🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
page 5
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
USERNAME NAMES
whattpad:Aishamaaruf1
Arewabooks:gimbiyaayshu2503
Facebook:Nawwal Binty Jahash
Wannan page din kyauta ne ga
Maryudah
Maryam
Surayyat Gambo
Ummu Anwar
Real miiirah
BOOK 1:CHAPTER 9&10
__________________________Bayan ta shiga motar Mami ta rankafo tace"yauwa kayan nan dake back seat naku ne,kin dai san yanda aka raba shi",na Mama naki dana Asiya,ke zaki dauki hudu tunda goma ne a wurin,yauwa Allah ya kiyaye,ta fada tanayin baya.
"Kasa ko da furta kalma daya tayi har driver yaja motar".
Suna tafiya suna hira amman da kaga fuskan Hauwa kasan tana cikin damuwa.
"Ba komai ke daga mata hanklali ba face kayan da Mami ta bata,batasan yanda zata yiwa Mama bayani ba".
Har kofar gida ya ajiyeta ya tayata ciro kayan daga bayan mota.
"Zaki iya dauka kuwa!?,dan naga dazu da kyar kika dauko shi".
Murmushi tayi har dimples dinta ya loba tace"zan iya fahh! yaya,karka damu nagode".
"Daukan kayan tayi ta nufi kofar gidan su zuciyar ta na bugun tara-tara,batasan Mama ta mata fada ko kadan".
"Tura kofar gidan su tayi bakin ta dauke da sallama".
"Zaune Mama take a tsakar gida kan kujeran tsugunno Asiya kuma na kan tabarma Mama na mata kitso suna hira,jin sallamar Hauwa yasa duk suka dago kansu".
"Tsit kake jibabu wacce ta furta komi".
"Jan Laidan Hauwa'u tayi har ta karaso gaban Mama ta duka ta gaishe ta".
Kin amsa gaisuwar Mama tayi tana binta da kallon tuguma.
"Dago kanta tayi da sauri jin Mama bata amsa ba,kallan da Mama ta aiko mata da shi ne yasa cikin ta ya bada wani kara kullllllll!"............cikin i'ina bakin ta na rawa tace"Mama ba abinda kike tunani bane ki fahimce ni wlh ban roke taba Allah Mama",ta karasa maganar ta hawaye na gangarowa daga idanta.
Sakin fuska Mama tayi sabida ta dau haske,ba abin da take tinani bane.
Basu labarin abinda ya faru tayi sannan ta gaya musu yanda akayi kayan ya biyo ta.
"Wlh Mama bani na roke taba,dana san mu take sai mawa da banma zabar mata ba wlh,kiyi hakuri Mamana,bana san kiyi fushi dani,wlh ban roke ta ba,ta karasa maganar ta tana sakin kuka".
Jawo ta Mama tayi ta fara lallashin ta tace"waya ce miki fushi nayi dake,ba fushi nayi ba,bazai yu naga kin shigo min da kaya niki-niki kuma kice bazan tanbayi ba'asi ba,amman kiyi shiru ki share hawayen ki banyi fushi ba",sai dai daga yau karki kara amsar komi kinji.
"Toh Mamana nagode",ta fada tana share hawayen idanta fuskan ta dauke da murmushi.
(Mata a kula dan Allah,da duk kika ga diyar ki ko danki da wani abu wanda ba ke kika siya mai ba ko kuma Baban shi ba,toh ki bincika idan ba kiyi haka ba toh tabbas kin jefa rayuwar danki ko yarki ga halaka,dan Allah ku gyara)
Lallabowa Asiya tayi ta zazzage laidan,i kuwa tana zazzagewa idan ta ya fada kan wani sliver color hills,ihu tayi tace"wow Mama takalmin nan yayi mugun kyau wlh",i da gani wannan nawa ne,ta fada tana kokarin sakawa.
Comb Mama ta dauka ta jefeta da shi tace"wlh ki kiyaye ni Ummi,zanci mutuncin ki,ubanwa yace ki zazzage kayan,na aike ki ne,wai mai yasa ba kida natsuwa ne?,maike damun ki ne?,bana san irin abin da kike fah,ki daina",Allah yasa bake ke aiki a gidan ba,dake ke aiki da wlh na shiga uku,maza kwashi kayan nan kafin na sassaba miki wlh.
Ganin yanda Mama ke ta fada yasa jikin ta yayi mugun sanyi,tsugunnawa tayi ta kwashe kayan tas ta maida su ta ajiye,ta dawo kusa da Mama ta zauna tace"Mama kiyi hakuri kinji bazan sake ba Allah"ta fada idan ta na tara ruwan hawaye.
Murmushi Mama tayi sabida inda sabo ta saba jin bazan karaba a bakin Ummi,"toh shikenan Ummi na karki sake kinji".
Rungume Mama ummi tayi tace"yauwa Mamana shiyasa nake mugun sonki,duk duniya banda wacce ta fiki,kece uwata kece ubana kece yan uwana kece komai namu Mamana",ta fada hawaye na zuba daga idan ta.
Mikawa Hauwa hannu Mama tayi alamum tazo ta hada dukkan su biyun ta rungume tace"ina san ku yarana,ina fatan Allah ya baku miji na gari da zai rike min ku da amana,wanda zai zamto kaman uba a gare ku ba kadai miji ba,ina Alfahari daku yarana.
"A tare suka Amsa da Ameen Ameen Mamar mu abin Alfaharin mu".
Tashi ki shigar da kayan ciki.
Bayan sallan isha'i suka ci abincin da Hauwa tazo da shi.
Suna cikin hira Mama tace ta dauko laidan kayan.
Dire kayan tayi a gaban Mama tace"gashi nan Mama".
Umurnin ciro komai daga cikin laidan Mama ta bata.
Daga kayan Mama ta farayi daya bayan daya,daga Hauwa har Asiya babu wanda yayi gigin taba kayan,sai da Mama ta duba kayan tas sannan tacewa Hauwa tazo ta raba kayan.
Da rarrafe ta karaso wurin kayan,cire jan atanfar nan tayi tasa a gefe,ta dau jallabiyar Mama ta mika mata haka zalika taba Ummi,sai tace"Mama ki fara zabar naki lace daya atanfa daya sai ki raba mana".
Murmushi Mama tayi tace"wanchan kuma da kika ajiye a gefe fahh!?.
"Rufe baki Hauwa tayi tana dariya".
"Girgiza kai Mama tayi ya zabar ma kowa,atanfar daya rage Mama ta mikawa Hauwa".
Toh wannan dai ke zaki raba tunda ke kika zabarwa ko wani kaya,sabida haka zaki fini sani.
"Murmushi Hauwa tayi,nan ta raba jakunkunan da takalman".
Asiya bakin ta har kunne tsabar murna,ana bata jakar ta ta bude su,tana bude na karshan ta zaro ido tace Mamaaaa!?.
Dagowa Mama tayi da sauri sabida jin yanda ta kira ta tace Ummi lafiya?,mai ya faru?,mai ya razana ki haka?.
"Bude baki tayi with shock tana nuna jakar tace...................................
Toh Masu karatu ku biyo ni dan jin mai ya razana Asiya(Ummi).
Daga Alkalamin
Gimbiya Ayshu💞💞💞.