TAEESH

CHAPTER TWENTY

by @zinariya0102

Tunƙwal-tunƙwal, sautin daka ke tashi, Abida ce take sirfa dawa duk ta haɗa gumi, gefe guda kuma yara ne sun fi goma suna ta wasa akan tulun wata jar ƙasa, da gani ɗaki ne ya rushe ya koma haka.

Wata tsohuwa ce ta shigo gidan hannunta ɗauke da ƙwarya, gero ne a ciki " ke Abida ga sirfe na nan yau Burabusko Delu za tai mana" Abida ta ta koɗe ta yi baƙi ta ce "To Iya aikuwa yanzu zan sirfe hi" Iya ta kwance bakin zani ta ɗauko naira Hamsin ta ce "Ga kuɗin" Abida ta ce"Da kin barhi ai naga babu yawa geron" "A'a karɓi ai sana'a kike kullum idan muka kawo sai ki ƙi amsar kuɗinki, ai ba a haka" ƙarɓa Abida ta yi tana faɗin "To angode" ta soke a jikin ɗankwalinta ta ci gaba da surfenta.

Haihuwar Abida huɗu a gidan Malam Sani (mijin da ta sake aura) marayun ƴaƴanta uku suna hannun Iyarsu, Baba Tanimu na kula da su, duk ƙarshen wata abin da Abida ta tara tana kaiwa gidan nasu, don a rage hidimar marayun ƴaƴanta.

Gidan Baba Tanimu ya zama filin dambe, tunda ya ƙara aure gida ya hargitse yau ayi faɗan kishiyoyi tsakanin Hanne matarsa da amarya Sailuba, gobe ayi da Wasila ƙanwar miji.

Tafe take ta lodo kayan koli a kanta, su robobi ne, kayan kwalliya ne dasauransu, "Sannu da zuwa Wasila" ce war Isma'ila yayansu da yake zaune a ƙofar gida, sai da ta ɓata rai sannan ta amsa, sanin halinsa na cin bashin tsiya.

"Daman ke nake ta jira ki dawo" sauke kayan ta yi tana faɗin "Ni fa gaskiya Yaya nagaji da baka rancen kuɗi, kalli kayan nan da na saro ko rabin wanda na siyo wancen lokaci basu kai ba, duk kuɗin yana wajenka baka ba ni ba, kuma yanzu ma ni bani da ko asi kaga dai daga kasuwa nake na kahe duk kuɗin da ke hannuna" Isma'ila ya ce "Kai jama'a wannan rayuwa idan ɗan uwanka bai rufa maka asiri ba to waye zai rufa maka, don Allah Wasila ki ɗan laluba ɗan tofinki, ki bani ko da ɗari biyar ce, kinga yanzu girbi ya rage mu yi, da na siyar da amfanin gona na zan haɗa duk kuɗaɗen da kike bina zan biya ki alkur'an" "Na gayamaka ni kam haka na dawo ba ni da ko asi ato" ta kama ɗaga kayanta zata shiga ciki.

"Ki yi wa Allah da ma'aiki ki bani, kinsan masifar Sailuba alkur'an yau idan na higa gidan nan ba ko anini a waje zan kwana" kallonsa ta yi ta kwashe da dariya sannan ta ce "Wani ya ce ka ƙara auren, kana zaune lafiya da ƴar matarka ba sawa ba fitarwa ka auro ƴar tasha ka haɗawa kanka gwarama, nikam ba ni da ko sisi ato" ta yi gaba ta shige ciki ta barshi nan tsaye.

Rasa abin da zai yi, ya yi har akai sallar magriba bai shiga gidan ba, yasan ba abinci zata ba shi ba tunda yau ma guduwa ya yi, shiyasa yake tsoron komawa gidan ba kuɗi, Baba Tanimu da ya ƙara tsufa ya ɗan ranƙwafa saboda tsufa ya taho zai shiga gida, ganin Isma'ila a zaune ya ce "kai Samaila lafiya kuwa?" Isma'ila ya ce "Baba alkur'an tsoron higa gidan nan nake, ba ni da kuɗi, na buga na buga bansamu rance ba, kasan irin wannan yanayin na girbin kayan gona ana rahin kuɗi to wannan matsiyaciyar matar ba za ta gane halin da ake ciki ba, hiyasa na kasa shiga ciki" Baba Tanimu ya ce "kayyah! Allah shi sauwaƙe" aljihun gaban babbar rigarsa ya sa hannu, kuɗi ya ciro ƴan dubu-dubu guda uku sai ƴan canji, gwalala idanu ya yi, don idanun sun fara rauni sai ya kalla sosai zai gane, ɗari uku ya waro a ƙananan canjin, ya ce "Ungo wannan ka ɗan lallaɓa" Isma'ila ya ce "Haba Baba nawa ne nan, jaka ce fa da rabi, yo wannan me zai min, don Allah ko guda ce a dubun nan ka ba ni" Baba Tanimu ya ce "Oh watukun ka raina abin da na bakan ko, to ba ni kayana" da sauri Isma'il ya janye hannu yana faɗin "Habadai ai alkur'an sun zo kenan" hahh hahh ja'iri ai da ka bani abina" ce war Baba Tanimu. A tare suka shige ciki.

Ƴaƴa ne a zazzaune suna cin tuwon dare, kwanon mata daban na maza daban, ƴaƴan Wasila da na Abida da na Hanne sune manya, ƴaƴan Sailuba amarya sune ƙanana sai waɗan da Hanne ta haifa sa'annin na Sailuba su biyu.

Tun shigowarsa ta ke galla masa harara, washe baki ya hau yi yana faɗin "Abinci ake ta ci kenan" yaran da ba su ganshi a ƙofar gida ba suka hau faɗin "Baba sannu da zuwa" Hanne ce ta fito yanzu ta idar da sallah, ita ma ta ce "Sannu da zuwa" ya amsa da faɗin "Yauwa ya gidan dai lafiya ko?" ta ce "lahiya lumi" ya wuce ɗakin Sailuba, ganin kishiya yasa bata hana shi shiga ba, bin bayansa ta yi, kwance ta ganshi a gadonta wanda ta gyara ta ɗame shi.

"Sakko, alkur'an sai ka sauko min daga gado" ya ce "in sauka in zauna a ina, haba Sailuba meyasa ba kya son zaman lahiya ne" ta ce "Zaman lahiya ai Isma'ila baka so ba, dan idan da yunwa babu zaman lahiya alkur'an" "Tsaya ki ji, kinsan dai na kusa fitar da amfanin gona ko, kuma kinsan duk hekara yadda nake wadata ku da abin buƙatun yau da kullum ko?" ta ce "Nasan wannan karatun amma ai ana tanadi saboda rani irin haka, ka fice ka barmu da ƴaƴa ga yunwa ga ba ko asi sai yanzu ka wani ɗauko sangalalon ƙafafuwa ka higo" ya ce "Tunda na fita nake ta faɗi tashin samo muku abin da zan baku, kinga wannan jaka guda da rabin alkur'an in banda su ba bu komai a jikina" ya faɗa yana miƙa mata su, ta ce "jaka da rabi me jaka da rabi za ta yi mana a gidan nan" ta yi ƙwafa tana soke kuɗin a jikin zaninta, ta fito tsakar gida, yunwa nata naɗe hanjin Isma'ila.

Tuwon ta sa masa ta kaimasa ɗakin "Gashinan ba don halinka ba" ya tashi da sauri yana faɗin "to, to Allah dai ya zundumaki a aljanna" ya ja kwano ya hau zuba loma.

Da safe ta dama koko ta bashi sannan ya nufi gona daga nan ya shiga zaga gari, ba shi da wata sana'a wacce ta wuce aikin noma, idan rani yayi yai ta garari a gari.

ƘAUYEN ƊAN KADA

La'asar sakaliya matasan ƴan mata ne su uku suka yi sallama gidan sunTAEESH, tana zaune tana rubutun allonta, ko wacce ta yi kwalliyarta riga daban zani daban, sun zane fuska da ɗige-ɗige.

"Assalamualaikum" Maimuna ce ta yi sallama, a ciki ta amsa tana ci gaba da rubutunta, A'i ta fito daga ɗaki tana fara'a, gaisheta su ka yi, suna zama akan tabarmar da TAEESH take.

"Maimuna, Kubra, Aina'u kune" TAEESH ta faɗa tana yi musu murmushi.

Maimuna ta ce "Daman nasan ba ki da niyyar zuwa shiyasa na ce mu biyo miki gaɗar" A'i na jinsu, TAEESH ta ce "Ni bazan je ba kinga ma rubutu nake yi" Aina'u ta ce "Ummi kin ji wai baza ta je ba, don Allah ki ce ta tashi mu tafi" Ummi da tasan halin TAEESH da kafiya yasa ta ɓata rai ta ce "Tashi ki kimtsa ku je, amma kar ku kai magariba" ba musu ta jingine allon, ta shiga ɗaki, kaya ta sauya, zani daban riga daban, naɗe gashinta ta yi ta cusa shi cikin ɗankwali kamar yadda A'i ta ke mata.

Bata shafa komai a fuskarta ba, farin ta mai ɗaukar hankali fau, ya fito sosai, idanunta tamkar tasa kwalli pink lips ɗinta sai glowing yake kamar tasa lips stick, tamkar ta yi light make-up haka fuskarta take, kwalliya bata dame ta ba. "To sai kun dawo, Allah ya tsare" ce war A'i, da murna suka tafi.

Cike dandalin yake da ƴan mata da samari, wasu na rawa a filin gaɗa, wasu na zance da ƴanmata, don ƴan sha uku sha huɗu su ne ƴanmata, su Aina'u kuwa sune ƙwailaye sai dai akwai rawar kai, tsayawa ta yi ta harɗe hannuwa a ƙirji, tana kallo, su Maimuna kuwa filin rawa suka shiga akai ta yi da su, mutum ta gani tsaye akanta, yana mata murmushi, matsawa ta yi, ya kuma matsawa, ganin haka yasa ta yi gaba don barin gurin, da sauri ya sha gabanta, ya ce "TAEESH meyasa kike gudun mutane ne, ni fa ɗan uwanki ne, tun kina shikin tsumma nake ɗaukanki" duk da batason magana sai da ta yi "Hanma Lamiɗo don Allah ka daina min irin haka, ni banason magana" ya ce "Na shani ai, amma a ce rayuwa za ta yuwu batare da jama'a ba, ki dubi nisan rugarmu, tun ina yaro nake zuwa shikin garin nan saboda kai, haba Innawuru, ko woni gashi, yo wa ndiyan ɗum e jam, mi anndaa mi yi’i maa no mbidan, ndun no mari neɗɗo e jam wala ɓe, yo a heɓi am ko ko ɗoo e jam, e nder kam e nder yimɓe.(Ko ba komai ai kya saki jiki da ni, ni ba cewa nayi ina sonki ba, yanzu kina jin daɗin rayuwa babu Yaya, ki ɗauki ni a matsayin yayanki mana Innawuru).

"Kai Jauro ware daga nan, alkur'an ko yanzu mu baka kashin tsiya" Lado ne ya faɗa yana shan rake, kayansa duk datti, Lamiɗo ya ce "Ni ba faɗa ne ya kawo ni garinku ba, TAEESH ƙanwata ce, ba wai yanzu tasan ni ba"

"Hahhh ku ji wani zance TAEESH ɗin ce ƴar uwarka, ku ji zancen banza, yarinyar da tsintarta aka yi, babu wanda yasan asalinsa, to kodai ubanku ɗaya don da gaske na fara ganin ɗan kamanni" suka hau yi masa dariya shi da abokinsa Abba, bai kuma ce wa komai ba ya wuce ya tafi.

Kalmar tsintarta aka yi, ke yawo a ƙwaƙwalwarta, juyawa ta yi, da gudu tana kuka, duk wanda ya ganta sai ya ce lafiya, bata sauraron kowa, a haukace ta faɗa cikin gidan "Ummi! Ummi!! Da gaske ne tsintata aka yi, da gaske ne ba ku ne kuka haife ni ba?" gaban A'i ne ya faɗi, butar da ke hannunta ce ta suɓuce ta faɗi, ruwan ya zube.

"In ji uban waye ya faɗi haka?" ta faɗa tana riƙo TAEESH wacce take a gigice a jikinta ta sata ta na faɗin "ƙarya ne ni ce nan mahaifiyarki duk wanda ya faɗi haka, sai na kai shi wajen maigari" TAEESH da ke kuka ta ɗago ta ce "Ummi haka su Inna ma suke ce wa, kuma yanzu ma Lado ya faɗa" ta ce "Ƙarya suke yi TAEESH ki daina kuka, nima idan ba so kike ki sakani kukan ba" ajiyar zuciya ta hau yi zuciyarta taƙi nutsuwa da abin da A'in ta faɗa.

Malam Ali ne ya shigo, ganin yadda TAEESH take kuka, A'i na ta ƙoƙarin mayarda da ƙwallar da ta cika idonta, ya ce "mene ne, wani abu ne ya same ta?" Da sauri ta saki A'i ta koma wajensa ta ce "Baba! Lado ne ya ce min tsinta ta aka yi babu wanda ya san asalina" Jiri ne ya fara ɗaukan shi, ya kamota ya na faɗin "Wannan ba gaskiya ba ne, ke baki da hankali ko baki san iyayenki ba, kalle ni nan, ni ne mahaifinki, Ummi ita ce mahaifiyarki, kuma wannan maganar ba zan barta ba don ba zan yadda ya ɓata min suna ba, zauna anan" ya zaunar da ita "A'i ba ni ruwa tasha" da sauri ta ɗebo a randa ta kai masa, da hannunsa ya bawa TAEESH ɗin, yana ƙara faɗin yanzu zan je ayi duk wacce za a yi akan wannan maganar ta Lado.

Zama suka yi, suka hau yi mata labarin haihuwarta da yadda A'i ta yi ta wahala da cikinta, da ranar da aka haifeta da sunanta, da duk shagalin da aka yi, sai ga TAEESH tana dariya tana kuma tambayarsu ni nayi kaza da kaza, suna ƙara tabbatar mata.

Nan da nan suka kwantar mata da hankali.

Sai da tayi bacci, sannan suka fara maganar a hankali A'i ta ce "Malam ina tsoron ranar da yarinyar nan zata san gaskiyar maganan nan" Malam A'i ya ce "Tabbas in dai muna cikin garin nan to kuwa dole watarana sai tasan gaskiya" A'i ta ce "To yanzu ya ya za mu yi?" ya ce "Bansaniba tukun na, amma ki ƙara kula da ita ki hanata yawan yawo don kar wani ya ƙara faɗa mata wannan maganar" ta ce "In sha Allahu malam" haka suka kwana saƙe-saƙe a ransu.

Haka rayuwa take ta tafiya TAEESH na ƙara girma, kyau da hankali na ƙara zuwar mata, tunda ta shiga step ɗin adolescent ta zama budurwa ƴar shekara goma sha uku, hankalin A'i yake a tashe, ganin yadda TAEESH take da kyau mai jan hankali, bata barinta fita ita kaɗai, ko aike ne to sai tasa gyalenta ta rufe gidan su tafi tare.

Da daddare Ai da malam Ali suna hira, TAEESH na ɗaki tana tunanin wani mummunan mafarki da ta yi, wai ga wani mutum kyakkywa akan farin doki ya zo yana son ya ƙwaceta daga hannun su Ummi, su kuma sun riƙeta gam, suna faɗin ƴarsu ce, ba za su bashi ba, mutumin ya nuna ƙarfin iko ya sa aka ɗaga ta sama, bayansa ya sata ya saki linzamin dokin suka gudu.

Addu'ar tsari da mugun mafarki ta yi, sannan ta fito ta zauna gurin iyayenta, yaro ne ya shigo yana faɗin "wai ana sallama da TAEESH" kallon juna suka yi, kowa zuciya ɗauke da fargaba, malam Ali ne ya ce "Ka je kace gata nan zuwa" takalminsa ya sa ya fita.

Muntari ne ɗan maƙotansu, ganin Malam Ali ne ya fito, yasa ya durƙusa ya gaishe shi, malam Ali ya ce "Kai ne ke kiran TAEESH?" cike da kunya ya ce "Eh Baba" malam Ali ya ce "To ma sha Allah, idan har da gaske kake ka sanarwa da mahaifinka ya zo mu yi magana kafin na baka izini" ya amsa da zai turo shi, sannan ya tafi.

Tunda ya sanarwa da iyayensa abin da malam Ali yace sukai ta faɗa, Mahaifinsa na faɗar "Yarinyar da bata da asali ba a san iyayenta ba za ka kwaso mana irin masifa, to alkur'an baka isa ba, ka je ka nemi kowace ƴa a garin nan zamu aura maka, amma banda ƴar wajen malam Ali TAEESH".

Duk da Muntari yasan wace TAEESH, don da wayonsa aka tsince ta, bai taɓa zaton iyayensa ba za su amince ya aure ta ba, haka Muntari ya haƙura da neman TAEESH ya koma wajen Aina'u ƙawarta.

Duk wanda yake son zuwa wajen TAEESH sai iyayesu su hanasu, daga ƙarshe kowa ya shiga jawa ɗansa kunne akan yarinyar, tun daga lokacin babu wanda ya kuma zuwa wajenta da sunan soyayya don aure, sai dai don a lalata ta, malam Ali kuwa duk wanda ya zo to sai ya ce sai ya turo iyayensa.

Malamansu na makarantar boko ma da suke sonta, Aina'u da Maimuna ne suka sanar da su wacece TAEESH, suma kowa ya kama kansa.

Rayuwar TAEESH ta zama abin tausayi, ga Lamiɗo su Lado sun hanashi shiga garin, duk inda TAEESH ta yi sai wani ɗan iskan ya biyota yana son taɓa ta, da gudu take komawa gida.

Abin ne ya ishi su Malam Ali sun rasa yadda za su yi suna tausayin ƴarta su sosai.

Tsahon lokaci yana ta nazarin wannan cukukuɗaɗɗen al'amarin, yanke shawara ya yi na barin garin gaba ɗaya, cikin dare TAEESH na bacci, A'i ta shiga tashinta a hankali, buɗe ido ta yi "tashi-tashi mu tafi" watstsakewa ta yi ta ce "Ina za mu je Ummi" "shiru!"Ai ta ce, tana ɗauko buhun kayansu da ta haɗa tun da rana, Malam Ali na riƙe da wani buhun ya ce " ku taho mu tafi" a hankali suka buɗe gidan nasu, suka kalli gidan idanunsu cike da hawaye, suka kama hannun TAEESH su ka bar garin cikin talatainin dare.................

ALHAMDULILLAH ANAN MUKA GAMA BOOK 1, MU HAƊU A BOOK 2.

EACH PAGES AT THIRTY NAIRA ONLY

Zinariya ce✍🏻