ALWASHI 2

5

by @rufaidaumar

ALWASHI

30

©Rufaida Umar

MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE

Yar uwa muna saida kowanne irin supplement na gyaran jiki wanda zaisaki fito fes kamar sabuwar Amarya, yar uwa shin kurajene suka dameki, ko matsalolin jikine kamarsu rama, ko kibace tayi miki yawa kikeso ki rage, bushewar fata ko karancin ni'ima ko budewa ne ko infection? Ko kuma so kikeyi fatarki tayi laushi ki dinga sheki kina haskawa wato kalar madara dai Haj to ki garzago

Yan uwa kusani duk wani supplement da zamu kawo muku sai munyi bincike mun tabbatar da ingancinshi, mun kuma tabbatar da cewa bashi da wata illa ga lfy

Akwai masu cewa sunsha supplement amma har yanzu basuga wani canji ba, to yar uwa kodai an baki fake ko kuma ba'a baki wanda ya dace dakeba, kokuma bakisha yadda ya dace ba, kisani yar uwa kafin ki fara shan supplement akwai ka'idoji daya kamata ace kin kiyaye kuma kin kula dasu matukar kinaso suyi miki aiki yadda ya kamata kuma cikin sauki ***

1. Akwai Supplements na gyaran jiki ciki da waje, munada set na uwargida dana Amare da masu jego

Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc

Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners da air wick, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number ***

***

Haka kawai ta ji a ranta za ta iya yarda da Zakiyya saboda koda ta gan ta sai ta ga kamar Sameerarta ta gani, wannan dalilin ne ya sa ba ta ji ko ɗarr ba har ta kai aya. Zakiyya wacce hawayenta sun ƙi tsayawa kamar yadda itama Lailar ke sharar nata, kunnuwa kawai ta buɗe tana sauraron dukkan abin da Laila ke faɗi tiryan-tiryan tana kuma jin wata ƙauna ta fisabilillah na Laila na ratsa ta.

'Ki bar ganin Laila tana maki haka, wallahi ba wai rashin ƙauna ba ce. Tsabar kulawa da tsaron da take son bai wa rayuwata ne ya sanya sam ba ta son na dinga shige-shigen gidajen jama'a don yi musu kitso. Ita fa koyaushe gani take kamar wai wataran za'a iya wulaƙanta ni ko a nuna min wata gadarar wanda ta san zuciyarta ba za ta ɗauka ba. Faɗi take za ta iya takawa har gidan mai shi ta ci musu mutunci. Amma wallahi ba ta da matsala da ke, ƙila don kawai ba ta sona da zuwa gidajen jama'a ne. Ke ko hirarki ba ta damu da yi min ba ballantana ta kawo min kushe a kanki.'

Ta tuno da zancen Sameera a watarana da take yi mata ƙorafin cewa Laila ta tsane ta ba ta ƙaunar ganinsu tare dalili kenan da itama ba ta taɓa bayar da ƙafarta da sunan ta yi mata ƙunshi ba.

"Ba zan ɓoye maki ba Laila, wallahi ban taɓa ji za ki yi abin da zai burgeni ba kamar wannan. Shakka babu na yarda da abin da Sameera ke faɗa a kanki, a baya gani nake kawai mu kika tsana. Ashe irin abin da kike gudu kenan. Da ace wulaƙanci na fatar baki aka yi wa Sameera da abin ya zo mana da sauƙi, amma keta haddi da ya yi sanadin mutuwarta a wurin haihuwa? Innalillahi..."

Ta ƙarashe cikin muryar kuka, Laila ta ɗan janyo kwalin tissue dake saman teburin falon ta zara ta miƙa mata, ita ma zarar ta yi gami da share majinar da ta ji ya cika mata hanci.

"Na shirya, Sameera ta cancanci komai a wurina, ina ji tamkar da sa hannuna a afkuwar abinda ya faru. Ina cike da nadamar rashin yi mata rakiya gidan kamar yadda ta buƙata tun farko. Ba na mantawa ta sha cemin ta fi kaunar zuwanmu tare duk sadda za ta shiga yi musu kitso, amma ni kuma na nuna ba zan iya ba. Na kafa mata hujja da makaranta a dole ta rabu da ni, kin fi ni sanin ba ta son takurawa rayuwar kowa. Wallahi Laila yadda nake jina a yanzu, da ace ina da ƙarfin iko sai na yi shari'a da Haj Salma da ɗan nata. Da kuma uban nasa Alh Sada. Ina goyon bayanki Laila, kar mu bari su ci banza, mu nuna musu Sameera ma ƴa ce ta halak da take da gata. Sai dai Laila za ki iya zama inuwa ɗaya da mutumin da ya yi sanadiyyar mutuwar Sameera? Za ki iya rayuwa kina ganinsa ku yi zama a rumfa ɗaya? Ba ma wannan ba, batu ake na aure. Magana ta aure dole akwai buƙatuwar magabata a ciki, me zamu ce da Mama? Me kike ganin zai faru idan ta ji wai za ki auri Areef? Sai dai kuma da gaskiyar Hajja Zayha din, auren ne kaɗai hanyar da zai zamo daidai ki rama abin da aka yi mana. Idan kina gidan tare da su, za ki rusa farin cikin yaron da ma iyayen nasa tunda tun farko sun nuna ƙiyayyar Sameera suka kuma goyi bayan ɗansu. To amma naki farin cikin fa Laila? Shikenan? Ba ki da wanda kike so?"

Laila ta yi ƴar dariyar takaici tana duban Zakiyya.

"Dalilin kenan da har yau ban bada ƙofar da wani zai samu matsuguni a zuciyata ba Zakiyya, ba na sauraron kowa da sunan wai masoyi. Auren ma ki sani, wallahi a yanzu dai ba wai shi na sanya a gaba ba, ina da burin karatu mai zurfi, sai dai i can do anything for Sameera, koda ace sai na auri Areef ne. Na shiryawa hakan. Abin da na yanke koda auren zai tabbata, zai kasance aure na sirri ne."

Cikin rashin fahimta Zakiyya ta girgiza kai,

"Ban fahimce ki ba."

Ɗan murmushi Laila ta yi

"Zan yi maki bayanin komai bayan na ji plan din ita Hajja ɗin."

"Shikenan, amma kar ki zurma da yawa. Su kansu ba abin yarda ba ne." Faɗin Zakiyya.

Laila ta ɗan ɗaga kafaɗarta.

"Ba ni da matsala da su, na sani they are against Areef and his Mami su ma, wannan bai zama matsalata ba idan har ni dai zan ɗauki fansa. Zakiyya ki sani, ba ruwana da ko me suke nufi, koda ace dukkan abin da Haj Zayha ta faɗa min ƙarya ne, na san me nake yi. Idan har abin da zasu aikata din ba kisa ba ne, kuma yana nufin jefa Alh Sada da Salma da shi kansa ɗan nasu cikin baƙin ciki, to na shirya haɗa ƙarfi da ƙarfe da su. Kisa ne kawai ba zan iya aikatawa ba."

Jinjina kai Zakiyya ta yi tana ɗauke hawayenta.

"Ina bayanki dai ki sani a kowane mataki ma. Kinga yanzu ma bikina za'a yi bayan sallah in sha Allahu. Yanzu haka siyayyar kayayyakin kicin ne ya kawo ni Kano, gidan yar uwar Babanmu nake zaune. Gobe zan koma Katsina don ba a nan zan yi sallah ba, wata na biyu a garin nan. A nan Katsina zan zauna."

Da murmushi Laila ta dube ta.

"Kai masha Allah, Allah ya sanya alheri ya nuna mana. Ba don Mama ba ai da na zo bikin, amma ana tare."

Murmushi itama Zakiyya ta yi. Kafin ta lalubi abin cewa suka ji sallamar abokiyar tafiyar Zakiyya. Koda suka amsa ta dube ta.

"Umma fa ta kira ni tace dare ya yi ba mu koma ba."

Nan da nan Zakiyya ta dubi wayarta, aikuwa har tara ta buga don ma dai watan ramadan ne kusan ba'a dare. Balle yanzu da kasuwannin Kano ba a fiye wani rufe su da wuri ba idan sallah ta gabato sosai.

"Ya Salam, wallahi ban kula ba. Mu je. Shikenan sai mun yi waya ko?"

Laila ta jinjina kai gami da murmusawa.

"Allah ya nufa. Muje na raka ku."

Ta ɗauki hijabinta dake ajiye hannun kujera ta zura. Ta ji sadda yarinyar ke tambayar Zakiyya ina Sameera din? Zakiyya ta kasa cewa ta rasu, ƙarshe ma ta ce ai tana Maiduguri da Mamarta. Hakan da ta faɗi ya sanya Laila sakin ajiyar zuciya, za ta fi ƙaunar haka. Nan ma dai har sauyin da fuskar Zakiyya ya yi tambaya, ta nuna babu komai kawai sun tuna baya ne.

Laila sai da ta taka musu har titi dayake akwai mutane a layin sosai ga kuma hasken fitilu kamar rana sannan ta juya ta koma gida. Ta dai gama yankewa ranta za ta auri Areef, ba kuma domin soyayya ba, sai don kawai ta cika alwashin da ta ɗauka a kansu.

***

Azumi ya kama mai talatin hakan ya sanya su Momi Fannah za su dawo kafin bikin sallah, a Kano za su yi sallarsu. Inda Mama da Haj Ruƙayya matar Daddy Barista da shi kansa Barista din zasu wuce Egypt don a duba Mama. Sauran yan uwa kusan duk a ranar suka taso.

Tuni Laila ta yi wa Ilham ƙunshi, ta kuma rufe ƙunshi ga kowa don itama ta yiwa kanta. Tana kallo Haseenah ba ta samu gidan ƙunshi ba, ta ji tana ta faman waya da tambayar masu lalle amma ba ta samu ba, ta sani ko me za'a yi Haseenah ta gwammace ta ci sallar a haka akan dai ta yi mata ƙunshi don haka itama ba ta ce mata uffan ba. Abu ɗaya ta saka a rai, akwai mutanen da ko me za ka yi ba za ka burge su ba, hakanan ba ka yi musu laifi ba amma ba sa ƙaunarka. To haka take kallon lamarinta da Haseenah ɗin, ba ta ƙaunarta tun farkon gani, kuma ba ta jin a gaba za ta yi wani mutunci a idanun Haseenar. Wannan dalili yasa ta janye ita ma. Kitso kuwa Haseena sun je da Ilham, ita kuwa Laila ganin babu lokaci ma ta haƙura da zummar ko washegarin sallah sai ta je ta yi.

Girki lafiyayye ta shirya na tarbar Momi Fannah da su Daddy Mu'az wadanda sai tara na dare za su iso Kano.

Ta kammala ta jera komai a saman tebur ta bar Asabe mai aiki da gyaran kicin din. Yara sai murna suke yi zasu je tarbo Momi da Daddynsu. Haseenah da kanta ta ƙara gyara ɓangaren mahaifin nasu da kuma shimfiɗa zanin gado a ɗakin Momi Fannah, ko'ina a gyare yake tas tunda Laila ba ta jima da ƙara gyarawa ba. Haka nan ɗakin Gwaggo Samha ma babu gyara ko kaɗan.

Sai bayan an idar da sallar asham suka fice da motocin gidan har biyu tarbar iyayen.

Suna isa ba jimawa jirginsu ya sauka, ba a fi mintuna goma ba suka fito, nan da nan yaran suka nufe su a guje har suna shirin kayar da Gwaggo Samha. Laila da Haseena su kansu baki ya ƙi rufuwa, haka kowacce ta rungume su ɗaya bayan ɗaya.

"Wai anya kun yi azumin nan kuwa? Na ga duk kun yi ɓulɓul da ku, ramar kawai a wuyanku ya nuna."

Faɗin Momi Fannah kenan tana duban Haseena da Laila, su kuwa dariya kawai suka yi. Daddy Mu'az wanda sai daga baya ya fito da wasu ma'aikatan da suka taimaka mishi da ɗaukar jakunkunan kayansu, shi ms ƙarasowa ya yi yaran suna ta kokawar rungume shi har Haseena, Laila kuwa daga gefe take mishi barka da isowa, ya amsa fuskarsa a sake.

Haka suka ɗunguma gaba ɗaya zuwa motocin, bayan shigar kowa suka fice sai gida.

Tun a daren aka fiddawa kowa tsarabarsa sai washe haƙora suke. Laila har zinare Daddy Mu'az ya siyamata domin yaransa biyu duka suna da ita. Ga kuma doguwar rigar abaya kala uku uku da Momi Fannah ta kawomusu ita da Haseena, iri ɗaya amma bambanci kaloli ne kawai. Na Haseena kalar da ta dace da baƙar fata ne ita kuwa Laila sai ta zaɓar mata kalolin da ta san za su dace da ita. Hakan bai yi wa Haseena daɗi ba ko kaɗan amma kuma kaifin idanun Gwaggo Samha dake wurin yasa ta gimtse bakinta kawai ta bar abin na cin ranta.

Momi Fannah ta ji daɗin ganin yadda gidan ya tafi kamar tana nan, ga kuma dukkan girke-girken da tace za'a yi na bikin sallah washegari su Laila da Asabe suka shirya yi din. Don haka madadin sun dawo ta zauna ta huta, sai ta wartsake ta shiga kicin din domin taimaka musu duk da cewa akwai yar uwar Asabe da ta zo wacce dama duk shekara takan zo taimakawa Momi Fannah da yin aikatau na kayan snacks.

Da magiya Laila ta fidda ta a kicin din wai ta je ta huta za su yi.

Washegari kuwa zuciyar kowane musulmi a faɗin duniya suka wayi gari cike da farin ciki na riskar wannan rana ta sallah. Ahalin Daddy Mu'az gaba ɗaya suka tashi da wuri suka shirya zuwa masallacin idi, suna dawowa aka zuba abinci bayan an raba har makwafta an miƙa kowannensu ya ci. Laila tsabar gajiya bayan ta kira Mama sun gaisa da mutan Maiduguri har Na'eem wanda ke sanar da ita shigowarsa Kano hutun sallah daga India inda can yake karatun medicine. Ta kashe wayarta gaba daya ta kwanta sai bacci.

***

KATSINA...

Kamar kowace rana ta sallah, dukkanin ahalin gidan Alh Sada idan ka cire matan da ke gidajen aurensu, sun haɗu a babban falonsa ana ciye ciye. Zakari shi ma ya shigo don gaida iyayensa daga masallacin idi. Areef ma na zaune cikin shirin babbar rigar wacce tun dawowa daga sallar idi ya cire ya ajiye saman kujera, men lace ne ya ɗinka mai tsada fari ƙal, kyau kam har ya gaji da yi. Kausar a sace take kallonsa don ji take ƙaunarsa na fisgar ranta. Alh Sada koda ya kammala wayarsa ya ɗauka da take faman ƙara yana amsa wayar Daddy Affan da ya kira don yi mishi barka da sallah. Dayake a handsfree yake amsawa, Areef na ji Alh Sada na gaisawa da Nihla har tana ƙorafin wai idan ta kira Areef ba ya ɗaga mata waya kuma ko yau da safe ta kira videocall don ta ga kwalliyarsa ta sallah nan ma bai yi picking up ba. Mami takaici duk ya ishe ta har ta ja guntun tsaki a kan idanun Hajja. Wani murmushi Hajja ta saki a ƙasan ranta kuwa faɗi take,

'Ba ki ga komai ba Salma, sai kin tsinci Sameera a matsayin matar ɗanki. Ki shirya akwai jan aiki a gabanki.'

Mami wacce ba ta san tana yi ba hankalinta na ga Abba wanda ya sa Lubna miƙawa Areef wayarsa bisa umarnin Nihla wai za ta ji muryar Areef din. Zuciyarta zafi kawai take, ta kula Abban ma ya lura da ita dalilin kenan da ya sa ko kallon inda take bai yi ba. Shi kuwa Areef wani kallo ya watsawa Lubna ba shiri ta sauke idanunta, ta yi azamar ajiye wayar a gefensa ta yi gaba. Ɗauka ya yi ya cire a handsfree sannan ya kara a kunne.

"Yes?"

Ya ji sadda ta saki wata wawiyar ajiyar zuciya kafin ta ce.

"God of mercy! Areef kana wahalar da ni wallahi. Don Allah me zan yi ka so ni ne wai? Uhummm?"

"Shi ne dalilinki na neman a ban waya? Ok ina abu yanzu, zan kira ki anjima."

"Promise?"

Ta faɗi a hanzarce saboda ta sani ƙarshenta ya kashe wayar. Nan ma bai amsa ba kawai ya katse ɗin. Khalid dake kusa da shi ya miƙawa wayar, ya karɓa shi kuma ya miƙa ga Abba.

'Shege kawai, ko da uban me ya fi saura da kowa zai dinga maita a kansa?'

Zakari ya furta a ƙasan ransa cike da jin zallar tsanar Areef ɗin. Yadda yake wani iyayi wai shi mai aji ya fi komai baƙanta ransa. Bai manta abokinsa Najeeb ba wanda yanzun ke rayuwa a can Abuja da matarsa, ya sha ce mishi Areef ya yi mugun ɗaukar kansa kamar ya fi uban kowa, tun a baya Najeeb ne ya fara ba shi shawarar ƙullawa Areef ɗin mummunan tarko akan Sameera wanda zai yi matuƙar wahala ya kuɓucewa tarkon nasu, sai ko Hajja da ta sani daga baya wacce ta goyi bayan lamarin, wato ba don ma tarkon ba da har yau bai san yadda zai tafiyar da al'amarin Areef ba.

Zakari ya yi ƴar kwafa, a ƙasan ransa godewa Allah yake da ya jefo musu Sameera karo na biyu a wasan. Ya na da tabbacin sai ta zamewa Areef tamkar dodo a rayuwarsa. Ya ji ya haƙura zai danne zalamarsa a kanta har zuwa lokacin da komai zai daidaita ta rabu da Areef shi kuma ya aure ta bayan ya mallaki dukiyar da Areef din ke juyawa a ƙarƙashinsa.

Haka dai aka watse a falon aka bar Mami da Abba. Kamar jira take kuma kowa ya fice bayan ƴanmatan sun gyara falon tas ta dubi Abban.

"Zuwa yanzu ya dace ka daina yunƙurin cusawa Areef yarinyar can tunda na tabbatar maka ya yi amanna da Kausar ta zamo matarsa."

Alh Sada ya dube ta.

"Idan na ƙi fa Salma? Akwai matakin da za ki ɗauka a kaina ne?! Har ni za ki faɗawa zancen banza? Ko an faɗamaki son da nake maki ne ya rufe min idanu da har za ki iya faɗa min son ranki na zuba maki ido ba tare da na tanka ba? Haifata kika yi?!"

Yadda ya yi maganar a zafafe sai ta kauda kai gami da ɗan sassauta murya.

"Allah ya ba ka hakuri to, amma ni ba wani abin nake nufi ba. Gani na yi bai dace a cigaba da sakawa Nihla rai da abinda muke da tabbacin ba za ta taɓa samu ba. Kai da bakinka ka ce ba za ka yiwa yaranka auren dole ba."

"Ke yanzu a kan Kausar auren me kike shirin yi mishi? Ko an fadamaki ban san cewa ke ce kika tursasa shi sai ya karɓe ta matsayin matar da zai aura ba? Salma ki kiyaye ni fa! Idan na ga damar aura masa Nihla ba ki isa ki hana ni zartar da ikona ba domin da ita da Kausar ɗin da kike magana duka babu zaɓin Areef a cikinsu! Don Allah tashi ki tafi kar ki ɓatan rai a ranar nan."

Za ta ƙara magana ya ɗaga mata hannu, dole ta miƙe ranta na zafi ta fice zuwa ɓangarenta. Tunani take kodai Areef ne ya faɗamasa yadda suka yi ne? Ta sani ta yiwa Areef din batun auren Kausar, farko ya nuna mata shi ba ya son auren zumunci, ba ta manta ba sai da ta nuna fushinta ƙarara kafin ya hau ba ta haƙuri ya kuma nuna amincewarsa da haɗin. To ya aka yi Abban ya san cewa tilas ta yi mishi alhalin ba ta sanar da shi ba? Ranta ya ɓaci sosai, ta kuma ci alwashin ko me zai faru babu abin da zai hana Kausar zama matar ɗanta. Ita ce zaɓinta.

***

Bayan Sati Biyu...

Daddy Affan ne zaune a cikin motarsa cikin farfajiyar wani park dake a birnin London yana zuƙar karan sigari. Ba jimawa aka ƙwanƙwasa murfin motar, ya buɗe wani baƙin fata ya shigo ya zauna ya rufe murfin. Bayan sun gaisa ne ya miƙawa Daddy Affan envelope. Ya karɓa ya buɗe ya soma kalla. Hotunan warehouse din ajiyar kayan kamfanin su Alh Sada ne dake a Newyork. Duk wani wuri da suke harkar kasuwanci a Texas, Miami da Los Angelas sai da aka yi ɗaukar masa hotunansu. Wani murmushi ya saki sannan ya fiddo maƙudan kuɗaɗe ya ba mutumin.

"Good job, John. Wait for my call."

"Thanks, will do."

Daga haka wanda ya kira da John ya adana kuɗaɗen sannan ya buɗe murfin motar ya fice. Shi kuwa wata dariya ya saki, a fili ya ce.

"Areef! Ba ka san waye Affan ba!"

Daga haka ya mayar da hotunan cikin envelope ya jefa a kujerar da John ya tashi sannan ya kashe sigarin ya tashi motar. Ya sani yanzu abin da ya yi mishi saura bai wuce ta yadda zai ɓullowa abin da yake son ƙullawa ba.

***

Ta ɗauki wayar ya fi sau a ƙirga amma sai ta mayar ta ajiye, a ƙarshe dai ta ji wani ƙarfi ya yunƙuro mata don haka ta sa hannu ta ɗauka ta danna mata kira.

Bai fi ƙara uku ba ta ɗaga, suka gaisa a mutunce. Hajja har tana faɗin wai ta yi fushi ba ta kira ta yi mata barka da shan ruwa ba balle kuma gaisuwar sallah. Laila ta ba ta haƙuri. A ƙarshe shiru ya ɗan biyo baya, can dai ta karya bille ta ce.

"Na yarda na amince zan aure shi."

Ta ji sadda Hajja ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kafin ta yi hamdala.

"Madallah da ke Sameera, haƙiƙa na yarda dagaske kike son cimma ƙudurinki yanzu. To shikenan, ki jira ni zuwa anjima zan kira na yi maki bayanin komai. Daga nan kuma zan turo maki lambar wayar Areef. Duk yadda na tsara, haka nake son ki bi. Kin ji ko?"

Laila ta gyaɗa kai kamar Hajja na gabanta sannan ta ce,

"Na ji Hajja, sai dai nima ina da sharuɗɗana."

Ƴar dariya Hajja ta yi.

"Kar ki damu, duk abin da yake akwai, zamu tattauna anjima kaɗan, yanzun ina tare da baƙi ne."

Sauke ajiyar zuciya Laila ta yi.

"Ok ba damuwa. A huta lafiya."

Daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar gami da runtse idanu, har lokacin ƙirjinta bai bar bugu ba.