KARAGAR MULKI

Page 23

by @cwtsumiey19988

*KARAGAR MULKI*

STORY & WRITTEN BY 
 (*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin 
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
   And now...*KARAGAR MULKI*
*YOTA*
BOOK 1 

PAGE 23

"Me yai zafi da tsanani har haka,ban ta`ba tunani ko haikacen za mu riski irin wannan matakin tsakanina da kai ba ya kai Kawuna ?"," Fiye da haka ma muna gab da kaiwa, ko da wasa ban ta`ba tunanin shirme da haukan ki ke ma ya kai har haka ba","Ko kusa ba haka ba ne,an yaudare ni ne, gami da shirya min zagon k`asa"....ya dakatar da ita ya na mai cewa,"Yi min shiru anan ko in k`araso in bige ki,ta ya ma zan yarda da ke ko abinda ki ka fad`a ,ina mai tabbatar mi ki da duk abinda ya faru ke ki ka jawo shi,ke ki ka kira sa da kan ki,ta ya za ki aje su a gurin da ya fi rashin tsaro,to ai dole ma za su gudu,kuma me ye dalilin ki na d`aure Ishmal a cikin kurkuku ko,ko ki na so ki d`arsar da tuhuma gami da zargi a kanki,ko a tunanin ki Malikat Juwairiyya a matsayin ta na Uwa mahaifiya za ta zuba ma ki ido ki cigaba da tsare ma ta d`a a kurkuku,duk da dai mun gama kame zuciyarta,bakinta da ruhinta sai abinda mu ka so kuma mu ka ga dama za mu bari ta aikata,amma ba komi ya kamata a ce kin ta`ba ma ta ba,domin shi d`a a k`ok`on zuciya da kuma ran Mahaifiyarsa ya ke rayuwa,duk iya k`arfin sihiri ko tsafin mai tsafi ba zai ta`ba gusar da soyayyar d`a a cikin zuciyar Mahaifiyarsa ba,ita soyayyar Uwa tamkar wuta ce mai ruruwa k`arni bayan k`arni ba za ta ta`ba gushewa ko mutuwa ba har sai randa wannan k`arnin ya shud`e,wannan shine munmunan kuskuren da ki ka tafka ka mai yiwuwa ki gyara ko kuma ki `bata rawar ki da tsalle","Ka yafe ni yai kai Kawuna kuma Sarkin Bokayen duk duniya, na tuba ka yafe ni ba zan sa ke aikata hakan ba","Hmmmmm idan kuskuren da ki ka yi ya gyaru ko ?",ya jefo ma ta da tambaya,"Ina jin zafin abinda ki ka aikata har cikin zuciyata, da alama wani abun na shirin faruwa a dalilin hakan,ko ma dai mene ne ba zan so ace na yi asarar tarin shekarun da na yi a ta dalilin sakarcinki ba,idan haka ta faru ba zan ta`ba iya yafe mi ki ba,domin kusan shekara Hamsin da bakwai na kwashe wajen k`ok`arin ganin na kai ku wannan matakin da ya fi na kowa,so samu ne a ce KARAGAR wannan ƙasar ta mu ce, amma mahaifin ku ya kasa cika min wannan mafarkin nawa k`arshe ya mutu a banza a wofi,sai yanzu ke ma ki tsiro min da wani sakarci na ki na daban tsaf zan iya sauya ki kamar yanda na sauya Asalin Sarauniya k`asarnan,yanzu sai in sa Zalikha a matsayin ki ta maye gurbinki",Har k`asa Sarauniya Junayyah ta zube ta nai mai ba shi hak`uri akan kar ya musanyata da `yar'uwarta da ta ke can k`asar BIHINAR domin aiwatar da wani aikin".... Shigowar Malikat Juwairiyya ne ya sa tai saurin tashi ta zauna ta na mai nannad`e k`afafunta tai zaman cin abinci gami da saurin share hawayen da ke kwaranya a saman fuskarta, duk da fuskarta ta nuna alamun rashin gaskiya `baro-`baro,shi kan shi Boka Dürsäås k`asa ya zube gaban Sarauniya Junayyah ya na mai had`a hannayensa wuri guda alamun dai tamkar shi ke ba ta hak`uri,dukkansu sun yi kalar ababen zargi da ka kalle su za ka shaida hakan.
" Me ya ke faruwa anan ne,na gan ku cikin wani irin hali,Allah ya sa dai lafiya ?",Eyeeh.....Na'am dama wai.... mun ma gama magana yanzu zai tafi ya sallame ni kuma na ba shi hak`uri ya hak`ura"....."Me ne ban gane ba,kamar ya kin ba shi hak`uri ya hak`ura, kuma wai ya sallame ki,kina cikin hankali da natsuwar ki kuwa, ko dai ba ki da lafiya ne?",da sauri Boka Dürsäås ya amshe zancen da cewa,"Ki gafarce ni ya ke Malikat Juwairiyya ta na cikin rud`u ne sakamakon abinda ya faru a safiyar yau, shiyasa na zo nan ina bata shawarwari da su ka kamata "," Hankalinta ta mai da shi akan Boka Dürsäås ta ce da shi, "A jiya kuma mene ne ya faru ?", nan ya kwashe duk abinda ya faru tun yinin jiya har kawo safiyar yau da su ka ne mi su Jamal su ka rasa da irin rikicin da Sarauniya Junayyah ta yi da Yarima Haisam, Hankalinta ba k`aramin tashi yai ba,har sai da ta dangana da inda Sarauniya Junayyah ta ke zaune ta kamota gami da had`a ta da jikinta ta na mai cewa," Na shiga uku ni Juwairiyya ya akai ki ka bari hakan ta faru,me yasa tun farko ba ki nemi shawarata akan wannan lamarin ba, ga shi yanzu ta kwa`be mai yiwuwa Yak`i ya `barke a ta dalilin wannan kuskuren muddin wa'inan fursunonin su ka Isa k`asarsu lafiya abinda zai biyo baya yak`i ne tsakaninmu da `yan k`asar BIHINAR",k`ara lafewa tai a jikin ta na mai k`arfafa kukanta tare da cewa,"Ni kuma yau na ga takaina yanzu ya zan iya dakatar da wannan fitinar ba na son a zubar da jini balle har a kai ga rasa rayuwar wasu mutanen a cikin k`asarnan","Kar ki damu zan yi duk abinda zan yi don gudun fad`awa cikin wannan munmunan had`arin ,na gane na yi kuskure da na yi saurin sakar mi ki ragamar MULKIN k`asarnan,a yanzu na dawo da ni za a dama a yi komi har zuwa sanda za mu ga k`arshen wannan musibar",da sauri Sarauniya Junayyah ta raba jikinta da na Malikat Juwairiyya ta na mai cewa,"Kamar ya Mahaifiyata ban gane abinda ki ke son cewa ba?","Hmmmm abu ne mai sauk`i daga yanzu zan sa hannu gami da taimaka mi ki game da sha'anin MULKIN k`asar BAIBAH ",ba Sarauniya Junayyah ba hatta da Boka Dürsäås sai da gaban sa ya buga da sauri ya na mai cewa,"Inai ma ki fatan tsawon rai Malikat Juwairiyya Uwa ga Sarauniyar mu,ta ya haka za ta kasance ba ki ganin kin tsufa shekaru sun kama ki ba abinda ya kamata da ke face ki ci ki sha ki kwanta ki huta ba wai ki damu kan ki da wasu `yan matsaloli na talakawan k`asarnan ba",sai da tai murmushi tace da shi," Haba Kai kuwa Boka Dürsäås, kalle ni fa ka gani,Ina abun ya ke wai maye ya lashe kurwar jariri,ai har yanzu da saurana, zan yi fiye da abinda na fad`a domin ganin hankalin `yata da na mutanen k`asarnan ya kwanta,a kullum ina jin haushi da takaicin dokar k`asarnan da su ka sharrand`a gami da farllanta MULKI akan `ya`yan su mata ba maza ba,da yanzu d`an'uwanki Ishmal shine zai ji da wannan tashin hankalin ba ke ba,balle har abun ya riske ni nima,hakan nema ya sa na yanke hukuncin fito da Ishmal da ga d`aurin zaton da ki kai masa a kurkuku "......" Me ki ka ce, garin ya za ki aikata hakan, wacce hujja ki ke da ita da ta nuna bai aikata abinda a ke zargin sa da shi", Sarauniya Junayyah ta ce cikin sauri"Hujja kuma ki ke tambaya Junayyah, kuma akan Ishmal ,ko kin manta shi d`in d`an'uwanki ne ?,a je ma ya aikata abinda a ka ce ta haka ne ya kamata ki ji da lamarin ?, mai ya sa ba ki tunkare ni da batun ba ki kai gaban kanki,ko ni ba sama da ku na ke ba?,ni ce na haife ku, ku duka biyun,ko da iya matsayina na mahaifiya kad`ai ai ya Isa ki tunkare ni da zancen ko da ba tare da ki yi duban na ta`ba Mulkar wannan k`asar ba,aje maganar hujja da ki ke cewa shin ke ki na da hujjar da ki ka tabbar da Ishmal ya na k`ok`arin sayar da k`asarnan a wurin wasu ko ko duk jita-jita ce da ke?",sai da Sarauniya Junayyah ta had`eye wani abu da ya zo ya tsaya mata a mak`okwaro sannan ta ce"Ki yi hak`uri ya ke Mahaifiyata domin na yi tunanin kamar zan takura ki idan na tunkare ki da wannan lamarin amma ki gafarce ni,na yi kuskure","Ba Komi duk da dai kamata yai ace kin tsaya ma sa a kowanne lokaci ba wai ki kasance macen da ke k`ok`arin kwance ma sa zani a kasuwa ba,ke ko da ya aikata laifin za ki wanke shi,ki kare shi gami da fidda shi daga zargin mutane,in ya so daga bayan fage sai kiyi masa duk hukuncin da ya can-canta da shi","Na bi Allah na bi ki ya ke Mahaifiyata amma dan Allah ki yafe min kuskuren da na yi, na amshi laifina da hannu bibiyu ,"Na ji dad`in fahimtar haka da ki kai game da abinda na zo mi ki da shi duk da dama abun ya dad`e ya na ta`ba ni a cikin zuciyata,sai dai kuma na rasa me ye ya hanani yin magana,da zaran na zo zan yi ma ki zancen si inji kamar an sa kwad`o an rufe min baki","Nima na jin dad`in niyar taimakona a `bangaren MULKI na da ki kai "," Ba damuwa ai duk yi ma kai ne ta ya Uwa za ta iya zama lafiya alhalin `ya`yanta su na buk`atar taimakonta, kin ga kuwa dole in tashi tsaye, Yauwa kin ga har na kusa mantawa in tambaye ki shin ba ki da labarin dawowar Gimbiya Junainah cikin wannan Masarautar ne na ga ta yi har kusan tsawon mako uku da dawowa amma baki ta`ba ko da lek`owa ne ki ganta ba duk da na san kin samu labarin zuwan ta har ma da rashin lafiyar da ta ke damunta",kanta ta duk`ar k`asa ba tare da ta d`ago ba tace da ita,"Ba zan yi mi ki k`arya ba amma tabbas na san komi da ya ke faruwa da `yata Gimbiya Junainah, sai dai a kullum zuciyata a raunane ta ke game da ita ina jin tsoran kar in je inda ta ke domin gudun wani abun kar ya sa ke samun ta","wannan kuskure ne ke fa uwace kuma mahaifiya bai kamata ki rik`a wofintar da lamarinta a kowanne irin tsanani ba,da tun farkon wannan lamarin ko in ce lalurar kin jajurce gami da mai da hankali tare da bata kulawar da tadace da bata tsane ki gami da son yin ne sa da ke ba har haka, duk runtsi da tsanani da akwai k`auna da Soyayyar Uwa a cikin zuciyar kowanne d`a ko `ya, da ita su ke rayuwa a koda yaushe,da kin so wannan Soyayyar ba za ta dakushe ba,da tuni ba wannan matakin ku ke ba, ki kalle ni mana shin akwai irin wannan matsalar a tsakaninmu",ba tare da barta ta ce komi ta cigaba da cewa, "A'a Babu dukk da ba wai babu wata matsala ko rashin fahimta a tsakaninmu ba,a'a kawai dai da akwai abinda mu ke iya jure zafinsa gami da kauda kai tare da iya koya ma kan mu hak`uri da shi me ya sa ba zai sa ki koya daga gare ni ba,in har haka za ki cigaba da tafiya matsaloli da dama za su bibiye ki game da mamaye rayuwar ki,ba iya nan ba hatta da da yanda ki ke MULKAR K`ASASARNAN ya sha ban-ban da yanda na gudanar,ke ba ma ni ba hatta iyayena ba su ta`ba gudanar da MULKIN kama karyar da ki ke ba,talakawa kullum cikin kuka su ke da ke",.... Da wani irin sauri Sarauniya Junayyah ta fad`i gaban Malikat Juwairiyya ta na tsananta kukan munafunci harda mirgina-mirginarta a k`asa tare da cewa," Na rok`e ki da ki dakatar da fad`ar tarin laifukan da na aikata, na rantse gami da yi miki alk`awari Zan gyara duk munanan d`abi'un da ki ka lissafo ",sai da Malikat Juwairiyya ta sa ki wani murmushi sannan ta shafa kanta gami da kamata ta mik`e tsaye tace da ita," Ba Komi ya ke `yata ai ba tuhumar ki na ke ba kawai dai abun ya dad`e ya na damuna ban samu damar fad`a ba sai yau,amma komi ya riga da ya wuce, yanzu ma haka tafiya zan yi ki turo min Wazirin ki zan sha shi ya gyara mana fada yan da za mu ji dad`in zama a cikinta zan sa ya jera mana kujeru hud`u ta wa,ta ki sai ta Gimbiya Junainah da kuma Kawunta Ishmal, domin so na ke mu had`a hannu da hannu wajen ceto k`asarnan daga halin mutuwa da rayuwar da ta fad`a,Yauwa dad`in gushi na manta ban sanar da ke ba Bokanya Aziza na kan hanyarta ta zuwa wannan Masarautar mai albarka domin kulawa da Gimbiya Junaina, Saboda wannan rashin lafiyartata ta matsa mata ta na buk`atar taimakon gaggawa ",ta na kaiwa nan a zancen ta ta juya ta tafi ba tare da fahimci halin da su ke a ciki ba,har Sarauniya Junayyah ta bud`e baki da niyar cewa wani abun Boka Dürsäås yai mata alamar tai shiru ba sai ta ce wani abun.