Thriller
by @maidambu41
ROYAL POLITICS
_AN YANKA TA TASHI!!!_
THRILLER Book 2
Idan ƙaddaranka ce ruguza zanzabira ƙaddara ta ce kare jinina! Ni Shago Ilu nayi rantsuwa da Ubangijina zan bawa zanzabira kariya ba iya zanzabira ba hatta takalmin Awatif sai na kare shi, kana da damar gudu ko ka boya, ni kuma zan farmake ka, kai da sauran shaidanun tsakiyar birnin zan yake ka zan kai ka kasa ka ajiye kalamai a duk matakin da kake ka boya ka yi gudu! Amma nasan tabbas zan farauce kamar yadda zaki yake farautar namun daji a dawa! Kaiiiii dan daudu mai boya a inuwar Mace fito idan har Uwarka da jini ta haife ka! Tsohon gaba ce idan kaso ka nemi sulhu idan kaso ka rike Awatif amma ka sake Uwar da Jariran suka samu tangard'a zanzabira zata yi ja madadin farin wata za'a samu jar wata na rantse da Ubangijina wannan shine sakona
Ƙaddarata.
Tun daga ranar da kome ya faru, kaf zuriar Masarautar Zanzabira tare da bloodline na Yayari suka san da cikin jikina, na daina barci cikin kwanciyar hankali sai Ummi tayi da gaske a kaina nake barci, haka yasa ta kara komawa wurin Baba titi, ya bata rubutu, tana kawo min na fara barci idan na sha ko nayi wanka da shi zan yi barci. Idan ka ga na fita a gidan awo zan tafi gani ga Ismaha ikon Allah, domin tun da cikin ya fara bayyana magen nan ta tattara rayuwarta ta makalewa cikin jikina, da yake cikin wata na hudu, duk da azumi aka fara wani lokacin haka zai farka naga kanta a jikin cikina tana barci, idan kuma ina zaune zata shiga rigana ta jingina kanta a cikin, tayi ta juyi a jikin cikin. Da na gayawa Mai Babbar daki, ta kira Tasi'u ya haɗa ta da Baba titi dariya yayi ya ce mata. "Meramo Ishama ta samu shugaban mace ko namiji, zata kasance da su har ta koma ga Allah wannan shine dalilin mannewa cikin. Zaku ga abin al'ajabi zaku yi mamaki zaku yi farin ciki amma haka zai faru ne idan Allah ya so! Haka muke fatan kasancewa.
Bayan abinda ya faru, haka muka cigaba da azumi, ina gidan mai babbar daki da ta je har gidanmu ta gaya musu halin da nake ciki, ganin yadda Mai Babbar daki ta tsaya a kaina sai Iyayena suka mata yakanah suka dauke kansu akaina, amma duk bayan kwanan biyu suna zuwa ganina, har aka gama azumi bayan mun cika guda talatin cib kuma ikon Allah haka nayi.
*****
Tsit garin ya dauko ko nace dajin ya dauka, hawaye da yake cike da idanuna suka zuba. Dafe cikina nayi a karo na biyu da naji yayi wani irin juyawa! Kallon dakin nayi da yake cike da duhu. Marana ne ya daure min, tun kwana uku da suka dauko ni nake jin wannan yanayin! Ji nayi kukan ma yaki zuwa. Na mike a hankali na leka babu kowa a kangon, a hankali na tab'a kofar naji a rufe to ina suka je? A hankali na ga kofar ya bude nima, fitowa nayi na ga babu kowa a gidan. Kafana ne ya rike tam. Na ciza lips dina na tsaya ina nishi. Can da ya sake ni na shiga tafiya ko gabana, bana gani saboda duhun dare sai kukan kwari. Ganin na fita a gidan na ji kamar ana hankad'a ni ina wani irin sauri kamar xan tashi sama, gudu gudu sassarfar sassarfa haka nake tafiyar, ban san karfe nawa na dare ba ne, amma nasan nayi tafiyar da ta kai dole ne fara jin abu yana bin kafana! D'ago kai nayi sama ina kallon garin yadda yayi duhu. "Yaya ba zaka zo ba? Yaya kana ina?" Na fada a matuƙar gajiye."
Haka na cigaba da tafiya a hankali ina jin ciwon na ta'azzara, kuma na kasa tsayawa. Haka na cigaba da tafiya har zuwa rabi da kusan kwatar dare. Hannuna na saka na shirfe zufar da take karyo min wanda ya kara min hango nisan daren sama da kowani dare a rayuwata. "Yaya kana ina?" Na kara fada a hankali saboda yadda cikin ya dunkule yayi ƙasa sosai. A daga nesa kadan na fara hango haske madadin nayi farin ciki, sai na tsinci kaina da tsoron mai zai faru, haka yasa na shiga tafiya ina dafa bishiyar da yake gefena, Allah ya gani na gaji, jin kafana kamar an daure ni a wurin, yasa na fara zare idanuna..zamewa nayi tare da jingina a jikin bishiyar. Kalamanshi ne suka fara yawo a kunnena. Ko ban kasance da ke ba, har Abada ba zan nisanta kaina da zama a gefenki ba Ikhlas, zan rike hannunku na taya ki haihuwa a duk halin da nake i will be on side! wani irin haki da nishi nake a lokaci guda na cire shegen pant din na wurga, na kara jinjina da bishiyar, tare da zamewa kaɗan. Na rasa mai zan rike, kiran Allah nake kawai bayan nan babu me taimako a cikin dajin nan. Babu kowa. "Ya Allah! Ya Allah!! Ya Allah!!! Kai kaɗai ka rage min! Allah ka kawo min sauki da sassauci!" Na fada da karfi, tare da sake wani irin nishi. ..
Kaf ahalin gidan Yayari suna cikin dimuwa domin Sarki Shago ya hana kowa barci kai baka isa ka koma daki ba kowa na tsaye akan kafarshi. "Ina Ikhlas take? Ina ta shiga?" Inji Hajiya Kubrah da hankalinta yake tashe, yau kwana uku amma babu ita babu labarinta. Ƙarar motar yan sanda ne ya cika gidan. "Kai Faruq kace kada su ketare wannan iyakar su juya! Awatif tana hanya." Haka aka suka hana yan sanda shiga gidan. Suka juya.
Yana tsaye a hasumiyar masarautar sanye yake da shigar sarauta. Mai Bauchi ya shigo wurin. "Allah ya baka nasara mai babbar daki ta farka!" "Hmmm!" Ya ce idanunsa yana kan hanyar shiga birnin! "Ranka ya dade!" Hannu ya d'aga mishi, a hankali ya dafe gefen zuciyarsa. "Tana kirana!" Haka ya wuce mai Bauchi ya fito waje, dagarai da bayi basu san me yasa suke wani irin biyayya a gare shi ba, amma tabbas babu me iya koda tari ne a cikinsu. Kowa tsoron wannan sarkin yake ya sauya bakiɗaya. Tare shi Faruq yayi yana faɗin. "Ba zaka fita ba sai dai ka sare kaina sai ka wuce!" Wani irin riko wuyar Faruq yayi cak sama ya ce. "Kul Bargaga!" Ya cilla shi can, ya juya ya bar wurin Faruq ya tashi da kyar ya bi bayanshi.
"Ya Allah ka gafarta min zunubaina, Ya Allah ka kawo sauki da dauki Ya Allah ka kare Zainab da abin cikinta! Ya Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkaka, Ya Allah nayi imani da kai, na yarda da kai Ya Allah ka kawo min dauki bani da tsimmi ba ni da dabara!"
A daidai gabbar da na gama cire raina da samun ceto, a lokacin na ga Ismaha a gefena, tana min kuka itama. Cikin azabar ciwo na ce mata. "Ismaha kece?" Wani irin doro ta yi min tare da kuka mai karfi a hankali wuta ya kama dajin, azabar ciwon da nake ji bai hana ni fahimtar kofar gidan da nake ba, "Ya Allah!" Muryan Baba titi ya ratsa dodon kunnena, "Tasi'u? Zaka iya kawo mana shi a wannan lokacin?" "Eh Kaka!" Ya fada cikin wani irin murya, hannu na mikawa baba titi ina niman abinda zan rike ba na samu na fitar da abinda ya tokare min gabana, aiki aka ce da ayi min saboda yaran cikina uku ne, cikin wani irin kad'awar iska, na kalle shi a gabana. "Yaya!" "Lu'ulu'a!" Ya tako da sauri, cikin karewar karfin da nake a shi jikina ya sake wani irin gajiya da barci nake ji, na ji an kaiwa cinyata mari tass. "Bude idanun!" "Ka riketa ka rike bayanta da kyau! Haihuwa ce ta gaji sosai!" Inji dattijuwar da ta mare ni,
****
Cikin tsananin duhun dare, take kallon wutar da yake ci a hankali. Gani take wutar na rabuwa gida biyu-biyu. Zubewa tayi tana mai da numfashi a hankali. "Me kika aikata min? Me kika min?" Ta fada da wani irin amo, kafin ta lumshe idanunta, bata kara buɗewa ba sai bayan awa daya, kafin ta bude idanunta a hankali. Wanda yake ci da wuta kamar yadda wutar gabanta yake ciki. "Kada ki manta ruhi biyu ne a jikinki, akwai mai girma Aojanah. Wacce ta kasance mai tsarki ce ita ɗin, shi yasa ta zab'e ki. Sai abu na gama ina son na tuna miki fansar mahaifinki ko kin yafe musu ne? Ko kin yafe mutuwar dan uwanki ne? Idan har kin yarda kin amince zaku kasance da mai girma Aojanah har karshen rayuwarki wannan shine dalilin, sannan itama tana da burin domin shagon ya farka da ba zai kara komawa ba. Wannan ne lokacinki kafin Awatif ta kara dawowa a gare ki! Domin ba Mai Babbar daki kaɗai ke taimakawa ba har da wasu ruhannin!"
Mikewa tayi tare da nufar kofar a hankali, ta juya tana kallon matar da take cikin duhun ta ce mata. "Haka kawai ba zaki tashe ni daga barci ba meye buƙatarki?" "Mulkin zanzabira ya dawo hannunmu....
"Alhaji Nafi'u waye yake saka ka aikin nan ne? Nima ina son sanin waye ne a cikin ahalin Yayari? Idan har zan shiga cikin masarautar Yayari dole sai na kirkiro yar karamar wasan kwaikwayo tunda abar wasannin mu ta gama mana aiki!"
"Ki je ki shirya akansa Salmanun Faris da kika sani da can ba shi bane anan, wanda yake nan fusatacce ne"
Dariya tayi tana faɗin"kasan me yasa Aojanah ta zabe Ni? Saboda ita din tsarkakakiya ce. Nima ban tab'a haɗa hanya da kazantarku ba. Fansa tawa biyan bukata taku!" Daga haka ta dauki jakarta ta bar parlourn tana wani irin tafiya mai jan hankali.
*
Zubewa tayi a gabana rungume da jaririnta, hankalina yana kan hisnulmuslim. Rarrafawa tayi gabana. Daya cikin bayanin ta ce mata.."ranki shi dade koma baya!" Kuka ta fashe da shi cikin shashekar take mika min jaririn. "Zunubi na ne yake ƙara ƙarfi a kansu, Zainaba shima mutuwa zai yi" ban amshe shi ba na ban kuma bata amsa ba, kaina a sunkuye tun mutuwar Ayyanah nake kara jin wani irin ciwo a duk lokacin da ka ayi wani mutuwa a cikin gidan tabbas akwai wani abu da yake bayan inuwar Yaranmu haka yasa Ayaan da Ayaad, tare da Ayat suka kasance basu shiga harkan kowa musamman Ayaan wanda ni kaina tsoro yake bani idan yayi wani abun. Tun rasuwar Ayyanah yaron ya koma kamar wanda wani abu yake tattare da shi, idan ka gan shi yana mai wasa shi da Ismaha ne. "Zainaba na tuba taimake ni kada ya narasa shi a karo na biyu!" Sai lokacin na amshi Yaron wannan shine karo na biyu da Nadiyyah take rasa jarirranta duk lokacin da ta haife su basu amsar suna ma suke mutuwa. Fitowar Ayaan da Ismaha a kafad'arshi ya ce min. "Mammy bata danta sun kashe shi, sai dai gaba idan ta kuma samun wani amma wannan shima kamar su Ayyanah sun sadaukar da shi." Sannan ya wuce tare da magen a kafad'arshi. Da gudu ta bishi tare da zubewa a gabanshi. "Ayaan waye ke kashe min su? Ayaan gaya min don Allah!" Wani doro Ismaha tayi a kafad'arshi tana wani irin kuka. Shafa kafadar magen yayi yana murmushi ya ce mata.."gubar a jikinki yake, ko.da zaki haifa dubu ne zasu kashe ki kawo kunnenki?" Matsawa tayi tana kuka. Ya ce mata. "Ita Addah sadiyyar ba kyale miki ita zasu yi ba, ke keka amshi ragamar rayuwarki a hannunki. Mammy Kuma Allah ta barwa nata rayuwar!" Daga haka ya fita waje, shafa magen yayi yana kallon Ijlal da Amaryan Babansu, hankalinsa kwance ya nufi hanyar waje. Yadda gate din kofar gidan ya bude kanshi ya juya yana kallonsu, murmushi yayi ya saka kai ya fita daga cikin gidan..
Kukan Nadiyyah ya dawo da ni duniyar tunani, na zuba mata idanun. "Ya isa ki kira Mai Martaba ayi jana'izarshi." "Zainaba haka xan rayu rayuwata a mace?" Zuwa yanzu da nake da cikin na biyu tsoron kowa nake ji, koda yake mijinmu mijina ya kara bani kariya tun bayan haihuwarsu Ayyanah, ya bani dukkan ni wani kariya, kofar gidana da Yarana suna cikin tsaro, Ayaan ne kaɗai baya bukatar kome na tsaro domin Baba titi ya gaya min cewa kaf duniya Allah kaɗai zai iya daukar Ayaan ba dai mutum ba, a yanzu haka da ya fita fada zai nufa wurin Babansu. Kuma tazarar da take tsakanin fadar da gidan akwai nisa. A yanzu Ayaan yake da shekaru huɗu zuwa biyar amma yasa kowa a gidan barci cikin salama, tun rasuwar yar uwarsa Ayyanah.
**
Kallonshi nayi lokacin da na fito parlourn da Uban cikina mai suffar randa na ce mishi. "Aure zaka kara? Ina zaka kai mu? Wai meye matsalarka da auren auren nan ne?"
Banza yayi min yana faɗin. "An gama magana Ummi!" Yadda ta dauke kai, ya saka shi yin murmushi "Allah ya huci zuciyarki" ya mata sallama ya bar parlourn, "Ummi aure zai kara fa? Ina Yaya zai kai mata ne?" Na fada da wani irin jin haushi. "Ki ji da cikin jikinki, Zainab lafiyarki ita ce mai muhimmanci, ba Mijinku ba." Tun bayan faruwar lamarin da na karyawa Nadiyyah hannu Yaya ya sauya kai tsaye yake abinsa ko jiya anan Ijlal ta wuni tana kuka, ga Amiratul Zaitunah da take jin jiki. Yanzu wata uku kenan, cikina yana wata bakwai, ta haifi Yarta mace ya ce ba zai yi suna ba, da danyen jegon tazo wurin Ummi, itama ta daure mishi gindi ta ce ba za ayi suna ba, tayi duk abinda zata yi ni wannan rayuwar da Ijlal take gani ya fara bani mamaki da tsoro bakiɗaya kowa ya tsane ta, ta zama kamar mujiya ace ba haihuwa miji ya maka wulakanci, ai gidan Ubana zan wuce haka kawai.
*Tun da aka yi auren na fuskanci akwai wata a kasa domin Amaryan a ranar da tazo Ismaha, ta hanata zama a parlourn gurnani da wani irin kai mata cafka kamar zata cinye ta. Sai da Yaya yayi kwallo da magen madadin ta fadi can ta dirko kan cinyata tana wani kare. Cikina tare da mikar da gashin jikinta da bindinta kamar zata kai farmaki. "Isma, ya isa haka Abba ne ba a fada da shi kin ji!" Kwantar da kanta yayi a jikina tare da wani irin dungure cikin ma sai da ya juya. Bakiɗaya naji kamar numfashina zai dauke. Jingina kanta tayi da cikin sai na ji ya tsaya cak. "Wallahi kika sake wani abu ya same abin cikinki, ta sanadin magen nan sai na konata!" "Lallai fa, ba mai tab'a min Magena wallahi oya Isma muje daki ko ki min tausaa.."
Kwana goma da zuwansu, bayan la'asar Mai Babbar daki ta tafi faran kasa ita da Mai Martaba gaisuwar mutanen, da aka yi musu ta shigo kamar mahaukaciya. "Gaya min me kika yi mishi ya kasa mancewa da ke? Me yasa sai ke? Me yasa sai ke?" Shafa Ismaha nayi ina mai daura daya kan daya, nayi murmushi nace mata. "Mai xan yiwa shago kuwa soyayyar Awatif lallai gaskiya ce, takowa tayi da wani irin fusata wani haske ya fito daga jikin Ismaha ya dakatar da ita wanda yayi sama da ita sannan ya buga can. "Aojanah, Barka da zuwa gidan shagona a karo na biyu ki tsammanci zuwa na, bayan na sauke nauyin da yake kaina kishi da yaki akan shi yanzu zamu fara....
****
Sake zama nayi da kyau na ce.
"Faruq ka rufe shi, kada ka sake ya fita. Ka tabbatar da an binciko duk inda Ikram Saddam Tanimu Jatau take, bata ci bulus ba."
"An gama Fulani Babba!"
"Ayaan da mai babbar daki sun isa Madina daga can zasu wuce Scotland kamar yadda kika shirya."
"Ka tura sakona ga ahalin Yayari?"
"An tura ranki shi dade!"
"Ya batun zabin waye akan gaba?" "Abid Junaid Gobir!"
"Ijlal fa?"
"Tana rufe a bangarenta."
"Na gode! Ka tabbatar an farauci Ikram, Gwaska dakare."
"Alhaji Nafi'u da Rilwanu ba?"
"Na bar mishi aikin ya ji da su....
"Alhamdulillahi gubar bata yi tasiri!" Inji Doctor Andrew da ya fito a hankali, yana faɗin. "
"Mun gode!" Na fada ina kallon dakin da ya fito. "Yarinyar bata yi kome ba, wannan shine karo na biyu da take kokarin kashe yarinyar dole a farauce su, a nime su a gurfanar da su, shi kuma Khalifa da Ahmad duk wnada ya kare su a gaya min zan ji da shi."
***
" A yanzu na fahimci, Zanzabira yana bukatar irinki Zainab a yanzu na fahimci dole ka tsaya a gefen Salmanun Faris. Na jahilce ki amma nasan a wannan lokacin, ni dai tawa ta ƙare, ga wannan naki ne ki yafe min, zan tafi na barki da dawainiyya Ni yafe min nasan nayi laifi amma kada laifina ya shafi Yarana, don Allah duk yadda zata kasance ki kare shi ki tsaya mishi, yakin da zaki yi yana buƙatar dukiya na tara, amma zaman lafiya nake nima mishi ki yi aiki da lokaci da hankali ki yi aiki a matsayin yar jarida.....
***
Nayi kuka nayi kuka nayi kuka na kara kuka na rasa mutane masu muhimmanci a rayuwata, na rasa dan uwana, na rasa Aminiyata, na rasa Yata, na rasa duk wanda zai kasance da ni domin nayi dariya, amma mai babbar daki tana gefena, shi yasa na tsaya na kara tsayawa domin mijina da kujeransa dole na kare dole na kare kowa na sayi kowa na saka an rufe shafin wasu. Ban sani ba ko Allah zai yafe min domin nawa bangaren mijina da zuri'ata tare da aurena na kare na kuma kare duk wani abu nawa idan na san zaka tab'a min ahalina zan saka a rufe shafukanka wannan shine asalin abinda Royal politics ya kawo cikin rayuwata wanka da datti koda kuwa kai tsarkake ne dole ka zama mai barna........
*Mulki da siyasa! Soyayya da kishi, cin amana da zalinci! Rayuwa da ƙaddara! Sadaukarwa, gwagwarmayar mai girman gaske! Yaki da zubda jini....*
"Nayi alƙawarin ba zan kara barin wani yayi kuka da Yayari ba,haka yasa a na kara hada kan Zuriar abokai uku wuri guda... Attahiru Shehu Yayari Allah ya jikansa da rahama
Junaidu Gobir Allah ya kai haske kabarinsa
Saddam Tanimu Jatau, Ubangiji ya gafarta masa, sun yi gwagwarmaya domin kafa Attahiru ni kuma na janyo Abid Junaid Gobir
Fadil Saddam Tanimu Jatau
Barista Khalisah Nafi'u Shaibah wacce ta tsaya a bayana.......
_Book 1 ya zama compelet book 1, 2&3 500₦ hajiyata babu yawa, ki shigo faka-faka ayi da ke! Inji Sa'adu bori ya ce mace kazama bata bori! Nima nace Yan ROYAL POLITICS addict's fans let me led you to Zanzabira..._
```5921536136 Ramlat Manga Moniepoint```
***
500₦
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu CE
Idan na ga ruwan sama amma na comments 😭 🙄 tabbas 90% is loading..,.........