Page 27
*JADEEDAH*
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 27 ❤🔥
"Anya Gloria ba akwai wani ɓoyayyen sirri da ke wanzu tsakanin Richal da Jadeeda ba ?",Mom Rebecca ta faɗa bayan sun gama yin dinner.
Shiru Momy ta yi ta kasa iya cewa komi sai can daga ƙarshe ta sarƙe da miyau, saurin ɗaukar Cup ɗin ruwa ta sha sakamakon ƙwarewar da ta yi,ko ta samu ya lafa.
"Mom wannan wacce irin magana ce,me ya kawo ta,kamar ba ta da muhalli a irin wannan wurin ","Hmmmmm Gloria kenanan dama na san irin haka ce zata faru,ba lalle ki yarda da duk abinda zan faɗa ma ki ba a yanzu ba,amma ki sani tuni zuciya ta daɗe da fara kawo zargi kala daban-daban a cikin tarayyar Richal da kuma Jadeeda"...."Mom zargi fa haramun ne,kuma ke fa tamkar Uwaki ke a gare su wannan bai kamata ya fito daga bakin ki ba",Girgiza kai Mom Rebecca tayi kafin ta ce,"To Shikenan tunda haka ki ka ce na bar maganar ba zan sake danganta su da irin wannan magana ba tunda baki yarda ba",tana kaiwa nan a zancenta ta tashi ta bar mata dinning ɗin gaba ɗaya.
Tun bayan fitar Granny da ga dinning room ,Momy ta shiga cikin ƙololuwar tashin hankali, Zuciyar ta sai faman saƙa mata munanan tunanin ta ke, kwakwalwar ta cushe,ta kasa samun natsuwa balle har ta samu damar da zata samu makama a cikin zancen,tun tasowar Jadeeda ta san akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin su,ya kan ɗauki dukkanin wani lamarin ta da muhimmanci baya taɓa manta wani abu da ya shafeta,duk da kasancewar ba a ƙasa ɗaya suke zaune ba hakan bai hana shi halartar duk wani abun da zai sa ta farin ciki,shaƙuwar su takai matuƙa har ta kai ya fi kowa sanin sirrikanta da kuma abinda take so,sai dai ko ɗaya bata taɓa kawowa a ranta cewa da akwai manufar hakan ba,sai yanzu zuciyar ta ta fara kawo mata hakan a matsayin zargi.
"Kai a'a hakan ma ba zai yiwu ba,Richal ba zai taɓa aikata min irin haka ba,ya na da hankali ya san girman sirrin da ke lulluɓe acikin wannan lamarin ba zai aikata haka ba",Gloria ta faɗi hakan ta na mai cigaba da kaiwa da komowar da ta ke.
"Idan kuma hakan ta kasance fa yake nan ?",wani sashe daga cikin zuciyar ta ya sanar da ita haka,sai da bugun zuciyar ta ya ƙaru kafin ta dafe saitin wurin tare da cewa,"Shakka babu kuwa da ya aikata babban kuskuren da bai taɓa aikata shi a rayuwarsa ba,zai yi dana sani mai girma,har sai takai shi ga jin dama bai bari sakarar kuma mayaudariyar zuciyar sa ta rinjaye shi ga aikata abinda ya aikata ba".
Tunani ne ya cinkushe mata kai har ta kai ga ta fara iya daina gane komi ji da ganin ta sun fara gushewa ,kanta kuma na tsananta mata wajen sarawa.
Amma duk da hakan ta kasa iya dakatar da kanta game da tunanin da take, abubuwa masu yawa sai yanzu suke zuwan mata,misali irin yanda suke ba junan su kulawa da kuma yanda shaƙuwar su take,kafin ka ce me tuni ta fara ganin duhu a cikin idanunta da ƙyar ta samu ta daga bango ta isa bedroom ɗin ta ta zube a kan shi wasu zafafan hawaye na son zubo mata amma zuciyarta ta ƙeƙashe kwata-kwata ba ta son ta yarda da zarge-zargen da suke kai kawo mata a cikin ranta,balle har ta yarda da su.
"Anty Jee wai ina za ki ne dare fa ya fara yi na ga sai faman kwalliya ki ke,is there anything special da ki ke expecting ɗin sa ne?","Yeah off course ko kin manta Uncle Miey ya na can yana jirana,zai yi Surprise ɗina da wani abu mai matuƙar muhimmanci,so ya ki ga fitar tawa ta fita ko in sake wata",ta kai zancen tana mai jujjuya jikinta yanda zata ganta sosai,sanye ta ke da mini skect sai wata half ɗin riga mai hannu guda,wacce ko cibiyarta ba ta rufe ba,ƙafarta sanye da high heel shoe,gashin kanta ya sauka har saman shoulder ɗin ta,komi nata shigar red and black, skect da bag ɗin ta black sai rigar jikinta da shoe ɗin ta red.
Da yatsun hannunta ta yi mata alamar ta kai maƙura,"Am bari in ƙara fiddo da Anty Jeee ɗina",ta kai zancen tana mai saukowa daga kan bed ɗin da take ta ɗauko eye glass black ta sanya mata,gami da tsara mata simple make up a saman fuskarta,sai da ta ƙara yi mata ɓarin mabanbanta tauraruwa a jikinta kafin ta juyar da ita saitin mirrorn dake ɗakin gami da cewa da ita,"Ya ki ka ganki yanzu nasan in ku ka haɗu da Uncle R ba zai iya noticing ɗin ki da sauri ba".
Dariya Jadeeda ta saki gami da kai ma Nora bugu ta goce tare da cewa,"Ba kyau zan yi ba ko da suffa za a sauya min in har Uncle Miey zai iso gare ni da bugun zuciya kaɗai ya isa ya gane ni,balle kuma wata kwalliya da ko matakin Princess ban kai a kira ni da ita ba","Wa ya gaya maki haka ai Auntyna ta wuce da wannan matsayin ,sai dai a kira ki da Queen ba Princess ba","Ma za ki cigaba har wani ya jiki,da anzo zan tsere jikinsa in ce ba ruwana","A haba ai nasan ba za ki aikata hakan ba,ke ɗin ta dabance,za ma ki iya ɗaukar laifin akan ki,saboda tsabar ji da ni da ki ke kin san wani time ɗin ina mamakin yanda wasu abubuwa na mu suka sha ban-ban da na ki,misali yanayin hasken fatar ki,ɗan ƙaramin jiki da ki ke da shi babu wani abu guda ɗaya wanda ku ke kamanceceniya da shi da wani a Gidannan komi na ki so special ke ka ɗai ke da irin sa".
Ta buɗe baki za tabata amsa Martin ya shigo a hargitse kamar wanda aka watso shi , Muryar sa na rawa yace da su,"Momy....Momy ....jikinta ya motsa tana can bata iya gane komi da alama ta na cikin mawuyacin hali na yi ta ƙoƙarin in ga ".....ko tsayawa su ji ƙarashen abinda ya ke faɗa ba su yi ba,su ka yi waje gami da budar Room ɗin ta don ganin halin da ta ke a ciki,ba ƙaramin tashin hankali su ka shiga ba lokacin da su ka ga halin da Momy ta ke a ciki,nan su ka fito suna neman agajin gaggawa gurin Driver, Gate Man da kuma sauran masu aikin Gidan.
Allah ya tai make su sun isa Hospital ɗin da wuri da ita cikin ƙanƙanin lokaci Doctors su kai ca kanta,sun yi iyakar bakin ƙoƙarin su kanta,duk da kasancewar Doctor Muh'd Jaheed baya nan,sun samu ta dawo cikin hayyacinta amma kuma cikin rashin sa'ah ta kasa iya tan-tance kowa a cikin su,ta kasa iya kama sunan kowa a cikin su, Jadeeda sai ta kira da Momy Rebecca ,Nora Kuma ta kira ta da Martin haka dai ta cigaba da soki burutsu,zance ba kai ba ƙafafu.
"Doctor hankali na a tashe ya ke ,ba fa ta iya gane kowa kamar ba ta cikin hayyacinta ?",Rev. Anderson ya faɗa ,da dawowar shi kenan ya iske lamarin.
"Am Sir she is out of danger bata cikin wani hatsari,za mu ɗorata akan medicine by the grace of God za ta koma normal", wannan shine abinda Doctor ɗin da ya duba ta ya ce,kasa haƙuri su kai har sai da su ka sake tuntuɓar wasu Doctors ɗin amma maganar ɗaya ce, cewa a hankali za ta koma normal,sai faman kai kawo su ke ,sun kasa kwantar da hankalin su,ga dare har ya fara tsalawa.
"Wai ina asalin likitan da ya duba ta ya ke,a kira shi ko ma samu ta fita daga cikin wannan yanayin ?",cewar Granny da hankalin ta yake a matuƙar tashe.
"Granny wannan Special Doctor ne ba kowanne lokaci ya ke zuwa ba","Jesus Christ oh father lord ka kawo mana ɗauki.
Sai tin bed ɗin Jadeeda ta je ta duƙa gami da dafa ƙafafun Gloria idanuwanta na zubar da hawaye ta fara yi mata addu'a,"Oh Lord Jesus hear me when I call,o God of my righteousness! You have relieved me in my distress have mercy on my Mom and hear my prayer,na sani kai ka faɗa a cikin littafin ka mai tsarki Jeremiah chapter 33 verse 3 kace call to me and I'll answer you show you great and mighty thing wich know not,bari Ubangijin sama da ƙasa ka yaye ma Mahaifiyarta wannan lalurar da ta ke fama da ita,oh Lord father kasa wannan cuta ta zama waraka kuma kaffara gare ta,bari Ubangijin halitta kasa ta miƙeta taka da ƙafafuwan ta,ka warkar da ita ,ka fidda mu daga cikin tashin hankali da ruɗun da muke a ciki ",ta kai zancen tana mai zubar da zafafan hawaye akan fuskarta.
"Anty Jeeyy mai zai sa ba zamu nemi alfarmar su kira mana shi ba ya zo ya duba mana ita ko da zuwa gobe da safe ne?",Martin ya ce da ita,"Sai dai mu kwatanta hakan idan zai yiwu,wani lokacin ba a cika yin dacen zuwan su ba","Kin ga Jadeeda ko nawane zan biya in har zai zo ya duba ta,ya ambaci iya amount ɗin da ya ke so zan biya shi matuƙar zai shigo cikin garin Abuja zuwa da safe","Shikenan Papa bari in Yi magana da wani daga cikin Doctors ɗin ko za mu da ce".
Haka ta fita sai dai me cikin rashin sa'ah Doctor ɗin da ke unduty a ranar ya shiga treater,sai da su kai jiran sanda ya fito kasa tsayawa ya sauraren su yai ƙarshe ma sai ya sake shiga wata treater ba tare da yaba su wani lokaci mai tsawo ba,wanda hakan ba ƙaramin sake jefa su cikin wani sabon tashin hankali.
"Yanzu Papa haka za mu zuba ma Momy idanu ba tare da mun iya taimaka mata da wani abu ba,zuciya ta sai ƙara karyewa ta ke".cewar Nora
Sai da ya janyo ta jikinsa kafin ya fara lallashinta gami da son kwantar mata da hankali,ringing ɗin wayar Jadeeda da ta ishe su tun ɗazun ne ta sake ratso kunnuwan su ,sai da ta saki tsaki kana ta jawo wayar da son duba waye ke kira,sunan Uncle Miey ta gani yana yawo akan screen ɗin da sauri ta ɗaga gami da fara ba shi haƙuri gami da sanar da shi abinda ya ke faruwa,bai jira komi ba ya katse kiran gami da nufo Hospital ɗin .
"Am ɗan dakata kamar fa ya taɓa bani wani card da zan iya contacting ɗin sa da shi", Jadeeda ta faɗa ta na mai yunƙurin fara laluban jakarta ba ta iya ta samu komi a ciki ba hakan ya sa ta juyawa gami da nufar hanyar fita,nan ta ci karo da Uncle Richal ya na shirin shigowa,a taƙaice ta yi ma shi bayanin abinda ke faruwa ya juya ya bita su ka nufi Gidan tare.
Ba su wani ɓata lokaci ba suka isa gidan duk inda ta san ta na aje wani abu mai muhimmanci sai da ta yi watsa-watsa da su ,har sai da ma ta fara cire rai wajen ganinta sanna Allah ya nuna mata ita,tsuru ta zubama card ɗin idanu,Wanda ba wani abu da ke jikinsa daga sunan mallakinsa sai phone number,a Zuciyar ta sai faman mai-maita sunan ta ke Doctor Hibba Ibrahim Neurological Doctor,"Ki kirata mana wata ƙila a dace", Uncle R ya ce da ita sautin maganar da ya yi mata ta sa ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi,jikinta har yana rawa ta sanya number gami da fara dialing ɗin ta, har kiran ya gama shiga ba ai picking ba,hankali tashe ta sake dialing ɗin number a karo na biyu,sai dai abinda ya faru da farko shi ya sake faru,amma duk da hakan Jadeeda ba ta sare ba haka ta cigaba da trying ɗin number kira bayan kira.
A firgice Hibba ta farka bakin ta ɗauke da salati gami da rarumo wayarta ta duba domin ganin ƙarfe nawa,ganin time ɗin da tayi ne ya sa ta saki wayar cike da tashin hankali ta nufi bed ɗin da Abubakar ke kwance cikin mawuyacin hali,wanda hakan ya hana lura da tararin miscall ɗin da aka tara mata,nannauyan barci ne ya kwashe ta tun bayan sallame sallahar Isha'i wanda hakan ne yasa bata samu damar sanya mashi Drif ɗin da ta ke sama da ba,lokaci bayan lokaci,baƙaramin tashi hankali gani da firgice ta shiga ba , wannan dalilin ne ya sa duk iya kiran da Jadeeda ta yi mata ba ta kula da shi ba.da ƙyar ta samu ta iya control ɗin halin da ta ke a ciki bayan wani dogon lokaci.
"My Angel wannan matar ƴar wulaƙanci ce ji bi duk tarin kiran da ki ke mata ta ƙi ɗagawa",....."Uncle Miey mana ka yi mata kyakkyawan zato mana ka sa ni ko ta na da wani uzurin da ya ke gabanta da har ya hana tai picking ɗin kiran","Oh sorry haka ne wannan tunanin bai zomin a rai ba",da haka su ka sake komawa can Hospital ɗin ba tare da sun yi nasara ba,dole sai haƙuri su kai ba tare da sun sami wani taimakon daga wani ɓangare ba,da ga ƙarshe da suka ga halin da ta ke aciki ya tsananta dole su kasa aka yi mata allurar barci.
Sai da gari ya waye Doctor Nass ya shigo Hospital sannan ya samu da taimakon Doctor Jaheed daya sanar da shi abinda yake faruwa ta waya ya sanarda shi duk abinda ya kamata ya yi,sannan fa aka samu ta fita daga cikin halin da ta ke a ciki.