KARAGAR MULKI

Page 20

by @cwtsumiey19988

*KARAGAR MULKI*
     
STORY & WRITTEN BY 
 (*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin 
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
   And now...*KARAGAR MULKI*
❤ Wannan page naku ne massoyana
❤ Allah ya bar mu tare forever and ever 

BOOK 1 

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 20
  Tamkar walk`iya haka su ka ga bayyanar wannan  haske mai d`auke da suffa sak irin ta Gimbiya Junainah,Kai tsaye za ka iya kiran wannan haske da ruhi ko kurwa ta Gimbiya Junainah don ko kusa ko kad`an ba su da banbanci, Kai hatta da tsayin jiki,yanayin k`ira ko sufar jiki sak duk iri d`aya ne,ba tare da `bata lokaci ko jiran wani abu ba wannan kurwa ta sauka a dai-dai saman fuskarta ta na mai bin duk ilahirin jikinta ta shige gabad`aya, sai da Gimbiya Junainah ta zabura gami da mik`ewa zaune ta na mai sakin wata naunauyar ajiyar zuciya sannan ta koma ta kwanta kan shimfid`ar da ta ke a kai ba tare da ta san hakan ya faru ba.
Malikat Juwairiyya da Kuyanga Jazila kam tsaye su kai su na zubama sarautar Allah ido, da kuma san ganin ya zata kaya,"Malikat kin gani kuma yanzu Ruhin Gimbiya Junainah ya dawo jikinta",Kuyanga Jazila ta ce ta na mai rarraba haruffan zancen na ta,da sauri Malikat ta jawo wani kwanan tasa sai faman shek`i da walwali ya ke, a cikinsa d`auke da ruwa ta fara k`ok`arin d`ura mata,amma ko da wasa ruwan bai shiga cikin bakinnata ba,hasalima yanda ya shiga haka ya ke fita ta gefan bakinta.
"Kin gani Jazila ko ruwa ba ya shiga cikin bakinta Anya kuwa ta kamo dai-dai,ina jin tsoro kar in rasata ban san me ye zai same ni ba in haka ta kasance ba"," A'a, a'a ba abinda zai sami Uwar d`akina da izinin mai duka za ta tashi har ma ta zauna kan KARAGAR MULKIN K`asarnan,sai ta gaje ki ta yi Sarautar k`asarnan ",ta k`are zancen ta na mai sharce hawayen da su ke faman kwaranya daga idanunta"," Kai na a cunkushe ya ke Kuyanga Jazila me ya sa haka ta ke faruwa da Gimbiya Junainah, me ta aikatawa wani,zunubin me ta yi da ta can-canci wannan horarwa,azabtarwa gami da cutarwar, ko dai hakan na nufin ba a son ta gaji KARAGAR MULKIN Mahaifiyar ta ne shiyasa a kai mata wannan munmunan surkullen,gami da tsafaceta ta koma tamkar wata abin tsoro","Ki gafarce ni Malikat Juwairiyya amma ni na dad`e da sanin wannan shine dalili kuma silar da Uwar Gijiyata ke fuskantar irin wannan rayuwar, a kullum burin su su tagayyara rayuwarta ya kasance ba ta da sauran mamora a doron duniya",Wani murmushi mai cike da tarin ma'anoni daban-daban Malikat Juwairiyya ta sa ki kana ta d`ora da cewa,"Ai ko ba wani d`an uban da ya Isa ya hana Gimbiya Junainah gadar KARAGAR MULKIN K`ASARNAN ko shi d`an abu kaza-kazan waye kuwa,na shirya fito na fito,tare da aikata komi akan koma waye daga yau za mu sa k`afar wando d`aya da shi,Zan nuna ma sa nima jinin Sarauta ce,na yi gadon Sarauta gaba da baya na, kuma na yi Sarauta da karan kaina, na MULKI k`asar da ta zo ta biyu a fad`in duniyarnan,wajen tara zakwak`urai kuma jajurtattun jarumai,ga kuma k`arfin ikon fad`a a ji a ko ina,kin ga kenan ya can-canta a ce na fi kowa iya sanin hanya ko makamar yanda a ke kulla kutungwuila,makirci,hassada,zagon k`asa,da kuma munafunci dam haka ki shirya zuba Ido ki sha kallo,ko da zan rasa duk abinda na gada da kuma wanda na mallaka da karan kaina kai ko da zan yi yawo tsirara ne,ko na rasa rai na sai na cetota daga halin da su ka jefata a ciki sai inda k`arfin ya k`are,kai ko".......da wani hanzari Kuyanga Jazila ta fad`i gaban Malikat Juwairiyya, ta na cewa,"Ina mai had`a hannayena gami da rok`on ki kar ki aikata abinda zai sa ke  jefa rayuwarta cikin wani mugun tashin hankalin da ba mu yi zato da tsammani ba","A'a ba zan aikata abinda ki ke tsoro ba domin ita d`in Jikata ce jinina ke kwaranya a jikinta don haka na yi ma ki alk`awari da gemun kakana,ba jimawa Bokanya Azizah za ta  iso cikin k`asarnan da zaran ta iso zan yi tafiya ba zan dawo ba har  sai na karya duk wani tsubbace-tsubbace ko asirin da ke jikinta","To idan har Bokanya Azizah za ta zo mene ne amfanin yin balaguran ki,ina jin ita kad`ai ta Isa kuma ta wadata ta magance matsalar Gimbiya Junainah "," A'a ba ta Isa ba, sai na k`ara da neman wasu hazik`ai kuma mashahuran Bokayen,wand`anda su ka gagari duniya Gabad`aya ,ina so inyi abinda zai tsorata tare da girgiza duk wanda ke k`ok`arin cutar min da jika,ko ya ke da sa hannu a ciki,sai na yi abinda wata mace a duniyarnan bata ta`ba yunk`urin aikatawa ba,abu na farko da zan yi zan fito da Ishmal daga cikin kurkukun da ya ke tsare,daganan sai mu fuskanci duk abinda zai biyo baya".

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
"Madaki da gaske ne abinda na ji ana fad`a a cikin gari wai ka tura Nurain k`asar BAIBAH da nufin ya je ya dawo da wad`anda a ka tsare a can?", ya fad`a cikin san sanin gaskiyar abinda ya ke faruwa." Ina mai ba ka hak`uri Me Martaba amma da gaske ne na tura Nurain zuwa K`asar BAIBAH, amma ba wai da nufin ya dawo da duka Dakarun ba a'a, domin Yarima Haisam kawai na turasa shi kad`ai na ce ya dawo min da shi ba tare da ya damu da wani a cikin sauran ba,ko da ko shi kan sa Nurain d`in ne ban damu ya mutu ko ya rayu ba,babban burina shine Yariman k`asar BIHINAR ya dawo cikin k`oshin lafiya "...."Dakata Madaki wai me ka ke nufi da wannan zancen, son kai da son zuciya ka fara ko mene ne ban gane ba ?"," A'a ba haka ba ne aikin da ka kasa ne na ke aiwatarwa,shiyasa na tura Nurain da ya je ya dawo da shi kuma shi shi kad`ai d`insa, tunda kai ba ka d`auke sa a matsayin d`an ka ba balle har ya sa ran wani taimako daga gare ka,shi d`in d`a ne na gari kuma na kirki,ya na son ka so mai tsanani,son so me yankan shakku ko da wasa baya tsallake umarninka ko da umarnin naka zai cutar da shi zai jure gami da jajurcewa a kan haka duk da kai ba ka kasance Uba Nagari a garesa ba"......saukar Mari a saman fuskar Madaki ne ya dakatar da shi daga maganar da ya ke,muryar Me Martaba Sarki Abdullah har rawa ya ke ya ce da shi,"Kai har waye da za ka tsaya a gabana ka na fad`a min irin wannan d`atatan maganganun ba tare da ka yi duba da matsayina ko girman da na yi ma ka ba","Ka yi hak`uri Me Martaba amma anan ana maganar tsatso,jini da kuma ahali ne,ko ka manta waye Yarima Haisam ne,to jininka ne tsatson da ya fara amsa suna d`anka a duniya,shine d`a na farko da ya fara shiga Ranka da zuciyarka,shin ko ka manta da hakan ne wai?","Ta ya zan iya mantawa da hakan,bayan a yanzu ba na da banbanci tsakanina da kai "," kamar ya ta ya za ka danganta kanka da kuma ni?","Saboda a yanzu ka aikata fiye da abinda ni na aikata a baya,idan har ni ina cutar da d`ana na ciki na ne kad`ai amma a yanzu ka jefa rayuwar mutum wajen Ashirin cikin had`ari ne,saboda son zuciya da son kai irin na ka","Ban damu ba ko da me ye zai faru ko da su duka za su rasa ran su,madamar dai Yariman k`asar BIHINAR zai dawo Gida ya wadatar da ni","To tabbas ka yi kuskure kuma Zan tabbatar ma ka da hakan,muddin wani abu ya samu Nurain sai na d`aure ka har igiya tai rara,sai na bi kadin duk d`igon jinin da ya zuba na su,sai ka biya kadinsa,ka rik`e a ranka gaban rijiya ba wajen wasan makawo ba ne,sannan kuma mai sulken yak`i  ba yajin tsoro ko d`aukar wargi",ya na kaiwa nan ya bar ma sa fadar gabad`aya dama sun gama zaman fada ne ya tsaida shi domin ya samu tabbacin akan zancen da ya ke ta yawo a cikin gari.