SHINGEN KAUNA

Chapter 15

by @khairatup01

SHINGEN ƘAUNA.
Khairat.
Watpad:khairi_muhd.
Paidbook #500
Last free page 15.

*

Capon7 park.
Airport road Avaition quters.


Yaran Yaya Muhammmd na kawo park yau. Da Mama da Faruk da Nazif (Daddy) mun shiga har mun biya kuɗin hawa lilo. Ina zauna kan kujera ina kallon yadda suke ta abubuwa suna jindaɗi ina musu vedio. Yara dai yara ni Nadeeya ina son su kuma ina roƙon Allah Ya bani nima.

Kawai gani na yi mutum ya zanuna a gefe na. 

Na juya bakina a buɗe na ce "lafiya Malam meye haka?"

"Kaitsaye suna na Saifullahi Idris Ƴan awaki. Ni ɗan kasuwa ne ina da mata ɗaya ina zaune a nan tudon yola. Yara biyu Aisha da Amina ƴan biyu ne,kin gan su can na kawo su nan suma su shana."

Na saki baki kawai ina ganin ikon Allah!

"Ɗan kulle bakin ba fa dodo ba ne ni mutum ne ni kamar ke kawai lokaci guda ne kibiyar son ki ya kama zuciyata."

"Ha!.."

"Na san me za ki ce. Bana son ka, ni ina da aure waɗancan ƴa'ƴana ne waye-waye ki dai ɗan ja min aji haka na sani to ki saurara ma ki ji sai da na yo homework a kan ki  . Duk baki da kuma ina roƙo a bani dama na ya yaɗa manufata."

"Wallahi kana da ƙarfin hali."

"Na sani." Ya faɗa yana dariya.

Kafin dai mu bar wurin mun jima muna hira muka yi exchange ɗin lambar waya. 

Ya sai wa yara snacks da icecream muka rabu a bakin titi ya ce min zai zo gida ya same ni.

Na koma gida da walwala yana da barkwanci da tsokana babu wadda zata iya ƙin kula shi.

Kamar yadda ya faɗa washegari kuwa da yamma ya kirani yace gashi nan a ungwar mu in kwatanta mai gidan ban yi mamaki ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gidan namu. 

Tun kan ya iso na saka aka yanka dankali aka soya da kwai.

Sitting room ɗin Baba na kai shi na waje ya zauna. A nan muka yi ta hira da shi ya dinga bani dariya kuwa. 

Wallahi yana da kirki da barkwanci. Cikin kwanaki biyu kacal muka saba. Kun san ni da saurin sabo dai dama. 

Ban ɓoye masa komai ba , da wani ya gaya masa a baibai gwara ni na gaya masa yadda zai fahimta. Yace min babu komai ai ana samun irin haka kada na wani ɗaga hankalina.

Shi ni yake so kuma mutane dama ba abinda suka iya sai son raba aure. Ya gaya min da gaske yake sona kuma ba so yake a wani ja lokaci ba tunda dai ni ba budrwa bace da za ace a ja abin sosai. 

Ya gaya min matarsa ma ta san da zamana yanzu kuma ta ce ya gaishe ni. Nayi mamakin wai matarsa ta san ni har tana gaishe ni anya kuwa wannan mutumin?

Kar kiyi mamaki ƴar'uwata ce kuma ƙawata ce , iyayenmu ɗaya a takaice dai auren zumunci ne kawai. Bana ɓoye mata komai ni.

A raina kuwa tunanin maganar sa nake baya ɓoye mata komai wannan za ayi sirri da shi kuwa?  Da haka dai muka rabu.

Baya wata ɗaya ya turo aka tsaida lokacin biki sati biyu masu zuwa. Amma Baba ya sa aka kara zuwa wata ɗaya sai ya gama bincike sosai a kan sa baya son a sake maimaita irin na baya
.


Nabeel.

Da gajiya na dawo yau, dama raina a ɓace yake. Haka na dafa indomie da ƙwai na ci. Na yi wanka na saka kaya marasa nauyi na zauna. 

Ina son zuwa Kano wani satin. Rigimar Hanan ta ishe ni. Haka na ƙara neman leave aka bar ni kwana biyu kacal fri-sunday zan dawo. 

Watsapp na shiga ina bin saƙonin mutane. Nan na ci karo da saƙon gayyatar biki na Hajiya da kanta ta aiko min da saƙon. 

Na aika mata da saƙon "Allah Ya sanya alkairi Ya basu zaman lafiya."

Ta aiko min da "Zuwa fa zaka yi ba wai iya addu'ar ba wannan karon ka zo ka taya ni farin ciki." 

"In sha Allah kuwa zan zo. Za shigo Kano ran Juma'a."

"Ga shi asabar ne ɗaurin auren sai ka zo."

"Ai kuwa in Allah Ya yarda za ki gan ni."

"Allahu Ya yarda."

"Amin."

Na koma cikin inbox ɗin Hanan aiko tana onlayin.

"Masoyiyata barka da dare. Fatan kina lafiya?"

"Nabeel anya kuwa kana sona?"

"Ke kin sani son da nake yi miki ba shi da adadi ko misali. Saboda haka ki daina ma tantama."

"In ka zo ka zo wurin Abba ka nemi aure na."

Bai bar mamaki ba amma haka ya maida mata amsa.

"Hanan , kin san fa ba ni da wurin zama ko? A yanayin gidanku ma ai sai na tara kuɗin ko? Ko a haka ake auren kaitsaye babu shiri?"


"Baka son nawa kenan?"

"Hanan me ya faru ne?"

"So nake yi ka aure ni."

"Haka nake da buri da fata. In sha Allahu kuma zan aure ki."

"To wannan zuwan ka zo ka samu Abba."

"To shi kenan zan zo amma zan gaya masa gaskiya yanzu nake tasowa ban wani tara dukiya ba sai chicken change."

"Ni dai na gaya maka ko a ɗakin ka na Lagos ne kawai zan zauna."

Na tura mata da emoji ɗin nan na dariya. Saboda maganar ta ba ni dariya. Wai a ɗakina na nan, a yadda na sani mahaifinta ba zai yarda ya ba ni ƴar sa ban da komai ba. Amma haka na biye mata nace zan je mu yi maganar da shi. Sai muka koma hirar soyayyarmu.

*

Bayan Sati Ɗaya. 
Asabar.

Wannan karan dai ba kamar wancan ɗaurin auren ba. Ba a taru kamar wancan karon ba. Amma hakan ma babu laifi. 

Ban gayyaci kowa a ƙawayena ba saboda can ƙasan raina ba na jin wani karsashi da daɗin auren. Ƙarfe biyu za a ɗaura auren. Har ma na je kasuwa na dawo na yi wanka wajen ƙarfe ɗaya na rana.

 Na yi wanka na sa ka leshi baƙi da adon fari a jiki ɗinkin doguwar riga ne kaftan mai kyau shi ma Yakasai ne ya ɗinka min a cikin ma kaya na ɗaukota na saka.

Su Mama ne kawai a falo suna hirarakinsu. Ni dai ina zaune a gefe. Can samarin gidan suka dinga shigowa sun ci kwalliya cikin shadda har ina tsokanar Zainu ne ma wayata ta soma ringing.

Ina dubawa naga lambar wayar Nabeel ce.

"Yakasai ka cika alƙawari."

"Na cika Hajiya ina ƙofar gida kamar wancan karon gamu nan muna dakon jiran lokaci."

"Ka shigo ciki mana to."

"Eh yanzu zan shigo. Na ga Yaya Imam ma yana kirana."

"To mungode."

Na ajiye waya.

Ina ajiye wayar na ga kamar kiran Saifullahi.

Bin sa na yi na kira shi amma bai ɗaga ba. Can sai ga Summaya ma ta zo da jaririnta ta haihu mace ta haifa.

Na karɓi babyn ina mata wasa nace "Yi mana hoto mana ƙawa".

Ta dinga ɗaukar mu a waya.


Farfajiyar Gida.

Su Baba sun shirya tsaf ana ta jiran su Saifullahi. 

Har ƙarfe uku babu wanda ya shigo yace an ɗaura auren na.  Mu dai muna ciki muna ta raha. Can matar Saifullahi ta kirani da ke tana kirana wani bin wai mu gaisa. 

Ina ɗagawa na ji ta soma min dariya. 

Ni dai na yi shiru ina ganin ikon Allah.

Can da ta gaji tace "Amaryar bogi kina can kina jiran guɗa ko? To saurara da kyau kiji mijina nawa ne ni kaɗai ba ki isa ki shigo min cikin gidana ba. Wai ke kin gaya mai komai bla bla bla. To na kai shi inda aka isa da shi aka fi ƙarfinsa an kuma dakatar da shirinki. Wato mu za ki yaudara ki cuta ai an gaya mana cutar Hiv ke damunki kin je kina raba jikinki wa maza mabambamta shi ne za ki zo ki cuci bawan Allah Saifullahi da matarsa da ƴan ƴa'ƴansa to Allah Ya fi ki . Lokaci na baku dama kuma lokacin ya cika kije can ki nemo abokin kwartacin na ki ku ƙare da wahalar ku mu nan gidan mun fi ƙarfin ki azaluma mara imani mai saida jikinta don kuɗi." Kit ta kashe waya na bi wayar da kallo. 

Mama ta ce "Yaya aka yi?"

"Mama matar Saifullahi ce ta kirani. Na labarta musu komai da ta gaya min."

Mama tace "Kai wai fisabililahi wanne irin sharri ne wannan? Waye ya gaya musu kina da cutar Hiv har kina bin maza. Mutane ba zasu ji tsoron Allah ba su dinga yaɗa ƙarya suna hana aure."

Wallahi na kasa ma kukan sai dai wai abu da ya tokaren maƙogwarona mai ɗaci. Nayi-Nayi ma na yi kukan amma ya ƙi fitowa. Na yi zugum ni dai ina jin zuciyta na bugu da sauri da sauri.

Falon ma tsit ya yi. Kana kallon Umma zaka san akwai tashin hankali kwance a kan fuskarta. Kuka ma ta soma Mama na lallashinta. Aunty Hibba matar Yaya Imam ta dinga bata baki. 

Ina ma ni ma zan iya yin kukan ai da na samu salama a raina.

Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai Zainu ya shigo da sallama da goro a hannunsa da kuma ledar alawa ya ajiye a tsakiyan falon . Daga bayansa ma Jameel ne da na sa kayan. Babu wani tashin hankali a kan fuskarsu , sai na ji wani sanyi  a raina na gayawa kaina da kaina tsoratar da ni kawai matar Saifullahi take yi don ta ɗaga min hankali.

Umma tace "Zainu yaya an ɗaura?"

"Umma kwantar da hankalin ki yau an ɗaura auren Hajiya Nadiya Nazeef."

A fili suka amsa a tare "Alhamdulillahi."

Zainu ya kaɗa kai ya fita. Jameel kuwa ya zo gabana ya tsugunna yace "Yaya Nadiya ina tayaki murna ango dai Ma sha Alllah!"

Nayi murmushi kawai na ce masa "Ba ka da kunya ko?"

"Aa dole ne na taya ki muranar samun wannan santalelen son kowa."

Na harare shi ya fita.

Muka ci gaba da sabgarmu.

Can na buɗe datar wayata na shiga group ɗnmu nan Summaya ta sanar da an ɗaura aurena yau ana ta taya ni murna da farinciki. 

Nima na je status ɗina na rubuta "Alhamdulillahi".


Amma na yi mamakin da Saifullahi bai shigo ba kuma bai kira ni ba.

Can saƙonsa ya shigo mini.

"Assalamu alaikum Nadeeya. Ina taya ki murna Allah Ya sanya alkairi ,Ya kaɗe fitina amin." 

Murmushi na yi kawai.

Baba ne da yayyauna suka shigo dasu Zainu da wani bawan Allah farin bafulatani wanda ban taɓa gani ba harda Alhaji Abba. 

Su Umma suka basu wuri suka koma ɗaya ɓarin suka zauna suka basu wannan wurin.

Ni da Summaya muka tashi zamu shiga ciki. Alhaji Baba ya  ce "Dawo ki zauna Nadiya ai zaman na ki ne."

Na ce "To Alhaji Baba."

Summaya tace "Ina sama."

Ita ma yace ta dawo ta zauna ai ni da ita duk ɗaya muke.

Ta zauna a gefena.

Yaya Muhammadu ya miko min kuɗi ya ajiye a gabana yace "Ga sadakinki dubu ɗari ne." 

Ban ce komai ba sai Summaya ce tace "Ma sha Allah! Allah Ya bada zaman lafiya."

Kowa ya amsa da amin.

Alhaji Abba ya ci gaba yace "Nadiya ki godewa Allah!. Ki kuma godewa wannan bawan Allahn da ya aminta ya yarda aka ɗaura auren ɗan sa da  ke bayan janyewa da Saifullahi ya yi a yau daga auren ki mahaifiyarsa ta hana shi ta ce sai ta tsine masa in aka ɗaura auren ki da shi."

Cike da tashin hankali na ɗaga kaina ina kallon Alhaji. "To wa aka ɗaura min? Waye mijina?" 

"Wannan bawan Allah ya baki ɗansa...."

Ban san yadda aka yi nace "Waye na aura Alhaji?"

Kwantar da hankalinki. Yaron kirki ne hankalina ya kwanta da shi da nagartarsa da nutsuwarsa. Shi Allah Ya zaɓa miki a matsayin miji."

"Abba waye?"

"Yanzu zai shigo ma ai. Kai jameel ku ce ya shigo mana yana ta tsaye a waje."

Idanuwana tar a kan ƙofa don na yi tozali da fuskar mutumin da aka ce an ɗaura min aure da shi a madadin Saifullahi. Wallahi da zaku sa hannu a kan kirjina da zaku ji irin bugun da yake yi. Tashi nayi zunɓur nace ......


Ina masoyana? A nan zan dakata da free pages. Domin samun ci gaban labarin ki biya #500 ta wannan account  ɗin.

9126022777
Opay
Sani ummulkhair panisau.

Ki turo shaidar biya ta wannan lambar.

***.

Sai a saka ki a cikin paid group a telegram.

Sai kun biyo ni don mu ga waye mijin Nadiya Nazeef?