馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰(GIDAN AURENA) BOOK 1.
page 6
馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒
ELEGANT ONLINE WRITER'S馃摎
BOOK 1:CHAPTER 11-12
__________________________"Mamaaaa! ",hannu tasa ta fara cire su ta ajiye a kasa.
Binta da kallo daga Mama har Hauwa suke.
Hauwa na ganin Ummi ta ajiye jakar a gefe ta fashe da kuka tace"wlh Mama ban san da shi ba Allah,ni ban san an saka wani kudi ba wlh Mamaaaa!,ta karasa maganar ta tana jan sunan Mama".
"Tagumi Mama tayi tana kallan kudin,ganin alamun rubutu a paper daya daga cikin kudin yasa Mama fadin miko min kudin nan Ummi".
Daukan kudin Ummi tayi ta karasa gaban Mama ta mika mata.
Juya daya daga cikin kudin tayi dan ta gane mai aka rubuta da kyau,"kudin dinki ne kuyi manage,kuma da Allah kar a mayar".
Sakin baki Mama tayi tana kallan kudin tace"kuyi manage",manage fahhh!kudi har dubu dari uku za'a kira da kudin dinki harda manage.
Ajiyar zuciya Hauwa ta saki na samun relieve,dan a fili Mama ta karanta.
Kuluwa kina ina aka saka wannan kudin.
"Wlh Mama ban masan an saka ba Allah,dana Sani i da zan gaya miki",kawai ki bani kudin na saka a laida in yaso gobe sai na mayar da kudin.
Girgiza kai Mama tayi tace"ba za'a miyar duka ba sabi da hada ni da Allah datayi,amman bazan karbi kudin duka ba,kudin dinki kawai zan cire".
Yanzu ku tattara kayan nan kuje ku tanbayi Auwal nawa zai mana dinkin kayan.
Tsaya kafun kuje Kulu fara dubawa ko shagon shi na bude.
"Toh Mama ta fada tana saka hijabi".
Bayan minti biyar ta dawo tace"Mama yana nan".
Toh ku duki kayan nan duka ku kai ku tanbaye shi nawa zai mana dinki.
Daukan kayan su kayi zuwa shagon shi.
Ina yini Auwal ya aiki,suka hada baki wurin gaida shi.
Auwal nawa za'a mana wannan dinki Ummi ta fada tana ciro kayan daya bayan daya.
Ehhhh! toh ya danganta da yanayin style ne,ba daga dinkin bane daga siyan kayan dinkin ne,kuna da style din da za kuyi ne.
"girgiza kai su kayi a tare".
"Toh na baku waya ta ku zabi style ne?".
Kallan juna Hauwa da Ummi su kayi kafin Ummi tace"ka bamu mu zabi style din".
sun dau tsawon minti sha biyar suna zaban style,har dana Mama suka zaba amman zani za'a yi mata.
Bayan yaga styles din da suka zaba yayi lissafin komi sannan yace"kudin dinkin ku ya kama dubu talatin da daya".
Zaro ido Ummi tayi tace"kasan waje zaka kaimu ehhh! haba Auwalu kaji tsoron Allah kudin nan yayi yawa ka".......
Riko hannun ta da Hauwa tayi ne ya sata yin shiru,murmushi Hauwa tayi tace"mun gode bari muje mu gayawa Maman mu".
Toh shikenan sai kun dawo.
Suna fita daga shagon Ummi ta fara masifa,dama bata daukan last a wannan fannin.
"Shiru Hauwa tayi tana jinta,dan tasan inta kuskura tayi magana sai ta mangare ta,barin ma ita ta hana ta yin masifan a lokacin da yafi cin ta".
Har suka shiga gida bata bar masifa ba.
Suna shiga parlor Hauwa ta gayawa Mama amount din da Auwal ya fada.
Daukan rafa daya Mama tayi ta fara girga kudin ba tare da tayi magana ba.
Sakin baki Asiya data tokare a bakin kofa tayi tace"Mama wai kudin zaki bayar,ba kiji kudin yayi yawa ba".
kirga kudin tayi chas taba Hauwa sannan tace"in zaki rakata ku kai toh!,in kuma baki iyawa sai ki dawo ki zauna".
Turo baki tayi ta juya zata fita.
Wlh karki kuskura ki furta komi in ba haka ba ranki zai yi mugun baci da daddaran nan.
Haka suka kai kudin suka dawo ba tare da Ummi ta furta komi ba.
Bayan sun dawo Mama ta nada sauran kudin a laida ta ajiye tace"gobe in Allah ya kaimu zaki miyar da sauran kudin,dama kudin dinki aka ce kuma na cire ba tare da ragin ko naira akan wanda tailan ya fada ba,sabida haka miko min jakar da zaki fita da ita gobe na adana shi a ciki.
Dauko jakan tayi taba Mama ta ajiye kudin tace"gobe zan baki in zaki tafi,dan Allah ki kula da kudin nan,ki rungumi jakar nan da kyau kin san ba namu bane,dan in tsautsayi ya fada kansu banda hanyar da zan same su.
Washe gari tun karfe shida ta gama shiri,Mama ta bata jakar tace ta saka a cikin hijabi sannan ta matse jakar da kyau.
Har Hauwa ta fita Mama ta kwala mata kira,hijabi Mama tasa ta rakata har sai da ta hau abun hawa.
Ko data isa gidan shida da minti ashirin,tasan Mami bata tashi ba,ba tayi gigin ajiye jakar ba,da jakar tayi duk wani aikin da tayi.
"Wannan tsaron duk dan kar kudin ya bata ne".
Bayan ta gama ta kaiwa su Baba da sauran masu aikin gidan abincin su,parlor ta dawo ta zauna tana kallon Tv.
Takwas da kwata Mami ta sauko cikin shigar ta na alfarma.
Da sauri Hauwa ta gyara zaman jakar a jikin ta sakamakon alamun tafiyar da taji.
"Ina kwana Mami"
Amsa gaisuwar ta Mami tayi tana zama kan kujera tace"ykk daughter ya kika baro su Mama da Baba da Asiya".
Murmushi Hauwa tayi tace"lafiyan su lau amman Babana ya rasu",ta karasa maganar ta muryar ta na cracking.
Allah sarki Allah ya jikan shi ya mai rahma yasa ta huta.
"Da Ameen Ameen Hauwa ta amsa tana share hawayen idan ta".
Taso ki zo,yi shiru bar kukan kinji Allah ya jikan shi,Addu'a za kiyi mai ba kuka ba kinji Hauwa kulu ta,yarinyar Mama da Mami kuma kanwar Asiya.
Murmushi Hauwa tayi har sai da dimples dinta ya loba tace"Mami muje kiyi break".
Mikewa Mami tayi tace"ke kinyi ne".
"Girgiza kai tayi alamun bata yi ba".
Kin kaiwa su Baba nasu?
"Ehh! Mami na bawa kowa".
"Toh shikenan zo muci namu".
A tare suka ci abincin,Mami dake ta lura da Hauwa ne tace"wai jakar nan bai ajiyuwa ne,naga sai lilo kike da shi tun dazu".
Murmushi Hauwa tayi ta bude jakar ta ciro kudin dake ciki ta ajiye a gaban Mami tace"Mama tace na mayar da sauran kudin wai sunyi yawa,tace ta cire dai-dai iya na dinki kamar yanda kika roka akan kar a mayar da shi".
Shiru Mami tayi tana kallan ta a ranta tace"this is a good family i will like to have daughter in law from,amman kashhhhh! is too late,amman bana cire rai da ikon Allah ba",ta karashe maganar ta tana murmushi.
Murmushi Mami tayi tace"Hauwa kenan,ki dauki kudadan nan ki maida su cikin jaka bazan amsa ba,nasan kudin sunyi yawa ma dinki,amman ku ajiye sauran kuyi anfani da shi,bana san jin ko da kalma daya ne daga bakin ki game da kudin nan,in kuma ban isa dake bane toh sai na sani".
"Jin abin da tace yasa Hauwa daukan kudin ta saka a jaka".
Da misalin karfe shida ta bar gidan Mami.
Tsaye take a bakin titi ta kai tsawon Minti goma tana jiran abun hawa,duk wanda ya wuce a cike yake,da kyar ta sami wanda mutun daya ne a ciki.
Tun data shiga napep din take tajan tsaki ita kadai har aka kai ta kofar gida ta sauka,bude jaka tayi ta dauko kudi ta mikawa mai napep sai taji guy din daya addabe ta da kallo a napep yace ki barshi Malama zan biya.
Shiru Hauwa tayi tana kallan shi kafin ta budi baki tace"nagode,Allah saka da Alkairi",ta juya ta nufi kofar gidan su.
Binta da kallo yayi har ta shiga gida.
Wani kayatatchan murmushi ya saki.
(Niko nace Allah kadai yasan fassarar Murmushin nan).............
Ko data shiga gida bata iske kowa a tsakar gida ba,kwance ta sami Mama a daki hannun ta rike da charbi.
Bayan ta gaishe da Mama tayi shiru tana tunanin yanda za tayi mata bayani.
Shahada tayi tace"Mamaaa!"
Dagowa Mama tayi ta kalle ta sabida jin yanda ta kira sunan ta.
"Mama taki ta amshi kudin",nan ta gaya mata yanda su kayi da Mami.
Shiru Mama tayi,bayan kaman minti biyu ta mikawa Hauwa hannu.
"ciro kudin tayi ta mikawa Mama da sauri"
Amsan kudin Mama tayi tace"jeki".
Tashi Hauwa tayi,har takai bakin kofa taji Mama tace"daga yau karki kara amsan komi,ina fatan dai kinji ni".
"Daga mata kai tayi alamun taji jikin ta a sanyaye".
*****BAYAN SATI BIYU*****
Daga Alkalamin
Gimbiya Ayshu馃挒馃挒馃挒.