Page 20
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 20❤🔥
"Granny I'm serious I hate this country, ke ce kawai ki ka matsa akan sai mun dawo ,but tunda,mu ka dawo ban ga wani abu da dawowarmu ta amfana maki ba,tunda mu ka dawo Momy sai ciwace-ciwace ta ke, kullum ba ta da lafiya"...
"Gidan ku Na ce Nora,haka ake yi ma nagaba da ke magana dama,mene ne ya shiga cikin kan ki,ko kina son ki zama disobedient gilr ne?", Revered Anderson ya katse da tsawa.
"Ka ga kar kai mata tsawa,she is my granddaughter ,hankali da tunanin ta bai nuna ma ta amfanin jajircewar da na yi akan ku dawo ba".
" Eh duk da haka bai kamata ta yi magana da ke a cikin irin wannan lafazin ba dan haka ya zama wajibi ta baki hak`uri don Gobe kar ta kuma ko kuma ta fuskanci hukunci na".
Sai da Nora ta matsa har kusa Mom Rebecca sannan ta bata hak`uri, janyo ta jikinta tai ta na mai rungume ta tare da cewa,"Ba ki yi komi ba my love rashin sani ne amma ki sani iya ganin ku kawai da nake a idona abu ne mai matuk`ar muhimmanci a gare ni,ina buk`atar ku a kusa da ni,duk mace da ta kai shekaru kamar irin nawa ba abinda za ta so face ta rik`a yin tozali da `yan jikokinta a kusa da ita".
"Na fahimce ki Granny im sorry ba zan k`ara fad`ar irin zancena na baya ba", Nora ta fad`i ta na mai sake shigewa jikin Mom Rebecca.
" Yauwa ban tambayeka ya jikin Gloria yake ba,ina zuci-zuci in samu in iso kafin time d`in ganin patient ya wuce amma haka bai samu a gare ni ba sakamakon goslwo da ya rik`e ni".
"Mun samu damar ganinta,Jadeeda ce ma farkon shiga kin santa da k`ulafu cin uwa,tunda su ka dubata su ka ce tana cikin yanayin da zamu iya shiga mu ganta ta fara kuka, har twins Nora da Martin sun fi ta dakakkiyar Zuciya da ta shiga ta dad`e ta na yi mata Addu'a bayan ta fito sai su Martin ,Ni kuma lokacin da Na shiga time ya k`ure dole ganin ka kawai na yi na fito,amma jikin da sauk`i sosai domin sun ce yanzu a kowanne lokaci za ta iya farkawa".
" Thank God ,Thank you Jesus, thank you for what Haven done for us",ta fad`a ta na mai had`a hannayenta wuri guda idanuwanta Na kallon sama,kafin ta cigaba da cewa,"Na ji dad`in wannan labarin hankali na har ya kwanta",Mom Rebecca ta kai k`arshen zancen.
Jadeeda ce ta matso kusa da ita tare da cewa"Ba k`aramin relief na samu ba da na ji Doctorn ya ce Momy should be okay za ta samu lafiya ta warke mu koma gida,don da fari har ma fara jin dama bamu baro UK ba, domin sanda muna can Momy bata fuskantar irin wad`annan ciwace-ciwacen".
"Na ga alamun yarannan ba sa san zaman ku cikin k`asar ku ta gado ku ke ba,sai yanzu na K`ara tabbatar da gaskiyar Mom da ta ke cewa kowa ya bar Gida Gida ya barsa,ba Dan barin Nigeria da mukai ba da ba yanda za ai ku sa son wata k`asa fiye da ta ku a cikin ranku har haka ba,har ku ke jin zaman can ya fiye mu ku nan", Cewar Revered Anderson.
" Haka ne Revered nima gani nai ba wani relative nawa a kusa da ni na koma rayuwa kamar wacce ba ta da wani gata,shiyasa fa na nace har sai kun dawo,iya ganin ku kawai ma da nayi hankalina ya dawo jikina,Na daina jin kad`aice da kewar Pastor Emeka, duk da har yanzu mutuwarsa ba ta sake ni ba".
"Mom I'm sorry domin na gane kuskuren tafiyar da mu ka yi muka barki,Na rasa me ye ya shige min kai da har na biye ma Gloria mu ka kwashe wad`annan shekaru masu tarin yawa, ba tare da mun dawo Gida ba".
Shigowar Martin ce ta dakatar da su daga hirar da su ke Wanda a hankali sai ga Easter da kuma Uncle Richal ya biyo ba, sosai shigowarsa ta ba su mamaki, kar ma Momy Rebecca, kanta gadan-gadan yai da sauri ta dakatar da shi ta na mai cewa,Stop! Don't ever touch me,kar ma ka matso kusa da ni,kai mutum ne mai son kan shi da yawa".
Bai saurare ta ko kad`an ba har sai da ya dangana da inda ta ke yana mai cewa," Haba Mom ya za ai ki ce haka,ko kin ta`ba ganin inda d`a ya rabu da Mahaifiyarsa ai duk inda ya je zai dawo".
Da k`yar ta samu ta cire shi daga jikinta ,sai faman zabga mashi harara ta ke,cikin Girmamawa su ka gaisa da Revered Anderson Mijin yayarsa,sannan daga baya Nora ta gaishe shi,Kafin Jadeeda itama ta gaishe shi ,wacce tun shigowar shi ta fara tsalle murnar ganin shi,bai amsa ba har sai da ya janyo ta jikinsa,"My love fatan dai ki na lafiya ba ki bari firgici da tashinhankali ciwon Momy ya cutar min da ke ba ?".
Cikin farin ciki da jin dad`i Jadeeda ta rik`e hannunsa kafin ta bashi amsa da cewa,"Gaskiya Uncle miey hankalina ya tashi,Na ji tsoro sosai,amma yanzu komi ya wuce tunda Doctor Imam ya ce ta na samun sauk`i","Doctor Imam waye kuma haka ?",ya tambaye ta a tak`aice," Doctorn da Asibitin ya d`auko ne Dan ya dubata ya san me ya ke sosai da ba dan shi ba da yanzu ba mu san a wanne hali Momy ta ke a ciki ba".
"Oh thanks to the Lord Jesus da ya kawo ma na shi domin ya zama silar samun lafiyarta".
" To the best Uncle in the world ka samu wuri ka zauna ka bar wannan parrot d`in d`iyarnan ta ka ka zauna ka huta ga abincinan Easter ta zo da shi a zuba ma ka ka ci",Revered Anderson ya ce .
"A'a kai ma kasan inhar ina tare da My daughter ba Na gajiya haka kuma yunwa ba ta da tasiri a kaina,saboda ita d`in ta daban ce komi na ta na daban ne a gare ni"....
Nora ta katse shi ta hanyar kiran sunan shi," Uncle ni fa,ba fa ita kad`ai ce Daughter d`in ka ba",ta yi Maganar cikin shagwa`ba.
"Wane ni Nora Kema ta daban ce a wurina,in ina kiranta da Princess ke kuma bari mu ga da me zan kira ki", ya kai zance ya na mai tafiya dogon tunani
Turo baki Nora ta fara yi ,Wanda hakan ya sa Momy Rebecca janyo ta jikinta tana mai lallashin ta tare da cewa," Rabu da su, can wata rana zamu gan su a rana,shima Richal d`in ai ba wani Garin arzik`i ba ne ba,wai ma ya akai kasan muna wannan Hospital d`in kuma yaushe ka yanke shawarar dawowa k`asarnan bagatatan ba tare da wani ya sani ba,bayan mun kwashe sama da shekaru muna Kira da son ka dawo ka k`i ?".Momy Rebecca ta kai zancen ta tana mai mai da akalar zancen akan Uncle Richal da sigar tambaya.
"Momynah kenan Na yi niyar surprise d`in ki ne kawai shiyasa na yo wannan tafiyar ta bazata,na samu labarin rashin lafiyar Sister,hakan ya sa na ji dole ina son in dawo Gida in ga halin da ta ke a ciki,bayan jirginmu yai landing Martin ya fara zuwan min a rai don haka sai na Kira shi a time d`in ya ke sanar da ni ya na Gida yanzu haka ya zo yai Fresh up sai ya koma Hospital d`in kawai sai Na jira shi, har ya gama sannan ya zo ya d`auko ni mu ka taho nan".
" Hmmmmmm Richal kenan idon ka kenan sai yanzu sai yanzu ka tuna da Gida sai yanzu ka tuna kana da Mahaifiyar ,sai yanzu ka tuna kana da wasu ahali da su ke buk`atar ganin ka a kusa da su,shekaru har nawa almost five years tun mutuwar Mahaifinku ba ka sa ke d`ora k`afarka a cikin k`asarnan ba, Na dad`e da daina yi maka Maganar Aure na barka da hankalinka ka yi duk abinda ka ke ganin shine dai-dai a gare ka".....
"Haba Momy ya isa haka for God sake, yanzu ba ga shi na dawo ba,I'm begging you ki manta da komi,I promise hakan ba zai sake faruwa ba,kuma ga su Martin duk suna gun".
" Da alama ba kasan zafi da rad`ad`in abinda ka aikata min ba, Ni kad`ai fa na koma rayuwa,I live the whole yers lonely tamkar wata mara gata,kuma da ka ke Maganar Yara ai nasan da su,ina maka fad`a ne a gaban su dan su san abinda ka ke aikatawa ba abu ne mai kyau ba,ina iya iyawa akan in ga ka sauya amma hakan ya faskara,ba zan so wani a cikin su ya rik`a aikata irin haka ba,ko kasan sai daga bayanan Gloria ta dawonan da zama ita da Zuri'arta duk dan saboda ni,da ba dan haka ba da bansan ta yarda zan cigaba da gudanar da rayuwata ba",ta kai zancen ta na mai had`iye wani abu mai zafi da d`aci .
Zaraf Richal ya baro wurin da ya ke zaune ya iso inda Mom Rebecca ta ke zaune ya na mai duk`awa saman gwuiwowinsa,fuskarsa har ta fara canjawa ya ce,"Momy na rok`e k`i ,for the sake of Father Lord ki bar tada wannan zancen I swear to the Jesus name haka ba za ta sake faruwa ba,I promise zan zama d`a na gari zan yi duk abinda ki ka ce amma dan Allah ki bar bayyana fushin ki a kaina ,tsinuwar Yesu Almasihu za ta iya riska ta in har haka ta kasance,da gaske Na shirya yanzu zan yi Aure zan haifa maki Yaran da za su yi ta wasa a gaban ki ko Sweet Daughter ?",ya kai zancen yana mai maida hankalin kan Jadeeda .
Kamar wacce ta ke jira a sata a zancen haka ta iso ta na mai duk`awa kamar yanda Uncle d`inta ya duk`a kafin ta ce,"Da gaske Granny Uncle miey ba zai sake tafiya ya barmu ba kuma zai yi Auren kamar yanda ki ke so,ni da kaina ma zan samo masa macen da ta dace da shi,amma sai kin daina fushi da shi".
Allah sarki Zuciyar Uwa nan da nan tai sanyi sai ga shi ba a d`au wani lokaci ba har murmushi ta ke daga k`arshe ta ce da shi ta,"Ban ta`ba ganin irin shak`uwa da Soyayya irin ta ku ba,ina ganin yanda hankalin ta ya tashi saboda ina yi maka fad`a ko ita na ke yi mawa sai haka".
Murmushi su duka su kayi daganan Jedeeda ta fara sarving d`in su lunch d`in da Easter ta kawo ma su,suna nan har dare ,sai dai ba su sake samun damar da za su ga Gloria ba ,dole sai su ka hak`ura sai zuwa gobe da safe.