TAEESH

CHAPTER SIXTEEN

by @zinariya0102

Jin furucin da ya yi yasa Yaya Sahura faɗin: "Allah ya yi maka albarka" "na ji ana kiran sallah bari in tafi masallaci" Malam Ali ya faɗa yana tashi, waje ya nufa don yana da alwala tun ta magariba. Yaya Sahura ta fito tana magana.

"Kai ma sha Allah yau na zo a sa'a ni nasan kowaye ɗan uwana Allah dai ya ƙara mana danƙon zumunci".

Ɗakin da Wasila take ta nufa, don daman shi kaɗai ne ɗakin saukar baƙi.

Wasila da take ta saƙe-saƙe a zuciyarta tana ganin Yaya Sahura da sauri ta ce "Ya yadda kuwa?" Sahura ta ce " Ai ɗan uwana ba shi da matsala don ko ban zo ba daman nasan ni zan yi hukunci da dukiyarsa"

Wasila ta ce " Ki yi wa Allah ki hana wannan abu da Baba zai yi, ni nasan wanda ya kawo wannan shawara ba zai wuce yayanmu Isma'ila ba, kuma alkur'an bai isa ba" Yaya Sahura ta ce "Kinga Wasila kawai ki yi shiru ni nasan yadda zan yi" tuwon dare suka ci, sannan suka yi sallar isha, Radiyo Wasila ta kunna musu, amma babu wacce take fahimtar abin da ake ce wa, kowacce ta lula duniyar tunanin wannan rikici da yake neman ɓallewa a cikin gidan nasu.

Har goma malam Ali bai shigo gida ba, A'i duk ta damu, fushin malam Ali yafi komai ɗaga mata hankali, yadda bai ci abinci ba tunda ya dawo, haka ita ma bata ci ba, damuwa da rashin nutsuwa sun kanainaye zuciyarta. Jin shigowarsa yana kulle gidan yasa ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin "Alhamdulillah" cikin ranta, "Sannu da zuwa" ta faɗa lokacin da ya ƙarasa shigowa cikin gidan, a daƙile ya amsa " uhumm" zatonsa Yaya Sahura tana ɗakinsa, hakan yasa ya nufi ɗakin A'i, binsa ta yi da sauri, haska TAEESH ya yi da touch ɗin hannunsa, yana kallon fuskarta, ganin yadda take bacci cikin nutsuwa sai ya ji daɗi. A'i ta durƙusa ƙasa ta ce "malam ka yi wa Allah da ma'aiki ka yi haƙuri ka yafe min, sharrin shaiɗan ne" gyara zama ya yi yana fuskantar ta ya ce "Dama haka za ki ce sharrin shaiɗan ne, ku yi abu ku dinga dangana shi da shaiɗan, bayan kuma kun san kaidin ku ya fi na shaiɗan ɗin zafi" ta ce "ka yafe min don Allah, nasan na yi laifi bazan ƙara aikata hakan ba ka yi haƙuri malam" ganin yadda duk ta yi laushi yasa ya ce "Shikenan na yafe, amma don Allah ko nan gaba kar ki ƙara biyewa Wasila har hakan ta sake faruwa" ta ce "yanzun ma ba da ni ta yi ba, ita da Rabi ne kuma kasan halin Rabi ba a nuna mata yatsa bata karya shi ba, ba yadda ban yi ba, don kar hakan ta faru amma sun fi ƙarfi na, alkur'an har danasanin zuwansu nayi" nan ta sanar da shi duk abin da ya faru, sanin halin Wasila da Rabi yasa ya gane A'i ba ta da laifi, tsakanin mata da miji aka ce sai a Allah, a daren suka shirya. Tare suka ci tuwon daren cikin farinciki yana ta santin tuwon ya yi daɗi, sai da ya gama sannan ya yi wanka, sanin yanzu dai Yaya Sahura ta bar ɗakinsa ya nufi can ya shirya ya yi kwanciyarsa. Daman tunda Wasila ta zo baya iya kwana a ɗakin A'i, wani lokacin sai dai cikin dare ya dawo, dukkansu a takure suke a gidan nasu.

Tun Asuba Yaya Sahura da Wasila suka shirya, A'i ta shiga ɗakin don gaishe da su, taga kowacce a shirye bayan an gaisa ta ce "Ba dai komawa za ki yi yau ba Yaya?" Sahura ta ce "Yau ɗin nan zan koma in Allah ya yadda" A'i ta ce "Da kin ƙara kwana ko biyu ne" "Mtswww iyayi da kinibibi" ce war Wasila tana ɗauke kanta.

A'i bata ƙara magana ba, ta fita ta hura wuta koko ta ɗora, murhu biyu ta yi ɗayan ta ɗora ɗumame, kafin Malam Ali ya shigo har ta gama ɗumamen, sai da suka ci suka ƙoshi, Wasila ta ɗauki kayanta kala biyu ta bar sauran, suka fito tsakar gida, Ali suke jira don shi bai san yau zata koma ba, yana shigowa ya ce "Lafiya na ganku haka?" Sahura ta ce " Tafiya zan yi, kar na rasa motar ɗaukan kaya ne in hau mai tsada yasa zan yi sammakon nan" ya ce "Tare za ku tafi ne?" Wasila ta ce "Eh Yaya Ali amma zan dawo akan maganar gonan nan zan je, nasan duk wannan hirin Yaya Isma'ila ne, kuma alkur'an babu wanda ya isa ya cuceka don anga baka garin" ya ce "ni dai banason tashin hankali Yaya Sahura da kin haƙura kawai" ya ƙarasa maganar yana kallonta.

Ta ce "Ba mu kuɗin mota banason wannan ragontar taka ta fusata ni" ɗakinsa ya shiga ya ɗauko ɗan abin da yake da shi ya miƙa mata, ta ce " Allah ya amfana, mu mun tafi" A'i ta ɗauko turare a kwalba, da sabulai da janbaki ta miƙawa Wasila ta ce "gashi babu yawa ku gaida su Kawu da kowa da kowa Allah ya tsare hanya" ta miƙawa Yaya Sahura ɗan kuɗin da take da shi ta na faɗin "Ga wannan babu yawa Yaya ayi wa yara tsaraba, Allah ya tsare hanya" a raine ta ƙarɓa tana faɗin "To Alla amfana" rakiya suka yi musu A'i ta tsaya a soro malam Ali ya rakasu sai da suka yi nisa sannan ya koma.

Cikin sa'a suka samu mota saura mutum biyu, suka hau, sai garinsu.

A can garin Dumama kuwa, Kawu ne tsaye da dillalai su malam Salisu da malam Iliya suna magana akan gonar. malam Iliya ya ce "Baba alkur'an ba ƙaramin alheri za a samu ba idan aka sallama gonar nan" "Ƙwarai kuwa zancenka gaskiya ne malam Iliya, don ko mu dillalai za mu samu la'ada mai kyau hahhh" ce war Malam Salisu, Kawu Tanimu ya ce "Yanzu dai an gama magana gona dai na sallama. "To,to madalla malam Iliya ai sai a kira Alhajin a sanar da shi su tawo da kuɗin ko ya ka gani?" malam Iliya ya ce " Yanzu kuwa malam Salisu" wata ruɓaɓɓiyar waya ya ɗauko daga aljihunsa, ya dinga wulwulata sama, yana faɗin "Babu niyowak (network) dole sai na kamo layin nasa" kusan mintina biyar ya ɗauka yana wulwula waya sama, sannan ya sauke hannu ya shiga latsa number Alhaji Inuwa.

Daga can Alhaji Inuwa ya amsa, jin dillali ne yasa ya san an sallama masa gona. Take Malam Iliya ya shiga faɗin "Yauwa Alhaji daman batun gonar nan ne, sun tsayar da shawara har sun sallama ma" "In ji uban waye ya ce mun sallama gona, to Alkur'an duk wanda ya siya to kuwa ya sai asara da kuɗinsa, gona ba ta siyarwa ba ce" Muryar Wasila ta daki kunnuwansu. "To rasa kunya ɓeran tanka, wa yasa bakinki a wannan maganar, jaɓa sa baki a bar miki dole?" Kawu ya faɗa yana jin haushin zuwan Wasila, Yaya Sahura ta ce "sannu Kawu fatan mun same ku lafiya" bata jira amsawarsa ba ta juya ga dillalan ta ƙanƙantar da idanu ta ce "Alkur'an duk wanda ya ƙara zuwa da maganar siyar da gona a cikin ku sai na makashi a kotu, don yanzu ma daga wajen Ali nake bai amince a siyar ba, don haka ku bi nan" ta faɗa tana nuna musu hanya.

Abin ka da mutanen ƙauye nan da nan hankalinsu ya tashi, malam Iliya ne ya ce "Allah ya sani ni daman bansan da maganar ba, malam Salisu ne ya zo min da ita don haka ni babu ruwana" malam Salisu dillali da ya taɓa zuwa wajen ƴan sanda dalilin filin rigima da aka siyar duk da maganar har gaban mai gari, amma waɗancen masu filin suka zo har garin suka kamasu suka kai wajen ƴan sanda, sai da ya biya la'adar da ya ci, bayan dukan da ƴan sandan ƙauye suka naɗa musu, aikuwa jikinsa ya hau ɓari yana faɗin "A'a fa nima ba ni na ce a siyar ba, shi Alhajin ne ya gani ya na so, amma tunda abin bai yuyu ba, malam Iliya kira Alhaji ka ce masa an fasa kawai" Kawu yana faɗin "A'a kul kuka kira hi, ni nan na amince a siyar ko suna so ko basa so" malam Iliya tuni ya ɗaga wasa sama ya fara wulwulata don kama network, yana yi yana gumi don tsananin tsoro, Wasila da Yaya Sahura kuwa sun sa su a gaba fuska a ɗaure.

"Assalamu alaikum yauwa Alhaji kar ku zo, babu zancen siyar da gonan nan, ashe mai ita bai amince ba,don Allah a yi haƙuri Alhaji a nemi wata" Alhaji ya ce "Idan kuɗin ne bai masa ba a ce na ƙara masa dubu ɗari biyar akai" fuzge wayar Wasila ta yi daga hannun malam Iliya ta sa a kunnenta "Kai malam gonar mu ba ta siyarwa ba ce, alkur'an idan ka matsa sai mun yi shari'a da kai, yo na ga macuci ni nan da kake gani kuɗinka bai isa ya buɗe min ido ba ahee" take Alhaji Inuwa ya ce "Shikenan kun yi wa kanku, matsiyata a haka za ku ƙare" gaka nan baban matsiyaci, asararre, mugu kaga dukiyar bayin Allah kanaso ka yi handama da babakere to aniyarka ta bika" kashe wayar Alhaji Inuwa ya yi yana ta zage-zage daman ɗan duniya ne bariki kawai yasa a gaba.

Kawu in banda ƙwalla babu abin da yake yi, "ungo wayarka tsohon najadu, billahillazi na ƙara ganin wani ya zo da sunan maganar gona sai na yi masa ɗiban albarka" Sahura ta ce "Me ai hukuma ce kawai za ta raba mu da mutum, don sai mun ɗaure shi a gidan yari" ta ja hannun Wasila suka shige cikin gida.

Kawu Tanimu ya buɗe baki zai yi magana, malam Salisu ya ce "Kar ka ce komai Baba, wannan magana dai a barta yauwa na barku lafiya" malam Iliya ya ce Tsaya ni mu tafi, Baba sai haƙuri waɗan nan matan ba mutunci ne gare su ba, alkur'an idan ka matsa duk da kai ubansu ne sai su kai ka gidan yari" suka kama hanya suka tafi.

A zuciye ya shiga gidan " Ina kuke marasa mutunci, ku dai kun yi asara" Yaya Sahura ta ce "Sai haƙuri Kawu, ita gaskiya ai ɗaci gareta" ta yafa gyalenta ta na faɗin "Ni na tafi" Inna Uwa kuwa sai tambayar meke faruwa take.

Wasila da tunda ta shigo kowa yasan mara kunyar gida ta dawo, sai maganganu take yi, Baba Tanimu ya ce "Kun zo kun wargaza abin alheri ranki ya kwanta dole ki ɗane ɗan kai da gyale ki tafi, marasa mutunci" Yaya Sahura ta yi tafiyarta, Wasila ce ta ce "Baba-Baba alkur'an ina jiye maka azabar da ake yi wa masu cin dukiyar marayu ranar gobe ƙiyama, hiyasa bazan bari ka higa halaka ba" "Rufe min baki munafukar banza munafukar wofi, shine kika biyota zungwi-zungwi kuka zubar min da ƙima a idon jama'a" Inna Uwa ta ce "Ba dai an fasa siyan gonar ba" ya ce "an fasa sun lalata komai" Abida da ke yi wa yarinyarta Shamsiyya tsifa ta ce "Shikenan ma zance ya ƙare kowa sai ya haƙura".

Isma'ila kuwa da ya haɗu da su malam Salisu a hanya sanar da shi komai su ka yi, tamkar ya tashi sama haka ya ke tafiya. Kan Wasila ya nufa zai daketa, ta matsa da sauri tana faɗin "A'a yaya alkur'an yanzu ba daa ba ne, kar ka fara wannan gangancin" "Ni kike wa rahin kunya, to ko zaki dake ni ne?" ta ce "A dai kiyaye don akan yaya Ali sai in da ƙarfi na ya ƙare, aure za mu yi bazan bari a salwantar masa da dukiya ba ahee" Abida ta ce "Wai ke Wasila me yasa ba za ki daina wannan haukan ba, yaya Ali fa ba aurenki zai yi ba, aurenki ɗai-ɗai ɗai-ɗai har guda tara fa, hmm iska na wahal da mai kayan kara" ta ci gaba da abin da take yi.

Faɗa dai a gidan Baba Tanimu daga an yi da wannan sai ayi da wancen, kowa yasan ƴar bala'i ta dawo, Wasila bata da kunya bata ragawa kowa.

Abin da yake kashe mata aure kenan, bala'i da masifa, faɗa dai ta yi da miji ta yi da danginsa, maƙota da abokansa ma yi take, da ta fito take samun wani mijin ta aura, wannan karon ne dai ta dage sai ta cika burinta na auren Ali.

Yaya Sahura ta koma gidanta cikin farinciki, labarin duk yadda aka yi ta ba wa mijinta da Mudan ɗanta, sun yi murna ganin ta hana a siyar da gonan, malam Kabiru yayi ta sa mata albarka, sai kuma ta rushe da kuka, hankalinsu a tashe suka hau faɗin "mene ne kuma?" ta ce "Ina tausayawa Ali idan ku ka ga yadda ya koma sai kun tausaya masa, mace ta shanye shi, sai abin da ta ce a gidan nan, ga ƴar shegen da ya ɗauko ta yi wayau sai gina su yake sun yi ƙalau da su" malam Kabiru ya ce "Yo kema kinsan wannan matar tasa ta riga da ta gama da shi, yana da halin ƙara aure amma ta hana hi, ko da ya yi sai ta kori matar, ba dole ya yi haƙuri ba" ta ce "Ai wannan karon bata isa ba yanzu ya amince zai yi auren" ya ce "uhm ai kema kinsan da zarar matarsa ta ji shikenan zance ya ƙare, kawai ku taya shi da addu'a Allah ya raba shi da wannan matar" ta yi shiru tana tunanin hakane fa, idan ba a ɓoye akai maganar ba, ba a auren, kuma idan an yi wata ko shekara ba a yi, sai su yi ta faɗa da Alin har auren ya lalace........

Zinariya ce✍🏻