KARAGAR MULKI

Page 22

by @cwtsumiey19988




*KARAGAR MULKI*
STORY & WRITTEN BY 
 (*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin 
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
   And now...*KARAGAR MULKI*
*YOTA*
BOOK 1 

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 22
Saukar k`arar Mari ne kawai ke tashi a wurin duk ta bi ta kunbura ma sa fuska ita kanta hannayen ta sun yi ja sai faman zugi da zafi su ke ma ta amma tsabagen rad`ad`i, jin zafin tare da k`unar zuci da ya addadabe ta sakamakon abinda ya faru ya sa ta kasa jin wancan zafin,k`arasowa Boka Dürsäås gami da rik`e ma ta hannaye ya sa ta dakata, "Haba Sarauniya Junayyah me ki ke aikatawa haka ba ki ganin halin da ya ke a ciki ko ba ki tsoran ya mutu ne a saboda wannan wahalar da ya ke sha ne?"," Ya mutu ma na ai ni mutuwar ita ce abin so na da kuma fatana",ta mai da ma sa da amsa ta na ta faman haki alamun ta gaji matuk`a gaya,"Ke kam me ye ribarki idan ya mutu shi ki na da wanda zai iya amsa ma ki tarin tambayoyin da ki ke da su,ko ki na da wanda zai iya nuna ma ki hanyar da wad`ancan sauran fursunoni su ka bi su ka gudu,Uwa uba wa ki ke da shi da zai nuna ma ki hanyar da za ki mallaki Sark`a da ke rataye a saman wuyan sa,shin idan ya mutu za ta sa ke bayyana a wuyan wa ni ne ko ya ya ?",zaman dirshan a k`asa Sarauniya Junayyah ta yi ta na mai sharce gumin da ke tsatstsafo ma ta tare da rabka tagumi hannu biyu,"Ni kam na mutu na lalace ,ta ya duk wannan abun ya faru da ni yaushe nai sakaki da har hakan ta faru,Ashe lalacewar tawa har ta kai wani ya yaudare ni kuma ya cuce ni ?","Ki gafarce ni ya ke Sarauniya k`asar BAIBAH amma ina mai tabbatar mi ki da har yanzu muna da sauran damar da za mu yi amfani da ita kuma har mu Kai ga cin nasara",wata irin zabura tai ta na mai fuskantarsa da ganinta inda ya ke ta ce da shi,"Da gaske ka ke Boka Dürsäås, ka na nufin har yanzu muna da sauran damar cikar burin mu?","Kwarai ma da gaske in har za ki bi duk abinda na ce kamar an kamo wad`ancan fursunonin ne ,kuma dole ko Yarima Haisam ya so ya k`i sai ya ba mu duk bayanan da mu ke so a wajen sa","ina sauraronka ma za gaggauta ka sanar da ni kowacce irin hanya ce komi runtsi da tsananinta ba zai dame ni ba,na rantse ma ka sai na bi ta madamar burina zai cika","iyakar wahalarwa kin wahalar da wannan mutumin to ki dakata hakanan domin a kowanne lokaci zai iya mutuwa da zaran ya mutu to mu ke da asara,zai fi mana kyau mu yi amfani da wannan damar wajen ganin mun tursasawa yai magana ko ta halin k`ak`a,idan ma ya k`i har k`asar ta su za mu iya zuwa da shi muyi masu barazana ko su ba mu abinda mu ke so ko mu kashe sa,idan kin amince zan yi ma ki bayanin komi da komi dalla-dalla yanda za ki gane,amma kuma sirri ne ya na buk`atar natsuwa kafin a aikata shi","Ba damuwa na amince yanzu haka mu je d`akin sirri na sai mu tattauna yanda ya kamata ",ta mai da hankalinta kan Dakarun da su ke azabtar da Yarima Haisam ta ce da suj ," Ku kwance sa ku ba sa abinci da abin sha kuma kar wanda ya sa ke aikata ma sa komi kai ko kusa da shi ban yarda wani ya je ba balle wani abun kuma ya biyo ba ya, duk wanda ya aikata sa`banin abinda na fad`a ya san sauran za mu gauraya da shi",ta na kaiwa na su ka fara yunk`urin barin kuntaceccen kurkukun.
Sai da Yarima Sadauki ya kwashej rabin sa'a da wasu dak`ik`u kafin ya dawo cikin hayyinsa har ya fara jan numfashi da sauri da sauri,jin shi ya ke tamkar ba a duniya ba ,duk da dai ba wannan shine karo na farko da ya tsinci kansa a kurkukun ba amma wannan izayar da ya sha ta ban-banta da sauran ,a baya san da Mahaifiyar sa ta rasa ranta sanadin sa an kai sa kurkuku domin mahaifinsa da kansa ya kai sa to amma komi ya zo ma sa da sauk`i sakamakon ba ya cikin haiyacinsa sann Madaki da kansa ya kasa ya tsare har aka fito da shi, motsin da ya ji a kusa da shi shine ya dawo da shi daga kogon tunanin da ya fad`a, Yarima Ishmal ne ya lek`o da kan sa ta k`ofofin k`arafunan da su kai ma su gatanga ya ce da shi,"Ya Kai matashin kuma jarumin saurayi kar ka bada Imani ga samartakarka,ko k`arfin damtsen da ka ke da shi,domin hakan ba madogara ba ce mai kyau a gare ka,domin a yanzu kuma a halin da ka ke a ciki Babu wani mutum a tare da kai face Ubangijin ka,shi kad`ai ne ke ji da ganin halin da ka ke a ciki,shi kad`ai ne zai saurari dukkanin buk`atar da ka ke da ita,kuma shi kad`ai ne zai iya taimakon ka ya fidda ka daga cikin tsaka mai wuyar da ka tsinci kan ka a ciki,ka rok`e shi zai amsa ma ka ",kyawawan idanunsa ya d`ago ya na mai sauke su a saman Ishmal hakanan ya ji wata natsuwar zuciya game da abinda ya fad`a,, hakanan ya ji zai iya d`aukar shawarar ko yarda da duk abinda ya ce da shi,sakamakon dattako tare da haibar da ya gani kwance a saman fuskarsa,k`afar shi d`aya ya jawo da k'yar wacce ta samu gocewar k`ashi ya tankwasar da ita yanda zai iya aje ko durk`usar da gwuiwowinsa a k`asa badan kasancewarsa babban jarumi kuma Sadauki ba da sai ya kwartsa ihu sakamakon azabar da ta ratsa ko wacce jijiya,k`ashi da kwakwalwarsa, sai da ya rufe idanunsa na wani lokaci tunkuna ya d`aga kansa Sama ya na mai kallon azarun da akai rufin saman d`akin kurkukun da su da nufin kallon sararin samaniya ya k`ara da d`aga hannayensa Sama da cewa","Yah Allah mai Sama da k`asa,wanda ke da iko akan Komi mai zarrar da Babu kamarta,mai fidda rayayye a cikin matacce,Allah dan sunayenka tsarkaka, dan hasken zatinka, gani cikiin wani hali mawuyaci,ba ni da madogara sai ta ka,ina ma rok`onka da ka kasance da ni kuma ka taimake ni,ka ba ni mafita game da wannan jarabta ko k`addara da ta riske ni ,lalle ni ba ni da tsimi ko dabara sai abinda ka zartar a kai na",ya k`are ya na mai sauke hannayen sa tare da lumshe idanunsa,"Da kyau jarumi uban jarumai na ji dad`in abinda ka yi yanzu,haka kowanne muslumin kwarai ya kamata ya kasance a duk sanda musiba ta same shi ya kasance ya na mai k`ank`antar da kan sa a wajen Ubangijin sa,gami da sakankancewa da shi kad`ai zai magance ma sa komi, kuma ya jarabce shi ne domin ya auna mizanin imaninsa hakan ne kawai zai ka wo masa maslawa cikin sauk`i da kuma gaggawa,ka sani ya kai wannan jarumin a halin yanzu zan iya cewa ka na cikin jarabawa ne kusan irin wacce a ka jarabci Annabi Yusuf,ka natsu ka tsaida zuciyarka wuri guda kar ka bari su rud`e ka ko su tsorata ka,kar ka yarda ka bari su ja ka aikata abinda zai sa Kai dana sa ni domin su d`in su kasance gafalallu kuma watsatstsu",....ya dakatar da shi da sauri,"Waye kai,me ka sa ni game da wad`annan ashararun mutanen,me ka ke yi anan ina nufin laifin me ka aikata da har suka ka kawo ka nan ?",shine abinda ya fara fita daga bakin Yarima Haisam"Hmmm abun zai ba ka mamaki idan ka ji cewa ni Yaya ne ga Sarauniya Junayyah,ni da ita Uwa d`aya uba d`aya mu ke "...." To amma ya akai ka ke zaune anan wurin ?",ya katse shi da sauri,"wani sirri ne da ba zai yiwu ka ji shi ba domin ya fi k`arfin shekarunka,kan ka ba zai iya d`auka ba","Kamar ya ni yanzu da akwai wani abu da zai gagare ni d`auka a yanzu","wannan dai ya fi k`arfika kuwa amma na ma ka alk`awarin zan sanar da kai wani abu da ga ciki in sha Allah, indai har mu na tare anan,amma tashi ka ci abinci ka sha ruwa sai mu ci gaba","Ba damuwa Zan jira har lokacin da ka shirya"