Chapter 7
by @khairatup01
SHIGEN ƘAUNA
Khairat.
Wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01.
Paid Book.
#500
free page 5.
Yau ma bikin wani abokinsu ake yi wai yau za ayi ball bai ma so zuwa ba amma Aslam ya dage sai sun je. Duk sun saka kayan ball ɗin amma ban da Nabeel. Shadda ya saka ya fito. Aslam na ganinsa ya gyaɗa kansa kawai daman ya sani ba zai saka ɗin ba. Mota biyu suka yi suka tafi wurin ball ɗin.
Misalin ƙarfe takwas ne na dare. Ƙawayen amarya ma sun isa amma basu fi su goma ba saboda yanayi na dare yawanci ba su zo ba sai na jiki sosai kawai da ƙannen amarya.
Ni ma ina cikin waɗada na zo ball ɗin bikin Summaya da mijinta Ahmad.
Abaya na saka baƙa na yi rolling da wannan veil ɗin da ake faɗa jersey veil mai laushi original ɗin na saka. Na saka gilas baƙi na rataya baƙar jaka doguwa ta gefe na saka wayata a ciki da mukullin motata.
Ni da Summaya muka shiga lokacin ma na fara bugawa sai sowa ake yi. Abin ya burge ni ina gefe ina yi musu bidiyo da yadda aka ce maza su zagaye ango amarya zata buga ƙwallo a raga. Ana dai ta sowa kamar ance in ɗago sai kuwa na yi tozali da Yakasai a zaune a kujera daga gefe. Shi ba ma su yake kalla ba wayar sa yake dannawa. Nayi mamakin ganinsa kam haka ya saka a hankali nace "Yakasai".
Shi ma a hankali ya ɗago kansa ya kalle ni. Sai na ga kamar bai gane ni ba ma sai na ɗan ji ba daɗi.
Na yi zaton ma zai taso ne sai na ga ya maida kan sa kan wayarsa yana dannawa sai na ji na muzanta wata zuciyar tace "Kai waye shi haka me ma ya kai ni kula shi tun asali? Mtsew."
Duk ba daɗi jikina haka na ci gaba da sabgogin taron. An yi hotuna daga nan muka ci snacks muka sha lemo.
Summaya ni dai na tafi sai gobe. Kin san bana son inyi dare sosai.
To na gode Allah Ya kai mu.
Amin.
Ango Allah huta gajiya.
Amin mun gode fa ƙawar mu.
Da haka muka rabu. Da zan fita sai na gan shi da wani ina ga abokinsa ne na yi gaba ba tare da na ƙara kallonsa ba.
Har na je gida ina jin haushin kaina da Yakasai da ya yi min haka. Allah Ya so ma babu kowa mu kaɗai ne kawai a wurin.
*
Ban gane ta ba sai da ta bar wurin sai na ji ban kyauta ba ko da ban gane ta ba bai kamata na yi mata haka ba. Na ƙudurta a raina cewa zan bata haƙuri in na kuma ganinta na san ta ji haushi. Cikin ikon Allah sai ga shi na ganta zata tafi amma yanayin yadda ta tsuke fuskarta ya sa na kasa kula ta ga shi dama Aslam na wurin zai iya yi min dariya in ta dizga ni.
Da na ga motar da take hawa ma sai na ji jikina ya ƙara yin sanyi lakwas duk yadda aka yi ƴar babban gida ce.
Haka muka koma gida nima ina ta ganin rashin dacewar hakan da na aikata. Bana kula mutane musanmman ma mata amma duk da haka bana wulaƙanta mutum ya zama dole na bata haƙuri.
*
Washegari Heena party aka yi. Gaskiya na ji daɗin shagalin bikin Summy sosai don na yi nishaɗi.
Washegari aka yi dinner party muka saka ankon bikin material ne army green duk anyi makeup ban da ni. Don ni ba gwanar kwalliyar ba ce fara ce ni sosai gashin idona da yawa fawda kawai na shafa na saka janbaki na baza gashina na faka ta baya na yi ɗaurin nan na zara buhari don ina son ɗaurin sosai.
Ni nake taka masu baya sai saura a bayan mu.
Ina raka Summy aka yi mana hotuna da ita na koma wurin zamana a matsayina na aminiyar amarya na zauna , na sa aka canjo min kuɗi dubu goma na sa aka canjo min ƴan hamsin da ƴan ɗari so nake na fito da ƙawata na yi mata kara.
Komai na tafiya cikin tsari. Ɗinkin ya yi min kyau sosai ni kaina na ji daɗinsa bai matse ba kamar ya auna ni tun can.
Aka kira ƙawaye suyi rawa ni dai ban yi ba na dai ce a sanar ina son a bani fili ni kaɗai da ƙawata.
Nan fa MC ya dinga shelar aminiyar amarya Hajiya Nadeeya zata fito ta yi wa aminiyarta kara.
Haka na fita na dinga yi mata liƙi sai da na liƙa mata kuɗin nan tas na rungume ta na fita daga filin aka dinga kallona. Da yawa mamakina suke yi. Shamsiya kuwa sai harare-harare take yi kawai.
Daga nesa na hango shi yana kallona , ni kuma na ɗauke kaina gefe na ci gaba da sabgogina.
Daga sama na ji magana a kaina "Asalamu alaikum."
A hankali na ɗaga kaina ina kallonsa na amsa masa don sanin girma da muhimmancin amsa sallama.
"Wa'alaikums salam."
"Zan iya zama?"
"Ka zauna mana ai ba kujeruna ba ne."
"To na gode."
"Uhm."
"Hajiya kiyi haƙuri bisa abinda ya faru jiya. Ba zan miki bayani ba don tabbas ban kyauta ba amma zan iya baki haƙuri."
"Ba komai ta wuce ban riƙe ka a rai ba dama."
"Aa Hajiya.."
"Nadeeya suna na."
"To nima a daina ce min Yakasai Nabeel nake."
Murmushi na yi masa kawai.Ƙasan raina kuwa yau na tuno da wani abu daga rayuwata wanda ya saka na ji ina son zama a irin wannan yanayin.
"Kayan sun miki kyau fa."
"Ɗinkin ya fito da kayan dai."
Muka yi dariya duk mu biyun.
Sama-Sama muka ci gaba da hirar. A nan aka kawo mana abinci muka ci. Ban tsaya an gama bikin dani ba na yi mata sallama na tafi. Har bakin mota ya raka ni.
"Allah Ya tsare hanya Hajiya."
"Bana so."
"Afuwa."
*
Tashi na yi da safe da wani tashin hankali. Wai hotona ne ta yawo da na Nabeel a soshiyal midiya a wurin dinner bikin Summaya muna hira muna dariya. Wacce kalar masifa ce wannan? Waye da wannan aikin?bani da amsa.
Ina saukowa falo na ji muryar Yaya Muhammad yana ta faɗa na kalli agogon bangon falon na yi tsaki a fili a raina kuwa cewa nayi "Da farar safiya masifa na ciyo shi ,shi ya sa ya wani taho don ya ɗagawa Umma hankali."
"Yauwa sauko nan. Zo ki gaya min waye wannan?"
Zaunawa na yi na gaishe da Umma tukunna. Sai ta ƙi amsa min tace "Tambayar ki fa ake. Yanzu da girman ki da ilimin ki."
"Umma ban gane da girmana da ilimina ba. Me na yi ne wai? Me na yi? Gaskiya baku kyauta min ba. Ba tare da jin komai daga gare ni ba zaku yanke min hukunci? Shin wai me ma kuka gani ne kuke tuhumata haka? Rungume ni ya yi ne ko wani mugun abu aka ga na yi?" Na tambaye su na tsatare su da idanuwa masu kaifi.
Sai suka yi shiru. Aka rasa mai bani amsa.
In ma na kula shi muna dariya sai meye?
Yaya Muhammad yace "Eh kya yi mana wulaƙanci mana kina taƙama kina da dukiya. To mu ba sa'anin ki ba ne dole in kika yi ba daidai ba mu gyara miki."
To sai ka gaya min laifin da na yi Yaya. Kuma meye ya kawo batun dukiya a nan in dai ba wani abu ka shirya ba a kaina?
Shiru ya yi. Umma taga abu zai koma faɗan cikin gida tayi sauri ta shiga tsakani tace "Ba fa na son wannan shirmen. Ya ishe ni hakan nan."
Shiru na yi ban ƙara cewa komai ba.
Shi ma Yayan bai ƙara cewa komai ba don ya san na fi shi gaskiya. In ma na kula.Nabel meye ba zan yi aure ba ne?
Ni da kaina na maimaita tambayar da na yiwa kai na ta "Aure."me kenan? Shi ne tambayar da nake yi wa kaina.