Page 21
*KARAGAR MULKI*
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 21
K`arar saukar bulala ce ke ratsa ilahirin k`untataccen d`akin da ya ke a ciki ,k`afafuwansa da hannayensa a k`ulle su ke ko cikakken motsi ba ya iya yi,duk ilahirin fatar jikinsa ta fashe jini sai man zuba ya ke tamkar an yanke k`aramar dabba,Boka Dürsäås ne tsaye da ga gefa ya na kallonsa ta kafofin k`arafunan da su ka yi ma su shamaki gami da zama katanga a tsakannsu, Yarima Ishmal na can da ga gefa ya na kallonsa zuciyarsa cike da rauni tare da zallar jin tausayinsa,k`ara matsowa Boka Dürsäås yai yanda zai fuskanci Yarima Sadauki ya kuma ji abinda ya ke son ya fad`a ma sa sosai da sosai,ya ce da shi,"Ba ka can-canci irin wannan azabtarwa da cutarwar ba domin kai ka fito daga Gida mai daraja kuma,tsatso mai albarka ne, shin ba na taimake ka,na ba ka shawara ba,kawai ka amsa tarin tambayoyi da mu ke ma ka, kuma ka fad`a ma na hanyar da za mu samu damar mallakar sark`ar da ke rataye a wuyanka,shikenan mu sallame ka ka yi tafiyar ka",cikin k`arfin hali da juriya ya mai da ma sa da Marta ni,"Da zan ba ku shawara ku ji kuma ku yarda har ku yi amfani da ita nima,da kun dai na tambayata komi ku kyale ni da ni da mutane na muyi tafiyarmu,Kai ko da ni ba za ku kyale ni ba su ku sallame su su yi tafiyar su "." Shin wai ba ka san cewa wanda ya fito daga gidan iko,gidan daraja ba,ba ya kula ko damuwa da halin da wasu `yan tsirarun mutane su ka shiga ba ?,idan ba ka sa ni ba yau ina son in sanar da kai wannan dad`ad`e kuma shekararen ilimin,kanka da rayuwar ka wai ya kamata ka damu da shi ba wasu asararrun Bayi ko Dakaru ba".......cikin `bacin rai fushi da zafin zuciya Yarima Ishmal ya dakatar da shi ta hanyar cewa"Kai banza wulak`antaccen tsoho wanda ya zo duniya a banza a wofi kuma zai koma a alakoro,kar ka sake kiran mutanena da asararru,ba laifi idan ka kira su da bayi ko Dakaru amma kar ka sa ke aibanta su ko k`ok`arin wulak`antasu",ya k`are zance da tsirta ma sa miyau a saman fuskarsa,Rasa me zai ce da shi yai sai sake bada umarni akan a cigaba da azabtar da shi da ya yi,ya na mai nufar hanyar da zai bar kurkukun da sauri,ya na cikin tsananin fushi ,"Matsiyatan banza mai zai sa ba za ku kashe ni anan gurin ba hankalin ku ya kwanta,idan har kuna son kwanciyar hankali to ku aikata hakan, idan kun kasa kuma ina mai tabbatar ma ku da sai na addabe ku na gagareku a cikin wannan k`ank`anuwar Masarautar".
Dakatawa Boka Dürsäås yai tamkar zai ce da shi wani abu sai ya fasa,amma k`arasowar Sarauniya Junayyah cikin rashin k`arfin jiki na fama da jinya da ta ke tun sa'adda ta yi yunk`urin ta`ba Sark`ar da ke sagale a saman wuyan Yarima Haisam ya ya juyo, sai da ta gyara muryarta yanda zai jiyota daga, can sannan ta ce da shi,"Ai k`arshenka ba zai zo da sauk`i ba ,domin sai mun kai matakin da za ka fara hurwa gami da rok`on mutuwa da kanta da ta zo ta d`auke ka amma ba za ta zo ba,za ka rayu ne kamar yanda na so kuma na tsara ma ka, haka ma mutu har in ta zo sai da sahalewata za ta d`auke ka","K`arya ki ke k`aramar Sarauniya domin raina da ni kaina na sun fi k`arfin ki,duk da na kasance ina d`aure kuma a tsare a hannuki,ki sa ni ruhi d`aya ne da ni kuma Ruhin nawa ya kasance ya na hannun ALLAH UBANGIJIN SAMAI DA K`ASSAI BAKWAI,Zan ranyu a sanda ya ke so kuma Zan mutu a sanda ya tsara min, na san da hakan kuma gami da amincewa,saboda haka azabtarwar da za ki sa amin ba za ta tsoratar da ni ba",sai da Sarauniya Junayyah tayi dariya iyakar iyawarta har ta gaji dan kanta ta tsagaita sannan ta ce da shi, "A lokutta da dama mutane su kan ji tsoran kan su da kan su sakamakon girmama shed`antar da su ke da ita,to ya ka ke ganin in su ka had`u da irina shed`aniya fitinanniya kamar ni,wacce zuciyarta ke cike da mugun kaidi wanda zai iya sawa a tashi duniya saboda girman sa,don haka ka shiga taitayin ka ka mai da hankalin ka a jikin ka, ka yi abinda ya dace ko za ka rabauta ka tsira da ko da iya rayuwar ka ne,domin Ni ba ruwana burin raina kawai na sani shike rufe a idona".
" Hmmmm da alama ke ba ki san ko ke wacece ba,a haka ki ke ikirarin za ki cutar da ni ko ki aikata min abinda zai sa inji tsoran ki,ke ce halitta mafi rauni da Allah ya fara halitta a doran duniya,saboda kasancewar ki mace sai da ya zagaye rayuwar ki da wad`anda za su taimaka ma ki ki samu wani abu a cikin rayuwar ki,a haka ne za ki zo kina min fankamar da d`agawa da nufin inji tsoranki,to bari ki ji ke a cikin matan ma mak`ask`anciya ce,wulak`antacciya kuma tagayyararra,tunda kin kasa tsayawa a bisa gaskiya da tafarkin da Allah ya d`ora ki a kai ba, don haka ni ko da wasa ba na jin tsoran ki ki je kiyi duk abinda ki ka gadama,na shirya d`aukar komi da ga gare ki","Hmmmm na fahimce ka kuma sak'on ka ya zo a dai-dai amma na san idan mutum bai ji tsoro saboda kan sa ba ya kan ji tsoro in an tashi cutar da wad`anda ya ke tare da su kuma ya ke shirin ba da ran sa fansa a kan su ko ba haka ba ne Boka Dürsäås ",ta k`are zanceta da sigar tambaya gami da maida kallonta inda Boka Dürsäås ya ke tsayse tun d`azu.
"Ina fatan dai ka fahimci ni tare da manufar da na ke nufi ?", ta jeho mi shi da tambaya kafin kwakwalwarsa ta gama juyawa daga furcin da ta fad`a, cikin sark`ewar murya ya fara cewa da ita,"A'a.... A'a dan Allah kar ki aikata haka ,kar ki cutar da su kimin duk abinda za ki min amma kar ki ta`ba su,domin ba su aikata mi ki komi ba",ba tare da ta saurare shi ba ta ce "Shamaki ma za je ka sa a zo min da su nan in sa a rik`ai ma su yankan rago wata k`ila hakan zai sa ya fara jin tsoro na har ya amsa min tambayoyina"," An gama ran ki ya dad`e yanzunnan za a zo da su "," A'a kar ka je na gane ka,ka da ka aikata hakan domin wallahi na rantse ba zan bar ku ba sai na illata ku ,ni ne nan zan zama ajalinku ka dawo kar ka tafi na hane ka",duk yana wannan maganar ne ya na k`ok`arin ganin ya kwance daga mugun kullin da su Kai ma sa.
Ba jimawa sai ga shamaki ya dawo da sauri tamkar zai kifa rawaninsa a hannu,sai faman haki ya ke,da alamama dai har da gudu ya had`a, Kai tsaye k`asa ya fad`i ya na mai kama k`afafuwan Sarauniya Junayyah tare da cewa,"Na tuba na bi Allah na bi ki,ki gafarce ni kar ki hukunta ni da laifin da ba ni na aikata ba,hasalima ban san sa da ya faru ba ,ba na da sa hannu ko wata masaniya a cikin abinda ya faru, kai ko ma",......"Kai Dallah Sarkin surutu da zuba tamkar kanyar da ba ta nuna ba ka dakata hakanan ka je kai tsaye ka fad`a min abinda ke faruwa","Zan fad`a amma dan Girman KARAGAR MULKIN ki kar ki hukunta ni ba ni da ruwa a ciki","Oh ba za ka fad`a ba ko","Aa ba haka na ke nufi ba",sai da yai k`asa da muryarsa tamkar mai tsoran kar wani ya ji shi, kana ya ce da ita,"Na je d`akin da a ke tsare da su sai da ko da wasa ban iske kowa a ciki ba ,kai dad`ai duniya ba a ta`ba a je wata halitta mai rai a cikin d`akin kurkukun ba,kuma na yi tambaya a gurin Dakarun da suke tsaron `bangaren da su ke sun ce ba su ga gilmawar kowa ba ko da wani d`aya daga cikin su"....."ka sa k`arasowa yai sakamakon kufito da Sarauniya Junayyah tai da shi can ya je ya bigi bangon bai ko motsa ba,balle a sa ran zai iya tashi..
"A'a wannan zancen k`arya ne domin ba yanda za ai haka ta kasance, wannan duk shaci fad`i ne,domin ba zai ta`ba sa`buwa ba,sarki da zama bawa,ta ya ma za ai in yarda da wannan k`anzan kuregen,duk tsaro gami da Dakarun da na baza a fad`in wannan Masarautar a ce sun gudu,Kai! abin da kamar wuya wai gurguwa da Auren nesa", duk ta na wannan maganar ne a rud`e sai faman kai da kawowa ta ke ta ma rasa tak`amaimai me ya kamata ta yi,,sai da ya tofar da jinin da ya ke ta faman kwaranyowa daga saman kan sa zuwa fuskarsa da bakinsa sannan ya ce da ita," Ki bar wani surutun ban za da wofi ki je ki gani sun tsira ko ba su tsira ba,anan ne za ki tabbar da mu'ujiza da girman iko na Ubangijin al'arshina",da wani irin ihu gami da kawa ta iso wajen sa ta na mai shak'e ma sa wuya da iya kacin k`arfinta tare da cewa,"Na rantse ma ka da kushewar uwata da ubana ba zan bar ka ba, in har ban iske mutanennan ba sai na ga ka gwanmace da ma ba a haifeka ka zo duniyarnan ba,sai na shayar da Kai ruwan azabar da ba ka ta'ba ji da gani ba,Kai sai "....ta ka sa k`arasawa sai faman d`aga hannayenta Sama da ta ke,k`arshema ta juya da matsanancin hanzari ta nufi d`akin da aka fara a je su Jamal d`in don ta gane ma idon ta zahiri har alkyabbarta na fad`owa ba tare da ta sa ni ba ko ta kula,gabad`aya jama'arta irin su Boka Dürsäås su ka mara ma ta baya , k`arin takaici Yarima Haisam ya bi ta da dariya cikin mad`aukakiyar muryarsa.
Tamkar zaburarrar karya haka Sarauniya Junayyah ta koma a sa'adda ta je ta ga ba su Ayub ba dalilin su tamkar Allah bai yi ruwan tsirar su a wurin ba,Kai tamkar wani mahahaluki,bai ta`ba zama a cikin d`akin ba,a wurace ta Isa idan Yarima Sadauki ya ke d`aure ta shak`e shi ta na mai kai ma sa duka duk inda ta samu a jikin sa tare da cewa," Ka fad`a min ina ka kai su,ina da tabbacin kai ne ka yi wani surkulle su ka `bace ba tare da wani ya gansu ba",banza yai da ita sai faman dariya rainin hankali da ya ke ma ta ,wanda ita kuma hakan yai matuk`ar tunzura ta gami da fusata ta,ta zari wata takobi a k`ugun wani dakare da ke tsaye kusa da ita ta kai mi shi Sara,in ba dan Allah ya so ya tsare ba da tuni ta sauya wa labarin su na, amma azama gami da saurin duk`awa da Yarima Haisam yai ne ya sa ba ta fille ma sa kai ba,sai dai takobin ta sauka a saman bayansa nan take tai masa wani munmunan yanka,da sauri Jakadiyar ta rik`ota gami da bata ba ki ,"Ki bar ni in kashe shi in ba zai fad`a min ina ya kai su ba kuma wanne irin tsafi yai su ka kore da ga ganinmu","A'a ba haka za ai ba,ya shugaba ta bin sa za ki a hankili na san zai fad`a mi ki inda ya Kai su",wani sakaran kallo ya bi Jakadiyar da shi na irin ba ki da hankalinnan,"Na rasa mene ne alak`ar da ke tsakanin na da ke da har ki ke k`ok`arin d`aukar rayuwata,me na yi ma ki ne har haka ?","Kar ka raina min wayo tun yaushe na ke gaya ma ka k`udirina amma ka yi biris da ni sai kuma yanzu ka ce da ni ba ka san akan me na ke maganar ba","Na manta ne kin sa kun wahalar da ni gami da gana min azaba mai yiwuwa hakan ne ya sa na manta da duk abinda ki ke buk`atar",sai da Sarauniya Junayyah ta shak`i iska ta fesar ko za ta samu sassauci daga tarin takaicin da sabon rainin wayon da ya tsiro ma ta da shi , da wanda ta ke kwasa a wurin tunda fari a wurin Yarima Haisam, tausar zuciyar ta ta yi domin ganin ta ke kamar wata damace da ta ke gab da samun cikar burin ta,ta ce da shi"Babban burina a duniya shine na mallaki ko na gaji KARAGAR MULKIN da tafi kowacce KARAGAR MULKIN girma a fad`in duniyarnan, amma hakan ba zai faru ba sai na fara Mallakar KARAGAR MULKIN k`asar BIHINAR,don haka ina son inci K`asar BIHINAR da yak`i na za ma ni ce ke MULKAR k`asar baki d`aya, wannan shine k`udirina da kuma fatana",sai da Yarima Haisam ya ya mutsa fuskarsa alamun bai fahimci komi daga zancen ta ba,"Me ye amfanin fad`a min wannan sokiburutsin na ki da ki kai ?,domin ni a ciki ban fahinci komi ba daga ciki ba da har zai sa ki takure min rayuwata har haka ba "," Hmmmmm da alama akwai wani abu da ka ke shirin aikatawa,Kai tsaye dai ina nufin ka nuna min hanyar da zanbi domin in shiga k`asar ku in ci ta da yak`i "....da sauri ya katseta da cewa," Me ki ka ce,Anya kuwa kina da hankali, ba na tunanin kwakwalwar ki ta na aiki yanda ya kamata,Wai tsaya ma kin san me ki ke fad`a kuwa ?"rasa me za ta ce da shi tai sai shine ya cigaba da cewa,"Mahaifina da kuma k`asata su ki ke son inci amanarsu kuma in ha'ince su saboda wani sakaran buri da tunani na ki,wai tsaya ma shin mahaukaci ki ka d`auke ni ko me?,da alama dai k`aramar kwakwalwa ce da ke,ke gabad`aya ma ki ba ki can-canci zamantowa Sarauniya a wannan Masarautar ba,domin kwata-kwata ba ki da tunani mai kyau"....",saukar bugu ta ko ina da ya ji ne ya hana sa k`arasa sauran abinda ya ke fad`a