JADEEDA

Page 37

by @cwtsumiey19988


Page 37

"Ah aha,ya na ga abincin haka  ba dai har ka ƙoshi ba,domin na ga kamar baka ci wani abin kirki ba", Ummu Nurain ta ce ta na mai bubbuɗe Food flask ɗin,ba tare da ya bar abinda ya ke ba ya ce da ita,"Na ƙoshi ne,ki haɗo min shayin Coffee na fi buƙatar shi a yanzu","Haba Abu Nurain duka-duka me kaci a cikin wannan abincin ,kuma tun ɗazu ina kula da kai gaba ɗaya hankalin ka ba ya kan cin abinci kafi karkata akan aikin da tun da ka shigo ka ke yinsa,na rasa wanne irin aiki ne da tunda ka shigo ka rungume system ɗin ka ko san ajewa ba kayi".
   "Ki yi haƙuri Ummu Nurain aikin ne ya zomin a ƙurarren lokaci,kin san gobe 28 to ina son in sallami duk wani ma'aikaci dake ƙarƙashi na ya ke kuma saran zai sami Albashin sa a Goben,kuma maganar abinci da ki ke,na ɗan ci wani abun ne kafin in shigo nan,zan fi son Shayin Coffeen a yanzu".
    Turo baki gaba Ummu Nurain ta yi gami da fara tattara kayan wuri guda,"Ka je can ka ci gurin wata ko,Hmmmmmm na rasa har sai yaushe komi na Gidannan zai dawo dai-dai,ita gata matar so ko",...."A'a Ummu kar ki ɗauki alhakin ta domin ba ki san gaskiyar abinda ya faru ba kuma abinda na ci ba daga gare ta ya fito ba","Ko ma daga wurin waye mi ba ruwa na domin kasan zan girka ma ka abinci ai,da wannan tirtsetsen cikin in tashi in ta fangan-fangan wajen ganin na girka maka abinci da za ka ci,sai ka ɗan yi Spoon da bai fi uku ba ka ce wai wani ka ƙoshi,ai ba adalci a ciki ,ai ko ba komi ko dan halin da na ke ciki ka ji tausayi na ka ci abinci ko ba dan in ji daɗi ba".
   Zazzaro idanu waje Jaheed yai ya na mai binta da kallo mai tarin mamaki,sai ya kalleta sai ya kalli flate ɗin da ya ci abinci ,shi dai a zahirin abinda ya ke gani a cikin plate ɗin ya ci kaso mafi yawa daga cikin abincin amma ga shi tana cewa wanda ya ci bai fi Spoon uku ba,ta na ankare da shi,har a cikin ranta tana cewa,ai baka ga komi ba sai na haɗa plan ɗin da zan dawo da ɗana gaba na ba tare da ka so ba,kana ji kana gani dole ka haƙura, "Allah ya baki haƙuri ba zan kuma aikata hakan ba",ya faɗa yana mai kama kunnensa",Af nasan haka za ka ce dama ai da Matar so ɗin ka ce ai ba za kai kuskuren aikata hakan ba balle" ......"Ya Salam Zeenat wai me yasa ba za mu taɓa zama mu tashi tsakanin ni da ke ba tare da kin ambaci sunan Gimbiya Ayush a cikin zancen ki ba,shin me ye alfanun da ki ke samu a ciki in kin ambaci sunan ta,alhalin ita in har ba ta yi dalili ba hakan ba zata faru daga gare ta ba?".
    "Ai dama na san in har za ka danganta ni da ita to ni ce zan kasance mai laifi a ciki ,kuma ai abun a bayyane ya ke ni ta shigarma cikin rayuwata ta yi bake-bake,ta hana ni gaba ta hana ni baya,ka ga kenan dole in sata a cikin raina gami da ambaton ta a kowane batu nawa,Ni da ban shiga rayuwar ta ba ai shiyasa ba ta yawon ambatona a zancenta,ita kuwa kullum shiga ta ke cikin rayuwa ta na yi min mulkin kama karya a cikinta".
     Ɗaga hannun Jaheed sama yai tare da fara addu'a ya na cewa,"Yah Allah ka kawo min ɗauki a cikin Gidana,ka shiryar min da wannan Matar ta wa,ka rage mata zafin kishin nan da ya ke damu ta gami da ɗawainiya da ita",kasa iya cewa komi Ummu Nurain tayi sai faman bin shi da idanu da ta ke,domin lamarin na shi ya kai ta ƙarshe har ta zama speechless akan sa.
"Ni fa ba wani abu na ce ba naga kin zuba min ido,kar ki sauya min manufa, Addu'a na yi ,kin san ba ni da wani buri a yanzu da ya wuce ace na ga Gidana ya zauna lafiya, sannan kuma in ga kin sauka lafiya,na tabbata da zaran kin sauka lafiya duk wannan tsiwar da neman fitinar da ke damun ki za ki bar su"...."Au dama kana fatan irin wannan abun alkairin a gare ni,ai na so ace itama ya zuwa yanzu itama na ta cikin yananan ,in yaso itama ta haifu ta ji irin wahalar da ake ji,in ya so itama ka fara fuskantar canji daga gare ta ,zama uwa ba wasan ne ba,raino da kula da yara ba na sangartacciyar mace ba ne ba".
     "Kin ga dan Allah mu kawo ƙarshen wannan lamarin domin na ga ya fara tsanani,don ban shirya kwana cikin tashin hankali a yau ba so Please mu kawo ƙarshen sa haka,zan iya samun Shayin Coffeen ?",tutturo baki ta fara yi gami da ɗaukar kayan da ta haɗa ta bar Parlon har ta dawo da Shayin Coffeen a hannunta ba ta saki fuskarta ba,yanayin yanda ya ga tana tururi bakin ne ya sa ya saki murmushi gami da ture System ɗin da ya ke amfani da ita gefe tare da cewa,"Allah dai yasa Babyn da za a haifo min ba zai biyo wannan neman rikici da wannan tsiwar ta ki ba".
     "Ai kai ma kasan duk abinda ka ga ina rikici a kansa to an taɓo ni ne,ko kuma an dainne min haƙƙina shiyasa zan tanka","Wannan Zeenat ɗin da na sani a baya ce ke da irin wannan halin amma ba ta yanzu ba",ya faɗa yana mai karɓar Black bhazar Coffeen da ta kawo mashi.
   "Me ka ke nufi da wannan maganar da ka yi yanzu,shin kana nufin da akwai ban-banci Zeenat ɗin yanzu da ta baya?",Sai da Muh'd Jaheed ya gyara zaman shi kafin ya bata amsa da cewa,", Banbanci mai yawa ma kuwa, Zeenat ɗin da na sani ƴar gayu ƴar kwalisa ce,mai aji mai natsuwa ga tsabta,komi nata cikin takatsantsan ta ke yin shi, ba ta da hayaniya,bata gardama bare a kai kan jayayya,ga girmama na gaba da ita,uwa uba ta iya tsantsara kwalliya da duk kalan nau'ikan suturu karma in tai shigarnan ta ƙananan ƙaya sai in ji kamar in ɗauke abata in Goya don burgewa",ya kai zancen fuskar shi ɗauke da shauƙin abinda ya faɗa,kafin ya ɗora da cewa,"Ban san ya a kai ba wannan Zeenat ɗin duk ta bar waɗancan kyawawan halayen da na santa da su,tun farkon cikin Nurain komi ta sauya ban san dalili ba,ko ƴar kwalliyar ma bana samu,ya kamata ki koma yin gayun ki,ko in siyo maki wasu sabbin ƙananan  kayan domin kina Min kyau a cikin su,don har na tuna wata shiga da kika taɓa yi na wani ƙaramin skirt da kuma wata half ɗin riga,kin kusa tashin kaina da wannan wanka,har yau na kasa mantawa da shi  .
    Da wata irin dariya Ummu Nurain ta kwashe,ta na yi tana kallon fuskar Jaheed,shima sai bin ta da idanunta yai,har sai data yi mai isarta kafin ta ce,"Amma Abu Nurain ka bani dariya taya da wannan ƙaton cikin zan yi Irin wannan shigar,ai yanzu ta fi ƙarfina baka ga muna da ɗa saurayi kamar Nurain ba,ta ya zan iya irin wannan shigar a gaban shi?","A'a Zeenat ba haka na ke nufi ,ina nufin in mun kasance daga ni sai ke,ai ba wai at random za ki riƙa sa su ba".
   "A'a Ni yanzu irin wannan shigar ba ta wani burge ni,taya zan sa kayan da za su bi duk su yi fitting ɗina ko motsin kirki in kasa ba wannan maganar,mu munci na mu zamanin mun bar ma ƴan baya,taya ina da wannan tirtsetsen cikin zan ƙarawa kaina wata sabuwar,in ma ji da wannan nauyin da na ke tare da shi","Akwai fa wasu na daban irin na ku na masu juna biyu,irin rigunan nan da su ka zarce gwuiwa ko wanda ba su kai su ba",......ta katse shi, da cewa,"Ni fa bana ra'ayin su,sai dai kayi haƙuri Allah Zuciyata ta fara raya min don cikin nan ba a jikin ka ya ke ba shiyasa  ka ke faɗin haka da kasan nauyin da mu ke ji da ba za ka ma fara irin wannan zancen ba".
     Rasa me ma zai ce da ita yai sa bin ta da idanu da ya cigaba,",Hmmmmm Ni ka ga tafiyata na fara jin barci,sai ka taho",da wannan ta yi shigewarta ta bar shi ya na bin ta da idanu

√√√√√√√√√√√√

"Hibba kallo ake kenan,na ga na shigo sai sallama na ke shiru ba ki amsa ba hankalin ki nakan television",Ummiey Maryam ta ce ta na mai shigowa ta samu wuri ta zauna a cikin Parlon.
     "Wallahi Ummiey Maryam idanuwana  ne kawai akai amma kwata-kwata ba na gane me su ke cewa","Ah aha wai wannan taronnan meye ne,kusan sau biyu ina zuwa in iske kina kallon shi ?","Taron Ester ne da ya gudana a wata Church dake Lagos,shine fa wannan tashar su ke ta yawan haskaka shi,Ni kuma kin san da kallon ba cika damuna yai ba shine ban damu da in sauya tasha ba".
    "Ikon Allah yanzu wannan kyakkyawar Yarinyar da ke tsaye Crista ce ba musulma ba?","Sosai ma da alama ta yi zurfi a cikinta irin ƴan na gada ɗinnan ne a cikinta,ina ma zaton kamar zabayar su ce","Kaico Kaico na kusa ince anyi asarar kyau anan dubeta kamar ki taɓa jini ya fito ni gani na ke ma kamar na taɓa ganin wani ko wata mai kama da ita","Ni ma kusan haka na ke ji akanta,tun ɗazu na ke kallon ta dalilin da yasa na kafe tvn da ido kenan amma na kasa gane asalin abinda na ke ji akan ta".
   "Kin ga watsar da wannan lamarin ga ƴar ki can ta zo sai faman rusa kuka ta ke,nayi nayi da ita ta faɗa min me ke faruwa ta ƙi","Ƴata kuma wacce wa ki ke nufi?", Momy Hibba ta tambaya a mamakance.
    "Zeenat mana yanda ki kasan wacce aka yi ma mutuwa haka ta shigo cikin Gidannan,inda Allah ya taimake ni ma ba wani wanda ta haɗu da shi daga cikin Mazan Gidan","To fa Allah ya sa lafiya,ko wannan karan me ya faru Allahu a'alamu","Ke dai bari tashi mu je ke ki tambaye ta wata ƙila ke ta sanar da ke abinda ke faruwa".
     A tare su ka bar Part ɗin da a yanzu Momy Hibba ke rayuwa da ita da Majinyacin Mijinta su ka nufi Part ɗin Ummiey Maryam,har suka isa gursheƙan kukan ta ke,da ƙyar Momy Hibba ta samu ta lalleshe ta kafin ta yi shiru ta fara sanar da su abinda take son sanar da su,kuma dalilin zuwan ta,"Ummiey ku ya fe ni,ban yi niyar zuwa in sanar da ku abinda ya ke faruwa dan in tadar maku da hankali ba, a'a sai dan kar nan gaba wani abun ya ɓullo ace laifi na ne tunda ni ce babba, wallahi Momy Hibba na gaji da irin rayuwar da na ke a cikin Gidan Abu Nurain kwata-kwata baya ganin ƙima balle mutuncina,ba ruwan shi da ni balle kuma haƙƙina da ya rataya akan shi,ko kwana na ne Part ɗin Gimbiya Ayush ya ke kwana,ba ruwan shi da ni,baya cin abinci na balle ai maganar kwana Part ɗina,idan nai magana ya ce na cika ƙorafi ba ni da haƙuri,ba yanda za ai magana mai daɗi ta shiga tsakani na da shi",ta ɗan tsagaita
       Kafin ta ɗora da cewa,Jiya mun samu saɓani  ni da Matar shi,anan take yada min maganganu,ciki har da wacce tai mugun tada min hankali,wai ni sakara ce ba ni da zuciya,na yadda kare ya ɗauka,an nuna ba a sona amma na nace,anmin kora da halin na ƙi ganewa,to in jira har sai an yi min korar kare tunda ita nafi ganewa,kuma wai ko dawo da Nurain nan Gidan ba hakanan ta faru ba, anyi hakan ne da wata manufa,Ni babban tashin hankali na anan ko dai Abu Nurain ya sake ni ban sani ba na ke rayuwa a cikin Gidansa ban tafi namu ba?".ta na kaiwa nan ta sake fashewa da wani sabon kukan da iya ƙarfin ta.
    "Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una wai duk Muhammad Jaheed ɗin ne ke aikata hakan ,ko dai ya samu matsala ne akan shi bai san illar da hakan zai haifar masa babbar gobe alƙiyama",Zaraf Ummu Nurain ta yi ta anshe zan ce da cewa,",Nima Ummiey abinda na ke gudun ma shi kenan, rayuwar gobe inda ba wani mutum da ya isa ya guje ma laifinsa da makomarsa", Cikin fushin Ummiey Maryam ta da ce ita,"Bar ni dashi zai gane kuren shi,tabbas sai na bi maki kadin haƙƙin ki da suka danne barima in kirasa"...."A'a Ummiey Maryam kar ki gaggawar yanke hukuncin,ki bar shi ba sai kin kira shi ba ba dai duk inda yake anjima zai zo ba,kin ga in kina kira shi yanzu ya san da maganar amma anjima sai dai kawai mu rutsa shi kun ga kenan dole ya faɗi gaskiya,to mu jira shi har zuwa sanda zai zo,tabbas sai ya yi dana sanin abinda ya aika","Kuma fa kin kawo shawara bari mu jira shi,ke kuma ta shi ki shiga wajen ƴan'uwanki Mata ki yi wanka ki shirya sai ki zo ki yi kalaci",da ha suka dakatar da case ɗin.