da a shigo ma sa da wani tulu nai d`auke da wani ruwa launika kala-kala a cikin sa sai faman za`bal`bala tare da turiri ya ke ,duk da ba akan wuta ya ke ba,Kai tsaye kan Yarima Sadauki ya nufa ya na mai watsa ma sa shi,bakinsa d`auke da wasu munanan kalamai nan take dukkanin inda wannan sihirtaccen ruwan ya sauka a jikin sutura Yarima Haisam,ta fara zagwanyewa ta na darewa gami da yayyagewa,idanuwan sa suka rine zuwa kalar ja,haka ma jijiyoyin jikinsa su ka tashi burd`un-burd`un,hatta da gashin kansa sai da ya mik`e tsaye tamkar ana busa ma sa iska, wata mahaukaciyar dariya Sarauniya Junayyah ta sa ki sakamakon ganin ta na kan k`adamin cin nasara akan cikar burinta,k`ara watsa ma sa ruwan yai a karo na biyu nan ta ke hatimin da ya ke zane a k`irjinsa saitin kafad`arsa ta hannun hagu da na wuyansa ya bayyana,sai da su Boka Dürsäås su ka ja baya, domin da fari tsorata su kai bisa dalilin d`ora idanunsu a kan abinda ba su yi zato da tsammani ba.
A kallon farko in Kai ma Hatimin saman k`irjinsa,idanuwanka za su nuna ma ka wata k`atuwar Macijiya ta fasa kai,harshen bakinta guda biyu har wani motsi za ka ga su na yi,tamkar su na shirin kawo ma ka hari ko farmaki ,idan ka natsu kuma ka sa ke zuba Ido za ka duba za ka ga banbanci daga abinda ka fara gani da farki,Asali Hatimin guda biyu ne,d`aya babba d`aya k`arami,Babban zanen wata da tauraro ne a jikinsa,k`aramin kuwa rantsatstsiyar hular Sarauta ce tare da wata takobi a jiki,Hankalin Sarauniya Junayyah da Boka Dürsäås bai k`ara ta shi ba har sai da su ka ga bayyanar wata Sark`a mai d`auke da wani haske da sai da ya disashe ganin duk mutanen da ke cikin d`akin kurkukun.
"Ya ke wannan Basarakiya ya ki ka ga k`arfin tsafi na wannan shine abinda na kwashe tsawon watannin a cikin tsibirin jaisham ina had`a mi ki domin ki samu nasarar Mulkar KARAGA mafi girman iko a fad`in wannan duniyar"," Tabbas na gani kuma na shaida cewa Kai d`in ka na da kwarewa gami da fasaha akan binciko abinda ya ke binne ko kuma ka na iya sa abinda ba zai iya faruwa ya faru ba",duk ta na wannan maganar ne cikin zakwad`i da d`okantuwa bisa abinda ta ke gani a gabanta.
Sarauniya Junayyah birkicewa tai gami da rud`ewa ba tare da ta jira komi ba ta tunkari inda Yarima Haisam ke tsaye,hannayen ta ta kai kan Sark`ar da ke wuyansa da nufin ta Ciro ta daga wuyannasa,wata irin jijiga gami da watsar da ita can gefe guda akai ba ta ko samu damar iya motsawa ba,da sauri Boka Dürsäås yai kan shi cikin fushi da zafin rai ya na ce mi shi,"Kai kai wofintacce kuma yasasshe d`a me kai ma ta,wanne irin tsafi kai ma ta idan har wani abu ya sameta ba Zan bar ka ba,sai na yi ma rayuwar ka muguwar illa, na rantse ma ka da k`arfin tsafi na",ya na kaiwa nan ya duk`a ya sa`bi Sarauniya Junayyah tare da umarta Dakarun da su ke a waje da cewa,"Ku gana ma sa azaba iya kar azaba har sai na juyo ta kan sa,sannan ya amshi sakamakon zunubin da ya aikata ".