9
DAGA AURENA
©️MEENAT A 'YANDOMA
DEDICATED TO
ASMA'U ABUBAKAR MUSA (JASMINE)
GARGAƊI
HARAMUN NE A SARRAFA MIN LITTAFI TA KO WACE HANYA, BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE KU KIYAYE.
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)
Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu masu nazari da aiki da ilimi burin kungiyar a koda Yaushe shine ta faɗakar ta kuma wa'azantar ta nishaɗantar da masoyanta
____________________
PAID BOOK, FREE PAGE
ZAKU TURO 500 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 2294023532 UBA BANK AMINA ABUBAKAR, KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER *** WANDA BASU DA ACCOUNT SU TURO HOTON KATIN 500 TA WANNAN NUMBER ***
PAGE 09
...Kokawa muka fara ina kokarin kwatar kaina ganin za a aikani lahira, Tamkar yadda ruwan sama ke daukewa haka komi ya tsaya cak! Sakina da akayi kasa ta yi daidai da dawowar wutar dakin. Numfashi nake mayarwa tare da shafa wuyana da nake jin kamar sawun hannu Kofar falo da aka bude ce ta sakani sake zabura zan gudu, Bilal da na gani ya sakani dakataw ko kallo ban ishe shi ba ya fada ɗaki na kuwa bi bayan sa ina mai sannu da zuwa. In bango ya tanka to Bilal ya tanka, sai ma fadawa da ya yi saman gado ya na mai kara wayarsa a kunne. Irin Fara'a da hirar da suke ita ta tabbata min da Hawwa ya ke waya, idona rufewa ya yi a fusace na fizge wayar tare da kwaɗata da ƙasa ta yi kwatsa-kwatsa Tamkar wanda aka harbo haka Bilal ya yi kaina jibgata ya ke da belt amma ban da mu ba domin burkina ya cika Na fasa wayar. Ganin da gaske kashe ni ya ke kokarin yi ihu na fara ko mai gadi zaiji ya kawomin dauki amma shuru. A guje na yi hanyar fita sai dai kafin in fita ji nayi ya yi kwadani da kasa kaina ya hadu da bango ji ka ke ƙum! Taurararin azaba na fara hangowa a daddafe na miƙe ga goshinta da ke min azabtar ciwo, hannuna da na ji ya fara fizgata na fara kokarin riƙewa amma ina a wannan karon ma na kasa control dinshi. Bilal kuwa dukawa ya yi da nufin cafkoni sai ji na yi hannuna ya kai ma wuyarshi cafke, kokarin kwacewa ya fara amma ina ji nayi na daga shi sama kafafunshi na wutsilniya a sama. Ihu na fara ina kiran sunashi ganin hannuna zai yi kisan kai, numfashin shi na ji ya tsaya cak! Tashin hankali na ninkuwa ya kara yi fiye da dazu ganin ya fado ba ya motsi. Girgiza shi na fara yi ina kira sunan shi gani wannan ba zai fissheni ba miƙewa na yi a guje zan kira mai gadi, gani na ne ya dauke na fara ganin dishi-dishi daga nan ban sake sanin mike faruwa ba.
Hasken ranar da ya shigo ta tagar dakin ce ya haske fuskar Bilal zumbur ya mike ya na kallon in da ya ke, gefen shi ya kalla Huda ce a kwance da sauri ya matsa kusa da ita yana kiran sunanta. Buɗe ido ta yi sai dai abinda ta yi tozali da shi ne ya sakani ja da baya ina mai saka tafukan hannu na rufe ido na ina mai kiran suna Bilal. Shi kuwa ganin ina ja da baya mamaki ne ya kama shi tare da yin kaina, ƙarin zaki mai dauke da haƙora zaƙo-zaƙo na ga ya nufi inda nake a tsorace na mike na fice a guje ya mara min ba. Muryar shi na ji yana fadar mai gadi ya rufe kofar, ka bude min in fita zaki ne ya biyo ni "kar ka kuskura ka bude kofar nan, in ba haka ba ka yi ta bakin aiki ka" ya karasa maganar tare da fizgoni ya dauke ni da lafiyayyan mafi "ashe ba ki da hankali? A haka za ki fita ba bu hijabi" Fita zanyi yau sai na bar gidan nan tunda ba gidan Ubana bane, dududu wata daya da sati da auren mu amma ka canza kana kokarin rabani da rayuwata na gaji, na karasa maganar tare da fashewa da kuka. "Huda ni ne zan kashe ki, mi kika yi min da zan kashe ki" kukan da nake ne ya tsaya cak! Har ka manta bugun da ka yi min, Bilal na gaji da renin wayonka "haba Huda, nasan ba ki min karya amma mi yasa yau kike fadar abinda ke ma kinsan ban aikata ba" Wallahi gida zan tafi na karasa maganar tare da rugawa da gudu ina kuka. Duk yadda ya so ya shawo kanta ina yi ta yi kamar ta hakura ya na shiga Toilet ta zari hijabi ta bar gidan. "Huda lafiya na ganki da sanyi safiya, mi nake gani a fuskarki haka?" Umma zai kashe ni kullum sai ya min duka na gaji da auren na, ku bar shi ya auri zaɓin mahaifiyar shi ni dai bazan koma ba. "Karya ki ke Huda! Ba zaku zubarmin da mutumci ba, maza ki ta shi ki koma inda kika fito aure kuma da kike fadar zai kara mace hudu aka yarje ma shi ya yi.'" haba don Allah! Ya ka ke abu tamkar ba kai ka haifeta na, ya sa me ta ya jibga kuma ta zo gida ma ba zata huta ba" "kiyi min shuru kafin in dauki mummunan mataki a kanki, ke ma ba ki wuci in miki abokiyar zama ba bare kuma mijin huda da ya ke matashi" "Alhaji Kishiya! Yau yau ni Malika na shiga uku! Huda ki tattara ki koma gidanki ba za ki janyoyin baka'i ba ina zaman zamana da mijina" "in kika bari na fito na iske ki zan shayar da ke mamaki, ke kuma muddun ki ka bari auren yarinyar nan ya samu matsala ke ma sai kin tafi gidanku" ya karasa maganar tare da shigewa daki. "Ki ta shi tafi zan turo Kubra da Zainura ki tafi kada ya fito ya iske ki" rufe bakinta keda wuya na hango shi ya fito da zabgegiyar bulalar da ya ba mu kashi da ita ranar bikina, a guje na yo waje "mai gadi rufemin kofa kada ka bari ta kufce maka" jin abinda ya faɗa ya sakani kara kaimi ina zuwa na yi sama da mai gadin na dai ji karar faduwar shi ni dai tunda na kubce ban tsaya da gudu ba sai da na zo bakin titi.
Bayan fitowar Bilal sai da ya bincike kaf gidan amma ba bu Huda a rikice ya ke tambayar mai ko ta fita "Bayan shigarku ciki ta zo ta wuce ina mata sai ta dawo ko amsawa bata yi ba" dafe kanshi ya yi "Shikenan sai da ta tafi gidansu" ya fada tare da fiddo makullin mota. Ya na karya kwana ya hango ta cikin keke napep tana faman share hawaye, ko kallon inda ya ke bata yi ba sai da aka sauketa kofar gidan. Da gudu-gudu ta shiga gidan ta fada daki tare da maida kofa ta rufe, rokon duniya ya yi amma ta ƙi budewa. Shurun da ta ji ya yi ne ya sakata bude kofa sai ji ta yi ya afko dakin yana huci. "Yaushe reni ya fara shiga tsakani na da ke?" Shuru na yi don har ga Allah yanzu tsoro ya ke bani. "Na ce yau she muka fara yar haka da ke, shi ne za ki fita ba tare da izinin na ba" ka yi hakuri karo na farko da na fara ba shi hakuri. Shuru na ga ya yi tare da dafe kanshi ya koma gefen gado " Huda kinsan ina sonki ba zan taba dena sonki ba har karshen rayuwata, in muna tare ji nake kamar ba ni ba tabbas wani bakin lamari nake ji yana samu na da zarar na bar gidan nan sai in ji komi ya dawo min normal" Kuka na ji ya kubcemin don nasan wannan duk makircin Hawwa ne. A ranar rikici bai kara hada mu ba sai ma nan-nan da ya ke yi da ni har wayewar gari, shaidamin ya yi in yi abinci da yawa yau zamu je mu gaida Hajiya in ya dawo da azahar Ba musu na hada abinci mai rai da lafiya muka nufi gidan ta, banyi mamaki ba don in da sabo na saba da rashin samun tarbar arziki a wurinta. Abin mamaki tunda muka je banga Jidda da Hawwa ba ki ina suka je. Abinda ya kara bani mamaki shine mutane da na gani dangin Hajiya kusan su goma a gidan. Ba mu baro gidan ba sai bayan isha'i tun a mota muka fara fada ganin kiran Hawwa ya shigo wayarshi. Ban tabbatar da ba ya a cikin hayyacinsa ba sai gani na yi yana kokarin bude mota ya watsoni waje, da kuka na nake rokon shi da kyar na samu ya amince in shigo motar sai dai har muka karasa gida waya ya ke da ita. Kiran Zainura ne ya shigo wayata ta ke sanar da ni gobe suna nan shigowa ita da Anti Kubra. Daren ranar ban iya tsuntsawa ba don da na rufe idona zan bude. Tunda asuba na ga ya shirya cikin sabon dinki ya sha babbar riga ya fi ce ba tare da ya ce da ni uffan ba, ban damu ba don in na tanka nasan ba rabuwar mutumci za muyi ba. Kofar da na ji a na bugawa tamkar za a karya ta ta sakani miƙewa, su Zainura ne suka ƙaraso lallashina suke tare da nake min wasu magunguna da aka amso min. Motsin da na ji a kuryata ne ya sakani miƙewa tamkar wadda aka tsunkula na shige dakin rufe kofar da na yi ta yi daidai da daukewar hasken dakin ya koma duhu dunɗum ko tafin hannunka baka iya gani...