Chapter 8
by @khairatup01
SHINGEN ƘAUNA
Khairat.
Wattpad:Khairi_Muhd.
Paidbook #500.
free page 8.
*
Mutumin nan da gaske ya ɗaura ɗamarar shiga rayuwata fiye da ƙima. Sau biyu yana zuwa gidanmu kuma ni na kasa yakice shi musamman da ya gaya min ƙanin Mami ne. Ga shi Umma ta saka min ido a kan sa.
Yana da barkwanci sosai akwai iya magana. Har nima na fara biye masa muna hira ba kamar farko ba.
Abeed ya zama na kusa da zuciyata sosai.
*
Ƙafata nake bi da kallo a zahiri amma a baɗini ba wai hakan ba ne a gare ni. Idan ina son na ci gaba a rayuwata tilas ne na maida hankali na nemi sana'ar da ta fi wadda nake yi a yanzu. Lokacin da zan yi amfani da kwalina ya zo kuma ya dace na yi hakan.
Sanyayyar muryarta na ji a cikin kunne na kamar ana busar sarewa. A hankali na ɗaga kaina na bi ta da kallo ina murmushi ni a karan kai kaina na san na kamu. Ni fa matsalata ban iya so ba. In ya kama ni ina shiga mugun yanayi. Da dama mata na wahalar mini da rayuwa in suka gano ina musu mugun so. Na yi zaton daga kan Firdausi ba zan kuma kallon wata ƴa mace da sunan soyayya ba, Sai ga shi yau na kamu da son Hannatu (Hanan).
'Ya ka tsaya daga waje maimakon ka shiga cikin farfajiyar gidan ga kujera ka zauna."
Yanzu dai tunda kin min izini zan shiga.
Ta nuna min hanya. A karo na farko da na je wurin budurwa babu rakiyar Aslam.
A kan kujera muka zauna. Ƙura mata ido kawai na yi ta yi min sosai ta kwanta min a cikin raina.
Ba zan yi miki ƙarya ba Hanan ina son ki kuma ina son na aure ki. Kin kwanta min a raina kuma ina fatan ba za ki kasance kamar sauran ƴan matan da na yi ba a baya? Na yi digree amma yanayi na ƙasarmu sai kana da hanya a gwamnati ka ke samun aiki to hakan ce gare ni nima amma fa ina da sana'a ta ni tela ne telan mata. Ko dayake na san kin san da hakan amma jikina ya yi sanyi yau bayan zuwa gidan ku da na yi na soma jin ke ɗin kin min nesa kin fi ƙarfina iyayenki ba zasu ba wa tela mata ba.
Gaskiya ka ɓata mini rai da ka faɗi wannan maganar. Kenan mu don muna ƴa'ƴan masu kuɗi ba mu da zuciya? ko gani kake yi don kuɗi nake son ka? Ni ba don kuɗi nake son ka ba tsakani da Allah nake son ka da zuciya ɗaya.
Ajiyar zuciya na sauke bayan na ji wannan maganar daga wurinta. Sai na saki jikina muka ci gaba da hira.
*
Alhaji Abba da kan sa ya kira ni gida don jin ta bakina a game da alaƙata da Abeed.
Cike da kunya na gyaɗa masa kai na kawai.
"kin tabbata?" Na gyaɗa mai kai.
Shi kenan je ki. Zamu yi magana da Alhaji Nazeefi. Sannan Kamal ya gaya min wai kayan ki sun taso shin kin sani?
E. Yaya Kamal ɗin zai shige min gaba. Ni ka san su suke min komai a fannin.
Duk da haka ki dinga sa ido da kan ki. Wani lokacin yarda da wasu fiye da kima na iya zama matsala.
In sha Allahu Abba.
Ki je Allah Ya yi miki albarka.
Amin.
Cikin gidan na shiga ina shiga hanyar corridor ɗin falon Mama kiran Abeed ya shigo min da murmushi kwance kan fuskata na ɗaga kiran.
"Masoyina."
"Masoyiyata fatan kina lafiya?"
"Ina lafiya lau, yaya kake ya juma'a?"
"Alhamdulillahi,komai lafiya sai dai kewar ki da ta ishe ni ta hana mini zuciya sakat shi ya sa ma kika ga na kira ki. Na zama addicted da ke masoyiya."
Nayi masa dariya nace "Kayya! Wannan zuciyar dai bata duba maka ba. Kana ina?"
"Uhmmm ina nan wani wuri na zo meeting ɗin da na gaya miki. Ki yi min addu'a Allah Ya sa harƙalar ta faɗa."
"In sha Allahu. Allah Ya bada sa'a."
"Amin."
Muka ajiye waya na mai da wayar cikin jakata.
Ban samu Mama a falo ba hakan ya saka na haura sama kaitsaye ɗakinta. Na tarar tana ninkin kaya na yi maza na amsa.
"Haba Mama da girman ki ina jama'ar gidan?"
"Na gaji da zaman ne kawai Nadiya. Yaushe kika zo?"
"Yanzun nan ban jima ba. Ina wurin Alhaji."
"Au yana nan ashe?"
Ina ninke kayan nace mata "E amma kamar fita zai yi."
"Yayi kyau."
Na ci gaba da jera mata kayan.
"Na ji ance za ki auri Abeed shin da gaske ne?"
"Muna dai soyayya amma ba a fara maganar auren ba tukunna."
Ta kama hannuna ta zaunar da ni gefenta.
Kar ki ɗauki maganata a hagunce. Kawai dai ina son ki kula sosai wurin zaɓar abokin rayuwa. Kin san mu mutane muna da wuyar sha'ani da fahimtar inda muka dosa. Ina son kiyi aure amma ba wai ki auri kowa ba aa sai mai son ki mai ƙaunarki da sanin ya kamata.
In sha Allahu Mama.Ki tayani da addu'a nima ina yi.
Allah Ya yi miki zaɓi mafi alkairi.
Amin.
GUSTO.
NIGERIA.
KANO.
"Ka saki jikin ka mana Nabeel."
"Ban saba zuwa irin nan ba ne."
Ta harareni. Wani ya zo ya ƙarbi oder ɗinmu. Ni ya kamata na biya ko na kawo ta amma ita take yi sai na ji na muzanta. Amma na ce ba a maida kyautar masoyi baya kuma ita bata nuna min wani abu ba ko a fuska ko na kaskanci ko ta nunan ba zan iya ba.
Muna tsaka da cin abinci aka kirata a waya ta tashi tace min tana zuwa.
Ina zaune ina duba wayar tawa chats ke ta shigo min. Sai kunnuwana suka soma jiyo min wata hira ban san me ya sa ba sai na ji ina son jin hirar. Na kasa kunne na da kyau.
"Yarinyar fa ta mato, na gama siye zuciyarta ita gani take ta gama dacewa baya ita a gurina .Ta soma bani tausayi ma sabida tana da kirki. "
"Tun farko abinda na guda kenan ka je ka faɗa son wadda bai kamata ba. Aiki zamu yi a kan ta kar ka manta hakan. Tana da dukiya mai tarin yawa dukiyar da zamu mora dukanmu da ni da kai ma saboda haka ka kula ka maida hankali."
"Na sani amma bana son na karya mata zuciya..."
"Amma ni ƙarya ta wa?"
Yadda wanda ake maganar akansa ya juya nima haka na juya amma a wayance.
Wata matashiyar ce fara doguwa amma kana ganin ta ka ga marar lafiya. Fuskarta duk ƙuraje.
Tashi ya yi yace "Ah Aliya yaya aka yi kika san ina nan? Me ya kawo ki?"
"Zuwa na yi na gaya maka abinda baka sani ba bayan ka rabu dani na tagayara na wulaƙanta."
Hannunta ya ja ya zaunar da ita yana yaƙe.
Ɗaya matar kuma ta girme su sai na ga ɓata rai tace "Wannan kuma fa Abeed?"
"Yaya Aliya ce tsohuwar budurwata."
"Ke me ya kawo ki nan? Bibiyar mu kike yi?"
"In ma na bibiye ku ban yi laifi ba. Yadda ya ɓata min rayuwa haka yake son ya ɓata ta wata? Kenan ni na tashi a tutar babu ? Ba auren ba saurayin ba lafiyar wata ta mora? Baka isa ba Abeed Wallahi sai ka aure ni kai ba iya aure na ba sai ka nema min magani."
Kalle-kalle ya soma yana magana ƙasa-ƙasa. "Aliya yaya kike mana ihu kin manta nan ɗin wurin jama'a ne ana jin mu? So kike ki tona mana sirri?"
"Sirri ka ce? Wanne sirri kenan? Saurara ka ji ka ga wannan takardar? Takardar saƙon mutuwar ka ce."
A tsawace yace "Aliyyaaaaaaa me kike faɗa haka?"
"Abinda kunnuwanka suka jiye maka saƙon mutuwar Abeed. Wannan takardar ta asibiti ce ina da cutar HIV kamar yadda kai ma kake ɗauke da cutar."
"What?" Da ƙanin da ƴar suka faɗa a tare.
Ni kaina na ji wani iri.
Ta kuwa kalle su sheƙeƙe ta sa dariya ta jefa mai takardar.
Ka duba da kyau ina da cutar kai ma kana da cutar tunda kai ne wanda muke mu'amala tsawon lokaci.
Aliya wasa kike yi amman?
Wasa? Na rasa da me zan yi maka wasa sai wannan? To baka da hankali ka saka wannan a ran ka ko ka dawo min muyi aikin tare ko na tona maka asiri ai na san yarinyar da gidanta ko ba Na....
Zan zo muyi magana a gida.
Aa ba sai ka zo ba ka kira ni kawai.
Daga nan ta bar wurin.
"Ina hankalin ka ya tafi ne?" Na juya ina kallon Hanan.
"No ba komai fa."
Na juya ban ga wanda aka ambata da Abeed ba.
Hankalina ya tashi sosai da abinda na ji. Na ji ina son na ƙubutar da wadda ake son cuta amma ta ya? Ban san su ba ban san wace ba ta yaya zan taimake ta? Take na soma roƙon Allah da ya cece ta daga hannun wannan azalumin. Haka muka ci abincin nan ban da wani karsashi. Ko da muka fita mashin ɗina na hau muka rabu da Hanan a nan.
Ina tafe ina tunanin yadda za ayi na samo asalin labarin.
*
Abeed.
Ban taɓa shiga tashin hankali kamar na yau ba. Sai na ji dama sanarwar mutuwata aka ba ni akan ace ina ɗauke da wannan cutar. Iya jin sunanta kaɗai ya razanar da ni ya saka na kaɗu. Na yi yawon duniya kala-kala na yi mu'amala da mata fiye da adadi amma ban taɓa kawo wa kaina wai zan ɗauki wannan ciwon ba.
Sitiyarin motar na daka na saki tsaki asibiti na nufa dole ne na je ayi min gwaji in ko ina da cutar na yi alƙawari nima sai na samar da ita ga mata da yawa suma su yi sanadin wasu ko da kuwa cikinsu akwai auren Nadeeya ne.
Amma Aliya ta cuce ni. Ta gama da ni ta kassara min rayuwa tunanin cutar kawai ya sa ruhina ma rawa yake.