JADEEDA

Page 29

by @cwtsumiey19988

Part 29

Zazzau ne su ke a cikin Parlon  ,kowa cikin su fuskarsa a sake ɗauke da haiba da kuma natsuwa,Alaranma Sama'ila,Kawu Salihi,Kawu Musa, Kawu Kabiru dama,Baba ƙarami da sauransu dai, duk nan suke zama idan ya kasance  babu karatun da za a gudanar tsakanin sallahr Magriba da kuma Isha'i,"Ya maganar tafiyar ta ka ina fatan ka shirya ma ta ,domin na ga tafiyar kamar ta ƙara so", cewar Baba ƙarami.
   "Eh Abba na shirya da so nai ma in yi zamana a can Abujan har zuwa lokacin da za ai taron sai kuma na samu saƙon sun maida taron Lagos shiyasa na dawo in ɗanyi ƴan shirye-shiryen da zan yi kafin in wuce","Ya Salam kace tafiyar ta ƙara yin nisa kenan?", Alaranma Sama'ila ya tambaya,"Eh wallahi Kawu haka tafiyar ta koma duk sun canja wasu abubuwan".
    Kawu Salihi ne ya tambaye su da cewa  "A'aha tafiya ce ta kama shi ne zuwa wani wajen"."Eh tafiya ce ta kama shi na manta lokacin da mu ka yanke hukuncin wakilta shi a tafiyar baka nan,amma kamar ai nasa a kira ka ayi maka bayani ko,kan taron Manyan Malamai domin samun haɗin      kan mazhabobi da za a gudanar a Abuja to ka ji ashe an maida shi Lagos","Af Af na tuna munyi maganar da kai kuma bayan haka na samu labarin gurin wani Abokin kasuwanci na a can Jigawa","Yauwa to tafiyar ce ta taso,ina tunanin saura kwana biyu ma tafiyar".Nan dai suka cigaba da tsara yanda za su yi tafiyar da kuma ƙarin shawarwarin da zai amfana da su, shigowar Baba Malam tare da Alƙasim nan su ka sake dawowa da zancen farko,daga ƙarshe kuma suka koma tattaunawa akan lamurran cikin Gida da na kasuwancin su.
      Sai bayan da suka gabatar da da Sallahr Isha'i sannan ya fara shirin tafiya Gidan shi,ya shiga cikin Gidan domin yi ma su Sallama,Momy Hibba ta ce da shi,"Ina Mai Gidan nawa ya ke na ga ka fito ba tare da shi ba,ko nan zai mana kwana",sai ya ɗan haɗe ransa kafin ya ce,"Momy yana wajen Ummiey,kuma ina ga ya dawo nan da zama sai ko zuwa wani lokaci ko da zai koma",itama ba ta kuma ce masa komi ba sai sauke ajiyar Zuciya da ta yi ,kafin kuma ta fara cewa da shi,"Ka yi haƙuri yana daga cikin jarabtar ka, bawa kuma baya tsallakewa ƙaddarar sa,zamu yi maganar ni da Ummiey Maryam kome kenan zan sanar da kai mai yiwuwa za a iya samun maslahar wannan lamarin","To Momy ina godiya,bari in zo in tafi dare na ƙara yi dama zuwa na yi in maki Sallama,Kuma ina son in iske Ummiey kafin tai barci","Okay to Shikenan Allah ya tsare a gaida mutanen Gidan mu ma zuwa goben za mu shigo mu ga mai jikin",da haka yai mata sallama ya nufi wajen Mahaifiyarsa .


~~~~~~~~~~~


"Momy Allah ba na son tafiyar nan jikin ki har yanzu bai koma normal ba,ina tsoran kar wani abu ya same ki bayan ba na nan",sai da Gloria ta tashi zaune da ga kwance da ta ke kafin ta ce,"My Daughter bai kamata ki yi loosing this opportunity ɗin ba,ba kowa ke samun ta ba taron nan yana da matuƙar muhimmanci a gare kin ga ba kowa ke samun wannan babbar damar ba,don haka za ki je wannan taron i promise to you babu abinda zai faru da ni har ki je ko dawo for the sake of father lord".
      Rau-rau Jadeeda ta yi da idanunta hawaye na son zubowa daga ciki "Kin ga matso kusa da ni,Papa ɗin ku kan shi ba zai ji daɗi ba in ya ji cewar kin fasa attaiding ɗin wannan taron,manyan mutane ne fa suka gaiyace ki,kuma ta hanyarsa ,to me zai sa ki watsa masa ƙasa a ido",haka dai ta cigaba da lallashinta har ta samu ta amince da za ta yi tafiyar,"Wai ina Edwin tun safe da ya shigo ya gaishe ni ban sake jin motsin shi ba ?",Min ta tambaya,"Ba ya wuce Room ɗin shi domin na ga motar shi babu inda ya je","Yana ɗaki kwance?,me yake damun shi wannan ba ɗabi'ar shi ba ce,to ko dai ba shi da lafiya ne ?","Momy ni dai ban sani ba amma Ni kaina na yi noticing sauye-sauye daga Brox Edwin,ya keɓe kan shi,bai cika shiga cikin mu kamar yanda ya saba,ba tsokana ko barkwancin da ya saba jan mu da shi,shi kaɗai kawai ya ke rayuwarsa,ko abinci ba ya ci tare da mu,a Room ɗin sa ya ke komi shi kaɗai".
     Shiru Madam Gloria ta yi,kafin daga bisani ta ce da ita,"Je ki ki gani in ya na cikin ɗakinsa and call him for me",ba tare da Jadeeda ta ce komi ba ta nufi Room ɗin Edwin,tun kafin ta ƙarasa shiga ta fara jiyo hayaniya daga cikin dakin ana cewa,"Guy kar ka bari wannan maganar ta zama dalilin da zaka sanya rayuwar ka a cikin haɗari say it out,ka fito fili ka sanar da abinda ke damun ka,ka na aikata kuskure ne fa,zurfin cikinnan ba abinda zai haifar maka da shi inda ka sake jefa rayuwar ka cikin wani sabon haɗari"....."Joseph baka da hankali irin wannan maganar ka ke ikirarin in fitar da ita,You Are Mad Ina tunanin ka samu matsala".
    "Kai ne dai ka ke da matsala amma ba ni ba,kuma za kaga ne hakan nan gaba,ni ba zan iya cigaba da kallon kana cutuwa ba,in har ba za ka fito fili ka sanar da ahalin ka abinda ke damun ka ba ,ni zan sanar da su",a firgice ya ɗago yana kallon sa fuskar shi cike da mamakin abinda kunnuwan shi su ka jiye masa,sai da Edwin ya kwantar da zuciyarsa kafin ya ce da shi,"Ka ga Jesoph ka fahimci ni ,komi na rayuwa family first bai kamata saboda wani buri nawa in sa family na cikin damuwa da tashin hankali ba,zan bi komi a hankali,okay dan haka bar min komi a hannuna".
   Kasa haƙuri Jadeeda ta yi sai ganin ta su kai a tsakiyar su,a ɗimauce Edwin ya miƙe tsaye,ya na mai nufo inda ta ke gami da kama kafaɗunta tare da cewa,"Jadeeda yaushe ki ka zo,a dai ki daɗe da zuwa ba ko,ina fatan baki ji komi gane da abinda muke tattaunawa ba ?",sai da ta zuba mashi idanunta kafin tace,"Ni ban ji komi ba,kuma yanzu na zo,Momy ce ta aiko ni ta ce ka zo tana san ganni ka","Na ji ganinan zuwa amma kafinnan ki tabbatar min da cewar ba ki ji komi dangane da hirar da muke tattaunawa ni da Abokina ba",saɓule hannun shi daga kafaɗar ta tayi kafin taba shi amsa a taiƙaice da cewa,"Ni banji komi ba",tana kaiwa nan ta bar mi shi Room ɗin gabaɗaya,kasa iya zama yai sai bin bayanta da yai cikin sauri da azama.
      A tare su ka isa inda Madam Gloria ta ke zaune,suna shiga suka iske Papa da Uncle Richal sun dawo daga sabon shopping Mal da aka buɗe ma Uncle Richal domin san hana shi komawa ƙasar da ya baro.
    "Lafiya ku ka shigo kamar an biyo ku",Papa ya tambaya yana mai bin su da kallo.
     Cikin rawar baki Edwin ya tari numfashi sa da cewa,"Papa ba komi Momy ce ta aike ta ta kirani"ya bada amsa a ɗarare.
,"Zo nan Edwin matso ka zauna kusa da ni",jikinsa a sanyaye ya isa kusa da ita ya zauna,da ganinsa kasan ba a dai-dai ya ke ba.
      "Edwin my son me yake damun ka ,da ganin ka akwai wani abu da ka ke ɓoyewa a cikin zuciyar ka",Madam Gloria ta tambaye shi,inda-inda ya fara kafin ya samu ya natsar da kan shi ya bata amsa,da cewa,"Momy ni ba abinda yake damina,ina tunanin gajiyar tafiya ce","Gajiyar tafiya kuma tun yaushe ka dawo almost a week,har yanzu ba ka huce gajiyar tafiyar ba?,a komi fa ka ware kan ka,ko saukowa ka kaci abinci da Familyn ɗin ka ba ka yi hakan duk gajiya ne",Momy ta sake jefa masa wata tambayar.
     "Momy i swear gaskiya na faɗa ma ki,yanzu haka ina tare da friend ɗina ne Joseph"....."Momy Allah da abinda ke damun shi,kawai dai ba zai faɗa ba ne ba,ni na riga da na san da haka tun kafin ya dawo ".
    Papa ne ya maida hankalin shi akan sa tare da cewa,"Fill free my dear son nan duka Familyn kane ka faɗi duk abinda ke damun ka we will sort it together,ba wai kai kaɗai abun ya shafa ba ,duka damuwar mu ne",duk wannan bayanin da Papa yake Edwin baya tare da shi,gabaɗaya hankalin shi,idanun shi da kuma tunaninsa nakan Jadeeda,zuciyarsa na gaya masa tabbacin ta saurari tattaunawarsa da friend ɗin sa.
      "Edwin kana ji na kuwa",Papa ya faɗa da ɗan ɗaga murya,hakan ne ya yai gigita shi tare da cewa,"Eh Papa zuwa anjima ma zan amso sauƙon",cikin mamaki Papa yace,"Saƙo kuma wa yai maganar saƙo anan?".
    Har Momy ta buɗe baki za ta ce wani abu Uncle Richal ya dakatar da ita tare da maida hankalin shi kan Edwin yace dashi,''Ka ga tashi ka tafi je ka wajen Friend ɗin naka ba damuwa",....Momyh tari numfashin shi da cewa,"Amma Richal taya za sallame shi alhalin ana irin wannan maganar mai girma da kuma muhimmanci","Sister bai kamata ku turken shi anan kusa lalle dole sai ya faɗa maku damuwarsa ba,mai yiwuwa lamarin bai kai yanda ku ke tunani ba,may be yana jin zai iya dai-daita komi, Edwin fa ba yaro ba ne ya mallaki hankalin sa bai kamata irin haka nashiga tsakanin ku ba,idan lamarin ya kai lamari bani tantama zai sanar da ku",da wannan bayanin Edwin ya samu ya sulale daga cikin su.
    "Richal ba ka fahince ni ba, dole sabon halin Edwin ya taɓa kowa a cikin Gidannan,kalli fa raha da wasannin da yake duk ba ya yin su kullum jikin sa a sanyaye,haba abun da rikitarwa gami da tsayawa a cikin zuciya da rai","Na sani Sister amma ba ta irin wannan hanyar ya kamata mu bi domin gano damuwarsa ba,hakan ka iya creating wata sabuwar matsalar",shiru su duka su ka yi kafin Papa ya ce,",Kuma fa maganar ka gaskiya ce,to amma yanzu ta wacce hanya zamu yi amfani da ita domin mu gano asalin abinda ya ke faruwa da shi","A bibiyi lamarin shi,ku sake ƙara janyo shi a jikin ku,inda halima a daina barin sa shi kaɗai".
      Nan dai su ka amince da shawarar da Uncle Richal ya kawo, sannan su ka cigaba da kawo wa su hanyoyin daza su yi amfani da su duk dan su ga sun kai ga gaci akan abinda su ka sa gaba,hatta da maganar tafiyar Jadeeda zuwa Lagos sai da suka yi daga ƙarshe Uncle Richal da kan shi ya ɗauki Jadeeda su ka nufi sabon shopping Mal ɗin sa ya zaɓa mata duk abinda ya tare masa gaba,hatta da kayan da za ta sa in ta isa Lagos shi ya zaɓar mata,komi ya gani in har ya ga zai mata kyau to sai ya ɗaukar mata wasu kayan ma set guda yake samata, choculate ba'a magana,haka su ka dawo da kaya niƙi-niƙi.