Page 29
*KARAGAR MULKI*
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 29
"Na rok`e ki Gimbiya Junainah ki dubi girman Allah ki bud`e k`ofar nan,ta ya mutum zai cigaba da rayuwa irin yanda ki ke a yanzu,yau fa yinin ki uku ba ci ba sha,ko kin manta yini uku mutum ya ke bai sha ruwa ba,sannan kuma yai yini bakwai bai ci abinci ba,muddin ya kai wannan lokacin,ba abinda yai ma sa saura face mutuwa,shin kin shiryama mutuwa ne ko me?, idan har wani abu ya same ki ba zan ta`ba iya yafe ma kai na ba,idan kuma kin shirya mutuwar ne to ki bud`e k`ofar ni ma in shigo mu mutu a tare domin zuciyata ba za ta iya jurar ganin ki a cikin irin wannan halin ba".....ta Kasa k'arasa zance sakamakon cin k`arfin ta da kuka ya yi,itama can cikin sheshshekar kuka ta ce da ita," Kin ga Kuyanga Jazila ki kyale ni,ki tafi ki je ki yi rayuwar ki ba ki ga ko Uwa mahaifiyar da ta kawo ni duniya ba ta damu da ni ba,ta wofintar da ni tare da duk wani abu da ta shafi rayuwata,ke ma lokaci ya yi da za ki bar wannan k`angin bautar ki tafi can wajen Mahaifiyar ki ki kula da ita",......"A'a Gimbiya ni ba inda za ni inanan tare da ke duk runtsi da tsanani in fiye da wannan kwanakin za ki sake shud`ewa ba tare da kin fito ko kin ci abinci da abin sha ba to ni ma zan dauwama anan ba ci ba sha ni ma,idan mutuwar da ki ke kira da fata ta zo d`aukar ki sai ki sanar ma ta da akwai wata hadima kuma baiwar ki ta na jiranta,bayan ta zare ranki ta k`araso ta zare nawa","Kar ki yi k`ok`arin lalata rayuwar ki a saboda ni,domin ni komi nawa ya riga da ya k`are zai fi mi ki kyau ki je ki fara shirin sabuwar rayuwa da tafi kamata da can-canta da ke ki yi Aure har ki haifi yaran ki, ni bani da wani gata a yanzu ba kuma wanda ya ke a tare da ni,Ina jin ki a jikina tamkar `yar'uwata don haka ba zan so wani abu mara dad`i ya same ki ba","Ina tare da ke a kowanne irin hali,kuma har in da gaske kina ji na gami da yi min kallo tamkar `yar'warki,to ki saurari abinda zance da ke, duk da na kasance baiwar ki,mai yi mi ki hidima gami da yi ma ki biyayya a kowanne k`adami,duk wani mawuyacin halin da za ki shiga zan kasance da ke,ki aminta da ni ki bud`e k`ofar nan mu had`u mu samar da mafita ga wannan rikitaccen al'amarin","Na ji zan bud`e k`ofar amma da zaran kin shigo zan maida in rufe ne","Na yarda na amince","Hakan fa na nufin kin yarda da duk hukuncin da zan yanke","Eh na amince kuma na yarda in mutu ko in rayu a saboda ke",kuyanga Jazila ta ba ta amsa,da wannan zancen a ka samu ta bud`e k`ofar amma kamar ta na jira Jazila ta shigo ta mai da k`ofar ta rufe,har da dannewa kamar ta na da tabbacin wani ya biyo bayan su,gashi sai faman haki ta ke kamar wacce tai tseren gudu.
Kama hannunta Kuyanga Jazila tai ta zauna da ita a kan mawanki(Gado ne da ada can ake amfanin da shi),ta ce da ita,"Da akwai babbar matsala da ke tunkarar ki wacce ta fi wadda ki ke a ciki girma da tashin hankali, ya kamata ki natsu ki mai do da hankalin ki a jikin ki kuma ki tsaida k`afafunki a k`asa ki zartar ma kan ki abinda ki ke ganin ya dace da rayuwar, kar da lokaci ya k`ure ma ki","Ban ga ne me ki ke son cewa da ni ba Kuyanga Jazila shin wa ni abu ya sa ke faruwa ne,ban sa ni ba ?",sai da murya Kuyanga Jazila ta fara rawa kafin ta ce,"A'a ni ba haka na ke nufi ba,ina dai tsoran hakan ta kasance ne shi ya sa ki ka ji na ce haka",ba tare da Gimbiya Junainah ta mai da hankali a halin da Gimbiya Junainah ta ke a ciki ba tace,"Kar ki wa ni damu Kuyanga Jazila in ma wani abun su ke son sa ke tsirowa a game da ni a shirye na ke da fuskantar ko ma me ye ,tunda yanzu na riga da na gama gane kaf a cikinsu ba mai k`aunata ba kuma wanda ya ke so na da gaske a cikin su ,Komi su ke so su aikatamin su aikata,dama mutum d`aya ne ke ji da ni gami da so da K`aunata kuma yanzu ya min nisa,nisan mai tsanani,Na san da yananan da haka ba za ta faru da ni ba, Kawuna Ishmal zai tsaya tsayin daka wajen ganin ya hana afkuwar wannan rikitaccen al'amarin a gare ni",",To in haka ne ki tada manzo(d`an aike) ya iske shi har zuwa can k`asar da ya tafi mana","Haka ba zai yiwu ba domin akwai tazara me nisan gaske a tsakanin mu kafin ma manzo ya riske shi duk me afkuwa ta afku a kaina,sanin hakan ne ma ya sa tun da fari na sadak`ar gami da mik`a kai akan wannan lamarin,na gwammaci in mutu da in amince da shawarar ko abinda su ke zuwan min da shi,na yi kaico,Na yi tir da alawadai akan ina ma da da akwai wata hanya da Zan sadar da sak`ona ga Kawuna Ishmal cikin sauk`i,ina ma da zan iya runtse Ido in ji muryarsa ko in gansa gani ga shi,ina ma da da akwai wani abu da zai d`auke ni mu tashi sama ni da shi ya kai ni har gaban Kawuna Ishmal ya aje,ina ma da da akwai wani abun hawa da zai tak`aita tafiyar da ta ke tsakanina da shi ina ma da hakan za ta faru ta kasance,sai dai ina ba ko d`aya da zai kasance a cikin jerin abubuwan da na lissafo "," Tabbas duk wannan abubuwan da ki ka lissafo ba wanda zai iya kasancewa,ga shi ke ko `yar tsuntsuwarnan da ake aike ba ki da ita,balle mu yi amfani da ita wurin aikata gun da mu ke da buk`ata","Ba ni da wata madafa shiyasa na gwammaci da in mutu,rayuwata ta k`are wata k`ila in na mutu za su yi farinciki, har su yi murna tunda matsalar su ta kauce ta ba su wuri,dama ni d`in na kasance annoba a gare su ,ni d`in fuska biyu ce da ni, in na rikid`ewa zuwa macijiya ba zan iya banbance su d`in su waye a gare ni ba,wanne matsayi su ke da shi a wurins,zan cutar da su in illata su ne kawai,ba ni da tantama hakan ne ya sa su ka zartar da wannan hukuncin a kaina domin su samu in matsa in ba su wuri su yi rayuwar su yanda su ke so","Bazan yi mi ki tantama akan duk abinda ki ka ce ba amma zan so ki runtse idanunki ,ki natsu ki saurari zuciyar ki,duk hukuncin da ta zo mi ki da shi ki amince da shi ba tare da shakku ba domin nasan Allah me sama ba zai ta`ba barin ki ki wulak`anta ba,domin kin tsaya tsayin daka akan ra'ayin ki ne,don gudun kar a sa`ba ma sa ne","Haka ne na San da hakan kuma na aminta","to me zai sa ba za mu yi wani abuba ?","me kenan ",Gimbiya Junainah ta mai da ma ta da wata tambayar," ki runtse idanunki ,ki natsu ki sa dogaronki GA mai du ka ,duk abinda ki ka ji ko ki ka gani shi ne mafita a wajen ki", "Anya kuwa Kuyanga Jazila ki na ganin hakan zai aiki kuwa ina tsoran kar in ji ko inga wani abun da ba zan iya d`auka ba","Kar ki karaya ma na shugaba ta,ba abinda zai faru sai alkairi",Tamkar me koyan yanda aje rufe Ido haka Gimbiya Junainah ta fara son runtse idanunta sai ta kusan rufewa sai ta bud`e, da k'yar dai a ka samu ta rufe,ta na mai d`ora hannayenta duk biyun saitin zuciyarta,ta d`auki lokaci kafin ta bud`e,sai dai ta na bud`e na ta idanun ta ci karo da Kuyanga Jazila itama ta rufe na ta idanun har da k`ank`ame jikin ta wuri guda,da badan halin da suke a ciki ba da ba abinda zai hana ba tai dariya ba,sai da ta sa hannu ta zungureta sannan tai zumbur ta bud`e idanunta ta na mai cewa cikin d`an firgici, "Me ki ka gani ?","Ni dai tunda na rufe idanuna abu d`aya na ke ta gani sai maimaita kan sa ya ke",sai da Kuyanga ta ya mutsa fuskarta sannan ta ce," Abu d`aya kuma ta ya haka zata kasance amma sake runtsewa mu gani",haka Gimbiya Junainah ta sa ke rufe idanunta amma abinda ta gani da farko shi ta sake gani,sai da su ka maimaita har wajen so uku ban da wanda su ka yi da fari abu guda d`aya ta ke ta gani,ita Kuyanga Jazila ta k`i bari Gimbiya Junainah ta fad`i abinda ta ke gani, don gani ta ke ba zai yiwu abu guda d`aya yai ta zuwanma mutum a rai ba ina laifin biyu sai ya za`bi d`aya ya bar d`aya,hakan ya sa ta kasa yarda har tana cewa,"Ko dai za ki k`ara gwadawa ne mu ga ni Gimbiya Junainah ?","Ke ni na gaji tun d`azu ba abinda na ke gani sai abu guda kuma sai cewa ki ke in ta mai-maitawa, na gaji gaskiya "," To na ji amma fad`a min mene ne ki je da gani eai",sai da fuskarta ta d`an can za alamun damuwa ta bayyana a jiki sannan ta ce"Fuskar Malikat Juwairiyya kawai na ke ga ni ta na cews in dai zan zauna a cikin Masarautar nan kuma in cigaba da amsa suna na na Gimbiya Junainah girka ba fashi sai anyi ko mu je can tsibirin zimbar "," To fa me hakan ke nufi ?",Kuyanga Jazila ta tambaya,"Ni ma Ban sa ni ba",Gabaki d`ayansu shiru su kai na wani lokaci mai tsawo,alamun duk sun fad`a cikin dogon tunani,can kamar an tsikari Gimbiya Junainah ta ce,"Hakan na nufin mu gudu mu bar k`asarnan kenan ?",sai da Kuyanga Jazila ta wuntsila daga durk`usan da tai a gaban Gimbiya Junainah, sai ga ta zaune tamkar mai zaman `yan bori,gaba ki d`aya ta firgice ta shiga tashin hankali da jin abinda Gimbiya Junainah kuma Uwar d`akinta ta fad`a, "Ki gafarce ni ya ke Uwargijiyata ba ina nufin ki yi irin wannan tunanin ba,tunani mai kyau za ki bawanda zai sa ke jefa mu cikin tsananin tashin hankali da masifa ba"," A'a mene ne haka ji bi yanda duk ki ka bi ki ka rud`e sai ka ce wacce a ka kama ta yi kisan kai, wannan ba mafita ba ce,da duk za ki tashi hankalin ki akan na ce haka ".....da sauri ta katse ta da cewa ba mafita ba ce sa ke cilla kai a cikin bala'i da masifa ne,nasan ba makawa sai an kama mu to idan aka kama mu sai muce me,da wacce hujjar za mu kare kan mu da ita"," Ke fa d`azu ki ka ce tunda na dogara da Allah ba zai ta`ba bari in wulak`anta ba sai kuma yanzu duk ki bi ki tashi hankalinki,na riga da na yarda da Allah kuma na san ya isar min don haka ba makawa a yau kuma acikin darennan sai mun bar Masarautar nan","To in mun tafi mu je ina,ina ki ka sani a fad`in k`asarnan, wa mu ke da shi da za mu tafi wurinsa ba tare da su Malikat Juwairiyya sun riske mu ba a kaf fad`in duniyarnan ?","oho ni dai nasan ina da Allah kuma ya isar min abu d`aya na sani yanzu zan tashi in yi alwallah in gabatar da duka sallolina na yau guda biyar ,sai in rok`e shi,duk abinda na ji bayan na ga sallahr to da shi za muyi amfani","Ni kuma yau na shiga uku na jangwalo ma Kai na abinda ba ni da mafitarsa yanzu da gaske tafiyar zamu yi ?", ko ta kanta Gimbiya Junainah ba ta bi ta tashi ta bubbuga alwallarta yanda ta ke tunani haka a ke yinta,Nan cikin d`akinnata ko Tsarki babu,ta gabatar da Sallahr ta duka guda biyar d`in cikin k`asa da dak`ik`a biyar tagama sallahr biyar raka'a sha bakwai, tana sallamawa ta janyo wani sanho(abun zuba kaya ne)ta wurga ma Kuyanga Jazila ta ce zuba ma na duk abinda ki ka san za mu buk`ace shi a wannan tafiyar "sai da Kuyanga Jazila ta d`ora hannayenta saman kanta sannan ta ce," waiyo Allah na yau ni kam na ga ta kaina na jawo ruwan dafa kaina ga shi ba ni da abin tare sa ya bar zu ba a kaina,Sam ko da wasa ban san wannan lamarin zai juya ya dawo kai na ba haka"....."ya Isa haka dan Allah idan ba za ki yi wannan tafiyar ba ki sanar da ni ba ki rink`a yi min irin wannan d`abi'un ba","Wace ni ni d`in banza ai dole ne ayi tafiyarnan da ni,in ki ka bar ni wurin wa zan zauna ai k`arshenta waccan munmunaar Bokanyar ta sa ai tsirena ta cinye,dan nasan kai tsaye za ta gano da ni aka shirya komi",duk tana wannan zancen ne tana jawo duk abinda ya tare ma ta gaba ta na dannawa cikin wannan sanho sai da tai sanho biyu,sannan ta janyo `yar sandar da ake sagalasa gefe da gefe ta sagala,sai da Gimbiya Junainah ta sauya kayan jikinta sannan suka fito a lokacin Sulusin dare ya shiga ba tare da sun ji tsoran wani abu ba su ka nufi hanyar da suke tunanin itace za ta `bullar da su sukai ga barin wannan Masarautar.
Hannayen sa toshe a saman kunnuwasa sai faman tutturza k`afafunsa a k`asa ya ke,gami da girgiza kan sa jikinsa ya jik`e sharkaf da gumi,muryarsa har disashewa ta ke wajen cewa,"A'a ba na son ji,indai ba so ki ke ki haukata ni ba,domin na rasa gane da ga wanne wuri ko `bangare ne na ke jiyo muryar ki",amma ina ji ya ke kamar ana k`ara kusanto da muryar da ya ke ji saitin kunnen nasa sai faman kiran sunansa ta ke,tamkar wanda a ka tsikara haka ya mik`e ya nufi saitin k`ofar kurkukun ,kamar abun almara haka ya na ta`ba k`ak`k`arfan k`arfen da ya zama tsakanisa da farfajiyar kurkukun, ba tare da ya yi la'akari da Ina ya ke jefa k`afafunsa ba,ya cigaba da tafiya,kamar makaho haka ya ke tafiya zuciyarsa ce kawai ke tafi da shi,saitin inda ya ke jiyo muryarta ya bi kawai,saboda bai san ko ina ba a cikin farfajiyar masarautar kamar a mafar ki haka ya ga giftawarta ta wuce shi a guje,sai wata na bin bayanta, da mugun gudun da bai ta`ba tunanin ya na da shi ba haka ya rufa ma ta baya,tamkar wanda a ka daskarar da k`ank`anra haka ya tsaya cak,gabad`aya jijiyoyin sa su ka dakata da aiki,gashin kan sa ya mik`e tsaitsaye,lokaci guda zufa ta fara kwaronyowa a jikinsa amma kuma asali a jikinsa sanyi ya ke ji tamkar wanda ya ke cikin yankin da su ke da dussar k`ank`ara," A'a dan Allah na rok`eka da koma waye kar ka bayyana domin a yanzu inada buk`atar in kasance a matsayin ni d`i na,Mahaifiyata na can na jira na sai faman kiran suna na ta ke,ka bar ni in amsa kiranta dan Allah na rok`e ka",wata irin k`ara ya saki wacce har sai da ta karad`e ilahirin Masarautar, duk`ar da kansa k`asa yai na wani lokaci kafin ka ce me Dakarun da su ke gadin lungu da sak`on Masarautar duk sun fito.
Mik`ewa Yarima Haisam ya yi ya na mai sa hannunsa ya tattare gashinsa ya d`auresa a tsakiyar kansa sa`banin Yarima Haisam da ya ke tara shi a k`eyarsa,wani murmushi ya ke mai ci ke da zallar k`eta da mugunta ya fara sa ki "Kauce Yarima Haisam wannan lokacin ba na ka ba ne ba,ka gama cin duniyarka da tsinke yanzu lokacin *HARZAN* ne", ya k`arasa zancen na sa da murya mai amo wacce ta zagaye gami da k`arad`e ilahirin Masarautar.
A:Rigiji gabji,tabbas yanzu ne wasan zai fara,domin a baya duk shimfid`a ce,don haka sai a sa ke gyara zama,ba mu yi komi ba domin a yanzu ne za mu koma Masarautar BIHINAR wacce ta ke ci ke da na k`alubalen, wanda ya nunnunka na Masarautar BAIBAH, akwai wani babi mai cike da wasu darussa da ba mu ko ta`ba shi ba,a cikin sa ne za mu baje kolin darasin wannan littafi.
B: Shin me ku ke tunanin zai iya faruwa a cikin Masarautar BAIBAH sakamakon bayyanar Harzan a jikin Yarima Haisam ?
C:GA dai Yarima Haisam ya fito neman mahaifiyarsa Giwar Masarautar,wacce ta ke a matsayin Gimbiya Junainah ya hakan za ta kasance,mene ne zai faru a duk sanda su ka had`u kuma ya gane ba ita ce asalin wacce ya ke nema ba ?,ga Yarima Haisam Gimbiya Junainah matsayin Uwa mahaifiya ya ke kallonta shin ita ma za ta d`auke shi da irin wannan matsayin ko-ko akasin haka ne za ta kasance
"Wanne asalin sirri ne ke binne tsakanin Boka Dürsäås da Sarauniya Junayyah, wace ce ita ,ina asalin Sarauniya Junayyah ta ke me ya faru da ita?
Wanne takun sak`a ne tsakanin ahalin Waziri da kuma ahalin Me Martaba Sarki Abdullah
Shin Wai waye Inuwar Masoyi a wajen Gimbiya Junainah, wacce irin alak`a ce a tsakanin su,shin Gimbiya Junainah ita da Kuyanga Jazila za su sami nasar tserewa kamar yarda su ka tsara
Ya batun Yarima Ishmal shin zai yi nasara akan abinda ya je nema ko kuwa,idan ya dawo ya riski labarin abinda ya faru da Gimbiya Junainah mene ne zai biyo baya?
Wanne zunubi ne Me Martaba Sarki Abdullah ya aikata da har ya ke bibiyar ahalinsa gabad`aya?.
To wai kuna hangen nasara ga Nurain da ya fito domin ya ceci Yarima Sadauki
Mene asalin dalilin bayyanar Ruhin Giwar Masarautar a jikin gangar jikin Gimbiya Junainah,wacce alak`a ce a tsakanin su ?
Shin ya k`arshen alak`ar da ke tsakanin Boka Dürsäås da Bokanya Azizah zai kasance waye burin sa zai cika ,kowa dai a cikin su ya na mugun nufi akan d`an'uwansa waye zai ci nasara
Malikat Juwairiyya ta yi ma Gimbiya Junainah alk`awarin ba ta labarin masarautu guda uku da abinda ya faru a tsakaninsu
Wanne irin mafarki ne Malam Musa yai da har ya ga Yarima Sadauki a cikinsa ,mene ne amfanin zoben da ya sama sa a hannunsa wannan Sark`ar da ta bayyana a jikinsa ta mece ce,ya labarin boren da Malam Musa su ke shirin shiryawa Sarauniya Junayyah wanda za su yi amfani da Hatimi
Ko kunsan gabad`aya labarin masarautu guda ukunan labari d'aya ne wanda dalili guda d`aya ya assasa shi har yai silar rikid`ewa ya zama tsananin gaba a tsakaninsu
Haka kuma gabad`aya wad`annan amsoshin tambayar duk su na a cikin littafin KARAGAR MULKIN kashi na biyu
Hakan ya sa na ke baku tabbacin akan duk wanda bai karanta KARAGAR MULKIN kashi na biyu ba to tabbas an barsa a baya,dan haka ku gaggauta na ku domin a dama da ku
_*ALHAMDULILLAH*
_*ANAN NA KAWO K'ARSHEN KARAGAR MULKIN KASHI NA 1*_