chapter 12
by @khairatup01
SHINGEN ƘAUNA.
Khairat.
Wattpad:khairi_muhd.
Arewabooks:khairatup01
paid book.
#500.
Free page 12.
Kasa bacci ya yi sai zarya yake a cikin ɗakinsa . Neman mafita yake yi ta ina zai soma hana wannan zalincin da ake son yiwa Nadiya baiwar Allah. Mace mai kirki marar girman kai ko ɗagawa da nuna isa da iko? Bai samu ya kwanta ba sai bayan da ya yi sallar asuba.
Da ciwon kai ya tashi wurin shaɗaya na safe shi ma Aslam ne ya tashi.shi.
Ya dai mutumin ka manta akwai tafiya a gaban ka?
Ban yi bacci ba ne sai bayan asuba. Bara na kimtsa.
To wayar kuka tsaya yi ne ?
Aa fa akwai abinda yake damuna.
Me fa?
Nan ya gaya masa komai. Aslam ya yi ɗan jin kaɗan sai kuma yace da shi "Ka ga ban ga abin tunani ba fa, yaya zaka ji idan aka cutar da wanna baiwar Allahn? Nan gaba kai a karan kan ka zaka iya haɗa ido da kan ka ko a mudubi ne idan ka tuna cewa zaka iya ceton ta amma ka ƙi saboda kana kokanton baka da hujja? Ni dai da ni ne zan gaya mata ruwanta ne ta yadda ruwanta ne kar ta yadda amma ko a gaba ba zata mata da kai ba kuma kai ma zaka ji ka samu kwanciyar hankali."
Haka ne bara na yi wanka na karya sai mu wuce daga can sai na tafi amma zan fara kiran ta tukunna. Tausayi ma take bani Wallahi tana da kirki. Gashi fitowar wannan zancen zai iya taɓa martabarta ka san dai yadda mu mutane muke kanbama abu mu mai da shi gagarumi.
To ya za ayi? Su mutane ai da kake gani aikinsu ne magana. Da son yin shari'a ko hisabi akan abinda ba ikon su ba ne ba. Sai dai fatan Allah Ya sa mu dace.
Amin.
Wanka ya yi ya shirya. Shadda ya saka ruwan ƙasa ya saka hula suka tafi. A kan mashin ɗin Aslam suka wuce. Ya riga da ya yi sallama da Babansu da matansa. Hanan ce da yayi niyar zuwa yayi mata sallama amma sai ya ga babu lokaci kar ya je kuma ya kasa isa akan lokaci bare ya hana auren.
*
Can Hotel kuwa Abeed da abokansa sun gama shiri. Ya yi kyau Ma sha Allah! Abeed na da kyau ba don hallayensa ba kawai. Sai ƙamshi yake yi kai ka ce ɓarin turare aka yi masa a kaya da jiki. Abokansa na ta tsokanarsa yana basarwa sai dai yayi murmushi. Hankalinsa na kan auren nan so yake kawai ya ji an ɗaura auren shi ne kwanciar hankalinsa kawai.
Yau sau ɗaya yana jin tsoro yana jin tsoron rasa Nady saboda ya lura kuma ya aminta ya kamu da sahihiyar soyayyar ta a cikin ransa. Da ya je mata ne don ya yaudareta ya aure ta ya samu ya wawashe mata dukiya ko ta halin ƙaƙa ne ,amma daga lokacin da ya fara mu'amala da ita ya fara sanin wace ita da yadda take kula da shi bai san son ta ya kama shi ba sai lokacin da ya samu labarin yan da cutar HIV. A nan ya fara jin tsoron kar ya rasa ta. Hakan ya sa in zaka nutsu ka kalle shi da kyau yaƙe kawai yake yi amma idanuwansa na bada labara kala-kala.
Abokinsa Ashraf ya dafa shi yace "Abokina muje ko?"
Murmushi ya fara yi yace "Muje."
Wani daga baya mai suna Khalid ya soma ihu "wuuuuu! Ango! Ango ! Gaskiya ka yi kyau sai ƙyallin angwanci kake."
Bai kula shi ba ya fice suka mara masa baya suka shiga mota.
Hakan nan ya ɗauko wayarsa ya lalubo lambar wayarta ya tura mata saƙo.
"Hi wife to be. Fatan kin shirya tarbata a matsayin miji. Kin san ina son ki don Allah ki yarda da dani duk rintsi kar ki bar ni."
Ya shafa screen ɗin wayar ya ajiye ta a gefe.
"Ya aka yi ne Abeed?" Inji Ashraf.
" Babu." Ya ba wa Ashraf amsa.
"Aa akwai. Ka gaya min maybe zan iya taimaka maka."
Dafa kafaɗar Ashraf yayi yace "Babu komai fa kawai am nervous ne."
"Haba kar ka bada maza mana. Wannan ai sai mata."
"Ba zaka gane ba."
"Hah! To riƙe kayan ka iya kai."
*
Nadeeya.
A cikin ɗakina ni da ƙawayena ne zaune ana ta raha. Na yi wanka na saka wani ubansun leshi na saka sarƙa da ɗankunne na gold da awarwaro. Ba wata kwalliya nayi sosai ba amma na ɗan taɓa fuskar. Na yi mamakin yadda na ga gidanmu ya cika a karo na biyu kowa ya zo ne dan aurena don ya taya ni murna da farin ciki hakan ya faranta min rai sosai.
Wayata nake ta nema amma ban ganta ba da zan yi bacci na saka ta a silent. Shamsiya na kalla nace "Shamsi kin ga wayata kuwa? Na san yanzu Hayati yana ta nema na bai ji ni ba."
"Awwwwwww!" Ɗakin ya ɗauki ihu da sowa.
Sai kuma muka ƙyalƙyale da dariya dukanmu.
Sai na tuna da lokacin bikina da Jj irin rawar kan da na zuba ko a ranar da aka ɗaura auren mu da ya zo wurina sai muka zagaya bayan layi jikin wani gidan Alhaji akwai wata dakali muka zauna muna ta hira mun shantake ma mun manta da mutane da mutanen duniya babu wanda muke gani ko muke tunawa kawai mu burinmu mu ji mu a tare ne kusa da juna kawai.
An jima ana nema na ba gan ni ba har lokacin kai amarya ya yi. In na tuna irin faɗan da na sha ranar sai na yi dariya. Yau kuma sai na ji hawaye sun zubo min yanzu shi kenan nan da wasu awanni dole in ajiye tunanin Jj ko? Na zama matar wani mallakin wani.
Shamsi ce ta dafa ni tace "Ya dai ƙawas?"
Ma gyaɗa mata kaina kawai na share hawayena.
Lami ce ta shigo da wayata a hannunta. "Uwarɗakina kin da shauni wa ke yarda waya a wurin taro? anjima ayi ta nema."
"Na manta inda na saka ta dama ita nake nema."
"Ai gata nan a hannun ma Baby na gani tana game."
"Kuma tunani na bai kawo min ita ce ta ɗauka ba."
Na buɗe nan na ga text ɗin Abeed na karanta ya kai sau biyar amma ban gane me yake nufi ba ina shirin kiransa ne kuma kiran Yakasai ya shigo wayata na yi mamakin kiran amma ba can ba sai na ɗauki wayar na yi sallama.
"Sallamu alaikum Hajiya."
"Wa'alaikum salam! Yakasai."
"Hajiya zamu iya magana yanzu?"
"Anya kuwa Yakasai ina cikin mutane ne."
"Maganar na da muhimmanci ne in ban gaya miki ba za ki yi da na sani a gaba in ba ki saurare ni yau ba."
"Wacce magana ce haka Yakasai? Me ya faru?"
"Ni dai ki ba ni dama ina nan ƙofar gidanku."
"Ƙofar gidanmu ai a cike yake na sani ta ya zan fito nan?"
"Hajiya nima tafiya ce a gabana na kasa barin hakan a raina ne maganar ta shafe ki sosai."
"Yakasai kana tsorata ni fa."
"Ki yarda da ni.
Shiru na yi na wani ɗan lokaci kamar ba zan mai magana ba sai kuma nace "Ina zuwa."
"Na gode."
Na kashe wayar kawai. Mayafina na ja na yafa.
Shamsiya tace "Ina za ki je ne?"
Summaya tace "Ina ruwanki kika sani ko oga ne ya zo."
Suka haɗa baki wajen cewa "Oooooooooooo."
Ni dai na fice gabana na bugawa da sauri da sauri.
Tun da na fara sauka daga matatakalar bene ake amarya amarya ina murmushi kawai.
Mama tace "Ina zuwa kuma?"
"Ba ko ina zan amshi abu ne."
"To ki hanzarta suna hanya."
"Tam."
Ina fita kuwa na ga jama'a a farfajiyar gidan. Kai kace yau ne zan fara aure.
Yayyuna sun yi kyau cikin farar shadda da hula iri ɗaya.
Sai na ga Yaya Muhamamd sai fara'a yake ta yi a nan na gane ba wai ƙi na yake yi ba kawai yana son ya ga nayi aure ne.
Karaf muka haɗa ido da shi yana murmushi ya yi min alamar meye da hannu na girgiza masa kaina kawai.
Ya ci gaba da sabgarsa ni kuma na kira Yakasai na tambaye shi yana ina yace min yana ƙofar gida na ce masa ya shigo ina nan farfajiya.
Idanuwana suna kan gate ina kallo ya buɗe gate ɗin ya shigo sai da na ji gabana ya faɗi. Tuni na soma rasa nutsuwata kamar koyaushe in na ga Yakasai ido da ido wani abu ne kamar mayen ƙarfe yake fusgata gare shi na rasa wannan wacce musibar ce ta tunkaro ni akan Yakasai tuni na soma ambaton sunan Allah ko na samu nutsuwa.
Cikin abinda bai fi ƙiftawar ido ba na gan shi a gabana.
"Hajiya."
"Yakasai." Na faɗa da ƙyar ina kallon ƙwayar idanuwansa kalar nan da ake kira sexy eyes.
"Me kike kallo ne?"
Nayi firgit na dawo cikin hayyacina. "Ba komai,kawai idanuwan ka ne..." sai kuma na yi shiru ina jinjina kwafsin da na yi.
Shi ma sai ya basar yace "Anyway ko zan iya ganin mahaifinki da yayyunki a nan?"
"Yakasai wai meye yake faruwa ne?"
"Magana ce a kan auren ki kar kiyi auren nan akwai matsala ko na ce yaudarar ki yake yi. Bai dace da ke ba ke bama ke kaɗai ba bai dace da kowacce irin nutsatsiyar mace kamila irin ki ba. "
Baki na buɗe ina kallon sa da mamaki sai na nem kalmomi ma na rasa ta ina zan fara.
"Ki daina mamaki zan gaya miki komai."
"Yakasai am strong zan iya jin ko ma meye. Ba sai su Baba sun zo ba."
"Gaskiya sai sun zo. Sensitive abu ne."
Ajiyar zuciya na sauke na hura iska daga bakina. Juyawa na yi hankali na soma tafiya har wurinsu Yaya na gaya musu su zo can inda Yakasai yake a tsaye daga nan na koma na kira Baba.
Ganin da jama'a a nan da yawa ya sa Baba yace mu shiga cikin sitting room da ke tsakar gidan.
Shiru ɗakin ya ɗauka. Kusan sakan biyar kafin baba yace "Samari sannu fa ance ka zo da wata magana mun suraronka."
Mutumin ya ba shi tausyai. Sai jikinsa ya yi sanyi , sai ya ji kamar ya fasa faɗa amma faɗar shi ya fi alkairi.
Gyaran murya nayi nace "Baba da farko dai sunana Nabeel Muhammad Yakasai. Ni mazaunin garin kano ne unguwar Yakasai. Ban san Hajiya Nadiya ba sai ta sanadin ɗinki. Na lura tana da kirki bai dace na ga abu marar kyau zai samu wani ɗan'uwna musulmi ba na yi shiru. Ba zan ja maganar da nisa ba kuma ba zan ce dole ku yarda da ni ba amma ni na sani abinda zan faɗa ba ƙarya babu ƙage a ciki. Kuma in na yi sharri bani da wata riba ciki. Duk da ban tabbatar ba amma ya dace ku dakatar da wannan ɗaurin auren zuwa wani lokacin."
Lokaci guda na ji kaina ya sara min ,ƙirjina ya soma harbawa da sauri da sauri.
Baba ne ya yi ƙarfin halin magana.
"Nabeel daga ganinka ba zaka yi min ƙarya ba na gamsu da kamalar ka da nutuwar ka. Sai dai ina son ƙarin haske a kan wannan batun."
"Baba shi wannan Abeed ɗin , da ke shirin auren Nadeeya yana da cuta mai karya garkuwar jiki."
A take ƴan ɗakin suka dinga salati ana innalillahi wa inna illahir raj'un.
Kasa ma magana nayi naji bakina ya yi min ɗaci tuni na nemi yawu na rasa a bakina.
"Kai Nabeel, ka san abinda kake faɗa kuwa? Ka san kazafin da kake yi wa Abeed kuwa?" Inji Yaya Muhammad.
Yaya Imam ne ya zaunar da Yaya Muhammad yace "Zauna Yaya. Kar ku yanke hukunci kuma kar ku tuhume shi. Abu guda ne a ji yadda aka yi ya san shi."
Sanyi naji ya ma kama ni. Jikina ya soma rawa. Kawai so nake na tashi daga baccin da nake.
Nabeel ya kuma gyara zaman sa ya kwashe komai ya gaya musu.
Sunan Aliya da ya ambata sai na tuno da waccar matar da ta zo gidana ta gaya min sunan ta Aliya kuma akan Abeed ta zo. Tsoro fargaba da tashin hankali suka dirar mata a lokaci guda.
Shiru ya ɗauki ɗakin. Sai Ac ke bada sanyi. Duk da wannan abin sai na ji dama ace karya ne.
Baba kuwa ya cire hularsa yace "In kuwa haka ne Abeed ya cuce mu. Ya saka mu a cikin duhu."
Yaya Imam yace "Baba yaya za ayi yanzu?"
"Wallahi Imam na rasa ma me zan ce."