DAYAN BIYU

Page 09

by @meenatyandoma

ƊAYAN BIYU

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

Page 09

...Har sauri Iya ke yi domin ta cimma matar da ta gani kofar gidanta. Domin ga dukkan alamu ita ce wadda ta zo gaisuwar Shuhuda kuma ta kawo ma Bintu uwayen kaya.

Sauri take tamkar zata tashi sama, sai dai kwatsam kefarta ce ta gurɗe, ba shiri ta yi kasa ita da goyon da ke a bayanta.

Sunan Allah ta kira tare da rufe idonta cike da azabar zafi da ke cinta, sai dai daga idon da zata yi matar ta ba ce bat! Babu ita a wurin.

Da kyar ta mike tana dangyasa kafa har ta karasa kofar gidan.

Dubawar duniya ta yi amma ko mai kama da matar bata gani ba.

Ganin ba ta da mafita ya sakata shiga gidan tare da mike kafarta da ke faman yi mata raɗaɗi.

"Anya zan iya, anya kuwa maganar Yafundo bata tabbata ba. Bintu na kasa jurewa karfina ya kusa karewa, mahaifinki da Inna tun bayan kawoki gidan nan har yanzu basu zo ko kuma su kawo wani abu da sunan ke suka kawo masa ba. Yau da a ce faduwar nan da na yi na karaya ko na goce ya Rayuwarki zata kasance a hannuna"

Ta karasa maganar tare da kafe Bintu da ke rike a hannunta cike da tausayi.

Daren ranar wani irin zafi jikin Iya ya yi da kyar ta samu bacci ya kwasheta. Shi ma din bata farka da wuri ba sai da gari ya waye tangaram, a gurguje ta yi sallah tare da yi ma Bintu wanka suka nufi gidan aiki.

Fada Hajiyar ta hau Iya da shi domin ita dama can ta rasa ya zata yi da Iya domin dai bata son yan aiki masu yaya.

Hakuri Iya ta hau bayarwa domin ta san laifina ne.

Haka rayuwar Iya da Bintu ta yi ta tafiya har ta yi kwana arba'in ba tare da Inna Ɗan Inna ya zo da sunan dubawa ba. Sai Hussaina da ke satar hanya wani lokacin ta zo ganin Bintu.

Bintu ta yi wayo sosai domin ta tasamma wata na biyu. Kyawunsa da haske ta ya kara bayyana, ga wani irin karfi tamkar shari'a.

Ta na da wata hudu ta fara zama ba tare da an jingina ta da wani abu ba. Ita dai Iya abin tsoro da mamaki ya bata sai kuma ta tuna ai jaririn yanzu ba irin na da ba ne.

Sai dai abinda ke kara tayar wa da Iya hankali shi ne wata irin kyakkyawar soyayya ce a tsakanin Bintu da ruwa. Muddun ta ga ruwa sai ta san yadda ta yi ta rabeshi In ba a yi sa a ba ma ta kifar da shi.

Watan ta biyar a duniya ta fara rarrafe, nan fa abubuwa suka tsananta domin sai dai Iya ta wayi gari ta ga Bintu cikin rubor wankan ta an cika ta da ruwa ta na ta wasa.

Abin da ta gagara ganewa shin wa ke zuba mata ruwan har ma ya sakata cikin robar?

Sai dai ta rasa gane wannan amsar har gobe.

Kamar yadda ta saba safiyar yau ma ta shirya sun tafi aiki, sai da ta tabbatar da ta gyara ko ina sannan ta shiga madafa domin hada masu abincin rana.

Goye ta ke da Bintu sai dai mutsurniyar da ta rika yi ce ta tilasta mata sauketa, da nufin in ta gama motsa miya ta mayar da ita a baya.

Sai dai da Iya ta san me zai biyo baya da bata yi gigin sauke Bintu ba. Juyowar da zata yi nan fa ta naimi Bintu sama ko kasa ta rasa.

Cike da mamaki ta yo falon Gidan sai dai nan ma watan babu kowa. Hankali a tashe ta yi kofar gida ko mai kama da ita bata gani ba.

ganin yadda Iya ke kai koma ya saka Hajiyar tambayarta lafiya.

Jin abin da Iya ta fada ya sakata mikewa da sauri.

"Bacewa kuma? A cikin gidan nan, kuma kin duba ko ina ba ki ganta ba?

"Wallahi Hajiya ko ina na duba ban ganta ba. Ni babbar damuwata ma kada a ce ta fita wani ya sace ta me zan fadawa ubanta?"

"Ai haka ma ba zata faru ba, in sha Allah za ki ganta. Kin duba har bayan gidan nan inda ƙatuwar robar da nake kiwon kifaye ta ke?"

"Aa Hajiya gani na yi me zai kaita can bayan gida. Shi ya sa banje ba"

"Tashi za ki yi mu garzaya tafiya mu duba"

Ta kasara maganar ita da Iya na rige-rigen fita.

Sai dai tun daga nesa suka shiga zallar tashin hankali domin ga kifayen Hajiya nan duk an yi watsi wajen ruwan wasu ma duk sun mutu.

Da gugu-gudu suka karasa bakin ƙatuwar robar abin da suka gani ne, ya saka Iya da Hajiya mutuwar tsaye gabansu na tsananta faduwa.

Bintu ce cikin ruwan tsundun duk kifayen da ke cikin robar ta kashesu domin babu ɗaya mai motsi. A gigice Iya ta fiddota daga cikin ruwan tare da ajiye ta a kasa.

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Iya me nake gani haka? Wannan Jikar ta ki da ma haka take? Da farko ma wa ya sakata cikin ruwan nan"

"Hajiya wallahi ban san wa ya sakata ba, tare da ke muka riskeku a wurin nan"

"To ai kuwa barin gidan nan ya zame miki dole domin ba zan ci gaba da zama da ku ba. Wata rana kamar yadda ta kashe kifayen nan Ni ma haka zaku kashe Ni?

"Hajiya ki yi wa girman Allah kada ki koreni, aikin nan dashi nake rufawa kaina asiri in kika kureni ina zan tafi wa ya zai taimake ni"

Ta karasa maganar tare da zubewa tana riko kafafun Hajiyar.

"Ai duk in da za ki tafi sai dai ki tafi, amma barin gidan nan farilla. Ni dama tunda na dora idanuwana a kan wannan jikar ta ki na ji sam ban yarda da ita ba. Kyawunta ya yi yawa dama nasan za a rina don haka ki tattara ki bar gidan nan. Kuma albashinki ba za a baki ba don bannar da ta yi mini Zan rage asara"

Ta karasa maganar tare da barin Iya a daskare tamkar dutse.

Da dai ta ga babu mafita face ta fice daga gidan nan haka ta goya Bintu da jikakkun kayan da ke a jikinta ta baro gidan.

Tafiya take amma bata san inda kafarta ke sauka ba. Kai tsaye gidan Yafundo ta nufa.

Bata boye mata komai ba hatta abin da ya faru ya.

Salati da Sallallahu ta shiga yi cike da tashin hankalin wannan sabon lamari.

"In ba ki manta ba na fada miki ki mayar da Bintu gidan mahaifinta, shi ne kadai fatan da za ki yi mata. Amma kika ki mayarwa, to ki sani rukont ba za ki iya ba ki mayar da ita tun kafin lokaci ya kure miki"

"Ba kin ta taki ba, amma Shuhuda da kanta ta bani amanar ta. Shin kina ganin idan na mayar da ita gidan mahaifinta ban saba mata alkawarin ba"

"Kin ga gaskiya daya ce. Babu wani cin amana da kika yi face taimakon goben yarinyar nan. A yanzu kin rike Bintu mahaifinta da Kakarta sun bar miki ita ko leko ku basu yi. Sun zame hannunsu a duk wani lamari da ya shafe ta, in kika cigaba da tafiya a haka nan gaba me kike tunanin zai faru. Ke daya kina iyawa da matsalarta ita ɗiya mace ce nan da karamin lokaci aurar da ita za ki yi, shin ke ce wadda zata hada mata komai na aure kiyi waliccinta ki hadata aure?"

Shuru iya ta yi domin kaf abin da Yafundo ta fada gaskiya ne, maslaha daya ce ta mayar da yarinyar nan gidan iyayenta ko don su dage da nemar mata magani.

Su sakata makarantar addini da ta zamani nan gaba.

Nan suka yanke shawarar Yafundo zata rakata su mayar da Bintu gidansu, duk bayan lokaci sauya je ta rika ganinta in ya so.

Kayanta tsaf suka hada mata tare da ɗaukar hanyar gidansu Inna

Tun a kofar gida Iya ke jin gabanta na faduwa don bata san wace irin tarbar Inna zata yi masu ba.

Da sallamarsu suka saka kafa cikin gidan, iya da ke fyace wake da katon tire dinta sakin tiren ta yi wajen ya watse cikin kasa.

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun"

Ta shiga nanatawa tamkar ta ga wata ankoba ko bala'i

Sake da baki suke kallonta. Murja kuwa jin Inna na salati ya sakata fitowa don ganewa idanunta abin da ke faruwa.

"Baiwar Allah amma haka bai da ce ba, kamata ya yi ki ba mu wurin zama ki ji me ke tafe da mu"

Yafundo ta fada.

Jiki a sanyaye ta yi musu iso suka shiga dakinta. Shigowar Husasaina da gudu ta fado dakin Iya ta mika mata Bintu da ke ta faman kyalkyata dariya ganin Hussainar.

"Bayin Allah me ke tafe da ku?"

Ce war Inna

Yafundo ce ta fara magana cikin kyakkyawan kalami irin na wadan da suka ga jiya da yau.

"Baiwar Allah ki kwantar da hankalinki. Munzo ne mu maido miki jikarki kamar yadda na fada da farko"

"Dakata baiwar Allah!"

Inna ta tari numfashinta

"Ban gane me kike so ki fada mini na, na ga dai Shuhuda ce ta haɗa kuma ta raba don haka abin da ta haifa ma mun bar miki shi."

"Subhanallah! Baiwar Allah. Anya kin san abin da ki ke fada Bintu fa jikarki ce Ubanta ɗanki ne na cikinki, me ya sa zaku bar mata jinjira tsawon wata biyar ba zuwa ba aike ita ɗaya ke gwagwarmayar kula da yarinyar nan. Shin baku gudun Ubangiji ya kamaku da hakkin jinjirar nan?"

"Ce wa za kiyi wata ki ka dauko ta zo ta yi min rashin kunya. Diya ce ba zan iya rikewa ba na fada na kara"

Inna ta karasa maganar tare da mikewa.

Ran Yafundo ya fara ɓaci don haka hannun Iya ta kama.

"To Alhamdulillah! Ga ta nan mun bar miki don Allah karshen kiyayya ki sakata rijiya ko kuma ki kamata ki yanka. Tashi mu tafi."

Jiki a sanyaye Iya take mata baya hawaye na fita a fuskarta.

Zage-zage Inna ke yi tare da tunanin ya zata yi da Bintu. Yarinyar da ko kallonta ta yi sai ta ji gabanta ya fadi.

Hussaina kuwa goya Bintu da ke ta kyarkyata mata dariya ta yi Ita ma ta na dariyar.

Murja da ke labe ta na jiran fitarsu Iya a fusace ta fito. Tare da fizgo Hussaina da Bintu

"Ke dan..."

Ta ya ba mata ashar

"Za ki ajiye wannan mayyar yarinyar ko sai na hade miki kai da bango. Ka ga mayya mai mugun hali irin na uwarta da ta mutu ta barmu da masifa"

Zafin fizgar da ta yi ma Hussaina ita ce ta saka Bintu fadowa cikin kasa.

Kukan da ta tsanyare shi ya fito da Iya ta na salati da salallami.

"Yau mu mun shiga uku! Murja me kika yi haka? Anya kina da hankali kuwa. Yarinyar karama za ki yi wa wannan jifar"

"Kinga Inna, KO me za ki fada ki fada. Ni dai ba zan rike wannan Annobar ba kai karewa ko yarana bana so in ga ta na kusanta"

"Yaro yaro ne. Murja tausayinki nake domin na san za ki ji a jikinki"

Iya ta karasa maganar tare da ɗaukar Bintu da rabonta da kuka irin wannan tun ranar da ta zo duniya. Sai kuma yau"

Gefe ta ajiye Bintu ita ma ta shige daki. Hussaina ce ta lallabo ta dauke ta suka fice daga gidan. Tunda ta saka kafa suka bar gidan Bintu ke bacci.

Bayan gari Karkashin wata bishiyar kuka ta zauna tare da Bintu da ke sharar bacci. Ita ma nan baccin ya yi awon gaba da ita.

A hankali hadari ya fara haduwa kafin ka ce me duhu sosai hade garin. Murja kuwa sai lokacin ta lura da ba Hussaina a cikin gidan, Hassan ta saka ya je ya nemo ta sai dai shuru ba Hassan bare Hussaina.

Ita dai Iya ido ya raina fata musamman da ta tuna a tare suka fita da Bintu.

Ɗan Inna da shigowarsa kenan Inna ke fada masa abin da ke faruwa ga hadari ya kusa tasowa.

Su duka biyun a tare suka fantsama neman su aka bar Murja kadai ta na rarraba ido.

Kwankwasa kofar gidan ta ji ana yi, da saurinta ta fito don a tunaninta anga su Husainar ne. Sai dai wayan bata ga kowa ba.

Gidan ta mayar ta rufe cike da ɓacin ran mai mata wannan abin sai an saka ta taso kuma a ruga ta ga ba kowa. Ta na sake komawa ta zauna aka sake kwankwasa kofar da karfi tamkar za a karyata.

A fusace ta bude kofar da nufin wanke yaran da ke mata wannan Wasan da mari. Sai dai yanzu ma kamar farko babu kowa a wurin.

Da wannan haushin ta juya da nufin komawa cikin gida. Kwankwasa kofar aka kara yi da karfin tsiya tamkar za a karyata a shigo.

A yanzu kam Murja ta matuƙar tsorata ja da baya ta fara yi cike da tashin hankali, kafarta ta ji tamkar ana fizgarta zuwa wurin kofar. Ihu ta ke so ta yi amma ina bakinta a rufe ya ke gam.

Kofar ce ta bude kanta da karfin tsiya. Abin da Murja ta gani ne ya sakata daskarewa a inda ta ke numfashinta na kokarin daukewa...

DAGA GOBE ZAI KOMA AINAKIN KUDINSA 500. ZAKU TURO 300 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER

2294023532 UBA BANK

AMINA ABUBAKAR