TAEESH

CHAPTER FIFTEEN

by @zinariya0102

Da hanzari nurse Kubra ta tare ta, jikinta ta faɗa a sume, gudun faduwa, sanin illar faɗuwa ga babba dalilin jin furgici ko razani na iya sawa ya kamu da mummuman ciwo wato stroke. Cerebrovascular Accident (CVA).

"Subhanallah" ce war sarki Suhaid, da sauri likitocin suka nufi kanta, don Bata taimakon gaggawa.

"ku ɗaukota" da sauri Abubakar ya saɓata a kafaɗa, suja yi room ɗin da ke kusa da na Ciroma, cikin rarrashi Abubakar ya bar ɗakin, doctors suka fara aikinsu.

Su shamaki kuwa tunda suka ga an wuce da Hajiya Binta a sume, suka san tabbas akwai babban al'amari, fatan samun sauƙi kawai suke ga ahalin masarautar.

Dr. Umar ne ya dawo gurin mai martaba, ya durƙusa yana yi masa bayani cikin ladabi "Allah ya baka nasara, kar ka damu in sha Allah duk za su samu lafiya, ita Hajiya furgici ne da tsoro ya sa ta suma ba wani abu ba ne" Sarki Suhaid kai kawai ya ɗaga alamar ya ji, sannan ya ce " dole a shirya fita da Ubaid waje, don bazan sake gangancin da na yi a baya ba" daga haka bai sake magana ba.

Dr. Umar ya ce" haka yake mai martaba, Allah ya bashi lafiya ya sa kaffara ne" laɓɓansa ne kawai suka motsa alamar ya amsa.

Fulani Tagabas na isa, ta ji mummunan labari a zahiri ta nuna alhini, su Ɗan maje, Shamaki, matawalle na ganinta, suka hau kai gaisuwa da girmamawa ga mai ɗakin mai martaba, kamar dole ta amsa tana shan ƙamshi, ɗakin da Ciroma yake aka nuna mata, babu mai shiga sai manya.

Tura ƙofar ta yi, ta shiga cikin tashin hankali (a zahiri) "Ranka ya ɗaɗe, ya jikin nasa" ɗagowa sarki Suhaid ya yi da kansa, ganin Tagabas ce yasa ya yi magana " wa ya ce ki fito?" a hankali ta zauna kusa da shi tana kalar tausayi ta ce" Allah ya ƙara maka lafiya daga airport nake ne na raka Fathiyya ta tafi, shine naga dacewar in zo in duba Ciroma tunda na fito, a gafarce ni mijina" ta ƙara tana sunkuyar da kanta ƙasa.

Jin bai ce komai ba ta kuma faɗin "ya mai jikin?" a hankali ya ce "Da sauƙi za a ce Hafsa don Ubaid na jin jiki" ta ce" innalillahi wa inna ilaihirrajiun me ya ke damunsa?" Sarki Suhaid ya ce" zuciya ce Hafsa, bansan me ya ke damunsa har ya ja masa mummunan ciwo haka ba" salati ta dinga yi cike da alhini ta fara magana " Allah sarki! Allah ya ba shi lafiya, ka kwantar da hankalinka ranka ya daɗe in sha Alah zai samu lafiya, idan ka na damuwa mu kuma ya kake so mu yi?" sai lokacin ya ji ɗan sassauci a ransa, zuwanta ya sa ya samu wacce ya faɗawa damuwarsa.

Ita kuma Hajiya Bintan fa, na ji ance ita ma babu lafiya yanzu da na zo?" ya ce" furgita ta yi da jin lalurar mijinta" sai da ta yinwani killer smile sannan ta ce" ayyah ai dole, miji fa a ce zuciya ta taɓu dole ta suma, da ni ce ma Allah ya kiyaye nasan mutuwa zan yi" furucin da ta yi sai da sarki Suhaid ya dara har haƙoransa suka bayyana. Ganin haka yasa ci gaba da faɗin: "hmmm ranka ya daɗe baka san irin son da nake maka ba ne, ina addu'a a kullum Allah ya sa na riga ka mutuwa ka binne ni da hannunka, akan ka mutu ka barni" hannunsa ya ɗora akan lips ɗinta ya na faɗin "shiittt a asibiti mu ke, ki daina wannan maganar, mu fuskanci damuwarmu ta rashin lafiyar ɗan uwana" ta ce" ranka ya daɗe, idan ina tare da kai wallahi manta komai nake, har kai na ma" tashi ya yi fuskarsa cike da annuri ya ce" mu je mu duba Binta" murmushi ta yi tana faɗin "an gama ranka ya daɗe" ita ta fara fita, da sauri dogarai suka hau zuba kirari da take musu baya haka aka rankaya zuwa ɗakin da aka kai Binta. Abubakar da Dawud ne zaune a gafenta, kanta a sama tana kallon sily, jin isowar Mai martaba yasa su Abubakar suka tashi tsaye don girmamawa.

Sarki Suhaid da Fulani Tagabas Hajiya Binta ta gani, abin da batai tsammani ba, don basa ga miciji tsakaninsu kowacce tana ji da isa da taƙama. " Barka da zuwa ranka ya daɗa" Hajiya Binta ta faɗa, tana daga kwance, drip ɗin yake kallo yana faɗin " Ya jikin naki" ta amsa "da sauƙi ya jikin nasa?" Tagabas ta amsa " Ciroma ya samu sauƙi, ya naki jikin?" ita ma ta ce "Alhamdulillah" Dr. Salim ya ce" ranka ya daɗe ta samu lafiya za ta iya komawa gida" dogarai da sauran hakimai ne suka ce " Ma sha Allah, an gaishe ka likita" Sarki Suhaid ya kalli Dawud da Abubkar cikin tausayi, ya ce "Ku kwantar da hankalinku Ciroma zai samu lafiya" suka ce "In sha Allah, ranka ya daɗe" duk da wasu manya ba ne amma akwai hankali da hangen nesa, don Abubakar shekarun sa ashirin, amma hutu da jindaɗi yasa sai a zata ya kai irin twenty-five years ɗin nan, Dawud kuwa fifteen yake, ɗan Hajiya Nafisa ne, Suhaid (Ameer) ne mai seventeen, amma tamkar wasu manyan samari.

Umarni Sarki Suhaid ya bayar Hajiya Binta ta koma gida don ta samu hutu, sai da suka koma ɗakin da Ciroma yake, sannan suka fito, ba a zaman jinya a kmc su Abubakar sun so zama, mai martaba ya hana, domin security dole suka tafi tare. A ka bar dogaran da za su yi gadi.

Tana tsaye a brander ta tana kallon jerin gwanon motocin da suka iso, ganin Sarki da tare da Fulani Tagabas yasa ran fulani Zaitun ɓaci, " Ashe wannan matar babbar munafuka ce, in je har part ɗinta don sanar da ita halin da Ciroma yake ciki, ta nuna min ba za a je dubiya ba, ita ta zage ta tafi" ƙwafa ta yi, tana barin brander'n.

Wannan zuwa da Tagabas ta yi ya ɓatawa su Fulani Zaitun da Amina rai, Rahama kuwa umarni kawai take jira, sanin dole sarki ya amince su je suga jikin nasa idan har basu dawo ba.

Mutum kawai ta gani tsaye ƙofar ta ta parlor, murmushi ta yi, ganin Zaitun ce, "hmmm Fulani Zaitun lafiya kuwa?" Zaitun ta kalli bororinsu, tana yi musu alama da su bar gurin, dukkan su suka watse, daga ita sai Fulani Tagabas. "Allah wadaran munafunci da munafuki" Tagabas ta haɗe rai, sannan ta ce "Zaitun ki shiga hankalinki, ni ba sa'ar yin ki ba ce, na fi ƙarfinki wallahi" Zaitun ta ce" dame kike taƙama sarauta, mulki, asali ko kuwa dukiya kinsan babu abin da za ki nuna mi, a hakan kike ikirarin haɗin kai tsakanin mu da ke, to babu wannan maganar mtsww aikin banza" zata ratsa ta gefen Tagabas ta wuce, ta ji an janyota, "Ke yarinya ce don haka na yi miki uzuri" ta tura ƙofarta ta shige.

Zuciyar Zaitun tamkar ta yi bindiga, direct sashin mai martaba ta nufa, ganin Fulani Amina da Fulani Rahama har sun iso, yasa ta kuma shaƙar takaici.

A nutse yake musu bayanin jikin na Ciroma Fulani Rahama har idanunta sun cika da hawaye mace ce mai raguwar zuciya. "Shigo mana Zaituna" ya faɗa yana ƙarasa sauke nauyayyen numfashi, don ba ƙaramin dukan zuciyarsa ciwon da aka ce yana damun Ciroma ya yi ba.

"Allah ya taimake ka ya mai jikin fatan da sauƙi" ya ce "Alhamdulillah da sauƙi amma gobe in Allah ya kaimu za a fita da shi ƙasar Singapore don a duba lafiyarsa yadda ya kamata" ta ce "yanzu abin har ya yi tsanani haka?" Fulani Amina ta ce "Ina tunanin Ciroma ya daɗe da ciwon cikin nan" sarki Suhaid ya ce "Tabbas nasan Ubaid tun muna yara ba ya faɗar rashin lafiya sai dai a gane.

"Ranka ya daɗe muna son mu duba shi kafin a fita da shi Singapore ɗin" kai ya girgiza sannan ya ce "Rahama kina mantawa da ku ne iyaye a wannan masarauta yawo bai dace da ku ba" Zaitun ta ce "eh da ke mu mune yawo bai dace da mu ba, amma ai Fulani Tagabas ya dace da ita, da yake ita Balarabiya ce tare ma kuka dawo" Sarki Suhaid ya murmusa sanin halin kishi irin na Zaitun, ya ce "ita ma airport ta je raka Fathiyya sai ta biyo ta asibitin, amma ba zuwan kai tsaye ba ne" Fulani Amina ta ce" uhmm ai wallahi ba wani adalci da ka mana, Talakawa dai ana musu, amma mu kam kowa yasan anfi fifita waccen matar akan kowa, kuma da sannu Allah zai mana sakayya" ta tashi ta na matsar ƙwalla ta bar parlorn, Fulani Zaitun ma da aka fama mata mikin da ke zuciyarta ta tashi tana faɗin " Ayyah! Fulani Amina baki san asirin Larabawa ba, ga shi dai wai bata ma sanar zata ba, amma bai ga laifinta ba, ranka ya daɗe ka sani adalci aka ce ka yi a tsakaninmu tunatarwa ce kawai" ita ma ta fice.

Fulani Rahama kuwa tausayinsa ne ya kamata, a hankali ta ce" ka yi haƙuri mai martaba, Allah ya huci zuciyar Sarkin Hauren Giwa, nasan kana cikin damuwa na rashin lafiyar da mai girma Ciroma ya ke ciki, ka yi haƙuri ka yafe mana" idanunsa da suka yi jajir don ɓacin ran maganganun da matansa suka gasa masa, kasa ce wa komai ya yi, kusa da shi Rahama ta koma, hannunta ta ɗora saman nasa ta shiga yi masa kalamai masu sanyaya zuciya, da tuna masa irin yadda Manzon Allah (s a w) ya yi haƙuri da matansa.

Sai da taga ya cire damuwa daga ransa sannan ta yi masa sallama ta nufi nata sashin.

Zaune take ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana amsa waya cikin harshen Larabci da gani da danginta take magana, Fulani Zaitun da Amina ne suka shigo, katse wayar ta yi, sannan ta miƙe tsaye, Zaitun da Amina kuwa suka haun zagaye ta kowacce fuska a ɗaure.

GARIN DUMAMA

Wasila ta ce" Yaya Sahura kallon mara hankali kike min ko hmmm, kinsan na daɗe ina dakon soyayya a zuciyata tun kafin nasan kaina nasan so don haka alkur'an Baba da ni yake zancen, ƙafar ki, ƙafata idan za ki koma, dole ne in je in yi musu kahedi".

"Ke dalla rufe min baki, har yanzu kina nan da shashanci da rashin wayo" Wasila ta kuma faɗin " kayyah-kayyah Yaya Sahura baki san yadda soyayya take ba ne hiyasa, daman ai Baba ya bamu labari, baki san mijinki ba shi ma bai sanki ba, sai da aka ɗaura aure, alkur'an da kinsan soyayya da ba za ki ga laihi na ba" Sanin gaskiya Kawu Tanimu ya faɗa musu yasa ta yi shiru, bata tankawa Wasila ba.

Har akai sallar magariba Malam Ali bai dawo ba, hankalin Wasila duk ya tashi, Ai da tasan wani lokacin yana kaiwa haka bata damu ba, Yaya Sahura ce ta ƙosa ta ce " ke A'i ina Ali ya tafi ne haka? har yanzu bai dawo ba" "Gona ya je Yaya ina tunanin ko aikin ne ya yi masa dare" suna hirar, suka ji yo kacau-kacau ɗin tsohon kekensa.

"Wai Allah daɗi alkur'an sai yanzu na ji daɗi, da na ji higowar hi" murmushi kawai yaya Sahura ta yi tana faɗin " mun gode wa Allah" "Assalamu alaikum" ya yi sallama.

"waalekumussalam sannu da zuwa".

Ganin Yayarsa ta dawo yasa ya cika da farinciki, tun zuwan da ta yi, ta ga TAEESH ta so ya mayar da ita, bata sake zuwa ba sai yau, "Yaya ke ce a garin namu yau?" ta ce " to ya za a yi tunda hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar, ai dole na zo in da kake Ali" dariya ya yi, yana kwance buhun dankalin Hausan da ya taho da shi.

A'i ta ɗauko tabarma a ɗakinta zata shimfiɗa masa, "Ke dakata banason gulma da munafurci watukun don ki ji sirrinmu hine kika wani ɗauko tabarma, to ɗaka za mu higa" ce war Yaya Sahura, jiki a mace ta juya ɗakinta, TAEESH da take dafa abu ta miƙe tsaye ta na tafiya, tana jikin gado tana ta tafiya ganin abin ɓarna da ta yi, Ai ta shigo ta zauna tana zabga tagumi, gaba ɗaya zaman gidan ya isheta.

Da labarin faɗan da aka yi ta fara bashi, idan ran Ali ya yi dubu to yau ya ɓaci, ƙarya da gaskiya haka Wasila ta karanta tana yi tana kuka, duk yunwar da ya kwaso ya nemeta ya rasa.

"Yanzu Ali wannan dangi sune dangin matarka? gaskiya kwata-kwata ba ka yi sa'ar surukai ba" ce war Yaya Sahura, cikin ɓacin rai ya fito daga ɗakin "Aisha! Aisha!!" da sauri Ai ta amsa tana fitowa. Yanzu abin da kuka yi kun kyauta kenan, ku tara min mutane a gidana, dambe a gidana" tunda ya fara faɗan kan Ai a ƙasa yake, bata tanka masa ba. "ah lallai ba shakka Ai wuyanki ya isa yanka, yanzu mijinki na faɗa ba za ki iya ba shi haƙuri ba?" Wasila ta yi sauri ta ce" tab bakisan matan garin nan ba, ai idan aka bawa miji haƙuri wai rainaka yake" "aikuwa dole Ali ya ƙaro aure wallahi sai Ali ya yi aure Ai ko kin ƙi ko kin so" abin ne ya yi mata yawa, shi bai ji ta bakinta ba, ya zo ya hau faɗa, kuma ba su barshi ba sun biyo shi suna ƙara zuga shi. Haƙurin take son ba shi, amma zuciyarta da bakinta sun yi nauyi.

Juyawa ta yi ta shige ɗaki, sai lokacin da samu damar fashewa da kuka. TAEESH na ta bacci tsaf-tsaf da ita.

Yanzu Ali haka ka koma a gidanka? Namijin ho-ti-ho mace ta raina ka innalillahi" ransa ya yi mugu-mugun ɓaci, kunya dai yau Ai ta bashi kunya.

"Ali yanzu haka zaka zauna mace tana juya ka, dole ka ƙara aure" ya ce "zan yi Yaya" ta ce" dagaske kake Ali?" ya gyaɗa kai don an kai shi ƙarshe yau.

Ayiririi yiriririi Allah na gode maka, burina zai cika, mu je ciki in sanar da kai, abin da ke tafe da ni kuma" suka koma ɗakinsa, tunda ya ji zancen gona ne yasa kansa sarawa, haka kawai ya ji Kawu bai kyauta masa ba, Yaya Sahura ta ce ni dai ban amince a siyar da wannan gonar ba, ya ce " yaya ni kam ba ni da ta cewa, duk yadda kuka yi shikenan.............

Zinariya ce✍🏻