FreeArewaPen original
BAYAN AURENA
- 1views
- 23chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
FATALWA BAƘAR TAFIYA SAKACI SALMA RAZANI WANI ƘARNI RUWA BIYU ƘULLALLIYA
Sample · Page 1
BAYAN AURENA©️MEENAT A 'YANDOMADEDICATED TO ASMA'U ABUBAKAR MUSA (JASMINE)GARGAƊIHARAMUN NE A SARRAFA MIN LITTAFI TA KO WACE HANYA, BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE KU KIYAYE.MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A) Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu masu nazari da aiki da ilimi burin kungiyar a koda Yaushe shine ta faɗakar ta kuma wa'azantar ta nishaɗantar da masoyanta____________________PAID BOOK, FREE PAGEZAKU TURO 500 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 2294023532 UBA BANK AMINA ABUBAKAR, KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER *** WANDA BASU DA ACCOUNT SU TURO HOTON KATIN 500 TA WANNAN NUMBER ***PAGE 01…Tamkar an wullo ni daga motar haka na fito ina ya mutsa fuska, ba shakka Bilal ya cika mara mutumci. Ashe da gaske ya ke a gidan kanwarshi za a yi kamun aurena? "Lale maraba sannunku da zuwa gidan karama gidan da ya yi bankwana da talauci ya kulla alaƙa da arziki. mi za ku ci akwai komi a wadace don na fuskanci kamar da yunwa ku ka shigo" Murja Kanwar Bilal ta karasa maganar tana turo kallabi gaban goshi. "Kama kanki malama! Ke ko sutturarmu ki ka kalla kinsan mun fi karfin a ganmu a ce muna tare da yunwa. Ko da ya ke na miki uzuri mutanen da suka kasa kama Hall na yi ni guda in ai zasu iya komi" Zainura ta karasa maganar a fusace. "A hayye nanaye! Ku fahimci wani abu ba wai kudin ne babu ba mana nuna maku iyakarku ne domin ba ko wace mace ba ce ta kai a kashe mata kudi, ke bari in fito maki a mutum mace da takai ita ake ma ɓarin kuɗi" "ƙarya kike Murja, ke kinsan in banda ƙaddara ba bu abinda zai saka Huda auren Bilal. Maganar mace da takai Alhamdulillah! Huda ba ɗiyar mace ba ce bare ku ce bata da tarbiyya" Rufe bakin Anti Kubra ƙasar Umma. A zafafe Murja ta ɗora daga inda ta tsaya "Kada ki ce za ki zagi Mahaifinmu da ke kwance a kasa, ku in banda na ci na Bilal da kuma ƙaddara mi ake da irin ku, in ba dan mace ne to ta gani ta likemai" Mukhtar Abokin Bilal ne ya fito ya na bada hakuri da kyar kowa ya nemi wuri ya zauna, Murja ta ja tawagarta suka yi ciki" "yanzu ke Huda tun kafin ki shiga daga ciki kin fara fuskantar haka ina ga nan gaba? Ni fa dama can ba kaunar shi na ke ba tunda na lura danginsa 'yan hau ne" Zainura ya zanyi? Ina ma Bilal wani irin so ta yadda in ban aure shi ba ina iya rasa rayuwata. Ni nasan shi din ƙaddarata ne. "Ai kuwa Allah ya rabamu da irin wannan mummunar ƙaddamar, ina amfanin dangi irin na bilal. " Anti Kubra ta faɗa a zafafe. "Ni anti Kubra da nasan wannan cin mutumcin zai mana wallahi da na kama mana wata event Center mai kyau, babban bakin cikina don su wulakanta mu ji wani ɗan iska mai Dj da suka kira ni fa na rena kayan aikin shi" "Ke ta Dj ki ke ni babbar damuwata Bilal bai iso ba har yanzu" suna rufe baki suka hango shigowar motar ango, hade fuska suka yi tamkar ba su taba dariya na. Ganin haka...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.