ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA

SHAFI NA ƊAYA

by @ummishatu

©️Love story 2025

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA....!

NA

*UMMI A'ISHA*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI.

1

Fatan alkhairi gareku ɗaukacin masoyana masu karanta rubutuna a duk inda kuke,thanks for always reading my novels. I see the love and i do not take it for granted,may Almighty Allah bless you all for me.

And to my besty FERTYMERH XARAH can't thank you enough lovely sis more grace to your shining elbow star girl.

I love you all❤️

***Cikin nutsuwa da dattako take takawa tana tafiya a hankali domin gabatar da jawabin da ya jima rubuce cikin kundin adana jawabanta na musamman shekara da shekaru, tun bayan da mai shela (MC) ya ambaci sunanta ranta ya sake jagulewa ya tashi zuciyarta ta karye hawaye ya cika idanuwanta, dattijuwa ce yar kimanin shekara 65 fara tas mai kumari wanda kallo ɗaya zai gamsar da kai cewa jin dadi da hutu da tarin dukiya sun jima da yi mata zama na dindindin, tamkar balarabiya take wurin kyau da kuma ado, tana sanye cikin leshi golden color da mayafi wanda ya dace da shigar tata inda ya rufe mata jikinta gaba daya, abun magana ta karɓa (loudspeaker) daga hannun mai shela bayan ta taka steps ta hau, idanuwanta sanye cikin baƙin gilashi wadanda suka ɓoye hawayen da ke cike cikin idanuwanta, cikin sanyin murya ta fara jawabi kamar haka,

"Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.... Hakika yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangin annabi Isah, da Musa da Haruna, da Annabi Muhammad yabo da amincin Allah su sake tabbata a gareshi.... Hakika yau ina cike da farin ciki da jin daɗi saboda ganin tabbatuwar wannan al'amari, babu wanda yayi mana face ubangiji Allah mawadaci kuma madawwami mai komai kuma mai kowa wanda baya neman komai a wurin kowa shiyasa zamu cigaba da gode masa da tsarkake shi har zuwa ƙarshen numfashinmu, wannan gidauniya (Abwabul khair foundation) ina mai sadaukar da ita gaba daya ga mijina marigayi Alhaji Ahmad Rufa'i da ɗan mu guda ɗaya Anaam Ahmad Rufa'i, fatan ubangiji ya sanya albarka acikinta...... "

Duka waɗannan jawaban tayi su ne cikin harshen turanci tsaftatacce kuma ingantacce wanda babu hayaniya ko kuskure a cikinsa, bayan ta kammala jawabin ta sauko masu hotuna da video camera nata ƙokarin daukarta. Duka sauran bayanan da suka biyo baya babu wanda zata ce ta fahimta ko kuma ta fuskanci me aka fada saboda tunani da damuwar dake cikin zuciyarta da haka har aka kammala jawabai da duk abinda ya dace aka tashi, haka kawai ta kasa samun sukuni cikin ranta duk da dama wannan yanayin ya jima da zamar mata jiki, motarta driver ya bude mata ta shiga ta zauna a owners corner tana kallon mutanen dake kai kawo ta cikin baƙin gilashin motar, zuciyarta cike da damuwa mai tarin yawa, ba zata iya cewa ga abubuwan da suka faru a hanya ba saboda gaba ɗaya tunaninta baya tare da ita kawai ji tayi motar ta tsaya Malam Bala driver yana yi mata magana,

"Ranki ya dade mun ƙaraso........."

Buɗe idanuwanta tayi tana kallon katafaren gidanta wanda yake ɗauke da dukkan wani nau'in ababen more rayuwa. Gida ne babba gari guda sannan komai na jin daɗi an tanadar dashi acikin gidan sai dai duk da yawan wannan arzikin nata bata da nutsuwa bare kwanciyar hankali,

"Ranki ya daɗe....." jin muryar Bala driver ya sake dawo da ita cikin hayyacinta a karo na biyu, bude idanuwanta tayi sannu a hankali ta ɗauki handbag dinta ta ziro ƙafafuwanta ta fito daga cikin motar ta nufi ciki, babu kowa tun daga babban falon dake ƙasa har zuwa falonta dake sama, a hankali ta buɗe bedroom ɗinta ta shiga sai dai kallo ɗaya ta yiwa ɗakin jikinta ya bata an shigo cikin ɗakin dan gaba ɗaya gashi nan an harhargitsa ɗakin ba kamar yadda ta fita ta barshi ba, zama tayi gefen makeken gadonta ƙirar ƙasar Italy ta dafe goshinta tana fitar da numfashi a hankali wanda ita kanta ta san ba normal bane. Jin motsin buɗe ƙofa ya sata mayar da idanuwanta da kuma gaba ɗaya hankalinta wurin, wata matashiyar budurwa ce ta shigo wacce a haife bazata haura shekaru 28 ba kuma a bisa dukkan alamu ɗaya ce daga cikin hadiman gidan wadanda ke yi mata hidima,

"Assalamu alaikum....." matashiyar budurwar ta faɗa kanta a ƙasa tana sanye cikin shuɗiyar atamfa dinkin riga da skirt sai farin hijabi wanda ya tsaya iya gwiwarta,

"Wa alaikumussalam warahmatullah..... Imaan..... Akwai wani abu ne?"

"A'a mommy babu komai.... Dama naga dawowarki ne lokacin ina can baya shine nace bari na zo nayi miki sannu da zuwa sannan naji ko akwai wani abu wanda kike buƙatar zanyi miki....."

Ɗan murmushin ƙarfin hali mommy ɗin tayi kafin ta kalli Imaan cikin dauriya tace,

" Nagode Imaan, sai dai bana buƙatar komai a halin yanzu dan haka kina iya tafiya.... "

" toh mommy... " har ta juya ta kusa kaiwa bakin ƙofa taji mommy tace,

" Imaan zo in tambaye ki.... Anaam ya shigo bedroom ɗinnan ne?"

Shuru Imaan tayi tsawon mintuna biyu kafin ta girgiza kai tace,

" banga shigowarshi ba gaskiya amma zata iya yuyuwa ya shigo lokacin da ina baya....."

"ya shigo.... Ai babu wanda zai shigo min bedroom irin haka idan ba shi ba..... Jeki kawai"

Juyawa tayi ta fita amma kuma koda ta shiga bedroom ɗinta ta zauna sai itama taji duk gaba daya jikinta yayi sanyi ta kasa aiwatar da komai, haka kawai take jin tausayin mommy har cikin ranta, ace ɗa ƙwaya ɗaya tal ya kasa zame maka sanyin idaniya? Shi kaɗai ya gaza saka uwar da ta kawo shi duniya cikin farin ciki? Shi kaɗai ne ɗan da ta mallaka a duniya amma yanda yake ɗaga mata hankali tamkar yara goma, lallai dole mutum ya kasance cikin addu'ar samun zuri'a ta gari babu dare babu rana ko dan kaucewa haihuwar yuyu, haka taci gaba da zama cikin damuwa itama dan mommy mutuniyar kirki ce mai haƙuri da ƙokarin kyautatawa duk wanda Allah ya haɗata zama dashi koda kuwa zama ne irin na makotaka, hakiƙa albasa bata yi halin ruwa ba sannan yanzu ne ta sake tabbatarwa kuɗi da tarin dukiya basu ne jin daɗin duniya ba, Anaam yana wahalar da baiwar Allahr nan mutukar wahalarwa kamar ɗan Allah bani haka yake, gaba ɗaya baya jin magana kwata kwata tamkar mai kunnen ƙashi, tana zaune tana ta wannan zancen zucin har lokacin sallar azahar yayi sai lokacin ta samu damar tashi ta nufi toilet ɗan ɗauro alwala. Bayan ta idar da sallolinta kamar yadda ta saba gabatarwa farilla da nafilfili zama tayi ta karanta littafi mai tsarki wato Alqur'ani mai girma wanda take karantawa bayan kowacce sallar farilla tun daga asuba har ishah, bayan ta kammala ta yi addu'o'inta ciki harda mommy dama kuma ta jima tana sakata cikin addu'arta tana yi mata fatan samun kwanciyar hankali da nutsuwa cikin ranta, ita ta rasa gane kan wannan mutumin Anaam shi da Allah ya zaɓeshi cikin dubu ya bashi komai tun daga asali, kyau, kuɗi amma duk ya gaza gane irin ni'imar da Allah yayi masa, ita sau da dama tana baƙin ciki da damuwa idan ta tuna ko ita wacece da kuma inda ta fito amma shi gashi ɗan gata sai dai sam babu tunani kai wani lokacin ma kallon marar hankali take yi masa, sannan irin waɗannan halayen nasa yasa taji gaba ɗaya ta tsane shi kamar yadda take da tabbacin shima ya tsane ta, ƙiyayyar da suke yiwa juna ta daban ce dan yadda bata ko son ganinshi haka shima yaƙi jinin koda ganin ta. Addu'a ta shafa ta tashi ta fita zuwa kitchen dan samarwa da mommy abinda zata ci.

***

Hannunshi riƙe cikin nata suke ƙoƙarin fitowa daga cikin hotel ɗin har zuwa haraba inda aka tanada dan adana ababan hawa, sanye yake cikin jar t shirt mai dogon hannu da baƙin trouser, sai p cap, baƙi ne kyakkyawan gaske dogo ma'abocin ɗaukar hankali da kuma burgewa, gaban jibgegiyar jeep ɗinshi ya buɗe mata ta shiga wacce a ƙiyasi zata kai kimanin kuɗi naira miliyan tamanin, fara ce ƙatuwa mai ƙiba tana sanye cikin jar doguwar riga taci ado har ta gaji, sai ƙamshi take fitarwa kamar wata sabuwar amarya,

"my..... Where are we heading to??" ta fada cikin raɗa da jan hankali,

Sai da ya zauna sosai ya saka seat belt ɗinshi sannan ya saka baƙin glasses a fuskarshi ya juya ya kalleta,

"Today's my woman's birthday.... Soo i can't be calm..... Tell me what you want please....."

"thank you my love..... I don't want anything.... I want you......"

Murmushi yayi ya juya kan motar suka fita daga harabar hotel ɗin suka nufi cikin gari. Wani ɗan ƙayataccen wurin hutawa da shaƙatawa suka je sai dai tun bayan da suka zauna ya lura da wasu samari guda biyu wanda ɗaya daga cikinsu ya kasa dauke idonsa daga kan Najla sai kallonta yake kamar zai cinyeta,

"my... Thank you for everything....."

"Don't mention it my love...." ya fada idanuwanshi na kan wayar hannunshi, "ya kamata mu shiga cikin boutique din ko saboda kaga ina da bukatar kaya"

"ok babu problem let's go"

Duka abubuwan da take so kuma take da buƙata ta kwaso kama tun daga kan dogayen riguna, jakunkuna har zuwa kan takalma, ta kwashi kaya sama da na dubu ɗari biyar, Atm card ɗinshi ya bada akayi withdrawing kuɗin sannan suka fito, dab da zasu shiga mota wannan guy din da ya jima yana ƙurawa Najla ido ya ƙaraso ta gefenta yana yi mata magana a hankali kan yana buƙatar phone no dinta,

"kai... Kai wawa ne? Mahaukacin ina ne kai? Baka ganni tare da ita ba?"

"to dan na ganka tare da ita sai me? Mace ce fa allura cikin ruwa.... Ai tunda ba matarka bace ina da right din da nima zan kula ta...."

"ƙarya kake..... You have no right.... Baka da wannan darajar, who is your father?"

Gaban motar shi kawai ya bude a zafafe ya ciro wata kwalba ya nufeshi da ita, cikin sauri Najla ta watsar da kayan hannunta ta riƙeshi,

" Anaam what are you trying to do? Please rabu dashi mu tafi.... " bai saurare ta ba ya fincike ya nufi guy ɗin baiyi wata wata ba ya kwaɗa masa kwalbar a kanshi take kwalbar ta fashe ta farfasa masa kai jini ya ɓalle babu ɓata lokaci mutane suka fara taruwa a wurin, daƙyar Najla ta saka shi cikin mota suka tafi duk da ta san yaudarar kansu suka yi kawai amma dole sai wani abu ya biyo baya kamar yadda aka saba dan Anaam mugun dan zafin kai ne haka kuma cikakken ɗan rigima ne dan ba ya rabo da rikici kusan kullum cikinsa yake. Hotel ɗin da suke suka sake komawa kamar yadda rayuwarsa dama can shi tafi yawa a hotel.................. ✍🏻

Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,

FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.

Ummi Shatu👌🏻