JADEEDA

Page 34

by @cwtsumiey19988

Part 34
Hango ta nufo inda ta ke ne,yasa zuciyarta ƙara karyewa a hargitse taƙaraso inda take,tana mai raɓa ta a jikinta,tare da cewa,"Sis me ya faru  da ke,daga ina ki ke,shin kin haɗu da Roberys ne akan hanya",kai kawai ta iya girgiza mata ba tare da ta furta mata komi ba,jikinta ta taɓa ta gami da taimaka mata su ka shiga cikin Room ɗin na ta,"Jesus Christ kar dai ki ce min abinda yasa me ki a cikin Hotel ɗin nan ya same ki,ina securityn hotel ɗin su ke?",Ruth ta faɗa a rikice,zaunar da ita tayi a kan wata seater bayan ta gyara mata ita yanda za ta ji daɗin zaman a kanta ,cikin gaggawa ta fara duba jikinta ,ta na mai tambayar ta ba abinda ya faru da ita,"Hey Jesus wannan wanne irin tashin hankali ne haka,jini fa na ke gani anan ,oh father lord waɗanne mahaukatan ne suka shigo miki har cikin Room su ka aikata maki irin wannan rashin imanin,okay okay kamata yai in natsu,in san me ya kamata in taimaka mi ki da shi, ko dai tashi za ki in kai ki Hospital in ya so in muka dawo sai mu yi reporting ɗin case ɗin,domin lafiyar ki na gaba da komi,wai  su ***** su ka aikata maki haka,kuma har su nawa ne ?",
Cikin sheshshekar kuka,muryarta ɗauke da zallar tsora,gami da razani ta ce mata,"Fredrick ne ya shigo min","...Mene Fedrick ?",Ruth ta tambaya cikin mamaki,da kanta tai tayi amfanin wurin yi mata comprming ɗin zancen da ta gaya mata
"Ko da yake   me yasa tun farko ba ki kira Resfetion kin sanar da su ya ake ciki ba, sai ki zauna ya illata ki a banza a wofi","Na rasa mafita Ruth,gabaɗaya a ɗimauce na ke ,ya rufe duk wata hanya da zan nemi taimako, babban abinda ya tsaya min a rai ta yanda ya shiga Room ɗin,na rasa gane ta yanda akai hakan ta faru", Jadeeda ta faɗa ta na mai ƙanƙame jikinta da zazzaɓi ya fara rufe ta," Ah abun a bayyane ya ke ,da sa hannun wani a cikin faruwan haka,dan haka bari in kira Hotel Manager idan mun ga hakan bai yi aiki ba,sai mu yi reporting wurin Police",..."A no kar ki kira su I'll handle it,tunda dai ba abinda ya faru da ni,na gode ma Allah","Kamar ya ki na nufin a bar maganar,kenan Fedrick ya ci banza akan duk abinda ya aikata ma ki,kin kuwa san illar da hakan za ta haifar maki anan gaba ba,idan ba dan Jesus ya aiko wancan mutumin ba da yanzu ba wannan labarin ake ba".
     Zaune Jadeeda ta tashi,"Bari ina zuwa",ta faɗa muryarta can ƙasa ta na mai nufar hanyar fita,ta na tafiya ta na rangaji,"Jeeey ina zaki a cikin irin wannan halin bai kamata ki fita ba",Ruth ta faɗa ta na mai son tare ta.
   Sai da Jadeeda ta dafa bango kafin ta ce da Ruth"Zan je wurin sa ina son in yi mashi godiya,daga nan kuma in duba hanunsa ,domin sanda ya tafi yana zubar da jini,kar wani abun ya same shi,da buƙatar in ga halin da ya ke a ciki".
     "A'a ki yi haƙuri ki bari sai zuwa da safe yanzu dare ya yi kuma  kina buƙatar hutu",......kasa tsayawa Jadeeda tai ta saurareta ta cigaba da tafiya ta na rangaji gami da niyar faɗuwa,a haka har ta isa bakin Door ɗin ta fara Knocking,Ruth na biye a bayanta ta na taimaka ma ta a duk sanda taga ta na niyar faɗuwa, kasa iya haƙuri tai ta cigaba da knocking ɗin akai-akai,sai da su ka ɗan ɗauki lokaci kafin ya zo ya buɗe ma su.
"Kkk....ki..kkk .ka zo mu je Hospital karda jinin ka ya ƙare wani abun ya same ka,in wani abu ya same ka ba zan taɓa iya .....",ta kasa iya idasawa sakamakon tafiya da tai luuuu za ta daɗi,da sauri ya tarota,yana girgiza ta gami da tambayar me ke faruwa da ita,cikin hanzarin ya shigar da ita ciki domin ya bata taimakon gaggawa, Allah ya taimake su cikin ƙanƙanin lokaci ta dawo cikin hankalin ta,dama sakamakon  buguwar da ta yine,a sanda ta faɗi kanta ya bugu da tyle.
    Idanuwanta ta fara buɗewa ganin ta da ta yi kwance a kan bed ɗin ta kuma a bedroom ɗin ta yasa tai saurin tashi zaune gami da fara waige-waige don son ganin ina saviour ya ke,"Ruth ina ya ke ba dai kin bari ya tafi ba tare da na yi masa godiya ba ?",ta ce ta na mai dafe kanta.
     "A'a bai tafi ba ya je ya siyo maki maganin da za ki sha,ko kya samu ki samu ƙarfin jikin ki".
     "Ni fa ina lafiya shi ya kamata ya je a duba shi,domin jinin shi na zuba kar wani abu ya same shi","Kin ga ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru da shi,tuni jinin ya bar zuba,don haka ki natsu,idan ma baki yarda ba ki jira yanzu zai dawo in ya sosai ki gani da idanun ki".
    Suna cikin wannan batun sai ga shi ya shigo hannunsa ɗauke da ledar magungunan da ya siyo,"Ya jikin na ki fatan ba kya jin wani ciwo a jikin ki,baya ga ciwon kan ?",ya tambaye ta"Ba na jin komi ya hannun na ka an yi treating ɗin sa ko","Ina lafiya tuni na yi treating ɗin wurin,don haka don't setress you self,ki na buƙatar hutu",da kai ta ba shi amsa ,nan yai mata ƴan allurorin da zai mata ya ba Ruth magungunan ta bata kafin yai masu sai da safe ya ya tafi,bayan ya jaddada masu da sun ji wani motsin da ba su yarda da shi ba su kira Receiption su sanar da su.

Tun da ya fita Sallahr Asuba bai dawo ba kai tsaye ya wuce    labrary da ke nan kusa da su  don yin wani research, Jadeeda kan jikin ta da sauƙi sai ɗan abinda ba za a rasa ba,tun da ta tashi ta ke fama Zarya ƙofar Room ɗin sa,tun a zuwan ta na farko ta tabbatar da baya ciki,amma duk da haka ta kasa iya haƙura da zuwa.
       "Jeeyyyy ya kamata ki sahale ma kan ki wannan zaryar ,tun ɗazu ki ke faman zuwa bayanan,zai fi ki  zauna ki huta"....." Ruth ba za ki gane ba,so na ke in mashi godiya,in masa sallama ba zan so in tafi ba tare da na sake ganin sa ba,ko kin manta Flight ɗina zai tashi around Eleven ,Amma yanzu har past ten ,ta ya hankali na ba zai ta shi ba,rayuwarsa fa ya sa a cikin haɗari saboda ceton tawa rayuwar,don haka kin ga kenan ya na buƙatar girmamawa, sadaukarwa ko ma fiye da hakan".
    "Na sani mana ya yi deserving duk abinda ki ka faɗa amma ko ba komi ki zauna ki huta har yanzu ba ki gama komawa normal ba","Haka ne Ruth amma ki sani in naga condition ɗin da ya ke a ciki ne Zuciyata da ruhina za su samu salama da hutu amma yanzu cikin raba ɗaya biyu ni ke,ki sani ko da missing ɗin Flight ɗin nan na yi ba zan ji komi ba","Ba za ki missing ɗin Flight ɗin ki ba domin tafiyar ki tafi cigaba da zaman ki alkairi domin ba mu san abinda ka iya faruwa anan gaba ba,don haka ki sama ranki zaki tafi Abuja yau kuma shi ma za ki gan shi har ki isar ma sa da saƙon da ke ɗauke a cikin zuciyar ki,wai Jadeeda ba ki mamakin taimakon da wannan Musulum preacher yai maki ba,duk da kasancewar kuna da mabanbanta addini,da kin gan shi kin ga kamala da natsuwa a tare da shi,amma ba ruwan shi ya shiga cikin lamarin da bai shafe shi ba duk dan ya taimake ki".
    "Ruth kenan ai dole abinda ya tsaya min a rai kenan,ko kin san ba wannan ne gani na da shi na farko ba","Kamarya dama kin san shi ne?","Yeah na san shi,shine Special Doctorn da ya duba Momy last jinyar da tayi wanda na ke baki labari,he is so kind and humble, maganar shi akwai natsuwa,tafiyar shi akwai natsuwa,shigar shi akwai natsuwa ke impact komi na shi akwai natsuwa a ciki,kar ki so ki ga jajurcewar da yayi akan lamarin Momy shiyasa na ke son in Jaddada masa godiyata kafin in bar Garin Lagos,shi mutumin kirki ne,ba zan ɓoye maki ba zuciyata ta ba shi wani matsayi mai girma a cikinta,ban yi tunanin samun taimakon Jesus daga wurin wani musulmi ba,sai ga shi ya shigo cikin lamarin ya ɗauki lamarin ,ya ɗauke shi tamkar ƴar'uwar sa ya riska a cikin irin wannan halin".
      "Irin haka na faruwa,akwai mutane masu halin kirki irinsa a mabanbanta wurare a faɗin ƙasarnan,don haka ki ɗauke shi a matsayin ɗan saƙo daga Jesus domin ya ce-ce ki a hannun Fedrick".Haka suka cigaba da tattauna batun har ƙarasowar time ɗin tafiyarta.
       "Sister Jadeeda da alama dole za ki haƙura ki tafi ba tare da kin samu haɗuwa da shi ba","A'a No ni ba zan iya tafiya ba","A'a Jadeeda kar ki yi jayayya da ni akan wannan maganar domin na fiki gaskiya,ba famu san abinda ka iya faruwa a yau ko gobe ba,dan haka ki tashi mutafi,in yaso ko saƙo ne sai ki bar masa a Receiption ","A'a Ruth ba zan iya tafiya ba",....."Dole ki tafi Jeeyy idan kuma kin nace akan ba zaki tafi ba,zan kira Papa ko Momy in sanar da su abinda ya faru",a ɗan dame Jadeeda ta kalle ta tare da cewa,"Haba Ruth don me za ki faɗi haka"..."To ki yarda ki tafi a yau tun jiya ki ka ɓata zancen da kin yarda an yi Reporting case ɗin da ba haka ta faru ba,yanzu fa a kodayaushe Fedrick zai sake dawowa,idan kuma kin ce za ki dawo apartment ɗina nan ma ba tsaro domin,Fredrick ya fi samun lasisin shiga cikinsa fiye da nan".
   Haka ba dan Jadeeda ta so ba suka fara shirin tafiya,Ruth na  jaye da  ɗan ƙaramin trolyn, Jadeeda kam jiki duk yai sanyi komi ta kasa,sai Ruth ke komi da kanta,a Receiption su ka tsaya bayan sun yi Checking Out, Jadeeda duk ranta bai so ba haka ta ke komi.
    "Ruth please mu ɗan ƙara jira ko na wani gajeren lokaci ne,ina ji a Zuciya ta kamar yana gab da dawowa","Haba Jadeeda mun fa jima mu na jiran shi,kar hakan ya sanya lokaci ya ƙare ki yi missing Flight,hakan ma wani sabon matsalar zai haifar".
   "Ruth na roƙe ki just give some  minutes in har bai dawo a tsakanin wannan time ɗin ba na haƙura zan tafi kawai"."Just give ten minutes ko","Eh haka na buƙata ",gefe su ka samu gami da samun ɗaya daga cikin jerin kujerun da su ke a wurin duk zauna suna mai cigaba da zaman kurame gami da jiran tsanmani.
    Tun Ruth na duba wrist brace ɗin da ke ɗaure a hannun ta har ta koma kallon Jadeeda kawai,ta fidda rai yau ba makawa sai Jadeeda ta ƙara kwana a cikin Lagos ba tare da ta tafi ba,sai ga shi ya shigo cikin natsuwa da kamala ya nufi wurin Receiptioniss ɗin da ke kula da gun don amsar key ɗin sa,anan ya ke sanar da shi ana jiran shi.
Sai a lokacin ya waiga ya gan su a wurin farin ciki kwance akan fuskar Jadeeda,hannunta ta ɗaga ta na mai cewa,"Hy ya ka ke,ya hannun na ka ya keda fatan dai da sauƙin ?".
Sai da ya maido hankalinsa gaba ɗaya a gare su,kafin ya ce da ita,"Alhmdllh ina samun sauƙin,kar ki fa wani damu ba wani ciwo ne babba ba, zai warke nan ba da jimawa ba da izinin Allah".
     "Haka ne Doctor by the grase of God,tun ɗazu na ke ta faman jiran ka  na kasa tafiya saboda ina so in yi maka bankwana tare da miƙo ƙarin godiya ta a gare ka,don yanzu haka na kusa yin missing Flight ɗina,Bai fi saura 15mnt Flight ɗin mu ya tashi ba","Ah ba wani abu ki yi tafiya ki,ki manta da duk abinda ya faru,domin abinda ki ka ga na aikata ya zame min dole na ne,domin duk wani aƙili ya ga abinda ke shirin faruwa dake zai aikata fiye da abinda na aikata,sai dai ina son in shawarce ki,akan game da abinda ya so faruwar da ke,domin in kina ganin kin tsira a yau ba ki san me gobe za ta haifar ba, sannan ko ba dan ke karan kan ki ba,za ki iya ceton wasu matan daga faɗa wa cikin irin wannan masifar,ki nemi wani na ki ki sanar da shi ko kuma ki yi Reporting ɗin sa zuwa gurin Police",sosai ya bata shawarwari masu amfani a taƙaice.
    "Zan yi kamar yanda ka ce ba zan kyale jinin da Fedrick ya zubar maka ya tafi a banza ba,amma ina da tambaya guda ɗaya","Ina jin ki fadi kai tsaye ","Shin nan ma ka zo ne a matsayin Special Doctor kamar yanda ka je can Abuja".
  Sai da Imam Jaheed ya saki wani gajeren murmushi kafin ya bata amsa da cewa,"A'a ba na zo nan a matsayi na na Doctor ba ne,na zo ne kan taron da zamu gudanar wanda ya shafi Addini,ko da wata tambayar ya ce da ita","A'a babu saura kawai dai zan so in sanar da kai ba zan taɓa mantawa da irin taimakon da ka yi min ba,kusan zan iya cewa ka bani farin ciki a cikin sauran rayuwar da ta yi min ragowa,zan so wata rana nima in saka maka da wani abu mai girma anan gaba in mun sake haɗuwa".
   "A'a da ba ki ci wani dogon buri akan haka ba domin ni na aikata abinda na ke ganin ya dace ne ,Kinga kenan No need ace za ai reponding ɗina da wani abu ba".
   "Hakan ba wani aibu ba ne da shi,sai dai kawai zan yi fatan haɗuwata ta uku da Kai ta zama silar mai kyau ba irin wannan da ta faru ba","To Shikenan Allah ya amintar damu akan haka,sai wata rana"...yana kaiwa  nan ya juya da nufin barin wurin ita ma ta cire ƙafarta da niyar tafiya taji igiyar takalmin da ke sanye a ƙafarta ya kwance,hakan ya sa ta duƙa domin ta ɗaure,shi kuma a dai-dai lokacin ya amso key ɗin sa shirin nufar Room ɗin sa.
    Har cikin ran shi ya ji baiji daɗin ganinta a cikin irin wannan halin ba,sanye ta ke da bon short iya cinyarta sai wata riga da ko cibiyarta ba ta rufe mata ba,kasa iya barin wurin yai,ya nufi inda ta ke ya na mai cire coat ɗin da ke a jikin sa ya ɗaura mata a ƙugunta,ba tare da ya ce da ita komi ba ya bar gun,su duk biyun sakin baki su kai suna mai bin sa da idanu har yaɓace ma ganin su.....