JADEEDA

Page 25

by @cwtsumiey19988

*JADEEDAH*
 
STORY & WRITTEN BY :
 (*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin 
        MENE NE ABIN YI ?
        KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*

*YOTA*
BOOK 1 



PAGE 25❤🔥

     "Yauwa Momy bari in k`ara maki da wannan so nake ki cinye komi dake soman table d`innan", Jedeeda ta fad`a ta na mai k`arama Momynta Plantains ɗin dake gabanta.
     " Jedeeda na k`oshi tun d`azu kin san ko lafiya na lau ban cika son cin abincin mai nauyi ba,Na ci omelette,Na sha Oat,kuma yanzu ki ce za ki k`ara min da plantaint,Haba ya isa haka".
     Turo baki gaba Jadeeda tayi kafin ta ce,"Momy so na ke fa na ga kin maida jikin ki,kalli fa duk kin rame,ba na son ganin ki a haka".
    "In banda abun ki Jadeeda,Ai sai da muce mun gode ma Allah, Matar da ko Tea bata son sha ,yanzu ta zage ta ci wad`annan,ai lamari yayi kyau", Cewar Granny da ke zaune a gefe.
    " Mom ai haka Jadeeda ta ke bata da natsuwa ko kwanciyar hankali indai akace maki Momynta ba lafiya,in kin ga ta huta to ta samu lafiya ne,duk wata d`awainiyar da kulawa ita ke yi mata ita".
    Uncle R ne ya sauke Cup d`in da ke hanunshi shi kafin ya ce,"My Angle ta musanman ce hakan ya sa na ke ji da ita,Ko ba komi tana da kyawawan halaye da za ai koyi da su"Ya ɗan dakata kafin ya cigaba da cewa,"Wai ya Maganar Voice of Convenant, ɗin da ki ke gudanarwa ya yanayin program d`in yake tafiya fatan kuna Succeeding yanda ya kamata?",ya kai zancen da sigar tambaya tare da maida akalar zancensa kacokan kan Jadeeda.
    Yanayin yanda ta fara raba idanunta ya sa Gloria ta fahimci akwai wani abu da ke faruwa ko ma ya riga da ya faru,a jiye Spoon d`in hannunta ta yi kafin ta ce da ita,"My Daughter ya dai,ko dai kun fara fuskantar wasu matsaloli ne akan program d`in na ku,shin wani abu ya faru ne?".
    "No Momy ba abinda ya faru,kawai dai bana attainding d`in komi,I'm focus on you ,hankalina baya kan komi ,tun ranar da aka kirani akasanar dani halin da ki ke a ciki ban sake zuwa wani Hall,meeting ko kuma Church ba,in har da sunan gudanar da program d`in da na saba ne".....,"Hah...Jadeeda.... Halalujah..wannan wanne irin hukunci ne ki ka yanke, ai bai kamata ba,aikin da ki ke yana da matuk`ar girma da lada kina fa kiran mutane ne to the word of God, so akan me za ki dakata,shin kin san iya adadin mutanen da suke amfana da abinda ku ke,ina Sister Zarah da kuma Madam Alena suke akan me suka bar ki,ki ka yanke wannan hukuncin?".
    Fuskar Jadeeda tamkar zata zubar da hawaye kafin ta ce,"Momy ke ce fa baki da lafiya,ta ya Zan iya maida hankalina akan wani lamari bayan ga ki kwance ba ki san inda kan ki ya ke ba"...."Ciwona bai kai yad`a bushara da ki ke yi ba Jadeeda ,haka kuma Ciwona bai kai rera wak`ok`in ban gaskiya da yabo ga Yesu Almasihu ba,ta ya ma za a had`a su ?".
    " Anty please kiyi hak`uri ban san wannan Maganar tawa za tai coursing d`in wata hayaniya ba,biside ma ta na da gaskiya bata da natsuwa taya za ta iya gudanar da wad`annan muhiman aiyuka za a iya samun Matsala so please ki yi mata hak`uri za ta koma kan aikinta idan komi ya natsa".Cewar Uncle R.
     "Ko ni ma mun yi wanna Maganar da ita,tunda fari uzirin da ta bani mai girma ne shiyasa na amince ma ta har da sake bata goyan bayan,ta na iya k`ok`ari ta yanzu haka Synagogue, Church of All Nations (SCOAN) da ke Lagos sun za`beta a matsayin wacce zata bud`e masu taro da dad`ad`an wak`ok`inta a ranar Easter".
  Gaba ki d`ansu murna su ke da jin wannan labarin dan ita kanta Jadeeda bata san da zancen ba,ba ta san san da ta je ta rungume Papa ta na ta zuba masa Godiya ba,"Kai wanna abun farin ciki ne,Anty J za ki tafi Lagos kuma wannan katafariyar Church d`in gaskiya da ni za ki tafi", Cewar Martin,Cikin murna Jadeeda ta ce da shi," Kar ka wani damu gamu can mun tafi tare,Nora Kema za ka biyo mu mu tafi tare ?", sai da ta ya mutsa fuska kafin ta ce,"No Anty J I'll Stay with Mom zan kalli komi a TV or through the Phone".
      Granny ce tace,"Abun murna ya same mu sai na ke ji kamar in tashi in taka rawa my Granddaughter zata je SCOAN",ta fara girgiza jikinta ta na daga zaune,nan fa suka dunga nuna murnar su a fili,har Uncle R na cewa nan gaba shine zai zamo Bodyguard na ta.
     "My Daughter matso kusa da ni in rungume ki,Na ji dad`i ban ta`ba tunanin zan wayi Gari in ga irin wannan ranar ba,sai ga shi Allah ya nuna min na rasa ta wacce hanya ma zan bayyanar da farin ciki na,tafiyar ma ta kusa nan da one weeks ne ko ?", "Eh haka ne haka suka sanar da ni so ya kamata ku fara preparing, in ya so sai mu tafi gabad`aya kamar hakan zai fi"..... Cewar Papa,da sauri Granny ta katse shi da cewa," Jikin Gloria har yanzu da sauran shi zai fi kyau ace ta na zaune wuri d`aya ko da na d`an wani lokaci ne,in ya so kai za ku iya zuwa ni sai in zauna tare da ita".
    "Okay Mom yanda ki ka ce haka za ai,kai lokaci ya ja yau ne fa Edwin zai dawo Na so in shafa'a,har zuwa yanzu ban tura Wanda zai d`auko shi ba".
    " What!! Yau Broz Edwin zai dawo amma ban sa ni ba ?","Kamarya ba ki sani ba Jiya jiyannan fa muka gama Video Call da shi,ni da na gaji ma nan na barshi shi da Nora, Martin da Granny yana ta faman tsokanar su,kin san shi da barkwanci har ma yana cewa da ya yanke zai Kira ki".
    Cikin rashin jin dad`i Jadeeda ta ce,"Mom I swear to the God bai kirani ba,ko na kira shi ma baya d`auka mun d`au lokaci mai tsawo a haka,baya picking call d`ina na rasa me na yi masa,kuma a baya ba haka ya ke min ba,muna da fahimta a tsakanin mu".
    "I'm sorry kin ji ban San haka na faruwa a tsakanin ku ba,da ni da kaina zan kira shi in ji ba'asi amma koma me ye I promise to you ya zo k`arshe tunda ga shi yau zai dawo Gida", Cewar Papa ya kai zancen ya Na mai bubbuga mata baya alamun lallashi.
    " Papa ka barni in je in picking d`in sha a Airport zan so in fara had`uwa da shi","Ba damuwa sai ku tafi tare da Uncle R da Martin nasan Nora ba lalle ta je ba,ta fi son ta kasance jikin Momyn ta a koda yaushe".Nan ya basu details d`in Flight d`in da kuma lokacin saukarsa,kana ya shirya ya fita dama yana da inda yake son zuwa tare da su Nora ya tafi ya aje su inda suke part time d`in su na koyan Computer kafin fitiwar Jamb d`in su.
    Haka suka cigaba da hirarrakin su har time d`in ya gabato
    "Uncle Miey let me take a shower before the flight arive","Take your time I'll Wait you in the car,but please kar ki dad`e ina so mu yi sauri mu dawo,akwai inda na ke son in kai ki I need to surprise you".
    Sai da tai hugging na sa kafin ta ce," I'll be right back ba zan jima ba,domin kasan ina son surprise d`in ka, dad`i na kusan kashe ni","To ki shirya ma wannan domin kusan ya fi na koyaushe",idanuwanta ta fiddo waje irin da sigar tambaya d`in nan,"Yes I'm sure ke dai don't waste my time ki yi sauri ki fito ",ya kai zancen ya na mai binta da wani kallo mai cike da tarin ma'anoni,ita ko ko a jikin ta sai mik`ewa tayi ta upstairs da saurinta domin ta shirya.
    Wani dogon tsaki Granny ta saki tare da cewa,"Haka za ka k`are kullum ba ka da aiki sai d`aukar your Niece kana yawo da ita lungu da sak`o amma ba za ka iya fitar da mata kai Aure ba".
    "Mom Haba mana na ce fa zan yi Aurennan to meye na irin wad`annan k`ananun zancen"," Oh k`ananun zancen ne ma to idan baka son k`ananun zancen ka bari ni in nemo maka Matar Auren ai ni hakan ba abu mai wuya ba ne a gare ni".
    "Ah no Mom ina da kalar type d`in Macen da na ke so ki bar ni zan nemo da kaina ,in dai Aure ne a bar Ni zan yi,zan za`bi wacce ta yi min", ya kai zancen ya na mai barin wurin gabad`aya.
    Cikin karyayyiyar murya Granny ta dubi Mom ta na mai cewa," Kalli Gloria ya tashi ya tafi ,ban san har sai yaushe Rechal zai ji ya kuma saurari Maganata ba,har Mahaifinku ya mutu ba shi da wani buri da ya wuce ya ga Aurensa amma Yaronnan ya k`ek`ashe idanunsa ya ce mi shi bai ga Matar da zai Aura ba har ya mutu ya na tuna hakan, yanzuma gashinan sai fama na ke da shi ya k`i ji,wata k`ila nima ba ni da rabon gani Auran na shi ".
    " God for bid Momy za ki ga Auran shi,by the grace of God, bari ya dawo ni nasan ta inda zan `bullo masa",haka ta ciga da lallashin ta har zuwa wani lokaci.
    Sanye da gowm wacce bata kai gwuiwarta ba ta fito gashin kannan nata ya sha gyara ta sake shi har gadon bayanta,kafarta kuwa sanye take da high heel shoe, sai k`amshin Oud da ke faman tashi a jikinta,yadda kasan yar bebyn roba haka ta ke taka k`asa,ta yi kyau matuƙa kamar ka sace.
    "Oh my Goodness Anya kuwa zan yarda mu fita tare da ke a haka,kar fa ki sa in rik`a had`a goslwo ko accident a saman hanya,irin wanna kyau haka,na ga alama da gaske so ki ke, ki samu wanda zai huf ya raba ni da ke".
    Ah Uncle Miey ba wanda ya Isa ya raba ni da kai,domin duk wanda zan rayu da shi zai so ni bayan son da ka yi mi ni ne,haka kuma zai kuka da ni akan kulawar da ka ba tun ina `yar karamata,har kawo girmaba".
    " Har yanzu ke Baby ce a gare ni,ban k`i in d`auke ki in goye a bayana in zagaye Gidannan da ke ba,ki sa ni kina da matsayin mai girma da muhimmanci a wuri na duk da kullum a cikin zullumi da fargaba na ke",ya kare zancen ya na mai matsowa kusa da ita.
    Cikin yanayin Maganar da ya yi ta shiga ranta ta ce da shi,"Uncle miey me ye yake sa ka cikin Zullumi da fargaba a kaina ba tare da na san shi ba?",sai da ya kamo hannunta ya rik`e a cikin nasa kafin ya ce da ita,"Ina tsoran ranar da za ki bar ni ranar da za ki za`bi wani sama da ni ranar da za ki fifita Soyayyar wani akan tawa ban San ya Zuciyata za ta kasance ba ,tabbas zan iya rasa rayuwata akan haka",da sauri ta kai hannunta saman bakin sa ta rufe tare da cewa,"Uncle Miey haka ma ba zata faru ba,kai jini na ne kuma rayuwata babu ta yanda za ai wani ya shigo rayuwata jiya ko yau ya ce zai maye gurbi ko matsayin ka a wurina ka sani ba zan ta`ba barin ka ba a koda yaushe zan rayu da kai ,a duk inda na ke ba abinda na ke tunawa indai har za a ambaci ko me irin sunan ka ne face na tuna,kulawa,Soyayya karamci da halacin da ka ke min".
     "Da gaske ba za ki barni ba,ko da kuwa nan gaba,ba za ki ce nayi ma ki tsufa ba", ya fad`a ya na mai damtse hannunta dake cikin na sa.Dariya sosai Jadeeda ta saki jin ya ambaci tsufa,`bata fuska ya yi,tare da cewa,"Au dariya ma na baki to shikenan sai ki cigaba tunda na zama abun dariya".
    " Oh sorry Uncle Miey ba haka na ke nufi ba,just kawai na hasaso fuskarka da furfura ne shiyasa Na ke dariya",shima dariyar ya yi gami da sa hannu ya bud`e mata front seat wurin zaman banza kafin ya shiga ya tada motar su tafi,suna tafe ta na tsokanar shi.