Son Kauna

2

by @nkds

SON ƘAUNA...🔥🏃💔

An ƙaddara su su ƙaunaci juna, an ɗaure su da nauyin iyali, zuciyarsu ta fashe sakamakon ƙaddara.

NOTE
*Na sadaukar da wannan littafi Mai Taken SON ƘAUNA ga dukkan yaran da aka yasar a faɗin duniya: ma'ana sadaukarwa ce ga duk wani yaro da ya tsinci kansa a Rayuwa ba tare da wani nasa ba.*

Story & Written By
_Nainarh KD⁂𝒩𝓀𝒹𝓈❦♡_

Copy is not allowed.¡!

Ba kuma zan Lamunci a canzan labari kota wata siga ba.¡!

MARUBUCIYAR:
1.  Sarauniyar Kyau
2. Tsantsar SO
3. Aneeserh (Innocent Girl)
4. Kin cuceni
5. Ranar biyan buƙata (rai ba'a bakin komai yake ba)
6. Ba Tabbas
7. Captain Ayusherh
8. Ummul-Jaannah
9. Ba Riba
10. So Dan Rayuwa
                    And Now
SON ƘAUNA!

02
*****
Cikin nutsuwa ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da suka ma ta nauyi har ta kai ga buɗe su gaba ɗaya sai dai dishi-dishi da take gani shi ne ya saka ta sake rufe idanun ruf, wannan karon kam ta ɗan jima sannan ta sake buɗe wa tana ɗan lumshewa sauke idanunta a kan saman ceiling na Ɗakin da take kwance da ta yi shi ne ya sa ta ƙoƙarin tashi zaune tana dafa kanta da yake sara ma ta lokaci guda kuma tana ƙoƙarin tuna abin da ya faru har ta tsinci kanta anan.

Sai dai abin da zata iya tunawa shi ne ibtila'in da ta tsinci Rayuwarta ciki da kuma abin da ya faru a wancan dare har ta gudu daga gida domin ceton rayuwarta sannan sai sama da taji wani abu da batasan mene ba ya yi da ita bayan ya buge ta wannan shi ne abin da zata iya tunawa.

Ƙarar fashewar gilas da ta ji a gefenta shi ne ya tilasta ma ta ɗagowa tare da sauke idanunta a kan wata siririyar mace fara tana riƙe da baki da alama ganinta a zaune shi ne ya sa abin hannunta faɗu wa garin ta rufe baki.

Kafin ta sama zarafin magana sai Matar ta juya da sauri cikin karaɗi take kiran.

“Maman Yara! Maman Yara!! Kizo baiwar Allah ta farka.”

Ta fita tana faɗa. Yayin da Emem ta bita da ido tana ƙoƙarin maimaita sunan da taji Matar tana faɗa cikin harshen Hausa.

Ba'afi mintina biyu ba kuwa sai ga matar ta dawo fuskarta cike da annuri tana biye da wata ƴar kakkaurar mace mai nutsuwa da kamala da sallama suka shigo Ɗakin, Emem ta yi musu shiru tana bin su da ido.

“Sannu baiwar Allah, kin tashi a lokacin da bamu taɓa tsammani ba godiya ta tabbata ga Allah.”

Cewar Matar cikin nuna farin cikinta. Tsawon Rayuwar Emem zuwa inda tasan zata iya tunawa shi ne batasan bayan yarensu na ƙabilarsu da kuma Turanci da take koyo a Makaranta ta iya wani yaren ba sai da ta tsinci kanta tana mai furta.

“Ina ne nan? Mene ne ya sameni? Ina so zan shiga banɗaki...”

Ta faɗa lokaci ɗaya kuma a jere tana kuma ƙoƙarin tashi. Sai kuma ta tsaya cak cikin mamakin kanta jin ta yi irin yaren da suke yi wato Hausa, ta lura suma da kallon mamaki suke bin ta.

“Baiwar Allah ai ina faɗa miki yau kimanin satinki guda ke nan a kwance cikin halin rai ko rayuwa ba abin da Likita da kuma Maman Yara basu yi ba domin ki farfaɗo amma Allah bai nufa ba sai yanzu cikin ikon sa kuma...”

“Haba Aani zaki fara ko wannan surutu naki da baki da matsaya? Bakiji ta ce tanason shiga banɗaki bane?.”

Maman Yara ta katse Aani tana yi ma ta kallo irin na ki rage azarɓaɓi.

Ƴar dariya Aani ta yi tana dafe goshinta ita kanta ta sani bakinta bashi da linzami sai dai duk da haka Allah ya gani tun ranar da Maman Yara tazo da wannan Mata da suke kira da baiwar Allah taji ta shiga ranta shi ya sa bata iya riƙe bakinta a kan abin da ya shafe ta.

Ita ta taimaka ma ta ta rakata banɗakin ta yi abin da zata yi sannan bayan ta fito ta sake riƙe ta suka koma ta zauna a gefen gado duk da ta ce ma Aani ɗin zata iya tafiya amma Aani sai da ta taimaka ma ta.

Shiru Ɗakin ya yi yayin da Emem take wasa da zoben hannunta da ta rasa dalilin da ya sa bata cire sa ba sai dai sanin zai yi ma ta amfani domin sanin Rayuwar da ta yi har ta sama ciki shi ne abin da ya hana ta cire.

Ƙuri Aani ta yi ma zoben dake hannun Emem zuciyarta na bugu na rashin dalili da sauri ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta ji take tamkar tana da wani alaƙa da wannan zoben.

“Baiwar Allah gashi bamu san sunanki ba, sannan ina mai baki haƙuri dalilin tuƙin gangancin da wancan yaron yake damu ya sa muka kaɗe ki sai dai Allah ya rufa asiri abin yazo da sauƙi sai dai kasancewar kina cikin halin firgici da damuwa ya sa kika faɗa suma kuma baki tashi farkawa ba sai yau.”

Tun da Matar da taji Aani ta kira da Maman Yara ta fara magana, Emem ta yi shiru tana saurarenta yayin da kanta ke ƙasa tana wasa da yatsunta ganin ta yi shiru ya sa ta ɗa go ido suka haɗa da matar, sosai take yi ma ta wani irin gwarjini hakan ya sa ta sauke idanunta tare da faɗin.

“Sunana Emem, ƴar asalin jahar Akwa ibom amma a ƙauye muke zaune da Ahalina Babana shi ne shugaban ƙauyenmu sannan ɗan ƙabilar Efik ne wanda a ka fi sani da Ibiobio, mu huɗu ne a gidanmu ina da yayyi maza da yaya mace shekarar da ta gabata na bar ƙauyenmu na tafi birni domin karatun boko bayan an kai ruwa rana da ahalina musamman ma babban yayana da yake ganin aure ya kamata nayi ba karatu ba...”
Daga nan Emem ta kwashe dukkan abin da ta sani da halin da take ciki a yanzu ta sanar da su har kasa iya tuna komai da ta yi. Haka kawai taji ta aminta da mutanen shi ya sa ta sanar da su komai bata ɓoye musu ba har dalilin barota gida a wancan daren ta ƙare da faɗin.

“Wannan shi ne iya gaskiya da na sa ni dangane da kaina da rayuwata sannan da halin da na tsinci kaina mai wuyar fahimta, kuma a wancan daren laifina ne ba na mai tuƙa motar ba domin fita a hayyaci da firgicin da nake ciki shi ne ya sa na shigewa motarku har abin da ya faru ya biyo baya ina mai bada haƙuri a kan hakan.”

“Karki damu ba komai kuma mun fahimce ki sai dai abin da zan ce dake shi ne ki ɗauka nan ɗin tamkar gida ne a gareki sannan ki saki jiki damu ki kuma cire duk wata damuwa da tunane-tunane a ranki ko domin abin da ke cikinki domin na fahimci a koda yaushe ma zaki iya haihuwa da alamu kin daɗe da shiga watan haihuwarki.”

Maman Yara ta yi maganar cikin nutsuwa da kuma sigar kwantar da hankalin wa Emem ɗin domin ta fahimci halin ƙuncin da take ciki kuma ta yarda da abin da ta faɗa domin yanayinta da kalamanta har ma da nutsuwarta bai nuna cewar ƙarya take ba daɗi da ƙari da irin ɗaci dake fitowa daga kalamanta ta lura tun daga ƙasan zuciyarta take.

Maman Yara ta juya ga Aani zatayi ma ta magana ga mamakinta sai ganin Aani ta yi tana share hawaye har da sheshsheƙa da hakan ya saka Emem da kanta ke ƙasa ɗago wa da mamaki tana kallonta da kuma son sanin abin da ya sakata kukan.

“Aani mene ne yake faruwa?”

Maman Yara ta faɗa a ɗan ruɗe.

Sai lokacin Aani ta kalla Maman Yara bayan ta saka hannu ta goge hawayenta sai kawai ta rungumo Maman Yara cikin sheshsheƙa ta ce.

“Bakomai Maman Yara kawai dai na tausayawa wannan baiwar Allah ne Imam gaskiya taga Rayuwa ko nace tana gani Allah Sarki...”

Sai ta ƙara bolum na kukan nata yayin da Maman Yara ta yi kasaƙe cikin al'ajabi ta ma kasa magana.

Emem kuwa wani irin son Aani ɗin ne irin na yan uwantaka taji yana shigarta jin wai daga taji labarinta shi ne take kuka kamar wacce akayi ma bishara da mutuwar uwanta.

“To ya isa ki bar kukan haka kinji? Kuma sunanta Emem ta ce ba wai Imam ba”

Cewar Maman Yara tana ɓanɓare Aani ɗin daga jikinta sai kuwa Aanin ta sake ta tare da komawa ta rungumo Emem tana ci gaba da kukanta ita Emem abin ma sai ya bata tausayi da dariya duk da kukan domin tausayinta ake yi.

Maman Yara ta girgiza kai kurum tana jinjina zuciya irin na Aani tana da rauni ta zuciya, a halayya ba ruwanta tana son mutane ga faran-faran duk da ita ma abar tausayi ce amma sai takeyi ma ƙaddarar Emem kuka bayan ita ma nata  ƙaddara abar a yi kukan ce. A shekaru Aani zata kai irin Ashirin zuwa da ɗaya Saboda haka ba wata babba ba ce yayin da Emem ba zata wuce Ashirin ba saboda haka za'a iya kiransu da kusan sa'anni, yayin da ita kuma Maman Yara ta girme musu domin aƙalla zatayi talatin da tara zuwa arba'in.

____
Kwanakin da suka biyo baya ga Emem masu daɗi suka kasance cikin wannan gida da take zaune tare da waɗan nan mutanen masu karamci, gidana ne amma irin gida marayu domin marayun ne a ciki Maman Yara ita da ƙanninta da take kira da wannan yaron duk da ba wasu shekaru masu yawa bane tsakaninsu domin bai wuce shekaru biyar ta bashi ba sai dai ɗaukarta da ya yi Matsayin uwa yasa take kiransa da haka yana da mata da yaro ɗaya mai shekaru biyu a duniya, sannan sunansa Alhaji Muzzafar shi da Madina wato Maman Yara da mutane ne suka saka ma ta wannan suna sakamakon karamcinta, sun rasa iyayensu tun basu da wani wayo sanadin hatsarin mota kuma da yake iyayen nasu sun rasu sun bar dukiya mai yawa shi ya sa rayuwarsu bata wani tagarayya ba a hannun Ƙanwar mahaifinsu kafin ta rasu suka taso bayan rasuwarta ne kuma Yaya Madina Maman Yara ta yi sha'awar buɗe gidauniya da zata ke kula da yaran da suka rasa iyayensu da waɗan da a ka watsar a titi kuma da yake da zuciya ɗaya ta yi niyya Allah ya kuma dubi zuciyarta cikin ƙanƙanin lokaci tare da taimakon ƙanin nata ta buɗe gidan marayun da take kula da Marayu cikin dukiyarta sai kuma idan wasu daga jama'ar gari sun yi niyya musamman masu abin hannu sun bada sadaka sai ayi wasu hidin-dimun da shi, cikin shekarun da ba za su gaza biyar ba gidan marayun nata ya yi suna sosai bisa taimakon marayu har da gajiyayyu da take yi, Yaya Madina Maman Yara ta taɓa aure sau biyu, sai dai na farko kishiya ta hanata saƙat haka auren ya mutu da sauran so na biyun kuma mai gidan nata ne ya rasu kuma bata taɓa haihuwa ba a ko'ina zuwa yanzu ma ta a je zancen wani aure a gefe kula da yara da gajiyayyu da dukiyarta da samun lada ta silar hakan shi kaɗai ma ya ishe ta a acewarta.

Ranar da motarsu ta kaɗe Emem lokacin sun dawo daga kai ziyara garin iyayensu ita da ƙanninta da matarsa da ɗan ta sun yi dare da hakan ya zama silar haɗuwarsu da Emem.

Shekaru biyu da suka gabata Maman Yara ta haɗu da Aani cikin wani mummunan hali da ta kasance an yi ma ta kurciya ne daga gida kuma bayan haka ma ba'a barta ba sai da aka haɗa da shafe ma ta tunani da kusan saka ma ta lalurar hauka sai dai cikin amincin Allah bata haukacen ba duk da tasha wuya kuma har yau bata iya tuna daga inda ta fito tun tana damuwa har ta haƙura tana zaune tare da Maman Yara cikin aminci tana kuma tayata da kula da gidan marayun da nata basirar duk da cewar har ma'aikata Maman Yara ke da masu taimakawa da waɗan da suke yi domin Allah dama waɗan da take biya.