SHINGEN KAUNA

chpter 13

by @khairatup01

SHINGEN ƘAUNA.
Khairat.
Wattpad:khairi_muhd.
arewabooks:khairatup01
Paid book.
#500.
Free page 13.

Yaya Muhammad yace "Wai kun yarda da shi? haka kawai baku san mutum ba ya zo ya faɗi abu ku hau ku zauna a kai in kuskuren fahimta ne fa? in ba shi ba ne ba fa? Gaskiya ban yarda ba."

"Zai iya yiwuwa..." Na faɗa bakina na rawa.

Suka dawo da kallonsu wurina. 

Na share hawayena nace "Kwanaki wata tazo mai suna Aliya ta so ta gaya min hakan amma shi Abeed ɗin ya zo ya saka aka korata. Na kuma yi niyan muje muyi asibiti ayi mana gwajin sai ya dinga kaucewa har ma ya daina zuwa sai ga shi yau ranar ɗaurin auren ta zo. Baba na shiga uku an tara mutane. Baba wane irin baƙinjini ne da ni haka? Baba me na yi masa yake son ya kassara min rayuwa ya cuce ni?" Na dinga kuka har ina shiɗewa.

Aka rasa mai rarrashina. 

Baba ma ya shiga tashin hankali kawai ya zaro wayarsa sai ji muka yi yana magana da Alhajinsu Jj.

Ba a jima ba Alhajin da Yaya Hamza suka shigo.

"Lafiya dai Alhaji. Nazif? Na kasa nutsuwa Wallahi akwai matsala ne?"

"Uhm Nabeel gaya masa abinda ka gaya mana."

Nabeel bai yi ƙasa a guiwa ba ya kwashe komai ya gaya masa.

Alhaji ya zauna daɓas ji yayi kamar an fizgo ƙafafuwansa daga ƙasa an maida shi sama haka ya ji. Innallillahi wa inna ilahir raj'un."

Yaya Hamza yace "Alhaji ba abin a ƙi yarda ba ne wannan. A kira Abeed a je ayi gwajin nan kawai. Don ba zai yiwu a cuci yarinya ba. Ni dama ba wani son wannan haɗin na ke yi ba."

Ni dai na daina ganewa sam-sam. Alhaji ne ya ce in tashi in koma ciki zai kira ni bara a nemo Abeed ɗin tukunna.

Wallahi ba zan iya tafiya ba. Ni ba zan iya tafiya ba Alhaji ku kira shi kawai.

Tausayina ne ya kama su. Sai suka kyale ni.

Yaya Hamza ne ya kira Abeed a waya sau biyu bai ɗaga ba.

Ya kalli Baba yace "Bai ɗaga ba fa."

"Bari na kira shi." In ji Yaya Muhammad.

Shi ma ya kira shi bai ɗaga ba.

Nima bai ɗaga ba.

"Ha'a." Alhaji ya faɗa.

Bara na kira babansa. Alhajin ya kira layin baban Abeed suka gaisa yace yana ina ne ya gaya masa yana ƙofar gida gasu nan da mutanensa ga ma Abeed nan sun iso da abokansa.

Alhamdullilahi Baba ya faɗa , ya ce to kana ji Alhaji ka shigo nan sitting room ɗin kai da Abeed amma bara ma na saka Hamza ya rako ku.

Ni dai na manne a garu a gefe sai aikin share hawaye nake yi kawai. 

Ba a jima ba sai gasu sun shigo ciki.

Alhajin yayi mamakin ganin mu a ɗakin da yawa.

Uban gayya kuwa Abeed sak ya yi da ya gan ni a zaune in kuka. Ya juya a hankali yana kallon duk ƴan cikin ɗakin. Ya hango baƙuwar fuska sai kuma ya fuske ya sanu gu ya zauna yana gaida su Baba.

Suka gaggaisa. 

Sai ɗakin ya kuma yin shirun. 

Can kuma Alhajin Abeed yace "Alhaji yaya dai ka yi shiru kuma. Akwai wata matsala ne?"

"Alhaji akwai matsala sosai. Ba ƙarama ba."

"Me ya faru?"

Nan Alhaji ya gaya musu komai.

Zo ka ga idon Abeed kamar kwaɗo a cikin mai .

Alhaji ya kusan faɗowa daga kan kujera ya ce "Na'am. Alhaji me ka ce?"

Yadda ka ji haka muka ji. 

"Abeed me nake ji?"

Abeed ya ce "Alhaji ƙarya ne. Ban san wannan maganar ba. Waye ya zo yake yaɗa wannan sharrin a kaina?"


Nabeel yace "Idan na yi maka ƙarya babu abinda zan samu. Kai ka sani ba ƙarya nake ba gaskiya ce. Idan kuma kace ƙarya ne a je asibiti."

"Ba zan je asibitin ba. Wai kuna nufin kun yarda da wannan sharrin? Ta ya zan samu wannan cutar alhalin ba wadda nake mu'amalar banza da ita." 

"Ya isa".

Falon ya kuma ɗaukar shiru. Wayar Nabeel ce ta ankarar da su.

Ya ɗaga a hankali yace "Ga ni nan yi haƙuri." 

Ya ajiye wayar ya miƙe yace "Alhaji zan tafi. Dama lagos zan wuce wurin aiki zan koma. Ana jirana a waje."

Yaya Muhammad yace "Ai sai dai ka ɗaga tafiyar ka. Don babu inda zaka je sai an tabatar da wannan lamarin. Idan kuma ƙarya kake yi sai hukuma ta raba mu."

Nabeel ya kalli Yaya Muhammad yace " In kun je ance ƙarya nake ga nambar wayata nan ga adireshina a zo a kama ni." 

Ya kalli Baba yace "Baba na tafi. Allah Ya sassautawa wannan al'amarin."

Ya zo fita ya zo gabana ya tsugunna yace "Hajiya ki daure na san ke jaruma ce. Ba zan iya ganin ana cutar da ke ba. In sha Allahu mijin ki na nan zuwa. Sai anjima na bar ki lafiya zan kira ki in ji inda aka kwana."

Ban iya ce masa komai ba. Kawai na gyaɗa masa kaina.

Ya tashi ya fice.

'Yanzu ta ina ma zamu fita ga mutane duk sun taru lokaci yayi. Gaskiya Abeed ka roƙi Allah wannan abin ya zama ba gaskiya ba." Alhajinsa ya faɗa.

Haka muka fita muka shiga mota mukaa fice aka bi mu da zugar kallo caaa. 

Baba ne yace a fuska a fice kawai.
Asibitin da Baba ya zaɓa aka je . Aka yiwa likita bayani. Daga ni har shi Abeed ɗin sai da aka yi mana gwaji. Ban yi mamakin don an yi min ba. Ni fa wata ma robot na koma sai yadda aka yi da ni. Ga waya ana ta yiwa su Alhaji lokacin ɗauri na wucewa gashi an tara jama'a a gida. Su Mama ma da Umma suna ta kira sai dai babu wanda ya masu bayanin komai. Zan iya cewa bayan rasuwa Jj ba a taɓa yi min abinda ya taɓa ni ya girgiza ni kamar wannan cin amanar ba duk da haka a ƙasan raina ina ta addu'a ne Allah Ya saka hasashen Yakasai ba gaskiya ba ne ba.

Abeed kuwa ba ji yake kamar ya zama tsutsu ya gudu. Bai san haka abin kunya yake da muni ba sai yau. Allah Ya sani yana son Nadiya da ,da nufin sharri ya shigo raywuwarta yanzu kuma ya kamu da son ta matsananci amma an zo an rusa masa shiri. Shi ko be kwanta da ita ba zai iya dinga kallonta kawai ba zai cutar da ita ba. Gumi yake ta ko ina. Sai roƙar Allah Ya ke yi Allah Ya sa a ce report ɗin nan zai ƙaryata na baya.

Kusan awar su uku kafin aka kawo result kowa sai addu'a yake baya ma ni da Abeed. Na sani ni da Abeed mun fi kowa shiga cikin wani yanayi.

Ance shimfiɗar fuska. Kana ganin yanayin fuskar likitan ka san akwai matsala. Na sadakar ni da Abeed mun raba gari. Abeed ba mijin aurena ne ba.

Likitan ya miƙawa Alhajinsu Abeed takardar yace "Nagative."

Suka hau salati a tare.

Yaya Imam kuwa a fili ya furta "Alhamdulillahi. Allah ba ya bacci kuma Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Nadiya bata da hakkin ka Abeed. Ka ji kunya ka ɓata wayon ka. Dake kai mugu ne ka san kana da wannan muguwar cutar kake so ka sakawa ƙanwar mu ko? Na godewa Allah da Ya saka ranar Nabeel ya je wurin abincin nan har ya ji abinda yake faruwa da ba zamu sani ba da shi kenan zaka manna mata wannan cutar. Ka je don kan ka."

Ni dai kuka na fashe da shi mai sauti.

Abeed kuwa kunya da nadama suka dirar masa ya kasa haɗa ido da kowa. Yana son yi min magana ya kasa. Gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi liƙis. 

Alhajinsa ne ya haɗa hannayensa biyu kansa a ƙasa yace "Alhaji Nazifi  Alhaji Jamil ku yi haƙuri da abinda ya faru Wallahi ban sani ba...." ya kasa ƙarasawa saboda baƙincikin abinda Abeed ya aikata. 

Baba ne yace "Kayya! Haba Alhaji bai kamata ba. Ai duk mu godewa Allah da abin ya tsaya a iya haka. Ba a kai ga da na sanin ba."

Yaya Imam ne ya kama hannuna yace "Mu tafi. Kuka me za ki yi Nadeeya Allah Ya kubutar da ke daga wannan masifar. Kar ki ɗaga hankalinki ba laifinki ba ne Allah Yana son ki da arziƙi ne. Mijinki yana nan zuwa."

Daga bayana na ji Abeed yace "Nadeeya ki yafe min don Allah. Nima ban san tana da shi ba in fact sau ɗaya na mu'amalance ta shi ma tsautsayi ne da sharrin shaiɗan ban taɓa yi ba..... Da bata gaya min ba ma da ba zan sani ba. Na yi laifi da na ɓoye miki ina son k.."

Juyawa na yi a fusace na tsinka mai mari.

"Kana sona a ina? Wallahi baka sona baka ƙaunata, da kana sona da ba zaka ma bari a zo wannan matakin ba. Ka bari aka tara mutane ka dinga sa min rai..... na haɗiyi yawu na ci gaba ba zan maka baki ba na yafe maka amma kar ka ƙara kirana daga yau. Ba ni ba kai." Na ja ƙafata na yi waje.

Har muka je gida kuka nake yi. Ƙofar gidan na kalla kamar ba ɗazu ne aka tara mutane ba yanzu wayam babu kowa a wurin ba kamar ɗazun ba kukan ya kuma zuwar min sabo na saka kaina a tsakankanin cinyoyina. Basu hana ni ba kusan mintuna goma muka yi ba wanda ya ce min komai.

Duk sun tsaya zugum suna kallona da tausayi.

Umma da Mama ne suka fito waje jiki a saluɓe.

"Lafiya Malam?"Umma ta tambaya.

Ya gyaɗa mata kai kawai yace "ku shiga ciki da ita don Allah ta samu wani abu ta ci , kar ku bar ta ita kaɗai."

"Wai me yake faruwa ne?" Mama ta tambaya.


"ku shiga ciki gamu nan shigowa."

Sukuku muka yi ciki. Ni dai ja na suke yi ina bin su ba wai na san me nake yi ba ne bana ganewa sam-sam. A falon sama muka yada zango. Babu jama'a a gidan kowa ya tafi abinda ya kawo su ba ayi ba. 

Ina zaunawa akan kujera na saki kuka kamar raina zai fita. Matan yayyuna da Mama da Umma suka hauro saman suna rarrashina gashi sai tambayata suke yi na kasa yi musu bayanin komai. 

Umma dai kamar tayi kukan ita ma. Don an ƙi gaya musu abinda ya faru. Zazzabi ma ya kama ni amma ba wannan ne ya dame ni ba. Da ace za a tari bokiti da tuni an tara hawayena bokiti guda saboda kukan da na sha ban san na saba da Abeed ba sai yau da abin nan ya faru. Kenan da Yakasai bai zo ba da yanzu an kai ta gidan Abeed da tuni ya cuce ta ya shafa mata bala'in da ba zata daina da na sanin sa ba.

Yaya Imam da ya kasa sukuni zuwa ya yi kusa da ni ya zauna a kan hannun kujerar da nake ya ɗago min kaina ina kallonsa yace "Haba Nadiya kukan bai isa haka ba? Ke da za ki godewa Allah da Ya ƙubutar da ke da wannan musibar? Kin zo kin kwazabi kan ki kina ta kuka. Kalli yadda kika koma yini guda kawai. "

Cikin shasheƙar kuka nace "Yaya me ya sa sai ni?  Yaya me ya sa ya sabar min da kan sa? Me ya sa ya ɓoye min gaskiya? Da Yakasai bai zo ba kenan a haka zai yaudareni ya aure ni ya shafa min cutar ko?" Na faɗa ina tsatsare shi da ido ina kallonsa.

Kaina ya shafa yace "To ya isa ai Allah Ya fi shi ba ki da hakkinsa kan sa ya yiwa."

"Yaya babu wanda zai aure ni, cewa za ayi nima ina da cutar ka san...." kamar dai na zautu haka na koma ana ta lalashina.

Ina jin Yaya Muhammad yana korawa su Umma jawabin abinda ya faru suka hau yin salati da ta'ajubin wannan lamarin.

Mama kuwa rungume ni tayi tana lallashi na ta min nasiha da ban baki. 

Abba da Baba suka shigo suka zaunar da ni suka min faɗan kuka da nake yi don ba ni ya kamata na yi kukan ba shi Abeed shi ne ya kamata ya yi kuka. 

Da ƙyar na samu na ci abinci ina ci ma na dawo da shi. Kan ka ce me zazzabi ya koma sabo jikina rau kamar an hura garwashi saboda zafi.