SHINGEN KAUNA

CHAPTER 3

by @khairatup01

SHINGEN ƘAUNA.
Khairat.
Wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01
paidbook.
Free page 3.

Abin kamar wasa ko a mafarki yau saura sati biyu bikina da JJ. Ta ko ina shirye-Shirye ake yi abin gwanin ban sha'awa. Wallahi ni kaina na san na gyaru ba kaɗan ba. Fatata har wani sheƙi take yi. Kayan gyara kuwa daga kamfani bojuwa herbs na siya ko in ce Aunty Ramlat ta sai min.In ya zo wurina da ƙyar yake tafiya ya yi ta ƙoɗa ni. 

An yi sabgar biki lafiya an gama lafiya gidana a tudon yola gaskiya iyayena sun yi ƙoƙari sosai na yi mamaki ƙwarai Umma ta zuba mini kayan kitchen daidai ƙarfin mu kuma masu amfani. Kujeruna coffe ne da rastin brown sun sai mi tv plasma ana saka mini dish falon yayi kyau sosai fentin fari ne amma an saka labubalaye coffe da ma duhu da mai haske ga hasken wuta falon nan dai fes da shi. 

Bani da ƙawaye daman Summaya ce kawai ta rako ni sai wata Amina a bayan layinmu islamiyar mu ɗaya da ita. 

JJ da abokan sa suka shigo siyen baki daman a falo muka yi zaman mu na ja lulluɓina na kuma kulle fuskata. Jj da neman magana gabana ya zo ya tsugunna yana son ya buɗe min lulluɓi na riƙe mayafin ta ciki da hannu da kyau ina murmushi. 

Yace "Kai ku ji min mata wai ni zata ma kunya? Ba zan yarda ba gaskiya ki sakar min na duba na ga fuskar matata."

Abokin sa Aminullahi yace "Gaskiya amarya kar ki buɗe sai ya siya."

"Ko nawa ne a saka min zan ƙara siya."

Muka yi dariya gabaɗayanmu.

Amina ce tace "Mun siyar Dubu ɗari in an siya a bamu hakkinmu mu baka izini."

"Aminulllahi ba su ɗari biyu kowacce ta rike kasonta su tashi su bar mini matata ni kowa ma ya tafi na gana da matata haba." Ya faɗa yana hararar kowa da ke wurin.

Aminullahi yace "Shi kenan mun bar ku lafiya. Amaren mu muje ko?" 

Suka yi min sallama suka tafi dukan su. Aka bar ni daga ni sai Jj.

"Matataaaa." Ya faɗa yana jan sunan da tsayi da sigar tsokana. 

Ban iya ba shi amsa ba ya tashi ya kama ƙugu yace bara ki ga ni. Kawai ji na yi ya ɗauke ni a hannunsa yana juyi da ni a tsakar falon nan. Na dinga masa magiyar ya sauke ni amma bawan Allahn nan bai sauke ni ba. Na sa mai kukan shagwaɓa ina dukan ƙirjinsa.

Yanzu kin shirya tarbata ko yaya?

Na shirya sauke ni don Allah.

Sauke ni ya yi na zauna kan kujera ina haki. 

Da kan sa ya kawo komai tare muka ciyar da juna kafin ya riƙe hannuna ya kai ni ainihin ɗakinmu, ɗakin yayi min kyau sosai da sosai fari ne a ciki komai hatta labulayen ɗakin farare ne masu rufi biyu da mai kaurin da mai shara-shara. 

"Ɗakin nan ya yi kyau abar ƙauna. Ya yi kyau sosai Allah Ya sakawa su Umma da alkairi."

"Amin." Na faɗa cike da jindaɗin kalamansa.

Ki zo muyi wanka muyo alwala mu zo mu raya sunna kuma.

Na harare shi waye zai yi wankan da kai?

Ke NadeeyaJabir.

Ya kan kira ni da wannan sunan a lokuta mabambanta NadeeyaJabir. Kuma ina jindaɗin sunan.

Sai da ya yi wankan nayi nima kafin na fito ya ciro min sleeping dress mai kyau a ido. Haka na saka na ɗaura zani na saka hijabi ya ja mu sallar.

Bayan mun idar ya yi mini tambayoyi game da addini na ina ba shi amsa.

Lallai matar nan kina da ilimi ashe ai na samu malama.

Na ɗauka ma zai min wani abu sai na ga kawai ya rungume ni mun kwanta bayan ya tofe mu da addua'a ya ce "mu kwanta mun gaji kuma gobe na san za a sha baƙi."

"Haka ne.Allah Ya tashe mu lafiya."

"Amin."

Misalin ƙarfe tara na safe na tashi. Na tashi da niyar ɗora tukunya ne. Hakan ya saka na suri silifas ɗina na sauka ƙasa. Gidan na kuma bi da kallo, ko ina sai da na shiga. Ɗakuna uku ne a ƙasa babba ɗaya sai sauran ba wani girma sosai ne da su ba. Sai kitchen da wani banɗaki spare a tsakiyan ɗakunan biyun da ke ƙasa. 

An yi dinning area an zub a masu kyau kuwa. Wurin ajiye tv ya burge ni sosai. 

Zan shiga madafi na ji kamar ana taɓa gate. Ashe da akwai maigadi. na leƙa ta taga sai na ga ƴan gidanu Jj ne. Tun kan su buga na isa na buɗe musu.

Gabaɗaya suka soma gaishe ni Aunty Nadeeya ina kwana. Ba wai na girme su ba ne aa tarbiyar su ce a haka na zama matar wan su dole na zama Auntynsu.

Abla da Afif suka shigo da kuloli a hannunsu. Sai Samir da ya shigo daga ƙarshe da flask ɗin tea.

Bakina kamar zai yage na ƙarbe su. Komai kan dinning suka ajiye suka dawo muka zauna. 

Nan muka sake gaggaisawa da juna suna tsokanata ban dai biye musu ba na tambayesu matan gidan suka ce duk suna lafiya lau suna gaishe ni. 

Tashi na yi na koma cikin kitchen ɗin na duba cikin fridge na samu lemo da ruwa a ciki kuwa. Haka na sako a cikin tray na kai musu falo.

"Maza ku sauko ku sha ruwa."

"Aa Aunty Nadeeya mu a ƙoshe muke tafiya ma zamu yi Alhaji ya ja mana kunne kar mu zauna a yadda yace ma Yaya Samir ya miƙo mu juya kawai."

"Gaskiya sharri kika yi ma Alhaji Abla."

"Da sassafe kun zo damuna? Na bar muku gidanku gidan ku ma ba ku bar ni ba."

"Haba dai Yaya ai babu batun rabuwa. " 

"Ato dai ku gaya masa babu wannan maganar kam. Barka da safiya."

Harara ya fara sauke min kafin ya ƙarasa saukowa yace da ni "Wata rana sai na make ki ni za ki wani cewa barka da safiya?haka ake gaida miji ne?"

Nayi dariya su ma suka taya ni sai da daƙune fuska ya zabga mana harara yace "Iye sabon salo wai ke nan kin samu sababbin ƴan wasa ko? Lallai ma sannun ku fitsararru."

Tashi na yi nace "Ka yi haƙuri mun tuba wasa muke maka ga abin kari nan Hajiya Mama ta aiko mana. Ka zo ka ci ku tafi tare ka gaishe mana da su."

"Korata kike yi matas?"

"Babu batun kora aljannarmu nake son ka je ka nemi albarkarta."

Jawo ni jikinsa ya yi ya sauke kwaɗayin da yake ta son saukewar ko kunyar su Abla baya ji. Ni dai na sunkuyar da kai na su ma suka kawar da kawunan su gefe." 

"Gobe ma ku ƙara zuwa gidan amarya da ango sai kun makance."

Suka ko sakar masa ihu sun san baya so ai kuwa ya fatattake su ya kora su zai zo ya same su ba da daɗewa ba.

Wainar masa ce miyar taushe ya ji nama da tantakwashi zuƙu-zuƙu sai ƙamshi miyar ke yi. Ɗaya fulas ɗin kuma dankali ne da kwai ga kuma tea da ya sha kayan ƙamshi na kamfanin jaysar_foods kayan ƙamshin nan duniya ne iya shaƙar shi kaɗai na ƙara maka so da ƙaunar shayi.(***)

Tare muka karya ya kuma umarce ni da na zo na taya shi ya shirya ya fita. Yadda ya ce haka aka yi na taimaka masa komai ya fito ras angonsa. Nima na yi wankan na shirya cikin atampa super ɗinkin zani da riga ya ko kashe mana kamera hotuna muka yi kala-kala sun yi kyau sosai. Ya yi min airdrop ɗinsu ya fita yana ce min "Kiyi status." 

Na harare shi na bi bayansa. A bakin ƙofa muka rabu da shi na rungume shi haɗe da yi masa sumba a goshi don na lura yana son hakan.

"Kar ki girka komai zan taho mana da abinci."

"Tam a dawo lafiya."

"Allah Ya sa."

Wunin ranar na yi baki kala-kala. Da na wurina da na wurin su JJ. Kafin dare na gaji. Bayan na yi sallar magariba na sake kwalliya na sauka kaya wando na saka da blouse mai kyau. Na gyara gashi na. Sai ƙamshi nake yi. 

*

Jj bai dawo ba sai wajen ƙarfe tara na dare. Na tarbe shi da farinciki tun daga falo ya yada zango kan doguwar kujera mai cin wurin zaman mutum uku ya jawo ni na faɗa jikinsa ya rungume ni tsam kamar za a ƙwace masa ni.

"Na yi kewar mi Habibtyna."

"Nima haka Habibina. Yaya ka baro su?"

"Kowa yana lafiya,duk sun ce a gaishe ki da kyau."

"Ina amsawa."

Ga kayan kwalam nan ki juyo mana mu ci yau ba ɗaga miki ƙafa zan yi ba ehe."

Na dalla mai hararar wasa nace "Yau na ga baƙona na wata."

Faɗo da mu ya yi daga kan kujerar. Yace "dan girman Allah? Bana son irin wannan fa."

"Da gaske nake yi maka fa. Ɗazun nan ne ya zo."

"Innallillahi. Gaskiya baki da mutunci ba ki kyauta min ba sam-sam. Ai da na sani jiyan ban tausaya miki ba. Ga shi ni na kwana a ciki."

Na kumshe dariyata na miƙe tsaye.ledar na ɗauka na je na juyo mana kaza ce sai turiri take yi na ɗauko kofi na kai na kuma komawa na ɗauko lemo da youghrt.

Ina kallo yana harara ta amma haka na basar na share shi na zuba masa komai ya ture gefe.Na kuma tura mai ya kuma turo min gabana na ajiye nace "Wai meye haka?"

"Bana ci fa."

"Aa gaskiya ka ci ka samu energy in ba ka ci ba ya za ayi ka iya da ni?"

Kallona yake yana neman ƙarin bayani. Da ido yake tuhumata.

"Wasa nake yi maka."

Hannu ya saka ya dungure mini kai "Ni za ki ɗagawa hankali?" 

"Afuwa my love."

Inda ana iya haɗiye masoyi da tabbas a yau Yaya Jj sai ya haɗiye ni, ban san yana sona har haka ba. Na ko ci ƙwa-ƙwa a daren nan.Kamar zai maida ni ciki . Na jigata sosai shi ya taimaka ya gyara ni ya kuma sauya zanin gadon ya saka cikin injin wanki ya kunna.

Ya saka sabo ya maida ni. Panadol ya bani na sha. Ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.

Zaman lafiya da kwanciyar hankali ake cewa ko? To tabbas ina samun fiye da haka a wurin Jj farin masoyina abin ƙaunata mai sona zaɓina. Wallahi ina son sa kuma ina fatan mu kasance cikin aminci da so da ƙaunar junanmu har abada. Bana jin akwai wani da zan ƙara jin son sa a cikin raina bayan Jj ba babu shi fa.

Wattaninmu biyar na ci gaba ma da zuwa makaranta. Naje gidanu ma na yini har gidajen yayyunsa mata da maza duk mun je. Ahalinsu mutanen kirki ne Wallahi mahaifiyarsu Allah Ya bata sakin fuska da jan mutane a jiki tamkar ita ce ta haife ka. 

Babban burina yanzu na samu ciki nima. 

Jj yana da kyauta amma ban san zai iya yi min babbar kyauta irin wadda ya yi mini ba. Bayan mun gama karyawa ne ya kirani ɗakinsa ya ce na zauna a kan kujerrar ciki.

Nan ya dinga ja na da hira muna yi. A nan ya ɗauko min mukullin mota ya bani ban fita daga wannan mamkin ba ya kuma miƙo min wata takarda original yace "Ƙarbi masoyiyata wannan gidan na baki shi halak malak mun gama komai a kotu sa hannunki kawai nake da buƙata. Sannan ina da wani sabon kamfani da na buɗe tun asali ma shi da sunan ki na buɗe sa wannan Alhaji ma ya sani. Ga takardunki nan ki adana. A gwamaja ma na bar maki wani gida haka na gayawa Yaya Kabiru ya saya miki rumfa a kwarri a zuba miki kaya ana kawo miki hakkinki.

Ban san kuka nake yi ba sai da na ji lallausan hannunsa a kan kumatuna yana share mini hawaye.

"Haba mana come on meye haka? laifi ne don na yi miki wannan a rayuwata ? Bayansu Mama da Alhaji waye yake da kusanci da ni sosai? Ko kwatan dukiyata ban baki ba wannan ni na yi niyar baki ba tambayata kika yi ba kuma sai da na yi shawara da su tukunnna suka bani dama sannan na baki. Don Allah kar ma ki soma yi mini godiya ba na so, ba na so Wallahi! Ni ke nake so ."

Rungume shi na yi kawai na saki kukan gabaɗaya a fili. Ya dinga shafa min bayana yana lallabani har na yi shiru. 

Ki zo ki shirya muje Gusto mu ci abinci.

Baka gaji ba Jj?

Aa ba gaji ba.Mu je ma sai na nuna miki ma gidan kuma a motar ki zamu tafi.

Yadda yace "Motarki" ɗin shi ya fi ba ni dariya. Ba tare da ɓata lokaci ba muka shirya abaya na saka baƙa mai ruwan ƙasa ta min kyau sosai. Zamana da Jj na zama wata hamshakiya na zama wata babbar mace in ka ga yadda na yi ƙiba nayi kyau na ƙara haske hutu na ratsani sai ka musa in ba wani mugun sani ka yi min ba. Lallai dace da masoyi daɗi.