KAWAICI

PAGE 8

by @zahraroyal

*KAWAICI*

*©Zahra Royal Star*

PAGE 8

*Sabuwar Abuja Kankia LGA, Katsina state Nigeria*

Kuka take tana fyace majina tana ƙara sakin ihu, cikin kuka take cewa.

"Wallahi Umma Amna ba ita kaɗai bace, daga fita ta fa bamuyi nisa ba wannan takalmin data goge min kawai naji ya gurɗe na faɗi, kawai sai dai naji ni a ƙasa ga ƙafata ta lauye wai ashe targaɗe ne naji, wallahi Amna akwai aljanu a jikinta wayyo Allah ƙafata".

Siya ta idasa faɗar haka tare da dafe ƙafarta tana matse hawaye.

Umma dake riƙe da ƙafar tana mata sannu sai mamakin Amna ke ƙaruwa sosai a tare da ita, zatai magana Ummi tayi sallama ɗaga kai Umma tayi ganin tare suke da Amna sun shigo ɗakin yasa Umma miƙewa da sauri tana nunama masu hanyar fita tana cewa.

"Karku sake ku ƙaraso wajan nan tare da wannan ƴar taki mai kanbun baka, yo idan ba kanbun baka ne da ita ba miye a jikinta?, ace yarinya bata taɓa maka fatan arziƙi sai na tsiya?, kuma komi ta faɗa na alkaba'i saiya faru da kai, da yake ita muguwa ce mai makon da rinƙa ma mutane fatan arziƙi suna samun mutane saina tsiya kawai?".

"Haba Umma babu fa wani kanbun baka a tattare da Amna, kawai canfi ne irin na mutane".

Wani duba Umma ta juyo tana jefama Ƙhamis daya shigo yanzu yana faɗar haka.

"Kai dama yarda zakai ne?, tunda an riga an shanye min kai, kaima ai yanzu ba wani yarda nayi da kai ba a'ato".

"Kawai fa Umma rashin jinta da kauɗi ne irin nata yasa taje ta gurɗe ta faɗi, amma babu laifin Amna a nan wajan".

"Dalla can rufe min baki shanyayye kawai".

Umma ta faɗa haɗe da ɗaga masa hannu, Siya dake zaune tana shan azabar targaɗe har lokacin tana kallon Amna haɗe da mata wani kallon banza, gani tayi kamar Amna na mata gwalo, ai ko ta fasa ihu tana nuna Amna tana cewa.

"Wallahi Umma gwalo take min".

"Gaskiya ne ba shakka Amna, wato kin mata mugunta kinzo kiga ta mutu shine kike mata gwalo?, to gata nan ras take bata kai da mutuwar ba, ke baki isa ki kasheta ba wallahi, kuma yanzu ta fara saki aiki, idan kinga dama wata rana kiyi mata fatan mutuwa mu gani".

"Aunty kiyi hakuri insha Allah Amna bazata ƙara ba, yanzu ma shigowa mukai ta bata hakuri ta duba ta".

Ummi ta faɗa tana duban Umma, wani irin kallon baki da hankali Umma tabi Ummi dashi tana cewa.

"Ku riƙe haƙurinku bama buƙata, saida ta cutar da ita zata zo tana wani bata hakurii, ai ba har zuciyarta take bada hakurin ba, tunda gashi nan a gabanki take mata gwalo tsabar ta kware wajan shaiɗanci".

"Umma dan Allah kubar maganar nan ta wuce haka, nifa laifin Siya duk nake gani, miye na kawai saita saka Amna goge mata takalmi?, dan kawai neman rigima".

"Kai wai bance ka daina sako mana baki ba Ƙhamis?, ai kai na kusa sallama mata kai, tunda gaba ɗaya an gama min da kai, kwata-kwata baka ganin aibunsu ko laifinsu, dan haka zo ka fice min a ɗaki".

Umma ta ƙare maganar tana nuna masa ƙofar waje, Murmushi ya saki kaɗan ya kai dubansa inda Siya take ya nunata da yatsa yana cewa.

"Daga yau idan na sake ji kinsa Amna wani aiki na rainin wayo irin naki, wallahi wallahi saina miki abunda baki tunani, sakarai kawai".

"Wayyo Allah Umma kinji miye yake ce min a gaban wannan yarinyar Amna?, ni wallahi Ya Ƙhamis ka siya min raini a wajanta wayyo Allah Umma".

Ta ƙare maganar kamar wacce aka kaima duka.

"Ke ke ke yi shirunki, kai kuma fice min a ɗaki na ce, idan ka isa idan na sata aikin ni kazo ka bige ni, ko kuma kace kar tayi aikin nawa, marar kunya kawai".

"Allah ya baki hakuri Umma".

Ya idasa maganar yana juyowa ya fice daga ɗakin yana mamakin Umma da Siya da neman rigima kullum su kar a zauna lafiya.

"Kema kama aljanar ƴarki ku fice min daga cikin ɗaki".

Umma ta faɗa tana nuna su Ummi haɗe da nuna masu hanyar fita.

Ba abunda Ummi ta iya cewa ta jawo hannun Amna dake bin Umma da wani irin kallon takaici haɗe da jin haushinta a zuciya.

*MUHAMMAD POV*

Kallonta yayi yana sauke gilas ɗin dake sanye a idonsa bayan ya ɗauke Computer dake gabansa a hankali ya nuna mata wajan zama yana cewa.

"Ki zauna mana".

"No Doctor Muhammad, mi yasa Matarka take so tafi ƙarfinka ne?, kawai daga na kira ka saita amshe waya ta kama ce min Karuwa?".

"Ki zauna yanzu dai, dama zan baki hakuri a madadinta, ai nasha gaya miki Matana tana da kishi sosai fiye da yadda zan faɗa miki, shi yasa bana so kowacce Mace na kirana mudun ina cikin gida, ina son Matata bana son wani abu ya rinƙa shiga tsakaninmu".

Kallonsa Hanan take da mamaki tana jin zafi da ɗaci a zuciyarta kamin ta ce.

"Ni kenan baka sona Doctor Muhammad?".

"Dama na taɓa faɗa miki ina sonki ne?, bana da ra'ayin ƙarin aure Hanan, shi yasa tun farko da kika nuna kina sona, nayi ƙoƙarin dakatar dake, amma kika nuna ina kefa bazaki iya rabuwa dani ba".

Wata irin ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana faɗar Innalillahi wa'inna alaihir raju'un a zuciyarta, sosai take mai-maitawa, idonta yayi jawur jiri ta fara gani, ganin haka yasa Doctor Muhammad ƙoƙarin taimaka mata ta zauna.

Sauke lumfashi tayi tana ɗan dafe kanta kamin ta ce.

"Baka san irin sonka da nake ba, da baka buɗe baki ƙila kace min haka ba, miye laifi na dan kawai na ce ina sonka?, kai ɗin fa ba kowacce Macece zata iya kallonka lokaci ɗaya ta iya kauda idonta akanka ba, kana kallon kanka kuwa?".

Wani irin murmurshin gefen baki ya saki wadda ya ƙara kashe zuciyar Hanan ta kafeshi da ido, shi ɗin kyawawa ne ba irin kyan nan can ba, idan ka masa kallo ɗaya ma zaka iya ce masa mummuna, wata irin baiwa garesa ta tsantsar kwarji, kyansa mai kwantar da hankali ne, ga wani sansanyen kyau da Allah ya zuba masa, komai yake cike da aji da kuma kamewa, tafiyarsa kaɗai cike da wata irin natsuwa ga wata irin izza wacce ta haɗe da kwarjini take ƙara masa farin jini a wajan jama'a.

"Na gode da soyayya Hanan, amma ki sani kowanne mutum da kalar tashi rayuwar, bana jin zan iya ƙara aure gaskiya".

Kawai sai dai suka ji an buɗe ƙofar da ƙarfi an shigo haɗe da cewa.

"Har sai ka zauna kana lallaɓa Karuwa marar aji da kamun kai?, ke bance miki ki kama kanki ba?, bance miki karna sake ganinki da Mijina ba Mlm?".

"Sakinahhhhh!!".

Muhammad ya faɗa da ƙarfi yana mamakin wacce irin Mace ce ya aura haka mai mugun kishi?, kishin dake rufe mata ido ta kasa gane dai-dai daba dai-dai ba.

"Miye zaka ce min?".

Ta faɗa tana kallonsa babu tsoro.

"Waye ya baki izinin zuwa wajan aiki na?".

"Ai tunda naji wannan ƴar iskar Karuwa ta kira ka tana kashe maka murya, ni nasan dama akwai abunda ta taka, ashe dai nayi gaskiya sonka take, to ki sani har abada Mijina ya zama haramiyarki wallahi".

Sakina ta faɗa tana nuna Hanan data miƙe tsaye tana kallon Sakina, tabbas Sakinar ta fita kyau da diri irin na mata, ga kyau mai fisgar mutum, komai yaji, amma bata jin zata sassuta mata itama sai inda karfinta ya ƙare wajan samun Muhammad.

"Ai ban taɓa sanin ke jahila bace sai yanzu, an gaya miki tsoronki nake ji ne?, to bari kiji idan har ina lumfashi a doran ƙasa ki rubuta ki aje saina auri Mijin naki idan ya so ki faɗi ki mutu".

"Hanan please kije waje".

Ya faɗa yana nuna mata hanyar waje.

"Ke har isa ki kirani da jahila?".

Sakina ta faɗa tana shan gabanta.

Batai aune ba taji saukar mari mai zafin daya gigita tunaninta da jinta da ganinta.

Wani irin zaro ido tayi bayan ta tantance wadda ya mare ta.

"Nika mara akan wannan ƴar iskar?".

"Idan baki shiga hankalinki bama saina miki abunda yafi haka wallahi".

Ya faɗa ransa a mugun ɓace, ganin yadda ransa yayi ƙololuwar ɓaci ne yasa Sakina shan jinin jikinta tana dawowa cikin hankalinta kaɗan, Muryarta na rawa ta nuna Hanan tana cewa.

"Akan wannan?, baka ji abunda ta ce min bane?".

"To ai baki da maraba da abunda ta kira ki dashi, kwata-kwata Sakina baki da hankali da tunani, an gaya miki kishi hauka ne?, kuma idan na tashi ƙara aure ko mutuwa zakiyi an gaya miki zan fasa ne?".

"Na shiga Ukuna an shanye min Mijina wallahi, Innalillahi wa'inna alaihir raju'un na shiga Uku".

Wani irin takaici da baƙin ciki ya ƙara cika Muhammad, hayaniyar da suke ta fara hawa kansa, dan haka ya nunata da yatsa yana cewa.

"Nan da minti talatin tayi miki a gida, daga yanzu idan har kika ƙara taka ƙafa kika ce zaki zo wajan aikina ba tare da na sani ba, to daga lokacin da kika fito ɗin karki sake ki koma min cikin gida, ki wuce kai tsaye gidan iyayenki".

Dafe ƙirji tayi tana mamakin lafazinsa wani irin tsoro ne ya shigeta, tasanshi idan ya ce abu baya canzawa, bare a yadda yayi mata maganar.

Saida ta tabbatar ta bankama Hanan wani mugun kallo haɗe da harara da kallon gargaɗi, kamin ta juya haɗe da sakin tsaki har tana bangaje Hanan saura kaɗan ta faɗi ƙasa, Allah yaso tayi saurin tsayawa da ƙafafunta, tana binta da kallon mamakin hauka da kishin rashin tunani da wasu matan keyi.

Tana fita ta juyo inda yake zatai magana ya ɗaga mata hannu haɗe da nuna mata hanyar fita kawai.

Jiki a sanyaye ta juya tana ficewa itama tana ayyana yanzu ne ma zata fara yaƙin shiga gidan Muhammad ɗin, tunda taga Matar tashi bata da cikakken hankali....

*Wannan book ɗin na kuɗi ne Free pages zai dakata daga na 10 ne insha Allah, biya kuɗinki kawai a tura miki complete nasa yana nan akan Naira ɗari biyar #500 kacal*.

Account number 👉*** Fatima Rabi'u Opay Bank

Shaidar biya 👉***