KAWAICI

Episode 7

by @zahraroyal

*KAWAICI*

*©Zahra Royal Star*

PAGE 7

*House No.10 Arabian Arena, Quarters Katsina state Nigeria*

Zama tayi akan kujerar parlon tana saka hannunta ta ɗauki romot dake akan santa table, tana ɗan taɓe baki kaɗan, haɗe da sakin tsaki kaɗan-kaɗan, sosai take jin zuciyarta na mata zafi, kunna Tv tayi tana zama haɗe da sauke ajiyar zuciya.

A hankali ya sakko tafe yake yana gyara rigar dake jikinsa, sanye yake da wasu Manyan kaya sunyi ma fatarsa masifar kyau, ɗauke yake da jakar aiki a hannunsa, ya ɗan dubi inda take kaɗan ya girgiza kai.

Ko kallon inda yake batai ba, tana jin bala'in kishin mijin nata, danji take kamar ta kamasa ta kullesa cikin gida kar kowacce Mace ta gansa, ga Mata da yawa dake binsa kamar karnuka.

Wani irin zafi take ji a zuciyarta tana tuno yadda suke dashi bayan ta fitowarta.

A hankali ta shigo ɗakin tana kallonsa ta bayansa ta biyu tana murmushi a hankali ta saƙulo da hannunta ta bayansa tana dariya kaɗan ta ce.

"Kayi kyau fa".

Murmurshi yayi kaɗan ya sake janyota sosai ya juyo da ita, yana ɗanja mata kumatu kaɗan ya ce.

"Au Allah Mrs Muhammad?".

Dariya ta saki kaɗan tana lumshe ido zatai magana ƙarar wayarsa ta katse masu hanzari.

Kusan lokaci ɗaya suka ɗaga kai suna kallon mai kiran, abokiyar aikinsa ce mai suna Doctor Hanan Al'ameen.

A rubuce a jikin wayar.

Wani irin kalar abu taji ya riƙe mata ƙirji a hankali ta raba jikinsa da nata, tana masa wani irin kallo.

Bai damu ba saboda yasan babu abunda ke tsakaninsa da ita, hasalima shi kullum gaya mata yake baya da ra'ayin ƙara aure Mata ne ke manne masa, ya ɗauki wayar yana sakata a amsa kuwwa, domin ma kar tayi zargin wani abu, sai dai da yasa ni baisa ta a amsa kuwwar ba, saboda muryar Hanan data fito cike da wani irin sanyi haɗe da karya murya tana kashe murya, kamar zata saki shagwaɓa.

Ai Sakina bata san lokacin data zo kusa dashi ta fisge wayar dake hannusa ba tana kallonsa ido cikin ido tana kallon cikin wayar ta buɗe baki ta ce.

"To annamimiya ballagaza masu kiran Mazajen mutane Karuwa kawai".

"What ni kike kira da karuwa?".

"An faɗa ɗin, miye marabarki da Karuwar?, kin kira Namiji kina wani kashe masa murya kina son tusa kanki a gunsa, to tun wuri ki kama kanki Mlm, Mijina yafi ƙarfin ki wallahi".

Da wani irin sauri Muhammad yasa hannunsa cike da ɓacin rai ya amshe wayar yana kasheta gaba ɗaya.

Baice mata komai ba, domin har gaji da mata maganar ta canza hali, bazata taɓa sauyawa ba, yana sonta tabbas amma halayarta ya fara gajiya dasu.

Ganin yadda ya wuce ya barta tana ɓaɓato ya shige toilet koci kanki baice mata ba, yasa ta yin kwafa tana cije yatsa ta fitar masa daga bedroom ɗin, tana tafe tana ayyana yadda zata ci uwar wannan Doctor Hanan ɗin, danta sha kamasa yana waya da ita.

*Unguwar Dokoki Rimaye Kankia LGA, Katsina state Nigeria*

"Wai gidan nan ace duk faɗin gidan a rasa wadda zai ranta min dubu goma?, haba da'allah dubu gomar banza".

Ɗaga labule Zahariyya tayi ta fito ɗaure da ɗaurin ƙirji zata shiga ban ɗaki tana duban Baba dake ta ɓaɓatu shi ɗaya tsakar gida, kusan a tare ita da Umma suka fito tsakar gidan suna duban Baba, Umma ce ta tafa hannu tana faɗin.

"Oh'ni Mlm, yanzu kai baka jin kunyar tabbayar ƴaƴan cikinka rancen kuɗi?".

Juyowa yayi inda Umma take yana nunata da yatsa har bakinsa na rawa ya ce.

"Hansatu kifa kiyaye shiga gonata na gaya miki, bana son shishshigi da Munafurci".

"To yanzu Mlm munafurcin miye nayi maka?, gaskiya ce dai baka so, amma kana Mai gida kana tabbayar ƴaƴanka kuɗi, wadda kaine ya kamata ka ɗauka kana basu".

"Wato dai baza kiyi shirun ba?".

Taɓe baki Umma tayi tana sake riƙe baki tana mamakin halayya irinta Mai gidan nasu, kullum ace ƙara taɓarɓarewa abunsa keyi, shi ko irin zuciyar nan bama yayi, sai dai yayi zaune sai ƴaƴa sun ɗauka sun basa.

"Yawwa ƴar albarka ko zan samu dubu goma nan a wajanki?".

Baba ya faɗa yana duban Zahariyya dake gaf shigewa ban ɗaki dan ita kota kanshi bata bi ba.

Dakatawa tayi tana ɗan dawowa baya kaɗan kamin ta dubi Baba ta ce.

"Gaskiya Baba bazaka samu dubu goma ba, domin kwana biyu kuɗi basa shigo min, saboda munyi faɗa da Alhaji na, amma ka bari Ma'u ta shigo ita sana'arta kullum tana kowa mata kuɗi".

Ta faɗar haka ta faɗa cikin ban ɗaki tabarsa shida Umma na sake cewa.

"Ohh ai wallahi anji dai kunya Mlm, wai ƴarka babu tsoro akan fuskarta take kiran wai sunyi faɗa da Alhajinta mai bata kuɗi yana latseta".

"Lah haula walakuwata Hansatu, ce miki akai latseta yake yana bata kuɗi?, bana fa son sharri Hansatu bana son irin haka, kiji tsoron Allah fa Hansatu zato zunubi ne koda yazamo gaskiya".

"Ba wani sharrin da nake mata gaskiya ce a fili na faɗeta, kaima son abun duniya ne ya rufe maka ganin gaskiyar, amma wanne asararre ne zai rinƙa ɗaukar kuɗi yana bata ba tare daya samu wani abu daga gare taba shima?".

"To idanma ta bada ɗin, ai tana abunda zata miƙa a bata kuɗin dai ko?, kefa naki ƴaƴan ki binciki abunda sukeyi Mlm kafin kizo kina shiga harkar da babu ruwanki, ni wallahi Hansatu mamaki kike bani, ke kullum kece kesa min baki a harkar ƴaƴana, ni wai kin taɓa ganin ina shiga harkar naki ƴaƴan ne?".

Inna ta faɗa tana fitowa gaba ɗaya daga ɗakinta tana riƙe ƙugunta tana fuskantar Umma.

Umma ta bankama Inna harara tana taɓe baki haɗe cewa.

"Koma dai miye ai kin san dai ƴaƴana sunfi naki natsuwa a'ato".

"Mlm kafa shiga tsakanina da wannan Matar".

Inna ta faɗa tana nuna Umma da yatsa.

Baba ya wani dafe kai yana faɗin.

"Ohh shi yasa duk cikinku nafi jin daɗin zama da baiwar Allahn can Halimatun Sadiya, baiwar Allah mai hakuri da KAWAICI, duk abunda ake a gidan nan da wuya kaji bakinta a ciki, ku duba fa kamar bata gidan nan".

Ya faɗa tana nuna ƙofar ɗakinsu Falmata.

Wani kalar baƙin ciki ne ya turnuƙesu gaba ɗaya, kusan a tare suka haɗa bakin wajan cewa.

"Munafurci dai ta fimu iyawa".

"Akwai wadda yafi ku iya munafurcin, ace mata kamar kuna ganin hanjin juna?".

Baba ya faɗa yana nunasu da yatsa.

Zai sake magana yajiyo sallamar Ma'u ta shigo gidan riƙe da wata ledar dake shaƙe da lallai da sauran kayan ƙunshin da yanzu daga kasuwa take wajan siyayyar kayan ƙunshinta da sukai ƙasa da yawa taje sayowa.

Ai ganinta yasa Baba washe baki yana cewa.

"Yawwa ƴar albarka kin dawo?".

Ɗan dakatawa tayi da tafiya zata nufi ɗakinsu tana kallon Baba ta ce.

"Eh Baba na dawo mi ya faru?".

"A'a dama ba abunda ya faru, rancen kuɗi nake so ki bani dubu goma ko zan samu?".

Wata dariya kaɗan ta saki tana kallon Baba da mamakin wai rancen kuɗi yake so?, shida baya biyan bashi, karma ka sake kuɗi su haɗaka da Baba, domin ko mi za'ai baya biyan bashi.

"Bashi fa Baba kake cewa na baka?".

"Eh ko bazan samu ba ƴar albarka".

Kallonsa kawai take da mamakin halayyarsa kullum ƙara gaba yake, wai ita ake kira ƴar albarka, saita rantse bata taɓa jin Baban nasu yana sa masu albarka ba, da wayonta dai, sai dai ko lokacin suna ƙananu kamin lamarinsa ya lalace.

"Ni Baba gaskiya bazan iya baka bashi ba, kama sani ai".

"Ke karfa kiga ina lallaɓaki, dama ke ba'a cin abun hannunki ta cikin sauƙi, garama Zahariyya ita zata baka amma bata iya kyauta ba, kyautarta bai wuce dubu biyu ko ɗaya duk kuɗin da take samu, amma ke sai ƙin ɓata ma mutum rai kin gama ja masa rai zaki ɗauka ki basa".

"Ni Baba ba cewa nayi bazan baka ba, zan baka a kyauta ma ba bashi ba, domin nasan ko bashi na ce to ba biya kake yi ba, zan baka amma sai zuwa gobe ko jibi, saboda yanzun nan daga kasuwa nake, duk na kaso sauran kuɗin dake jikina, ka jira zuwa goben da anzo ƙunshi an bani kuɗin ƙunshi zan baka".

A fuskarsa baiji daɗin rashin samuwar kuɗin a yau ba, yaso ya samu yanzu, amma sai ya saki murmushi yana cewa.

"Ai shikenan Allah shi kaimu goben, ai dai ke kikai min alkawari?".

"Eh Baba kuma zan baka ne".

Ta ƙare maganar tana idasa shigewa ɗakinsu.

"Kai jama'a".

Umma ta faɗa tana tafa hannu.

"Haka zaki ƙare Hansatu dasa ido".

Baba ya faɗa yana kallon ɗakinsu Falmata, ya kwaɗa mata kira.

Gaban Falmata ne ya ɗan faɗi, tana zaune ita da Mama a ƙasa tana mata ƙitso, duk yau basu fita tsakar gidan ba, shi yasa ma ba'ayi wani faɗa dasu ba, Mama ce ta hana fitarsu tsakar gidan idanba kitso aka zo ma Falmatar ba, shine take fita da mutum tayi masa.

"Ki tashi kije mana".

Faɗin Mama.

"To Mama kiran miye yake min tsakani da Allah?, idanma kuɗi ne ni dai Allah kuwan bazan iya basa ko sisina ba".

"Toni nasan kiran da yake miki ne marar kunya?, zaki tashi kije ne ko kuwa saina saka hannu na mangare ki?".

Turo baki tayi tana miƙewa, Shamsiyya ta ɗan tashi daga kwancen da take akan kujera ta ce.

"Ai ko bai wuce kuɗi yake so ba daga gareki kema, tunda naji kamar bai samu ba a wajan Ma'u itama".

"Wajan nawa ma ba samu zaiyi ba wallahi".

Falmata ta faɗa tana ɗaga labulen ɗakin ta fice waje, tana jin haushin abunda Baban nasu yake yi, baida aiki sai tasa su a gaba su basa wani abu, baccin shi duk wani haƙƙi nasa bai sauke masu shi ba......

*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai dakata daga na 10 ne insha Allah, biya kuɗinki kawai a tura miki complete nasa yana nan akan Naira ɗari biyar #500 kacal*.

Account number 👉8130479973 Fatima Rabi'u Opay Bank

Shaidar biya 👉***