chapter 11
by @khairatup01
SHINGEN ƘAUNA.
Khairatup.
Wattpad:khairi_muhd.
Arewabooks:khairratup01
paidbook.
Free page 11.
___________.
Nayi hanyar railways naje wani abun. Kawai na tuna na yi wa Abla alƙawarin zan je gidan ta. Na kira ta bata shiga ba kawai sai na yanke zan shiga ai na san gidan.
Ina zuwa aka buɗe min get ɗin gidan na shiga na yi fakin ɗin motar tawa a gefe.
Na sauko daga motar na kuma kiran layin na ta amma bata shiga ba duk da haka. Na jujuya ban ga kowa ba sai na yanke bara na shiga cikin gidan kawai.
Ina zuwa na yi knocking aka buɗe a take na yi mamakin hakan amma ban fasa shiga ba.
Muslihu na gani a tsaye.
Yana ta washe min baki.
"Ah! Yau muna da babbar baƙuwa ashe. Bismillah sannu da zuwa."
Yaƙe na yi kawai nace "Yauwa na gode. Ba sai na shigo ba Abla fa? ina ta kiran wayar bata shiga."
"E bata nan ta je gida Mama babu lafiya."
"Me ya samu Mama?"
"Jininta ne yayi ƙasa wai."
"Na gode da ka gaya min. Sai anjima."
Sai kawai mutum ya sha gabana ya harɗe hannyensa a ƙirji.
Na bi shi da kallon meye haka?
Am Nadeeya kin gane...
Zan dai gane in ka ganar da ni.
Ina ta so muyi magana da ke. Tun lokacin da na ganki kika burge ni naji ina son na kasance da ke. Ban san ko kin gane me nake nufi ba.
Ban gane ba har yanzu Muslihu ina son ka buɗe min karatun yadda zan fi fahimta.
Zauna to muyi magana.
Aa hakan ma ya isa. Ai magana da kunnuwa ake ji.
Haka ne. Ranar da na ganki a gidansu Abla na ji dama ke na fara gani. Kin haɗa duk wasu kwalitis da ake so a jikin mace, kin burge ni in fact na ji ina son ki ina son kasancewa da ke. Amma kin ga yanzu na riga na auri Abla da kunya aa aure ki, sai dai in kin bani haɗin kai zamu dinga mu'amala a ɓoye ba sai wani ya sani ba kin gane abinda nake nufi ai?"
Ji nayi kamar na mare shi a bayan kunnnensa.
"Muslihu haka kake dama? Da a ce a wancan lokacin ka nuna min halin naka Wallahi ba zan bari ka auri Abla ba saboda baka dace da ita ba sam-sam. Kai ɗin ɗan bunsuru ne. Ni zaka kalla kace naci amanar Abla? Ka san ko wace ni? In taƙamar ka kuɗi ka san baka isa ka nuna min ba ko? Don mijina ya bar min abinda ƙila kai ba za a bar maka ba. Yau ka faɗa amma kar ka sake faɗa ya zama na farko ya zama na ƙarshe da zaka kwata min wannan shirmen.
Hey! Ya kike yi kamar bamu san komai ba? Kin ɗauka ba mu san kina yin hakan a ɓoye ba?
Ban yi mamaki ba don na jima ina jin wannan maganar a bakunan jama'a da suke ganin naƙi aure ne ina bin maza.
Baka isa na yi maka bayani don na kare kai na ba ,duk a yadda ka ɗauki abin ka ɗauke shi a hakan bai dame ni ba amma kayi hattara ni wuta ce in kace zaka yi wasa da wuta kuma ƙonrwa zaka yi. Ka riƙe a ranka ni Nadeeya Nazeef na fi ƙarfinka. Ba zan kashe auren Abla ba amma zan roƙi Allah Ya shirye ka Ya sa ka koma hanyar dai-dai.
Kar ki gayawa kowa zancen nan don in nace za ki yi mamakin abinda zan miki.
Dariya nayi mai nace masa "Ni nan da kake gani zan iya yin komai ciki harda abinda ba ka taɓa zata ba. Ka sani ko yau in ka fita ba zaka dawo ba?"
Sai na ga ya kalle ni da mamaki.
Kwarai ba wai ka yi hatsari ka mutu ba, za a iya ɗauke ka a neme ka a rasa ka ɓata bat shi kenan sai.... ina fata ka gane nufi na?
Sai yayi shiru wataƙila bai san na kai haka ba ko gani yake ni bani da hayaniya zai iya takani yadda yake so. Zama da mutane da dama ya saka dole ne na zama irinsu.
Na sa kai ma fice na bar shi. Na soma tunanin me yasa Abla? Bata dace da miji ba ,in har wannan ne halin mijin nata bata yi dace ba. Na kai zuciyata nesa sosai da sai na zabga masa mari kuma sai na tona masa asiri. Kenan neman mata yake ko kuwa? Ya ɓata min mood ɗina ina ma a wancan lokacin kafin auren na su ya gaya min makamanciyar wannan maganar da sai Ya gane shayi ruwa ne don ba zata bari ya auri Abla ba. Yanzun ma ba zata bar maganar ba sai ta ɗau mataki.
Kaitsaye gidan Maman ta nufa. Can ta tarar da ƴan ɗakinsu Jj sun zo duba mahaifiyarsu. Ganinsu da nayi duka sai da zuciyata ta tsinke wurin da ya saba zama in aka yi irin wannan haɗuwar na kalla idanuwana cike taf da ƙwalla.
Yaya Ameer ne yace "Ya dai Hajiya?" Na girgiza masa kai kawai. Hannu na saka na toshe bakina saboda kukan da ya taho min.
Suka yo kaina da tambaya lafiya,me aka yi min?
Mama ce tace "Ku kyale ta ba wani abun ba ne akan samu irin haka dama. Mijinta ta tuno bayan ganin ku full house.
Aunty Ramlat ta zaunar da ni tace "Yaya za ayi Sis? An jima fa kin ga yanzu gidan wani za ki je ba zai yuwu kina tuna tsohon mijinki haka ba. Addu'a kawai Jj yake buƙatar mu yi masa."
Kai na gyaɗa mata kawai. Ɗakin yayi tsit. Tausayina suke ji.
Nace "Mama yaya jikin naki? Ni shi ne ba a gaya min ba sai ji na yi. "
"Kiyi haƙuri. Ina Umma?"
"Tana gida bata ma san zan zo ba nima unguwa naje sai na bi ta gidan Abla kuma bata nan mijinta ya gaya min tana nan baki da lafiya."
"Aunty zuwa kika yi?"
"Eh."
"Kash! Yanzu sai yaushe za ki kuma zuwa gaskiya ban yadda ba."
Na ji zan sake zuwa amma ba yanzu ba.
Har dare muna can tuni na sanarwa Umma zan jima.
*
Saura kwana biyu bikina da Abeed na yi baƙuwa. Ranar ina gida don tun satin bikin ban kuma fita ba nima hutawa nake.
Zainu ne ya shigo da gyɗa a hannunsa. Mayen gyaɗa ne nima ya koya min cin ta musammam tuɓus.
Tun kan nayi magana ya miƙo min leda "Gata na san in kin gani sai ki ce kule."
Nayi murmushi nace "Tun da ka sani ai shi kenan."
"Baƙuwa fa ki ka yi a waje."
"Baƙuwa kuma? Wace wannan?"
"Ban san ta ba fa. Shi yasa nace gwara na fara sanar miki."
"To ai ba za a barta a waje ba,ka ce ta shigo."
Ya juya ya fita ba a fi minti biyu ba sai ga baƙuwar nan ta shigo.
Tun da ta shigo nake bin ta da kallo so nake na tuna in da na santa amma na kasa kawai sai na haƙura da takurawa ƙwaƙwalwata.
"Sannu da zuwa."
"Yauwa sannumu. Ke ce Hajiya Nadiya Nazif?"
"Ni ce ke fa?"
"Ke ce dai kike ƙoƙarin shiga gonata?"
"Gonar ki? Wacce gona kenan?"
"Abeed."
Nima na maimaita sunan Abeed. Ina kallonta.
"Hum! Naga baki san waye Abeed ba. Baki san ina kike ƙoƙarin tura kan ki ba. Ina mai tabatar miki da in kika sake kika auri Abeed daidai yake da kin kai kan ki kabari ne."
Baki na buɗe cike da mamakin furucinta wai "kabari" wane irin kabari kuma.
Sunana Aliya. Ni budurwar Abeed ce. Ko nace....
"Kee wato maitar taki bata tsaya a iya tsakanina da ke ba ? Sai da kika biyo ta don ki ɓata min suna? Ke wai tare aka haife ni da ke ne kin dame ni kin takura min ana soyayya dole ne?"
Abeed ne ya shigo ya tare mata numfashi.
Ta juya tana tafa hannayenta biyu tace "Ai na gaya maka tunda baka aure ni ba bazan bari ka auri wata ba. Sai dai a rasa a tashi a tutar babu daga ni har kai."
"Da gaske idan baki bar gidan nan ba sai na kira miki ƴan sanda. Kuma kin san zan iya."
"Abeed! Kyale ta don Allah ta gaya min abinda ban sani ba. Tsaya ma wai ka santa da ma?"
"Na santa tsohuwar mayya ta ce. Tun a kudu ta manne min ta maƙale min. Don ta ji za ayi bikina shi ne ta zo ta tarwatsa komai. Kar ki yadda da ita. Kar ki yadda ta komai da zata faɗa miki."
Hannu na ɗaga masa nace "Ka barta nace ta yi magana."
Abeed ya bi ni da kallo kawai.
Aliya ta ci gaba da magana.
"Abinda kawai zan gaya miki shi ne , ki fita daga sabgar Abeed mayaudari ne ,macuci ne, maha'inci ne,azzalumi ne kuma makiri ne. Tun wuri ki maida hankali akan magana ta kori wannan mutumin."
"Baiwar Allah bai dace ba ko ma me ya shiga tsakaninki da Abeed bai dace ki zo har gidana ki na irin wannan abun ba. Tsakaninki ne da shi kar ki kuma zuwa min gidana. Ga hanya nan ki koma ta inda kika shigo ki fita ta can. Na gode da shawarar ki ko me zai faru zan gani daga baya amma yanzu ki tafi."
Da ganin yanayin fuskarta na san ba haka ta so ba. Ta saka min shakku amma bana son na bar abin yayi tasiri a kaina saboda alaƙa da zargi ba zata ɗore ba. Haka ya saka na maida mata martani tun yanzu.
Nadiya kiyi haƙuri hakan ba zai ƙara faruwa ba. Ita ce take sona ba ni nake son ta ba. So take yi ta haɗa mana fitina tsakaninmu ni da ke. Ki yarda da ni ba zan cutar da ke ba.
Abeed bana son na san past ɗin ka ya riga ya wuce. Gaya min ya aka yi na gan ka na ɗauka kace sai jibi zamu ga juna?
Eh wucewa nake yi fa nace gwara na zo na ɗan gan ki na rage zafi.
Na harare shi cikin wasa na koma na zauna. Sai a lokacin ma abin ya zo min na ce "Au na manta ma ina ta so na gaya maka ya kamata muje ayi mana test don sanin status ɗinmu."
"Zamu yi." Kawai yace min.
Nima ban maida hankali ba nace masa "To."
Bai wani jima ba ya tafi. Nima na shiga sabgata.
Sai dare na ga kiran Yakasai. Na ko bi kiran nasa.
"Zan kira ki Hajiya , ina wurin Hanan."
"To." Kawai nace na kashe wayar na yi tsaki na ajiye ta a gefe.
Yakasai bai kirani ba sai washegari da rana kawai sai na ji bana son na ɗaga kiran nima. Na yi tsaki na juyar da kaina gefe kamar yana wurin. Daga baya ma sai na zauna ina tambayar kaina wai lafiyata lau kuwa? me yasa nake jin haushi in na ji yana maganar wannan yarinyr? Tsaki dai na yi shi a karo na ba adadi.
"Na kira shi wai yana gun Hanan zai kira ni tun yamma bai kira ni ba sai yau da rana saboda ya raina min hankali mtsww dan rainin wayo kawai. Ba zan ɗaga wayar ba nima akwai abinda nake yi."
Ni kaɗai na yi ta bambanin bala'i.
Ina zaune Abeed ya kira ni wai zai bani saƙo yana waje abokansa sun haɗa mai wata ƴar dinner ta mutum ashirin kati zai bani na bawa ƙawayena bayan ɗaurin aure da daddare za ayi. Nace masa to muna tsaka da magana ne kuma sai na ga Yakasai a machine da abokinsa Aslam riƙe da wata jaka a hannu ƴar daidai.
Da mamaki nace "Yakasai waya kawo ka gidanmu?"
Ƙafarsa ɗaya a ƙasa yana murmushi yace "Tuba nake Hajiya. Na san na makara. Jiyan nan ina wurin Hanan, kin san in ina wurinta bani da nutsuwa gashi gobe zan koma."
Na harare shi nace "Kai ka sani romeo ɗin ƙarshen zamani. Ina kayan an gama ko kuwa?"
"Na isa in ƙi yi miki? Na gama."
"Tam nawa kuɗin?"
"Ki ɗauka gudunmowa ce na baki. Allah Ya sanya alkairi Ya bada zaman lafiya ba zan samu zuwa ɗaurin auren ba aiki na jirana a can birnin Ikko."
"Haba dai ayi haka Yakasai ,ba zaka amshi kuɗin ɗinkin ba?"
"Wallahi ba zan amsa ba."
"Na gode. Allah Ya bada sa'a. Ga fa maigidan ma baku gaisa ba."
Sai a lokacin Abeed ya ajiye wayar da yake yi.
Nabeel na ganin sa ya ɗan yi sak ya sha jinin jikinsa ya san fuskar tabbas ya san fuskar amma ya manta a ina yana ƙoƙarin tuno fuskar ya ji ta ambaci sunan "Abeed ga Yakasai."
"Yakasai ga Abeed."
Abeed yace "Sannu abokina."
Da ƙyar ya iya cewa "Yauwa."
Kafin yaje gida sai da ya gano waye Abeed shi ne wanda ya gani a Gusto da budurwarsa da ke da HIV kuma ta faɗa yana da ita.
Anya kuwa ba zai gayawa Hajiya Nadiya gaskiya ba?