1
by @nkds
SON ƘAUNA...🔥🏃💔
_An ƙaddara su su ƙaunaci juna, an ɗaure su da nauyin iyali, zuciyarsu ta fashe sakamakon ƙaddara.
NOTE
*Na sadaukar da wannan littafi Mai Taken SON ƘAUNA ga dukkan yaran da aka yasar a faɗin duniya: ma'ana sadaukarwa ce ga duk wani yaro da ya tsinci kansa a Rayuwa ba tare da wani nasa ba.*
Story & Written By
_Nainarh KD⁂𝒩𝓀𝒹𝓈❦♡_
Copy is not allowed.¡!
Ba kuma zan Lamunci a canzan labari kota wata siga ba.¡!
MARUBUCIYAR:
1. Sarauniyar Kyau
2. Tsantsar SO
3. Aneeserh (Innocent Girl)
4. Kin cuceni
5. Ranar biyan buƙata (rai ba'a bakin komai yake ba)
6. Ba Tabbas
7. Captain Ayusherh
8. Ummul-Jaannah
9. Ba Riba
10. So Dan Rayuwa
And Now
SON ƘAUNA!
01
Kaɗan daga cikin tarin tambayoyin dake kara-kaina cikin kwakwalwar kanta shi ne wace ce ita? Sannan cikin waye a tare da ita? Waye uban cikin? Shin ta wani hanya aka samar da cikin?
E tabbas tana da buƙatar sanin hakan domin ta hanyar sanin hakan ne zata sama amsar duk wasu tambayoyi dake jibge a kwanyarta.
Son tasan wacece ita da takeyi ba wai don batasan kanta bane ko kuma ta manta wacece ita a'a sam duk da dai kusan hakan ne amma da banbanci.
Wani ɗan ɓangare kaɗan na cikin Rayuwarta takeson sani ɓangaren da ya zama mafari na sabuwar ƙaddararta ɓangaren da ta kasa tuna komai a kai tun bayan farkawarta ta tsinci kanta a gadon asibiti ɗauke da ciki na tsawon watanni tara.
Tabbas ta shiga ruɗani, tashin hankali da kuma firgici domin duk iya kar ƙoƙarin ta a kan ta san gaskiyar abin da ya faru da ita shekara guda baya tun bayan barowarta daga garinsu amma abu ya cutura.
Ta yi kuka ta yi kuka sannan ta addabe kanta a kan ko ya ya ne ta samu ta tuna abin da ya faru har ta tsinci kanta da ciki haihuwa Yau ko gobe bayan tasan ita dai budurwa ce amma garin ya ya ta rasa wani ɓangare na tunanin ta sannan duk iyakar binciken Likitoci basu iya gano ko wacce matsala ba ko dalilin da ya sa ta sama shafewar tunani.
Gaba ɗaya duniyarta ta juya zuwa wata kalar duniya mai cike da tashin hankali tun da ta baro asibiti sannan ta shiga mota domin zuwa garinsu duk da batasan da wani baki ko wasu kalamai zatayi ma mutanen ƙauyensu bayani ba ta sani Mahaifiyarta zata iya fahimtarta to amma mahaifinta da ya kasance shugaban ƙauye fa ga kuma yayanta mai jan ragamar ƙungiyar nan ta fusatattun matasan ƙauyen nasu masu ɗaukar hukunci a hannu a kan duk wani abu da ɗan ƙauyen nasu zai aikata wanda ya saɓa wa addini da al'adarsu.
Ita kam bata da wani wurin zuwa in ba ƙauyen nasu ba sai dai tana fargaban abin da zata tarar acan ɗin.
“Ke Mata! Ke Matar nan ki tashi mana an iso inda zaki sauka!”
Maganar da taji a dodon kunnenta cikin tsawa-tsawa shi ne ya sa ta buɗe idanunta da suke lumshe sai dai sun yi wani irin ja, ta sauke ajiyar zuciya tana kai hannu ta shafa fuskarta da ta haɗa gumi saboda baccin da batasan lokacin da ya ɗauke ta ba sakamakon nisa da ta yi a Duniyar tunane-tunane.
Fitowa ta yi daga motar dama tun kafin ta shiga ta biya kuɗinta hakan ya sa ta ci gaba da jan akwatin kayanta dake tare da ita kwallin kwal ta fara tafiya tana ƴan waige-waige cikin sa'a kuwa ta sama abin hawa ta tare shi sai da suka daldale zai ƙari sa da ita har cikin ƙauyensu sannan ta hau babur ɗin suka kama hanya ƙirjinta yana bugun lugude.
A wannan ɗan taƙin ne kuma ta sama kanta da fara tariyo asalin wacece ita ina ta baro da kuma dalilin batinta garinsu zuwa inda zata iya.
Cikakken sunanta shi ne Emem wato Salama ko Zaman lafiya ma'anar sunan ke nan bisa ƙabilarsu, mahaifinta kuma Nsikak ma'ana Albarka ko Arziki kuma shi ne shugaba a ƙauyensu dake cikin wata ƙaramar hukuma cikin jahar Akwa ibom Nijeriya.
Kabilar Efik ko ace Ibibio ta kasance cikin Akwa Ibom da Cross River a Kudancin Najeriya sannan akwai wasu sassa na ƙasar da mabiya ƙabilar ke Rayuwa.
Sun kasance ƙarƙashin addinin gargajiya ne da aka fi sani da Ekpe ko Obon, amma a yau mafi yawanci Kiristoci ne.
Tsaurin Al'ada:
Ana da wani abu mai kama da fattening room ga ’yan mata kafin aure – ana koya musu al’adu, tarbiyya da kula da miji.
Idan mace ta yi ciki ba tare da aure ba, a wasu lokuta ana yi mata hukunci kamar korar gida, tsarkakewa ta al’ada, ko hana ta shiga wasu lamurra na addini ko al'umma.
Wani lokaci ana ɗaukar hakan a matsayin bala’i ko laifi da ke iya kawo wa iyali ko kauye matsala, don haka ana ɗaukar mataki mai tsauri.
Emem ta taso ita ce wurin Ɗiya ta huɗu a gidansu tana da yayyi maza biyu sai yaya mace sannan sai ita da ta kasance Auta.
A da a tsarin al'ada da ƙabilarsu namiji ya kan aure mace fiye da ɗaya musamman idan namijin yana da ƙarfin tattalin arziki da matsayi a al'umma. Amma: zuwa yanzu an sama sauyi namiji baya auren mace sama da ɗaya a tsarin ƙabilar.
Emem ta taso Yarinya ce mai cike da ƙiriniya da kuma kazar-kazar ga farin jini shi ya sa ta shiga ran da yawa na mutanen ƙauyen musamman da ya kasance mahaifinta shi ne shugaba a ƙauyen.
Tun tasowar Emem bata da wani buri da ya wuce na ganin ta yi karatu na boko mai zurfi duk da kasancewar ba kasafai mutanen ƙauyen suka saki jiki suna barin yaransu sunayin karatun bokon ba.
Sai dai abin yasha banban tun bayan tasowar Emem saboda nacinta da kuma kafiya ya sa mahaifinta a dole ya bari take zuwa makarantar boko da hakan kuma ya zama Alkhairi ga sauran yaran ƙauyen masu son karatu kamarta domin ganin shugabansu ya bar ƴarsa tana zuwa makarantar ya sa suma mutanen garin suka bari nasu yaran suke zuwa.
Bayan da Emem ta kammala secondary school ne kuma rikici yaso ɓallewa domin ta kafe a kan ba zata yadda a yi ma ta aure ba ita birni zata tafi karatu yayin da shi kuma Babban ɗan Mahaifin nasu ya ce aure zatayi musamman ma da ya kasance babban amininsa yana mutuwar son ta sai dai bai isheta da kallo ba dan karatu ne a gabanta da yake mahaifin yana tsananin son ta ba kuma ya ganin laifinta shi ya sa ya amince ma ta zataje birni ta ɗaura da karatun gaba da secondary haka kuma aka yi yayan yanaji yana gani a ka gama yi ma ta duk wani abu da ya dace na zuwa birni karatu haka ba yadda ya iya tun da an fi ƙarfinsa Emem ta tafi birni karatu zuciyarta cike fal da tarin kwaɗayi na yin karatu mai zurfi ko domin ta kawo sauye-sauye da dama ta fuskar zamani a ƙauyen nasu shi ne kaɗan daga burinta na son karatu mai zurfi.
Sai dai ba tare da saninta ba ashe wannan tafiya birni da ta yi shi ne zai zama mafari na buɗe war sabon babin K'ADDARArta domin kuwa cikin abin da bai gaza shekara ɗaya da barinta ƙauyensu ta tafi birni karatu ba Rayuwarta ta yi wani irin yin juyin kwad'o da kuma batasan ta ina zata fara ba a halin yanzu.
****
Lokacin da ta sauka a babur ɗin cikin hanzari ta nufa cikin gidansu cikin rakuɓe-rakuɓe domin kota kan yaran layi da suke ta faman ihun murna suna faɗin ga Emem nan ga Emem ta dawo daga birni batabi ba.
A kan Mahaifiyarta wacce da alama ihu da karaɗin yaran da zuwa yanzu sun biyo bayanta cikin gidan shi ne ya sa ta fitowa daga ɗaki domin tabbatar da abin da kunnuwanta suke jiyo ma ta sai kuwa suka yi ido huɗu da ɗiyar nata sai dai wani irin yanke wa ƙirjinta ya yi lokacin da idanunta suka sauka akan cikin dake jikin Emem ta zazzaro ido cikin tashin hankalin da ya gaza ɓuya a fuskarta ta ɗa ga hannunta dake rawa tana nuna Emem dake tsaye rakuɓe da gini kamar kace kyat ta arce saboda a matuƙar tsorace take musamman ganin halin da Mahaifiyar nata ta shiga da ganin abin da take tare da shi.
“Ku bani hanya naga Autana!”
Muryar Mahaifinsu da ta jiyo shi ne ya daɗa ɗugunzuma zuciyarta cikin fargaba da tashin hankali a rikice ta juya daidai lokacin shi kuma da ya sawo kansa ciki yana ci gaba da faɗin.
“Shi ne zuwa haka na bazata babu sanarwa....”
Sauran maganar bakinsa suka maƙale cikin razani ya zaro idanu ƙur a kan Emem a lokacin da ta juyo suka yi ido huɗu.
“Emem! Mene ne wannan?”
Fusatacciyar muryar Yayan nata da yake tsaye gefen mahaifin ya daki dodon kunnenta da hakan ya haddasa ma ta zubewa saman gwiwowinta domin a matuƙar razane take.
“Laaa Emem tana da cikin haihuwa, yeee za'a haifa mana jaririyar birni....”
Abin da yaran suke faɗa ke nan cikin ihu da karaɗinsu babu ruwansu suna tsalle da murna dan basu da hankalin da za su fahimci babban laifin da ta yi duk da ba'a san me zata faɗa ba.
Wannan kalamai na yaran shi ne ya ankarar da iyayen daga faɗa wa duniyar mamaki ruɗani da suka yi na ganin ƴarsu da ta tafi birni karatu ta dawo da ciki.
Nan take Akpan Bassey (Yaya Bassey) wato babban yayan nasu ya rufe ta da wani mahaukacin duka ko damuwa da cikin dake jikinta bai yi ba da sai da ƙyar a ka samu a ka janye ta daga wurinsa sai dai ya yi ma ta rauni sosai.
Ai kuwa nan da nan labari ya karaɗe ƙauyen a kan Emem ta dawo daga birni da cikin shege ai fa kamar jira a ke shikenan kuma ƙauyen ya ɗauka musamman ma da ya kasance sanadin karatun boko ta fita birnin har wannan abu ya kasance.
Sai dai duk wani irin abu da za'ayi ma ta domin ta faɗa gaskiya a kan cikin nan an yi amma Emem taƙi magana daga ƙarshe dai amsa guda take basu shi ne bata sani ba ita kam ba zata iya tuna komai da ya faru da ita ba tun bayan barinta ƙauyen. Sai dai sun ƙi yarda da abin da ta ce a ganinsu ma rainin hankali da wayo take nema ta yi musu banda haka shi cikin da kansa zai tsiro ne a tare da ita da zata ce hakan.
Ba tausayi bare tausayawa suke gana ma ta azaba da horo mai tsanani wai duk dan ta faɗa gaskiya a hakan ma wai sun ma ta da sauƙi ne saboda su mutanen gari cewa suke a koreta domin wannan abin da ta yi zai iya ja musu wani babban bala'i a ƙauyen.
Emem ta sha wuya fiye da tunani sai dai duk yadda a ka so domin jin wani bayani daga gareta abu ya cutura mahaifin ya ɗauki dogon fushi da ita ko inda aka ware ma ta take zaune baya kalla.
A wani dare ne kuma cikin tsananin tashin hankali Emem tana zaune Mahaifiyarta ta shigo Ɗakin cikin firgici da tashin hankali take faɗin ta gudu ta bar ƙauyen domin a kunnenta ta ji Bassey yana tattaunawa da wasu ƴan ƙauyen a kan zasu biyo dare kawai a kasheta domin abin da ta yi alamu sun nuna Babban bala'i ne ga mutanen ƙauyen, cikin tsananin damuwa mahaifiyar ta rungumeta tana faɗin ta gudu tun kafin su zo su kashe ta gwara ta tafi can wani wuri ta yi Rayuwarta.
Kuka shaɓe-shaɓe haka Emem takeyi suka rabu da mahaifiyar zuciyoyinsu suna tafasa na ƙunar rabuwa.
Gudu kawai take yi sosai ba saurarawa tun da ta fito daga cikin gidan nasu har ta yi nisa da ƙauyen bata ma duba inda take jefa ƙafafunta har ta nufa titi bata cikin hayyacinta tana tafiya tana waigen baya cikin rashin tsammani motar da ta taho titin ta yi ciki da ita duk da kasancewar motar ba gudu take ba sai dai yanayin yadda Emem ta shigarwa titin gaba ɗayanta bata lura da motar ba kuma duk yadda motar taso kauce ma ta abin ya faskara sai da suka yi ciki da ita, Emem ta zube a sume a tsakiyar titi daga nan bata sake sanin abin da yake wakana a duniyarta ba.