Page 24
*KARAGAR MULKI
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 24
"Me ya sa za ka dakatar da ni ?,Ai da ka bari na yi magana da ita wata k`ila in iya sawa ta dakatar da zuwan Bokanya Azizah",
"Ai da yi ke ma wata k`ila ki ka ce,kin ga kenan tun a zancen ki kin sa rashin tabbas a ciki,duk abinda ki ka gani ya na d`aya daga cikin abinda ki ka jawo mana,da ba ki aikata abinda ya faru ba da hakan ba ta kasance ba ,daga dukkan alamu aikin da mu kai ma Malikat Juwairiyya ya sa ke ta,hankali da tunanin ta duk sun dawo jikin ta tunda har ga shi ta na maganar `ya`yanta da kuma sarautar da ta gada tunda dad`ewa",", To yanzu MENE NE ABIN YI ?,Zuciyata ta karaya,ban San me ya kamata inyi ba Kai na duk ya cushe ","A dajin da Babu zaki Kura ma d`aukar kanta a matsayin Sarauniya ta ke sai ta jangwalo ma kanta masifa da bala'i sannan ta ke gane kuranta,ki barta ta nuna iya iyawarta mu gani daga baya za mu sami hanyar da zamu `bullo ma ta"," Anya kuwa ayi haka inajin tsoro Boka Dürsäås, au na shafa'a ka gafarce ni,ina nufin Kawuna na kan ji ma su iya magana na cewa kaji tsoran farkawar tsohon zaki daga barci ,domin a matuk`ar haukace tare da mayunwaciyar yunwa ya ke farkawa,ba ka tunanin Malikat Juwairiyya ta dawo da shirin da ya fi namu ne ?,ji fa yanda kai tsaye ta ke mana magana game da isar da sak`onta cikin da jin kai da d`agawa","Safiya ke nan duk sanmakon ka wani a tafe ya kwana,ko kin manta ansa da wuyan biri amma a ke k`ullesa a k`ugunsa,don haka ki zuba Ido ki sha kallo muddin ina da rai sai na cika burin kaka na na hud`u "," Me ne kakan ka na hud`u dama shine wanda ya ja mana wannan fitina da bala'in, har ya sanyaka ka d`ora mahaifinmu bisa tafarkin da ya zama sanadiyar mutuwarsa a k`asar BIHINAR, an ya kuwa muna da asalin mai kyau dukkanin ku na ga a wulak`ance a tagaiyare ku ke mutuwa ko dai ?",......"A kullu d`in ki na hane ki kar ki kuskura ki k`arasa abinda ke saman bakin ki in kuwa kin k`i zai zame mi ki danasani na farko a rayuwar ki,zai fi ma ki kyau ki mai da hankali a kan abinda ya ke gabanmu ki nemo hanyar da za ki hana Bokanya Azizah za ma a cikin Masarautar nan","Hmmmm bazan ce ma ka hakan ba zai yiwu ba ,amma abumafi a'ala mu samu wata hanyar ta korarta ko kuma yin sulhu da ita","Ta ya ki ke tunani za ki samu yarda ko aminci a wurin wannan maha'inciya kuma mayaudariyar Bokanyar,ita kanta abar tsoro ce a karankanta to ta ya za ki mik`a mata ragamar rayuwar ki,ai kai tsaye jifan gafiyar `baidu za ai bawan ba k`ani,ko kuma ai mik`i talek`o ta koma ko a Kira labarin na ki da bad`i ba rai,ta sannin ta sanki cikin ba hatsi ba,tayi ma na mugun sani hatta da da k`udirin mu ta sani ke har ke ta san asalin wacece ke "," Na shiga uku ya za ai mu yi ji da wannan matar kar ta za me mana k`adangaren bakin tulu,a kassa a kashe tulu a barshi shi ya `bata ruwa mai zai hana ba za ka bata wani kaso mai gwa`bi da ga cikin abinda mu ke saran samu ba,wata k`ila ta yarda tunda na San ita d`in tsohuwar makwad`aiciya ce","Da kyau `yata na ji dad`in wannan batun na ki,hakan ya tabbatar min da ke tsatson mu ce mai yiwuwa hakan yai aiki,bari ta zo sai muyi mata tarba ta musanman".
Tunda Malikat Juwairiyya ta fita sai faman waige-waige ta ke a cikin masarautar gani ta ke kamar an sa ke masarautar,ko kuma an yaye ma ta wata yana da ta lullu`be ma ta saman idaniyarta,daga can gefe ta hango wani kamar ta san shi sai faman musayar miyau a ke da shi da'alama dai wani abun ya ke so Dakarun da su ke tsaron k`ofar shigar su ka hana shi,kamar wacce a ke sarrafata haka ta juya ta nufi wurin,kusan su duka a tare su ka zube su na mai kwasar gaisuwa a gare ta,"Wa na ke gani anan kamar Malam Musa ? ",ta jeho mu da tambaya ba tare da ta amsa gaisuwar d`ayansu ba," Ni ne ya shugabata, na zo ne da niyar neman izinin ganin `Dan'uwana kuma a bokina Ishmal amma wa'innan sakarkarun Dakarun sun hana ni","kamar ya sun hana ka akwai wata doka ne da ta zartar da wannan hukuncin ban sa ni ba ?",ta sa ke tambayarsa,"A'a sun ce wai Sarauniya Junayyah ce ta ce kar wanda a ka bari ya gansa sai da izininta,to na zo nan ne domin in neme izinin a wurinta sun hanani,jiya ma na zo sun kore ni, shine yau na tsaya tsayin daka a kan sai na ganta","Ka yi kyan kai, to amma garin ya haka ta faru,shin wa'innan Dakarun ba su da hankali ne da har su ka kamanta matsayinka da girman ka a masarautar nan ne ko me?",Da sauri Malam Musa ya d`ago da kansa ya na kallonta yaushe rabonsa da wannan matsayin ,ko fadar ma ya manta yaushe rabon da ya halacci zamanta,"Ai ran ki ya dad`e abubuwa da dama duk sun canja tun bayan saukar ki daga kan KARAGAR MULKI Komi ya ta`bar`bare hatta da talakawanki kullum cikin kuka da MULKIN kama karyar da a ke gudanarwa su ke","Kaico tur da kasancewata cikin wannan yanayin na rashin sanin kai na ,yi maza ka je ka sanar ina son yin zama da duk wani mai matsayi ko fad`a aji a cikin Garinnan, hatta da `yan kasuwa attajirai da masu kud`in Garinnan,duk wani mai matsayi a cikin fada yai saurin hallara wannan sak`o ne daga bakina ni Malikat Juwairiyya da izinina da kuma miyan bakina,ai saurin aikata hakan ",wasu zafafan hawaye ne su ka zubo daga fuskar Malam Musa muryarsa na rawa ya ce," Lalle ne yau na k`ara yarda gami da sakankancewa da lamarin Ubangiji da kuma girman k`udirarsa,tabbas komi girma ko nisan abu dole ne wata ran k`arahensa ya zo kar ma in akace an keta hukunci da dokar Allah, yau ga k`arshen zaluncin k`asar BAIBAH ya fara zuwa,yanzu za a aikata duk abinda ki ka ce da izinin mai duka ",Da a kayi wannan zaman ba k`aramin tashin hankali Malikat Juwairiyya ta shiga ba,Wai ya akai haka ta faru kuma duk ta na inane hakan ta faru mene ne ya faru da ni da har na kasa ji da ganin duk abinda ke faruwa,talakawa na kullum a cikin kuwa da ihu su ke amma ban ta`ba ji ko ganinsu ba,ko da wasa ba na ji kawarsu daga k`arshe da k'yar ta iya mik`ewa da niyar barin wurin,har ta kusan fita ta juyo ta ce," Malam Musa ka tafi kai da Waziri ku fito da Ishmal, ka kai sa sashensa bayan kwana biyu ya huta za mu sa ke wani zaman dan mu samo mafita game da dukkanin abinda ya ke faruwa a k`asarnan",aiko wannan zance ba k`aramin dad`i yai ma Malam Musa ba, Kai tsaye ba tare da ya jira komi ba su ka nufi gidan kurkukun.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
"Me hakan ke nufi in dai har da gaske su Jamal sun gudu daga cikin kurkukunnan, kenan haka na nufin da gaske Ummata Mahaifiyata ta zo cikin k`asarnan har cikin d`akin kurkukun da mu ke,shin wacece ita a wanne matsayi ta zo wurina,shin fatalwace,aljanace ko-ko kurwace,Kai ko ma wacece na yi farinciki da ganinta kuma a kowanne matsayi ta ke zan iya rayuwa da ita,Kai ko da zata zama abu mafi muni da jin tsoro a duniya indai za ta cigaba da zuwa inda na ke da sufar mahaifiyarta abar k`aunar ta,to zan bita kuma zan yi rayuwa da ita,Kai ko da kowa zai guje ni a duniya in har zan yi rayuwa da fatalwar,ruhi ko kurwar mahaifiyata zan rayu da ita ni kad`ai, Kai ko da Aljana ce me irin sufarta na yarda na amince zan yi rayuwa da ita,ko da hakan zai zama hanya mafi had`ari a gare ni ko kuma ya zama sanadiyar mutuwata na ji na gani kuma na amince", wannan duk zance zuciyar Yarima Sadauki ne a lokacin da ya samu kan sa,hannunsa rik`e da wani kaifaffan dutse ya na zana hoton fuskar da ya gani ajikin bangon d`akin kurkukun da ya ke a ciki,da ga gefe can Yarima Ishmal ne ke hangensa duk ya birkice ma sa tunda tunanin zuwan mahaifiyarsa cikin kurkukun ya d`arsar ma sa a zuciya shikenan ya rasa gane kan sa balle k`afafunsa,ba kalmar da ke fita daga bakin sa idan ya takura ma sa da tamba sai kalmar, "Mahaifiyata,Ummata ko kuma Noor jahan", shikenan abinda ke fita daga bakin sa,duk yanda ya so ya ga zanen da ya ke zanawa ya kasa domin ya kare,hakan ya sa ya hak`ura ya na mai zuba ma sarautar Allah Ido gami da sa shi acikin addu'o'in da ya ke yawan yi ,wad`anda sun riga da sun kama masa baki.
Jin motsi tare da hayani na kusanto inda su ke ne ya d`an d`auki hankalinsa,bai k`ara shan mamaki ba har sai da ya ga Waziri da M.Musa sun shigo cikin d`akin da su ke.
" Malam Musa Kai ne idanuna ke gani,ko-ko gizo su ke minAllah ya sa dai ba wani abun ne ya faru da har ka zo wannan wurin,ince da ba wani sharrin su ka lak`a ma ka ba kai ma,in kuwa hakan ne da sun gama zama cikakkun azzalumai ?","Ka kwantar da hankalin ka,Abokina ba wani abun da ya faru ba ka ga da wa na ke tafe ba Waziri ne fa da kan shi ya ke tare da ni kuma da miyan Mahaifiyarka Malikat Juwairiyya mu ke tsaye a nan","Kar ka zolaye ni da wannan maganar domin girmanta ya kai matuk`a gaya","Na rantse ma ka da wanda raina ya ke a hannunsa da gaske ne batun da na zo ma ka da shi","Tabbas wannan maganar ta zomin a sanda banzata ba,kuma a tattare da ita akwai tarin mu'ujizar Ubangiji shi kad`ai ne ke yin yanda ya so kuma a sanda ya soba dan isar da ikonsa ,ta ya haka za ta kasance, yau kimanin shekara wajen Goma sha biyu kenan rabon da in samu wata kulawa da ga gareta,sai kuma ga shi yau da karan kanta ta ce a zo a cire Ni daga wani halin k`ak`anikayi da na ke ciki","Tabbas wannan haka ya ke kuma abinda ya faru a yanzu kad`an ne daga cikin buwaya gami da d`aukakar da ikonsa, in ya so sai ya aikata fiye da hakan kuma anan take",Waziri ne ya matso kusa da su yace ya kamata ku zo mu tafi duk sauran maganganun kwayi su daga baya "," To ba damu mu je",cewar M.Musa nan take d`aya daga cikin Dakarun ya zo ya bud`e Yarima Ishmal su ka juya da niyar fita,har sun fara tafiya M.Musa ya dakata ya na mai waigo gami da sauke ganinsa a kan Yarima Haisam da ko wani kwakwkwaran motsi bai ba balle su saran zai d`ago ya kalle su,"Waye wannan matshin saurayin,shin ba shi da lafiya ne ko-ko ya na da wata matsala ne ta daban ?",ya tambayi Ishmal,sai da ya sa ki murmushi ka na ya ba shi amsa da cewa,"Wannan yaron ba gama garin mutane ne ba kamar wanda ka saba gani,idanunsa kad`ai in ka kalla za ka yarda da abinda na ce,shi d`in tamkar wata ne mai dusashe hasken fitila,shi d`in k`ugiya ce mai janyo Alkairi a duk bigeren da ya yada zango","Hakanan na ji ka kwad`ai ta min son ganinsa,na ji ina son in had`a idanu da shi","A'a kar ka je a yanzu ya na cikin wani rikitaccen yanayi da ni da kaina na kasa gane kan sa don haka ma dawo wani lokacin "," A'a ina zuwa",ya ce da shi duk yanda Ishmal ya so ya dakatar da M.Musa akan kar ya je inda Yarima Haisam ya ke bai ji shi ba balle kuma ya yarda da abinda ya ke ce da shi,ko da ya k`arasa hannunsa ya d`ora a saman kafad`arsa, da sauri ya juyo tare da bige hannunsa da ke jikinsa gami da sauke idanunsa a cikin na sa,da wata irin zabura Malam Musa ya ja ba ya na mai cewa,"Tsarki ya tabbatar ga Ubangijin talikai wanda ya fitar da Annabi Isa d`an Maryama ba tare da uba ba, wanda ya sanya jariri yin magana,mai fitar da rayayye da ga cikin matacce",...."Lafiyar kuwa Malam Musa, mene ne ya same ka ko ka gani a tare da shi da har ya kid`imaka gami da sanya wannan sambatu?",cewar Ishmal.
"Na ga wani abu a cikin idanun sa ne mai kid`ima wanda ya gansa,tabbas na yarda da Maganarka na cewa shi d`in ba gama garin mutum ba ne ba,a tattare da shi a kwai wani `boyayyen sirri,shi d`in ya kasance fitila ma haskawa,da sannun zai zama takobin da za tai sanadiyar datse igiyar zaluncin wannan k`asar,domin neman wani kwai da a ka binne shi a cikin k`ark`ashin k`asa dole ka nemi mabud`i ko makamar da za kai amfani da ita, shi d`in ya kasance mabud`in da zai tona sirrin da ke binne a ban k`asa na wannan Masarautar, dole ne duk wani azzalumi ya shiga taitayin sa saboda bayyanar sa in kuma ba haka ba zai riski kansa a cikin masifa da bala'in da bai ta`ba zato da tsammani ba"," Haba M.Musa ta ya za ka tasa mu a gaba da irin wannan zancen da ba mu ga ne komi a cikin sa","ku gafarce ni,nima abun ya zo min ne kawai ba tare da ina da masaniyar akan hakan ba,amma za mu iya tafiya,duk da dai ina son in yi ma ka tambaya guda d`aya kacal,Shin ko ka san me ya ke rubutawa ko zanawa a can ne da yaduk`ufa ba ya ji ba ya gani","Da alama dai ba za ka barmu mubtafi ba, don haka zan ba ka amsa a tak`aice zanen hoto ne ko kuma in ce ma ka taswirar fuska ce ya ke zanawa duk da bai gama zanen ba na so in san wata me irin wannan fuskar amma na kasa ganewa ko tuna ina mu ka had`u da ita tun safe ya ke abu d`aya har kawo yanzun bai gama ba ya ci ba ya sha,haka kuma ba ya uhm baya uhm uhm,in ka ga ya tashi to lokacin sallah ne yai,shine iya kar abinda na sa ni daga gare sa in kana buk`atar k`arin bayani ne sai ka kawo ma saziyara ko da zuwa gobe ne",Ishmal na Kai wa nan ya juya ya fita ba tare da ya tsaya balle har Malam Musa ya k`ara yi ma sa wata tambayar shi kan shi Yarima Sadauki sai da ya d`an jinkirta gami da fad`awa dogon tunani game da kalaman wannan bak`on ganin ya kasa iya gane Komi da ke ciki,ko da ko kalma d`aya ce ya sa ya watsar ya cigaba da zanen fuskar Mahaifiyarsa a jikin bangon,har Malam Musa su kusa fita daga cikin kurkukun gabad`aya ya dawo ba tare da ya tsaya jin ko sauraren abinda su Waziri ke cewa da shi ba,bai zame ko ina ba sai cikin kurkukun wajen Yarima Haisam, shi kanshi Yariman sai da yai saurin d`agowa ya zuba ma sa idanunsa don san fahimtar abinda ya ke tafe da shi,hannayensa duka biyun ya kama ya rik`e ya ce da shi"Ka gafarce ni ya Kai wannan matashin saurayin hak`ik`a na kasa iya rik`e abinda na ke ji a game da kai tabbas ka gasgata wani abu da ya ke k`aik`ayi gami da sosa min zuciyata,na ta`ba tsintar kaina a cikin wata rayuwa wacce na kasa gasgata shin mafariki ne ko gaske domin ni dai na san idona biyu na ga duk abinda ya faru a cikin wannan rayuwar tabbas na ganka da idona na ga tsantsar tsagwaron jarumtarka ,a lokacin abin ina d`aukar da a shashance amma kuma duk da hakan ya na damuna a cikin rai da zuciyata",k`ok`arin son cewa wani abu Yarima ya ke amma ya rasa me ma zaice,"Kar ka damu ba zan cutar da kai ba,kuma za Kai nasara a aikin da ka zo yi cikin k`asarnanta BAIBAH ga wannan zai taimaka maka",ya kama yatsan shi na biyu ya sa ma sa wani zobe da ya fiddo da shi daga cikin jakar da ya ke rataye da ita a ko da yaushe,"Allah zai k'are ka,ba zai ta`ba ba su damar da za su cutar da kai ba na barka lafiya",ya na kaiwa nan ya juya ta fi ba tare da Yarima Sadauki ya ce da shi komi ba.