SHINGEN KAUNA

chater 9

by @khairatup01

SHINGEN ƘAUNA
Khairat.
Wattpad:khairi_muhd.
Arewabook:Khairatup01.
Paid book.
#500.
Freepage 9


*

Kaitsaye asibiti ya tafi. A sirrance ya ga likita yayi masa bayanin matsalar sa ya kuma biya shi kuɗi don ya yi masa aikin da gaggawa. An yi duk wani gwaji da za masa ya samu gu ya zauna da ya ma kasa nutsuwar tashi yayi ya ci gaba da zarya yayi hagu yayi dama ya koma gefe ƙafafuwansa har rawa suke yi saboda tashin hankalin sakamakon. In har Aliya da gaske take yi masa tana da cutar to zai yi wuya ya rasa yana so dai ya tabbatar ne tukunna amma ba don haka ba.....

Abeed! 

Da sauri ya juya yana kallon likitan. 

Shi ma likitan shi yake kalla. 

A cikin idanuwan Abeed tsoro ne ƙarara tsoron rasa rayuwarsa kamar ta kowa. Yau dai ga ranar bariki.

"Ka biyoni ofis."

A baya ya bi shi. Suka shiga cikin ofishin tuni ya jiƙe da gumi.

"Likita.."

Miƙa masa wata farar takarda ya yi ya koma ya jingina da kujerar sa yace "Am sorry!Sakamakon ya nuna mana cewa kana ɗauke da cuta sida mai karya garkuwar jiki (HIV)."

"Ka duba da kyau likita?"

"Na duba amma za a sake dubawa sau uku zamu yi mun yi ɗaya sauran biyu amm.."

Miƙewa ya yi tsaye yace "Hmm, na gode likita zan dawo amma don Allah ya zama sirrina."

"An gama bayanka na hannu mai kyau babu mai ji."

Fita yayi daga asibitin. Cikin mota ya shiga ya yi mata key ya hau kan kwalta. Sai dai zuciyarsa ta karaya ya samu gu ya faka ya damke sitiyari ɗin motar ya saki ihuu har jijiyoyinsa suna fitowa. Bai taɓa sanin mene ne ainihin tashin hankali ba sai yau bai san haka ake ji ba sai yau da ya tsinci kansa a matakin da ba zai iya yin wata dabara don cetar kansa ba. Haka ya kunna motar ya ci gaba da tafiya. Yayarsa ta kira shi ya fi a ƙirga amma ya kasa ɗaga wayar to me zai ce mata?  Ko Alhajinsu ya ji wannan maganar ma babu zaman lafiya don sai ya gwammaci kiɗa da rawa. A hakan ma yana fama da tsangwama saboda hallayensa ba shi da kusanci da Alhajin kamar sauran ƴan gidan saboda rashin jin sa ya fi na kowa to ina ga ya ji wannan mugun labarin? 

Aliyaaaahhhhhhhh! 

*

     Tun jiya bai kira ni ba , ni kuma abubuwa sun min yawa mun sha aiki na lissafi kaya sun shigo mana.

Da safen nan ma Abla ta kira ni ta gayyace ni gidanta na gaya mata ba zan iya zuwa ba amma ta bari wani satin zan zo. Kawai zuciyata bata son zuwa ban san me yasa ba kawai bana son zuwan ba.

Wayata na jawo na kuma kiran layin Abeed. 

Bai ɗaga ba hakan ya sosa min raina don na tsani na kira mutum ya ƙi ɗaga min waya Wallahi. Tsaki na yi na yi jifa da wayar kan gado. 

Wanka na shiga na yi. Na shirya. Ina son zuwa Zariya gidan Yaya Imam kuma na gaya masa ma amma ba zan iya tuƙi da kaina ba. Dole na nemo Zainu a waya ya gaya min yana Daura amma gobe zai dawo na ƙara jadadda masa da ya tabbatar ya zo da safe mu tafi da wuri yace mini to.

A falo na samu Umma tana karyawa , nima na zauna kusa da ita muka karya tare. Fanke ne da kunu ta dama. 

Baba ya tafi kasuwa Jameel ma haka. So nake ma na maida shi Egypt ina ta processing ɗin fitar ta sa da cike mai makaratar tukunna sai na gama zan gayawa kowa.

   Umma ta kurɓi kunun ta ajiye kofin ta kalle ni tace "Yauwa na ji ɗazu Babanku yana gaya min za ki Zariya?"

"Eh na yi wa Yaya alƙawarin zuwa na jima ban je ba."

"To Allah Ya kaimu amma ai ya dace ki gaya min ko? Har yanzu dai ni ce uwar ki."

Murmushi na yi na ajiye fanken hannuna nace "Haba Umma, ai ba a canjawa tuwo suna. Ni fa Umma na lura ma ba sona kike yi ba tun bayan da muka dawo nan kika sauya min fuska. Ina son na gaya miki abu amma ina ɗar-ɗar, ina son ki ja ni a jiki amma ke ture ni kike yi daga jikinki. Sai abinda Yaya Muhammad ya gaya miki shi kike yi. Ni fa ya kamata ki ja a jiki Umma amma na gwammaci na gayawa Baba saboda kawai na san ba za ki gaya min magana mai daɗi ba." Na tashi zan tafi ta kira suna na tace "Nadeeya zo nan." 

Jiki a sanyaye na koma na zauna a kusa da ita ina share hawayena.

"Ba wai bana son ki ba. Ina son ki amma ina gudun maganganun mutane a kan ki. Ana yi mana kallon tun asali auren kuɗi kika yi da JJ. Babu abinda ba mu ji ba har an sha gaya mana Wutsyar Raƙumi tayi nesa da ƙasa ina ke ina Jj amma sai Allah Ya yi za ayi auren sai kuma ya karɓi abin sa. Ya bar miki tarin dukiya muka dawo nan. Nadeeya so nake yi kiyi aure ki tare a ɗakin ki kiyi zaman ki a ƙarƙashin mijinki koma meye kiyi daga ɗakin ki ya fi miki daraja da kwanciyar hankali. Bana son ki dinga zama a haka. Ba wai bana son ki ba ne. Babu uwar da zata haifi ɗa a cikin ta tace yau bata son sa. Kina so ki sauya halaye ne , kina son ki dinga nunawa kamar ke ɗin kin kai wani mataki."

"Umma kin san ba haka ba ne ba fa. Kin sani ina kiyayewa, ina ƙoƙarin na ga na kare mutuncina da kimarku duka a da ban yi rashin ji ba yanzu ma ba zan yi ba da yardar Allah."

"Na sani Nadeeya amma duk da haka, ina son ki gaya min wa kika fitar a tsakanin Abeed da Yusuf."

"Ummmmaaaa..."

"Ki gaya min kawai."

"Umma ba ko ɗayansu."

Zata kuma magana na yi sama da gudu ina ji tana kirana amma na ƙi komawa.

Waya ta na ɗauka na duba ko Abeed ya kira ni ko ya turo min saƙo amma ban gani ba. 

Na ji ba daɗi kenan na fara son sa ne? Ko dai da gaske ne ya kamata na yi aure? Saboda ni a karan kaina ina jin ina da buƙatar auren  ina kewar masoyi a rayuwata babu abinda na rasa sai mai ce min i love you. Ba wai bani da kyau ko diri ba ne duk ina da shi amma ana min kallon matakin da nake ciki na rayuwa yanzu ya wuce matsayin baya samari ba son kula ni da sunan soyayya. Akwai wanda ya ce min kwarjini gare ni ,ni matar manya ce bata yara irinsu ba don ni ɗin na zama tauraruwa mai wutsiya.

Yinin ranar a ɗaki na yi shi ban fita ko nan da can ba. Abincin ma ɗaki aka kawo min. Na yi oder ɗin pizza da milkshake. Na san Umma bata cin wannan sai na sa aka siyo musu tsire mai zafi.

Ina ci ina duba waya. A instagram na ci karo da sunan Nazif sai na shiga na tura mai friend request na ga ɗinkuna da dama da ya yi na dinga mai liking. Na jima  ina kalle-kalle kafin na sauka daga kai.

Watsapp na koma na koma kallon status ɗin mutane. A nan na kuma cin karo da lambar wayarsa ya ɗora rubutun soyayya an haɗa sunan sa da na wata Nabeel-Hanan. Na ji ba daɗi amma me yasa? Bani da amsar tambayar.

*

"Ka duba portal kuwa?" Aslam ya tambaye shi.

"Aa ban duba ba na san ma ba samu zan ba."

"kayya! Daɗina da kai saurin karaya ka gwada mana ka gani ai abin sa'a ne da rabo. Ka sani ko lokacin yanzu ne?"

"Ni..."

"Ka duba."

"Don dai ka matsa min ne amma da ba zan wahalar da data ta ba."

"Eh na ji duba ɗin."

Wayar ya zaro daga aljihunsa ya kunna datar ya soma da shiga mail ɗinsa tukunna. Yana shiga ya ga saƙo ya shigo mai.

Kamar fa an samu.

Don girman Allah?

Wallahi kamar saƙonsu ne.

Duba mu gani mutumina Allah dai Ya sa an dace.

Amin Ya ALLAH.

Yana ko shiga ya ga sakon an ɗauke shi aiki.


NNPC.

"Congratulations ,you have been selected."

Alhamdulillahi Aslam na samu wannan karon an dace.

Alhamdulillahi sai me kuma?

Sun ce na shirya na kai takarduna sannan za ayi medical check up.

Ga kuma resuption letter.

Ina kenan zaka je?

Can Lagos.

Ma sha Allah! Gaskiya abokina ina taya ka murna sosai.

Wallahi na godewa Allah sosai ,na gode ƙwarai. Bara na je na sanarwa Baba na kuma kira Ummi.

Ya kamata nima bara na shiga area na sanarwa gayu.

Akwai party yau a area.

Akwai fa. Suka tafa suka rabu.


A ƙofar gida na ga Baba yana alwala. Na tsugunna  a gefensa  na gaya masa na samu aiki da NNPC a lagos zan je na yi reporting. Ya dinga murna yana shi min albarka sai na ji daɗi da farincikina ya ƙaru fiye da lokacin da na ga saƙon.

Ina jin yana gayawa abokansa ai na samu aiki ne da matatar mai a can legas zan koma can. Na shige ina dariya ni dai. Na kira Ummi na sanar mata ita ma ta ding shi min albarka tana godewa Allah. Ita ma ta dinga sanarwa abokan zamanta.

Lallai in abin alkairi ya same ka akwai daɗi. Yadda aka dinga celebration a layin mu da wurin aikinmu na yi mamaki sosai kai kace zaɓe na ci. Nima bakina ya kasa rufuwa. A status na saka "Alhamdulillahi jira ya ƙare Allah abin godiya."

Daga nan saƙon Hanan ya shigo min tace da ni.

"Me muka samu masoyi?"

"Aiki.Ba na gaya miki ina neman aiki da NNPC ba?"

"Kar dai an dace?"

"Gashi kuwa."

"Kai Ma sha Allah, Alhamdulillahi."

"Ina ne?"

"Lagos."

"Kai amma na ji daɗi sosai. Sai dai zan yi kewar ka masoyi."

"Nima haka amma ai kin ga kan mu zan nemawa ko saboda gobenmu da ƴa'ƴanmu."

"Haka ne. Amma don Allah kar ka je ka yi budurwa a can."

Na tura mata da emoji ɗin dariya nace mata "Ban ce miki daga ke ba ƙari ba amma ki sani ke ce kat."

Ta turo min da alamar karayar zuciya tace "Ka karya min guiwa."

"Am sorry love kawai ni kin san bana ƙarya ne don na burge mutum iya gaskiyar kenan. Ba zan miki ƙarya wai ba zan so wata ba amma kema ina son ki sosai kuma kowace a bayan ki take. Ina soma samun yadda nake so zan turo gidanku."

"Da gaske masoyi?"

"Nayi miki alƙawari."

Alamar kunya ta turo mini da wannan ƴar bebin mai rawa.

Nace da ita "Sai an jima zamu yi magana zan shiga gida."

"Tam."

Ina son Hanan sosai bayan nan ne na rubuta Nabeel-Hanan da alamar soyayya a jiki.


Da safe na shirya mislin ƙarfe goma na safe. Kamar yadda muka yi da  Zainu ya iso tun tara na safe. Ya gaya min yana waje wurin hutawa a zaune da su Amiru suna hira. Abaya na saka fara na naɗa jearsy veil baƙi na yi kwalliya ta kamar yadda na saba ni ma'abociya son kwalliya ce. Na zizara kwalli a lebena na saka man leɓe mai kaurin nan na saka na murza bakina. Na ɗauki turare na saka na shafa khumra mai sanyin ƙamshi da daɗin shaƙa na saka. Na ɗauko orbit na jefe a bakina na soma taunawa na ɗauki jakata fara ƴar daidai na sauko ƙasa.

Zulai na saka ta ɗauko min ƙaramar akwatin da na saka kaya kala uku  ciki da wasu ƙananun kayan amfani na sa a ciki.


"Umma na fito."

"To yayi." Ta miƙ min wata baƙar leda tace "Ki bawa auntyn taki kayan amfanin tuwo ne su daddawa da kuka da kubewa da kanwa masu kyau ne."

"Zan bata. Shi kuma Yayan fa?"

"Me zan ba shi ni ko?"

"Ko ɗan biskit haka."

Ta harare ni ta miƙo min kuɗi "Wannan kuma babanki ne yace a baki ki sa mai."

"Kai amma na gode kam. Kamar ya san aljihuna babu kuɗi."

Ta kuma zabga min harara. Na fita ina dariya.

Ina duba agogo na ga ma sha ɗaya tayi. Na yi tsaki na yafito Zainu da hannu na.

Ya taso da ɗan saurinsa ya fito da mota muka tafi.

A hanya muka yi yar siyaya ta tsaraba ta yara muka ɗau hanya da sunan Allah a bakunan mu. Yau don kwaɗayi har su kantu na siya da aya mai suga na sa a jaka a gaba na zauna dama muna tafe muna hira. Yake gaya min ai budurwa ya yi a Daura can yaje ƙanwar abokinsa ce kuma da gaske shi son ta yake yi. Sunan ta Hassana ƴan biyu ne. Na ce Allah Ya sanya alkairi ya sa mai tarbiya ce. Yana ta yabonta har hotonta ya nuna min ni dai ina mai dariya. Daga ƙarshe wayata na ɗauka na hau watsapp na ga me duniyar take ciki. Group ɗinmu na fara shiga nan na ga ana ta cafta an tarfa Amina Said ana ta tsokana ta kasa kare kanta nima na yi mata n ware.

Status na kuma bi na hau kan na Yakasai na ga yana ta hamdala yana taya kansa murna sai na tambaye shi me aka samu haka?

Na yi mamaki ma da ya amsa min.

"Hajiya aiki na samu a Lagos a ma'aikatar NNPC."

"Kai Ma sha Allah. Lamari yayi daɗi kam Allah Ya sanya alkairi Yakasai."

"Amin na gode."

"Yanzu shi kenan an daina min ɗinki?"

"A haba wa zai manta asalin sa? Akwai yarana ai su ma sun iya nima in na samu lokaci zan na zuwa ai."

"Amma na fi son naka ka iya sosai." sai da na tura na lura kamar na yi katoɓar ne. Sai na kashe datar kawai don na ji kunyar abinda na faɗa kuma ya riga da ya gani na sani. Ban kuma kunna datar ba na ɗan maida kujera baya na kishingiɗa sai bacci.