Page 39
Part 39
"Ƙarfin zuciya bai zama da sauƙi ba, musamman idan kalmar gaskiya ta tsaya a maƙoshin wanda ya kamata ya faɗe ta",shine abinda ya fi tsayawa a cikin rai da zuciyar Edwin.
A tsaye Jadeeda ke kallon Edwin, jikin shi na rawa, idanuwansa sun kumbura da hawaye, bakinsa ya kasa furta komi. Har yanzu bai faɗi komai ba. Sai kawai ya juya ya koma kan kujera, ya dafe kansa kamar wanda ke gudun tunani ya cinye shi.
Jadeeda ta taka a hankali ta zauna kusa da shi, ta ɗora hannunta kan kafadarsa,tare da cewa,"Bro Edwin... ka tsorata ni," ta faɗa a hankali, murya cike da laushi.
"Ba komai ne zai sa kai kuka ba, sai abinda ya fi ƙarfin zuciyar ka... kuma duk da haka kana ƙoƙarin ɓoye shi. Amma me yasa?"
Edwin ya ɗan ɗaga kai, idanuwansa sun cika da wani irin zafin da ba za a iya fassara shi da kalma ba. Sai dai ya faɗa.
"Na jima da ɓata hanyar da zan iya komawa asalin yanda ne ke,ki bar ni in cigaba da rayuwa a haka kamar hakan shi yafi dacewa da ni... Na rasa komai Jadeeda, na rasa kai na... kuma bana son ki rasa kan ki ke ma."
Zuciyar Jadeeda ta buga da ƙarfi. Wani abu na cikin wannan maganar yana nuna cewa ba lafiyar jiki kadai ke damun Edwin ba... akwai wata annobar sirri da ke cinsa a hankali.
"A'a Edwin, ba zan bari ka ɓace ba.ba zan bari ka sake cilla rayuwar ka cikin ƙaƙanikayi ba, Ka dade kana riƙe ni lokacin da duniya ta juya min baya. To yanzu sai na tsaya tare da kai har ka tsira, har ka murmure ka dawo asalin yanda ka ke,na yi alƙawari..."
Ya riƙe hannunta sosai, kamar kar ya saki, kamar wannan ƙananan lamarin ne kadai ke hana shi ruɗewa gaba ɗaya,ya so ace ƙaramin dalili ne ke cin sa a ransa ,da ya sanar da ita ko ya samu ya kwanciyar hankali da natsuwa a saman fuskarta,amma ina lamarin ya sha kan shi ya kuma fi ƙarfin zuciyarsa.
Sai kuma ya ce da ita a hankali kamar raɗa,"Jadeeda, idan na faɗa miki gaskiya, rayuwarki zata canza... wata kila za ki ƙi ni... wata kila za ki ƙi dukkanmu...ki tsane ni ki tsani kan ki da kan ki"
Hawaye suka cika idanun Jadeeda, amma ta daure, ta ce:,"To ka faɗa. Koma me yene, faɗa ɗin kan ka tsaye. Sai dai ni ka sani ba zan juya maka baya ba na yi alƙawari akan hakan."
Sai dai kafin ya buɗe baki ya ce wani abu zuciyar shi ta sake bugawa har hakan ya sa ya runtse idanunsa gami da dafa saitin Zuciyarsa, alokacin da Edwin ya dafe hannunta kamar yaro mai jin tsoro, ya rasa ko ya zauna ko ya miƙe tsaye. Kamar wanda za a yanke wa hukunci ne.
Sai dai wannan karon… ba zai iya gudu ba,Ya buɗe baki da murya mai sanyi amma mai nauyin gaskiya,"Jadeeda… Ina son ki. Da gaske. Amma ba da irin son da ke da kyau wanda mu ɗauka kamar na ƴan’uwa ba. Ina son ki da zuciyata amma na san wannan so haramun ne…”,Zuciyar Jadeeda ta tsaya. Gaban ta ya fadi. Kamar a mafarki. Kamar ruɗanin da ba shi da fassara,ko motsin kirki ta kasa.
“Wannan sirrin na damuna har tun kafin na san ke wacece. Amma tun daga lokacin da na fara jin ki,na saurare kalamanki, jin kukanki, jin karayarki so ya shiga zuciyata. Na ƙi amsa masa, na yi addu’a, na roƙi Allah, na karanta Littafi Mai Tsarki… na karanta inda aka ce
“Kada namiji ya auri ‘yar uwarsa.”Na karanta inda aka ce“So da ƙauna su zauna cikin tsarki,amma ina Zuciyarta ta ƙi ji ,na kurumce gami da makancewa akan haka,na yi tur da halina na tsani kaina,na la'anci shaiɗanin da yake tare da ni har ya ke son ya cutar da ni amma ina lamarin ya fi ƙarfina ya girmi hankali da tunani na.”
Sai ya runtse idonsa ya ce, “Amma duk da haka… zuciyata ta ƙi ƙyale ki. Kuma yau, na kasa ɓoyewa. Ban san yadda zan fuskance ki ba… amma na fi tsoron ƙarya da boye gaskiya.”
Jadeeda ta zare hannunta daga nasa. Ta miƙe tsaye kamar wadda aka zuba wa ruwan sanyi. Hawaye na gangarowa fuskarta, zuciyarta na ɓari.
Ta ce da karfi, kamar wadda ke magana da kanta,"Ka haukace Edwin,da gaske ka samu matsala a cikin kan ka,kana buƙatar,a duba lafiyar ka da gaggawa".
Edwin ya durƙusa ƙasa, hawaye ya ƙi daina zuba. Sai dai shiru ne a bakinsa.
Jadeeda ta fashe da kuka. Ta fuskance shi, ta ce da tsawa mai rauni,"Ka daina sona Edwin. Ka manta da ni! Ka manta da ni gaba ɗaya. Kai ba dan Krista na gari bane idan kana iya soyayya da ƙanwarka!”
"Kin ga ki fahimce ni nasan da hakan haramun ne,shiyasa na zaɓi in rayu a cikin ƙunci da kuma ɗacin zuciya......ya ɗan dakata numfashinsa yana barazanar rabuwa da gangar ƙirjinsa,kafin ya cigaba da kokowa da shi.
“Ko kuwa....dai .... ka sauya addini ne domin ka samu damar sona?,Domin Ni na san a cikin Bible, kaf babu inda aka halatta ɗan'uwa ya auri yar'uwarsa. Ko kuwa kai na na dab ne, Edwin?”,ba na tunani akwai wani addini a duniya da ya amince da irin wannan kwamacalar da ka zo min da ita".
Edwin ya zube ya fashe da kuka mai ƙarfi. Bai iya ce mata komai ba sai dai numfashi ya dinga ja kamar mai shirin mutuwa.
“Ina fata Allah ya gafarta maka,” ta ce cikin hawayen da suke ƙona mata fuska.
“Ka ƙaryata tsarkin addininmu. Ka ƙaryata martabar ɗan’uwa. Ka ƙaryata ni.”
Ta juyo da sauri. Bata waiwaya ba. Bata saurari komai ba. Ta bar Edwin a ƙasa, cikin ruɗani da sirrin da ya shanye zuciyarsa raunana gami da son tarwatsewa a lokacin.
√√√√√√√√√√√√√√√
"Safina kin yada ni ba ki da kirki ko kaɗan","Hmmmmm Zeenat kenan to ba dole in ɗaga ma ki ƙafa ba kin san ni kin san hali na,in dai maganar gaskiya ta zo dole in faɗa maki ke kuma abinda ki kai hannun riga da shi kenan".
"Na yi tunanin taren mu ta wuce mu bar wani abu ya shiga cikinta yai tasiri har ya kai ga shiga tsakanin mu,ki tuna fa tare mu kai yarinta,mu kai wasan ƙasa a tare mu ka yi karatu atare impact komi namu a tare mu ka yi sa,amma yanzu sai ki kwashe wani tsawon lokaci ba ki ziyarci inda na ke ba,in kuma ni na zo sai ki fara shamin ƙamshi,na kasa jure hakan abun ya na min zafi,ga shi kuma ban san dalilin faruwar haka ba".
"Ba na son mu tsawaita zancennan mu bar shi kawai Zeenat","A'a Safina ba zan yi shiru a har sai mun kawo ƙarshen wannan lamarin,ki sanar dani abinda na yi miki ko kuma wani ne ya ke son shiga tsakanin mu ban sani ba ?".
"A kan me wani zai shiga tsakanina dake,to idan wannan tunanin ki ke,to ki sauya in ma da akwai wanda ya shiga tsakanin tarayyar mu to ke ce da kan ki,haba dan Allah Zeenat mai ki ke so,mai ki ka nema ki ka rasa,da har ki ka maida rayuwar ki haka,kefa matar Aure ce amma kalli shigar da ke jikin ki,ko kunya ba kya ji ki kazo gidan Surukan ki da irin wannan shigar".
"Ai Safina fuska za ki cimin kan na zo wurin ki domin mu sulhunta tsakanin mu,mu gyara ɓarakar da ta shiga tsakani tarayyar da mu ka gina tun yarinta,to wallahi na gargaɗe ki domin kin san tun da can bana ɗaukar raini balle yanzu da girmana har da igiyar Aure a kaina,kin san ko a cikin ƙawayen mu na fi ƙarfin raini wallahi ."
"A da kenan ban da yanzu ko?,Ni ƴar'uwar ki ce ta haƙiƙa,bawai ina maki wannan zancen da sigar cin fuskar ba, a'a wallahi har cikin raina ina jin zafin yanda ki ka sauya ki ka mai da kan ki tamkar wata illitrate,haba Zeenat wallahi kin sauya ina mamaki gami da jin takaicin ssuyawar ki,na kan tuna yanda mu ka yi rayuwa dake ,komi na ki gwanin ban sha'awa ,kina ɗaya daga cikin ko in ce mace ta farko mai capacity acikin class mate ɗin mu,amma yanzu du babu,sabo duk kin zubar da shi,shin yaushe rabon da ki ga ɗaya daga cikin ƴan Click ɗin mu takawo ma ki ziyara,duk sun bari,domin duk wacce ta zo ta yanda ki ka banzatar da rayuwar ki sai ta ga ta wuce da ajinki sai ta bar ki,a duk sanda wani abu ya faru mu ka yi taro ko muka haɗu da wasu daga cikin sai an yi hirar ki gami da mamakin sauyawar ki,ina jin zafin haka domin tamkar ni ake suka in aka soke ki,amma ke kullum sake tsiro da sabbin halaye ki ke,ke ce rashin tsafta,haukan kishi kin biye ma Baba Asabe to ki sani son tarwatsa maki rayuwar Aure ta ke."
"Safina duk kin san wannan ce-ce ku ce ɗin da ya ke faruwa amma ba ki taɓa zuwa kin sanar da ni ba,kenan gulmata ma kuka koma yi".
"Na sha yunƙurin hakan amma duk sanda na zo da na fara yi maki maganar sai ki fusata ,ki nuna ma ba kya buƙatar jin labarin,kuma maganar gaskiya ba gulmar ki ake ba,kin aikata abinda za'a yi magana akan shi ne,Ni kaina ina baƙin ciki in zo gidan ki in ga yanda ki ke tafiyar da rayuwar Gidan ki,kamar ba Auren soyayya ku ka yi tsakanin ki da Yah Imam baamma komi a hauka ce cikin fitina da tashin hankali,duk da na san Auren ku na haɗi ne amma kafin Auren ai kun yi soyayya mai zai sa ba za ki maida wannan soyayyar ta zama linzamin gina rayuwar Gidan ki,ba ki ƙare kullum cikin baƙin ciki da tashin hankali."
Ta ɗora da cewa,"Wallahi Zeenat ki gode ma Allah,wasu matan Mijin ma su ke nema amma ba su samu ba,ke kuma Allah ya baki kina wulaƙantawa,ki je ki cigaba watarana in kika zubar da garin ki kya koma cizon yatsa daga baya
Shiru Ummu Nurain tai kamar Safina ta san ta taɓa mata inda ya fi sosa ma zuciya ta ciga da cewa,"Da za ki ɗauki shawara da kin gyara kuskuren da ki ka aikata na tsawon shekaru,har yanzu lokaci bai ƙurar ma ki ba,za ki iya mai faɗa soyayyar ki a cikin Zuciyar Yah Imam gama dana ba daina son ki yai ba halayen da ki ka tsiro ne ba ya so,kin ganni ko ba aure ne da Ni ba amma akwai abubuwa da dama da ki ke aikata su wanda ko karan hauka ya biyo ni ba zan iya aikata su ba".
"Ba zaki gane ba Safina domin bana tunani haka za ta yiwu, Gimbiya Ayush ta tsare ko ina ,domin Abu Nurain ko kallon arziƙiba ya shiga tsakaninmu saboda ita ta shiga ta raba mu."
"Ba wani shiga da tai ta raba ku,in ma ta shiga ke ce ki ka bata fuska,ta hanyar watsar da kan ki da ki ka yi,eh mana watsar da kan ki da ki ka yi mana,domin duk kin watsar da wasu responsibilities na ki na matsayin ki na matar Aure kuma Uwar Gida mai Capacity,ke kin zubar da na ki Capacityn ita kuma ta kwashe,ki farka daga nannauyan barci daki ke kwada ki gani in ba ki kwato Capacity ɗin ki ba,wai wace ce ma Gimbiya Ayush in ba matar cushe ba,don haka ki manta da ita anan ne za ki dawo da asalin ko ke wace ce,zamantakewar ki ba ya nufin ki banzatar da duk wasu buƙatu ko ra'ayi na Mijin ki ba."haka Safina ta cigaba da faɗawa Zeenat gaskiya da kuma hanyoyin da za ta bi don ta magance matsalolin da ta ke fuskanta a Gidanta,har zuwa sanda yamma ta yi.
"Au ashe kana tafe na sha yau ba zaka shigo Gidan ba", Ummiey Maryam ta ce da shi tana mai gyara zaman ta,"Ina tafe Ummiey yau tun safe muna Companyn Auduga ne yau zamu fitar da kaya shine fa sai yanzu na shigo,na taho ne a hanya na haɗu da Nurain sun ta so Islamiyya".
"Tooh ka Nurain maza je ka sashen Momy ka kira Ummanka ta na can".
Da ɗan sauri Jaheed kuma cike da mamaki ya waigo yana son yi tambaya ,shi kuwa Nurain fuskarsa ɗauke da murmushi ya nufi inda aka aike shi,"Ummiey...Ummu Nurain ta zo nan ne,Ni a tunani na na baro ta Gida kuma ba ta sanar da ni zata zo nan ba?","Uhmmmm ta zo tananan",ta ba shi amsa a daƙile.
Shigowar Momy Hibba da kuma Ummu Nurain ɗin ya hana shi sake cewa komi sai daman bin ta da ido da yake,a kallo ɗaya da ya yi mata yasan ba alkairi ne ya kawo ta ba da walakin goro a mita.
Momy Hibba ce ta umarce ta da ta sake maimata duk abinda ta ce da fari,haka ta jero su,sai da wannan karon muryarta na rawa,ta kuma kasa yarda ta hada ido da wani a cikin su,sai a yanzu take dana sanin zuwan ta gidan gabaɗaya.
"Mai ka ke son ka zama ne Muh'd,kana da da ilimi fa,shin baka san haramcin abinda ka ke aikatawa ba,me ye amfanin nuna banbanci ko fifiko tsakanin matan ka",sosai Ummiey Maryam ta ka sa ka shi a gaba ta inda take shiga ba tanan ta ke fita ba,shi ƙarshe ma rasa laifin me ya yi da har aka gurfanar da shi a wannan kotun,ga shi ko kusa ko da wasa Ummiey ta hana shi damar da zai yi magana ko ya kare kan shi, dole ba dan ya so ba ya bar ta ta yi iya yin ta,Duk abinda ake Momy Hibba ba tace komi ba sai bin su da Idanu ta ke a haka ta fahimci duk zancen da Ummu Nurain ta zo da shi ƙarya ne ba abinda ya faru a ciki ,ƙarshe Momy Hibba ta yanke hukuncin su ta fi da Nurain in ya so kullum a riƙa tura Driver ya riƙa ɗauko shi,motsin kirki kasa yi yai,zuciyar shi cike da ƙuna amma ba halin ya bayyanar da hakan ya rasa me ye a cikin kan Zeenat da ta ke aikata irin wannan aiyuka da duk mai hankali da tunani ba zai aikata ba,haka ya kwashe su ya su ka nufi Gida,jikin Zeenat kam a sanya ye ko haɗa ido da shi kasawa ta yi..