馃尲馃尲ZUBAR HAWAYE NA馃尲馃尲

page 16

by @gimbiyaayshu

馃尲馃尲 ZUBAR HAWAYE NA馃尲馃尲

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒

ELEGANT ONLINE WRITER'S 馃摎

               PAID BOOK

NORMAL GROUP 200

VIP 400

COMPLETE DOCUMENT 500 A GARAPASA.

ACCOUNT NAME: AISHA MAARUF

BANK NAME:UBA

ACCOUNT NUMBER:2245462427

NUMBER OF EVIDENCE VIA WHATAPP:***

NAGAMA FREE PAGES DINA ALHMD SAURA NAGAMA LITTAFIN ALLAH YA BANI IKON GAMAWA LAFIYA.AMEEEN.

WHATPAD NAME:AISHA MAARUF

AREWABOOKS:2503

FACEBOOK:AYEESHA ASHRAF MUHAMMAD.

INA GODIYA GA MASOYANA WA'INDA NASANI DA WANDA BANSANI BA,INA GODIYA,ALLAH YA BAR KAUNA.

PAGE 20/21

________________________________Alhmd su Nasreen sun kammala exam din su lafiya inda aka basu hutu,A hutun nan Mummy ta dauke ta suka bar kasar zuwa garin Dubai saboda wani business din ta,inna ce muku Arif yaji dadin tafiyan nan nayi karya,dan"tun kafin su tafi yayi ma Mummy magiyan ta barta ko kuma a je da shi sai ya dinga mata aike tare da wasu abubuwan",Amman mummy kememe Taki tace bawani Aiken da zatayi, yayi zaman shi da baban shi,in ta kwashe su duka baban kuma fah,wa zai zauna da shi,yayi rokon yayi magiyan Amman duk busuyi aiki ba,Da Mummy tagaji da Abin da yake tace wai mai haka ne Arif yaushe muka fara hakan da kai inajin dai ba yau nafara tafiyan ba,ka taba cewa zaka bini y This time,"shiru Arif yayi Dan his totally speechless and hope less,tun da su Nasreen suka tafi Arif ya Zama kaman wani mara lafiya,kullum sai ya kira Mummy sunyi waya bayan sun gama gaisawa sai yace aba Angel,ba musu Mummy ke bata waya suyi fin awa suna waya ko mai suke cewa oho! Mummy ko ita abin har mamaki yake bata,in ita kadai ce a daki sai ya maida akalan wayan zuwa video call yayi ta kallan ta, inta ce maiyasa yake kallan ta, sai yace yayi missing din kanwan shi ne kawai,in yace haka shikenan sai dai tayi ta washe hakora tana mishi shiriritar ta.

Satin su Nasreen biyu suka dawo Nigeria,wannan satin biyun da sukayi Arif ya dinga ji kaman shekara sukayi,Arif ne yaje tarban su a Airport,mintin shi 15 da tsayuwa jirgin su Mummy sukayi landing,Nasreen da Mummy ne kesaukowa daga matattakalan,Hango Arif tayi da tsauri ta saki hannun Mummy ta ruga da gudu ta nufi wurin shi,tana isa batayi wata wata ba ta rungume shi,shima hannun shi yasa ya matse ta a jikin shi yana sauke ajiyar zuciya sai kace wanda yayi gudun kilometer ashirin '20',rada mata i miss u yayi a kunne,dagowa tayi tace i miss u too my lovely yaya, murmushi yayi sossai har sai da hakoran shi suka bayyana,cire ta daga jikin shi yayi sakamakon irin kallan da Mummy ke aika mai da shi,karasowa wurin su tayi tana auna ma Arif harara,gaishe da Mummy Arif yayi,amsawa Mummy tayi a dakile,wurin mota suka nufa suka shiga suka nufi gida.

Ko da suka isa gida sun iske daddy na gida,tarban Mummy da daughter shi yayi,bayan sunyi refreshing suka sauko suka ci abinci,bayan sun gama suka yada zango a parlor aka bude babin hira,tunda aka fara hiran Arif ko uffan bai ce ba,jingina yayi da kujera yana ta kallan su,daddy ne yace son was wrong with you,are u okh son,amsawa Arif yayi da Yes daddy, Mummy ko kallan shi tayi ko kala bata ce ba,da misalin karfe 10 duk suka watse.

***********************************

A bangaren Anty lauratu yanzu watan ta biyu da Aure,tasaki jikin ta sossai a gidan mijin ta,sai dai har gobe Nasreen na zuciyar ta,wani lokacin inta tuna ta sai taci kuka,kuma tayi mata Addu'a.

Anty lauratu ne ta tashi ta nufi bayi da gudu sai yunkurin Amai take Amman ta kasa,wanke bakin ta tayi ta dawo parlor,Bata kaiga Zama ba wani yunkurin aman ya taso mata,haka ta nufi bayi da gudu dan ji take kaman zai zubo,a ranar wuni tayi a kwance komi ta kasa yi,gashi mijin ta bayanan tunda ya fita bai dawo ba,kuma wayan ta na daki ta kasa zuwa dakin. Kwance take wuraren karfe 6,tayi dai-dai a kasa sai nunfashi take da kyar,Ahmad ne wato mijin Anty lauratu ne ya shigo parlor su inda ya hango matarshi kwance a kasa,da tsauri ya karasa inda take yana tanbayan ta lafiya amma ta kasa amsa mishi dan ta galabaita ba kadan ba,mikewa yayi ya nufi daki da sauri ya dau mata hijabi,sunkutan ta yayi ya nufi wajen gidan da ita,bai zarce ko Ina ba sai wani Asibiti,amsam ta akayi da gaggawa aka fara bata taimakon gaggawa,bayan ta sha Allurori aka daura mata ruwa,tuni barci wahala yayi awon gaba da ita,diban jinin ta akayi aka nufi lab da shi bayan anyi test aka kawo ma Ahmad result,budewa yayi yana dubawa,baisan sanda ya mike tsaye ba bakin shi ya kasa ruhuwa,hannu ya daga yana gode ma Allah da ni'iman daya mai,"Ba komi ke kunshe a takardar nan ba face test din da aka ma Lauratu,kuma angano cewa tana dauke da ciki kimanin wata daya da sati biyu wanda shine ya haddasa mata wannan aman da rashin kwarin jiki datake fama da shi.

Kwanan su biyu a Asibiti aka sallame su,inda doctor ya bashi shawara yanda zai kula da matar shi da kuma abinda ke cikin ta,bayan an sallame su bai zarce ko ina ba sai gida,ruwa ya daura a gas,bayan ruwan yayi zafi ya ha蓷a ya kai bayi,towel ya dauka ya Bama Lauratu bayan ta tube ta daura,taimaka mata yayi har bayi,bayan sun shiga ya kulle kofa,kokarin kunce towel dinta yake, kallan shi tayi da sanyyin jiki tace ka bar shi zan iya,girgiza mata kai yayi alamun "sam bazai sabuba bindiga a ruwa"kunce towel din yayi sannan yayi mata wanka tare da gasa mata jiki sossai,bayan ya gama ya daurota a towel ya kaita daki shirya ta yayi cikin kayan barci mai kauri da yake dare ne,hijabi ya bata ya shinfida mata darduma,bayan ta idar da sallah ya kawo mata abinda ya siyo,yayi feeding din ta,sai wani tattalin ta yake kaman kwan da baisan ta fashe.

A bangaren su A'isha kuwa soyayya suke sha ba kama hannun yaro,satin su biyu da Aure,kuma har yanzu Mustapha bai koma bakin aiki ba wai shi yana honey moon.

************************************

A cikin garin Kaduna ko Nasreen ce ke shirin makaranta dan yau zasu yi resume, inda zasu Fara jss3,bayan ta gama shiri ta fita sakar gaidan wurin driver,da yake shike kaita makaranta,Arif ne ya fito daga dakin shi sanye da coat kalan sky blue yayi kyau sossai,gashin shi sai kyalli ake kai da gani kasan gashin nan yaci kudi,hango driver yayi ya zai shiga motan,kwala mishi kira yayi,da sauri driver ya amsa ya bari wurin motan ya nufi inda Arif yake da tsauri, tanbayan shi Arif yayi inda za shi,Amsa mishi yayi da girmamawa akan zai kai Nasreen makaranta ne,umurni Arif ya bashi akan yaje ya huta shi zai kai ta tunda fita zaiyi,da toh Alhaji Driver ya amsa sannan ya wuce,parking space Arif ya nufa inda yaje har inda Nasreen take ya ja hannun ta zuwa inda motan da zai fita da shi yake, bude mata front seat yayi ta shiga ya kulle kofan,zagayawa yayi zuwa Driver seat ya shiga ya kulle motan,kunna motan yayi yana warming,sunyi minti uku a wuri daya,ita ko Nasreen tuni ta fara kumbura,Horn yayi tun kafin ya karaso gate din,yana zuwa fita kawai yayi abin shi,school ya kai ta,parking yayi a wajen makarantar inda Arif ya Fara Mata wa'azin Banda kula samari,tana fadin haka bata jira ya kulle baki ba tace wai mai yasa kake fadin haka ne yaya Arif,Ni baka san inyi Aure ne,bude baki Arif yayi yana mamakin ta, murmushi kawai yayi ya dauke kai,kallan ta yayi yace zaki Aure Ni,"jin maganan Nasreen yayi wani iri,dagowa tayi a kaikaice ta kalle shi tace mehhhhhhhhhh!,Haba yaya ina ka taba ganin yaya ya Auri kanwa i ba'a haka,gani tayi lokaci ya tafi dan taga discipline master ya fito,yarfa hannu ta farayi tace wayyooo! Yaya kasa nayi latti, yau zanci duka,tuni ta fara hawaye", murmushi Arif yayi a zuciyar shi yace sai shegen tsoro ga surutu,fita yayi daga motan yace ta fito,rike hannun ta yayi har ya shiga da ita gate din makaranta,gani nayi yana magana da discipline master, ko mai yace mai oho,bude mata gate discipline master yayi,juyowa tayi da alamun mamaki a fuskan ta ta shige ciki,daga mata hannu Arif yayi alamun bye bye, murmushi ta danyi sannan ta wuce," barin haraban makarantan Arif yayi, bai zarce ko Ina ba sai gun Aiki,da misalin karfe 3 Arif yazo ya dauke Nasreen daga makaranta,tana shiga cikin motan abin da ta fara tabbaya shi ne "yaya mai kace ma discipline master da safe,ta fada tana kura mai ido","dariya Arif  yayi a zuciyar shi yace dama nasan sai ta tanbaya",turbune fuska Nasreen tayi ta nade hannun ta a kirjin ta tana kallan shi,"barin dariyan da yake yayi yace mai yasa kike san sani", turo baki tayi tace haka nan,"girgiza kai Arif yayi yace 'cewa nayi na kaiki Asibiti baki da lafiya", kwalalo ido Nasreen tayi tana kallan Arif da mamaki,daga mata gira Arif yayi tare da kashe mata ido daya,kunna motan yayi suka bar haraban makarantar,basu suka isa gida ba sai karfe uku da minti sha tara'3:19'.

Da misalin karfe uku da minti Arba'in da biyar Nasreen ta fito daga dakin ta a shirye,samun Mummy da Arif tayi zaune a parlor,Zama tayi kusa da Mummy ta kwantar da kanta a kafadan ta tace Mummy zan wuce islamiyya,da toh Mummy ta amsa sannan ta mika mata goran coke din dake saman centre table,amsa Nasreen tayi tace Nagode Mummy na,ta fada tare da daura ma Mummy peck a kumatu, murmushi Arif yayi yace Acici ba,daure fuska Nasreen tayi ta fara kumbura,dariya Mummy tayi tace bazaku kashe Ni ba,Mummy Kinga Yaya kohhh!,ta fada hawaye na fita daga idan ta"A duniya Nasreen ta tsani ace mata Acici, kuma tsap Arif ya sani,Amman yake Fadi in yanasan naiman rigima,Amman na yau ya taba shi 蓷an baiyi tsanmanin zata yi kuka ba"Kallan ta Mummy tayi ta kalli Arif ta Kuma kallan su duka, Nasreen ta jawo ta kwantar da ita kan cinyar ta ta fara bata hakuri,"Arif naganin haka ya ri茩e kai dan yasan sai ya sha fada",iko bai gama tunanin zuci ba yaji Mummy tace kaga kasa min yarinya kuka kohhh! Toh daga yau karka kara in ba haka baaaaaa! Ta fada tana nuna mai yatsa alamun zai sani,ajiyan zuciya Arif ya saki a buye,Dan yayi tunanin fadan zafi haka,kallan agogon hannun shi yayi yace Mummy lokaci na tafiya bari mu wuce",da toh Mummy ta amsa sannan ta mikar da Nasreen ta raka su har suka shiga mota,ta bangaren Nasreen ta tsaya tace idan yayanki yayi miki wani abu a hanyyan ku na tafiya ki gaya min kinji,ta fada tana kallan Arif,dagowa yayi suka hada ido da Mummy,saurin dauke kan shi yayi dariya nasan subuce mishi,fita sukayi da ga gidan,ba Mummy ta bar haraban gidan ba har sai da taga fitar motan su daga gidan,A hanyyan su na tafiya Arif ya saya yayi Sallah,bayan ya dawo daga sallah yace mata in mun kai karki mata kiyi sallah kinji Angel,daga mishi kai tayi alaman taji,Daz my girl cewar Arif,bayan sun kai islamiyya zata sauka Arif yasa hannu ya ri茩e hannun ta,juyowa tayi ta kalle shi ta turo baki da shagwaba tsansa," I LUV U ANGEL" Kwalalo Ido Nasreen tayi taji kaman jiri ya dan 蓷ebe ta,zama kawai tayi a kan kujerar motan ta dafa kanta,riko ta Arif yayi yace Angel Mai ya faru,kanki na ciwo ne,daga mishi kai tayi alamun ehhh!,muje gida toh!girgiza mishi kai tayi da sauri tace zata iya zama,sake ta yayi ya zagaya ta inda take,jakan ta ya ri茩e sannan ya riko hannun ta har ajin su,kafin su rabu yace Angel karki manta kiyi sallah,da toh Yaya Arif ta amsa mai.

Biyar da minti hamsin dai-dai tayi ma Arif a makarantar su Angel din shi,bayan an tashi direct parking space ta nufa,bude motan tayi ta shiga,gaishe shi tayi da fara'a,Arif ne yace wannan murmushin haka sai kace an miki Albishir da gidan Aljannanh,dariya Nasreen tayi ta fara ba shi labari shiko yana sauraran ta,na dariya yayi dariya na comment kuma yayi,haka suka dinga yi har suka isa gida.........................................

COMMENT AND SHARE

BY GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒.