SHINGEN KAUNA

Chapter 4

by @khairatup01

SHINGEN ƘAUNA
Khairat.
Wattpad:khairi_muhd.
Arewabooks:Khairatup01.
Paid book.
#500
free page 4.

Tun yamma muke yawo ni da shi har bayan isha na ji daɗin fitar nan sosai. A state road ne ma bai bari na fita ba ya faka daga can tsallaken nan na wurin bikin nan na Minna event. 

"Na ga ka faka ina zaka kuma?"

"Bara na ƙarasa valentino na siyo miki ice cream."

"Don Allah ka bari na ƙoshi Wallahi. Cikina ya cika. Bana so mu tafi gida kawai ka ji?"

"Aa gaskiya sai na siyo ni ina so."

"To na ji amma muje ka yi turn me amfanin ka faka tun a nan ni tsoro nake ji."

"Aa jira ni can ɗin babu daɗin fakin bana son na zo na kuma zagayowa ne."

"Amma duk da haka zaka iya ƙara kai mu gaba mana." Na faɗa a ɗan hasale ni kaina ban san dalilin hasalar da na yi ba lokaci guda kawai na ji zuciyata babu daɗin gabana faɗuwa yake yi kawai.

"Kayya. Ki daure mana yanzu fa zan dawo shalele."

Haka kawai ba don ina so ko na gamsu ba nace masa "To ka kula don Allah."

"Na ji ma'am."

Wayata na ɗauko na kunna data na shiga watsaap. Da saƙon summaya na fara cin karo tana min tsiya wai na daina hawa onlayin ɗin ma. Na ce mata ni lokacin  sukutum na mijina ne yanzu bani da lokacin ɓatawa a chatting. Ta turo min emoji ɗin zuciya tare da wannan ƴar magen me hoton zuciya biyu a ido. Na tura mata da gwalo. Fita na yi daga wurin saƙon ta na shiga lamba Jj. Tun da muka fara chatting nake bin saƙonin ina sake maimaitawa ina dariya. Saƙon sa na ƙarshe ne ya bani dariya na jiya yana kasuwa ni na je gidan Umma daga makaranta.

"Har wani tsokanata kike yi ko don kin je gun Umma?" Zan rama ne yarinya."

"Sai dai ka rame wowul."

"Hah! Hadda gwalo ƴar nan? Lallai yau za ki yi bayani sai na turo miki kyankyasai da kunnami sun cije mini bakin tsiwar nan da tsokana."

Na tura masa da dariya. 

Na ce mai "Ai shi kenan ka turo su ɗin sai ka gaya min da wa zaka kwana yau.?"

"Na tuba matas ai ke ce gadon mahaɗin baccin in kika bar ni  a gantale ai an samu matsala."

Na tura mai da dariya nace "Da wuri haka abokin kyakyasai?"

"Yaushe za ki taho ne?  Nima yanzu zan koma."

"Anjima in Baba ya dawo na jima ban gan shi ba."

"To ki zauna ma kawai zan biyo mu tafi tare."

"Tam sai ka zo."

"Ina son ki."

"Nima ina son ka."

Wata iriyar birki aka ci wadda ta saka ni sakin wayar ma daga hannuna a tsorace. Zabura na yi kaɗan na soma ƙoƙarin leƙawa na ga abinda ya faru.

Ƙirjina dukan uku-uku yake yi sosai. Fita na yi tun kan na isa jama'a sun taru a wurin tazarar bai fi taku uku ba ne tsakanin wurin da inda nake a cikin mota. Gefe na kalla na ga ledar valentino da icecram sun yi na su wurin. Wani irin sarawa kaina ya yi lokaci guda na dafa shi nace "Innalillahi wa inna illahir raj'un." Tun kan na isa na gama aminta cewa Jj ne mota ta buge.

Mutane na ta haya-haya ana zagaye da shi.

Kutsawa na yi na shiga tsakiyar su.

Sandarewa nayi a wurin kawai murza idanuwana na fara yi ina son tabatarwa kaina ba shi ba ne.

" A kai shi asibiti akwai ragowar numfashi a jikinsa." 

Faɗuwa na yi ƙasa  gabansa na kamo shi na ɗora kan sa a kan ƙafata. Jini ne kawai yake fitowa daga kan sa fuskar nan ta wanke da jini sosai kamar an yanka kaza.

Bakinsa ma jinin yake fitarwa. 

"Ko matarsa ce?"Wasu suke faɗa wasu kuma cewa suke yi "Wacce ce wannan?"

A hankali a ƙasan maƙoshi nace "Jj tashi ba na son irin wannan wasan tashi mu tafi dare yana yi. In so ka ke ka tsorata ni na tsorata ka tashi ka cinye wasan ni na faɗi.

Wani ne yace "Hajiya baya cikin hayyacinsa asibiti ya kamata mu kai shi. 

Aa Malam wasa yake min tsokanata yake yi, yanzun nan fa ya ce min zai dawo in jira shi wane baya cikin hayyacinsa? Kar ka kuma faɗa.

Wata ce ta yi ƙoƙarin rabani da jikinsa don in suka bar ni za a iya rasa shin.

Riƙe ni tayi gam ina son fusgewa tana riƙe ni. Jj ne fa ake magana a kan sa mijina abokina yayana. Innalillahi wa inna illahir rajun.

Ina jin suna cewa a nan lamiɗo crecent akwa asibiti ya fi kusa nan za a kai shi.

Na ce da su ku sa shi a bayan mota waye ya iya tuƙi ya kai mu ba zan iya ba.

Haka aka saka shi a baya nima can na zauna na ɗora kan sa a kaina ina ganin yadda ƙirjinsa yake sama yake ƙasa jini bai bar zuba ba. Ɗankwalina na saka na tare wurin da ya fashe jinin ke zuba.

Mutumin yace "Ki kira wani namijin ba za ki iya yin komai ba." 

Na san gaskiya ya faɗa wayar na nan a ƙasa a miƙo min.

Yana bani hannu na rawa na kira lambar Yaya Kabiru shi ne babban yayansu dukan su.

"Salamu alaikum NadeeyaJabir yau an tuna da yaya ne? Ina kwarkwar ɗin mijin na ki ya bar ni nan a gatale ya ce zaku zo kuna nan lugard road?" 

"Wayyo Allahna!" Na faɗa cikin kuka na ma kasa yin magana. Wannnan wacce kalar ƙaddara ce?

Ta ciki sai Hello!Hello!Hello! Yake faɗa dole ɗaya mutumin ne ya ce masa "Yayi hatsari ne mijin matar nan muna hanyar kai shi asibitin NOL ne nan lamido crecent." 

"Na gode nima ina kusa gani nan zuwa."

*

Yaya Kabiru ne ya kira Alhaji da sauran ƴan gidasu yace su haɗu a can Jj ya yi hatsari mota ta buge shi.

Muna zuwa aka yi ciki da shi hannuna ya riƙe gam-gam har yau in na tuna da riƙon da ya yi min sai na yi kuka. Kuka rabuwa da masoyi kukan sabo.

A nan na zauna a ƙasa bani da sauran ƙarfi.

Mama ce na fara jin maganarta suna tambayar ko an kawo Jj. 

"Ga matarsa nan." Ta nuna musu ni.

Da sauri Mama da Aunty Ramlat suka iso inda nake.

Iya jinin da suka gani a jikina ya nuna musu ba ƙaramin abu ba ne ba.

Mama ta jijiga ni Nadeeya..

Mama wasa yake min ko? 

Ai ba shi ba ne? 

ki gaya masa ya daina yi min irin haka ba na so zan dain kula shi gidanki zan taho.

Mama kin ga fa jini , a kan sa fa yake fitowa sun ƙi shiga da ni na gan sa. Mama na gaya musu..... na hango Alhjji ta tashi ina subalewa na kuma faɗuwa ƙafafuwana sun yi sanyi babu ƙwari a jikinsu.

Tausayina ya kama su.

Alhaji da kansa ya ce min.

"Haba Nadeeya, ke fa musulma ce kin san tawakalli ai?" Na gyaɗa masa kai na.

"Tashi daga nan zo ki zauna in sha Allahu babu komai da zai faru da Jabiru."

"To Alhaji amma ka je ka ce ya daina yi min wanann wasan ya tashi." 

"Zan gaya masa amma sai kin zauna a nan."ya nuna min kan wata kujera na zauna.

Mama ta rungume ni cike da tausayin halin da ta gan ni a ciki. Aunty Ramlat ma tausata take yi kamar dai n  fi kowa buƙatar lallashi   a wurin.

Jj na mutane ne,mai zumunci ne mai girmama mutane ne haka ya saka jama'ar gidansu da abokasa suka cika asibitin nan har waje. Baba,Yaya Muhammad da Umma da auta ma duk sun zo. Kowa addu'a yake yi wa Jj ya samu lafiya. Ajiyar zuciya kawai nake saukewa akai-akai. Hawaye kawai nake yi ina jijjiga ƙafafuwana wai Jj ne a nan bai san waye a kan sa ba tabbas ɗan adam ba kowa ba ne , sannan lamarin ubangiji sai shi. Yanzun nan fa muke tare amma lokaci guda komai ya sauya a cikin ƙiftawar ido.

Wata nas ce ta fito da sauri tace"Nadeeya, Mama da Alhaji da Baba suna ina?"

Da sauri muka amsa mata "Gamu."

"Yauwa ku zo ciki."

Har rige-rigen tafiya ake yi.

Jj na hango ana goge masa fuska, an naɗa masa bandeji a kai. Kallona yake yi kallon da ya tsorata ni da ƙyar na ƙarasa kusa da shi idan sa ma ya kumbura a rufe yake da ɗaya yake gani.

Ban san me yake cewa ba sai da na sunkuya daidai saitin bakinsa na ji me yake cewa "Ina son ki Nadiya. Am sorry ban cika alƙawarin rayuwa da ke ba..." 

Na yi baya nace "Me kake cewa ne haka?babu abinda zai same ka da kai zamu yi rayuwa tare zaka warke."

Ya kalli iyayensa yace " Ku yafe min in har na taɓa saɓa muku."

"Baka mana komai ba. Allah Ya baka ikon wucewa lafiya. Ni na yafe maka duniya da lahira."Alhaji ya faɗa bakinsa na rawa.

Mama ma addua'a ta masa ina jin yana basu amanata kuma yace kar wanda ya ɗaga min hankali ko ya tada fitina bayan tafiyarsa. Ya roƙi Baba da ya bar ni na yi kasuwanci na ci gaba da kula mai da ofishinsa.

Ya kamo hannuna yace" Ina son ki!." Bai saki hannuna ba na ji yana ta ambatar kalmar shahada yana yi ina maiaita masa. Kawai ji na yi yayi shiru amma hannuns a cikin nawa.

Da ɗaya hannun na jijjiga shi "Jj ya ka yi shiru?  ka ci gaba mana ina jin ka. Ma...ma...mama ya yi shiru ko bacci ya yi?"

"Bacci ya yi Nadeeya Allah Ya karɓi bakwancin sa. Allah Ya jikan ka Babana."

Hannuna na saka na kuma sakawa a cikin hannunsa na ce "Zai kama.Ka kama su gani Jj ka nuna musu bacci kake." 

Alhaji ne ya fita ya sa aka zo aka min allurar bacci don na ƙi bari ma a zo a taɓa shi.

Babu zuciyar da take jin zafin mutuwa sai ainihin wanda aka yi wa rashi. Ina jin ana zancen mutuwa ban san haka ɗacinta yake ba sai da na rasa bangona. Sai da na rasa ainihin masoyina. Mutuwa bata da sauƙin mantawa lokaci-lokaci zata dinga dawo maka, zata dinga kuma sukar ka a zahiri da kuma baɗini. Na gama yarda cewa ba zan iya ci gaba da rayuwata kamar da ba. Tunda na rasa Jj na rasa asalin kaina.

Yau an wayi gari kwanan Jj uku a cikin ƙasa a kwance cikin ainihin gidansa na gaskiya mu ma in lokacin mu ya yi can za mu tafi. Shi da ya riga mu tafiya ba sauri ya yi ba mu da muke raye ba jinkiri muka yi ba mu ma muna jiran lokacin mu ne. 

A gidansu Jj na yi takaba. Ina tausayin Mama sosai duk da bata fitowa ta nuna ainihin raɗaɗin rashin ɗanta da ta yi , amma muna gani a cikin idanuwanta. Dole na sauke ta wa damuwar ,dole na haƙura na ke ɓoye ainihin abinda nake ji a cikin raina. 

Ƙunci ba zai hana na ci gaba da rayuwa ba duk da rayuwar ba zata zame mini mai daɗi da sauki irin ta da ba amma dole ne na ci gaba da rayuwa musamman don mutanen da nake tare da su.

Na koma makaranta duk da su Summaya sun wuce ni da shekara ɗaya  don ni bayan mutuwar Jj ban koma ba. Sai yanzu da na ji don raddin kaina zan iya ci gaba da rayuwa. 

Na samu kason gado daga cikin dukiyar Jj sosai. Jj ya tara dukiya mai tarin yawa ta gumin sa kuma halak ɗinsa. Bai dogara da Alhajinsa ba tun asali mutum ne shi mai ƙwaƙwalwa da nasibi.Komai ya sa wa hannu sai Allah Ya buɗa masa an ƙarba da hannu biyu. Dukiyar da na samu bata rufe min ido ba , kuma bata sa na manta da ni asalin ƴar Malam Nazif ce ba. 

Ina da motoci , ina da gidaje , ina da plaza sannan ina da rumfa a kwari. Adadin kuɗaɗen da suke cikin account ɗina ma ban san su ba ni ma. Hakan kuma bai ɗora min girman kai ba. Sai dai ni ɗin mai tsiwa da yawan magana da tsokana na ɓata a karan kaina na manta yadda ake walwala ,na manta komai nima na san na sauya rashin Jabir a rayuwata ya rufe mini dukanin wata ƙofa ta farinciki da walwala.