JADEEDA

Page 41

by @cwtsumiey19988

Page 41


Kiran dare ya ratsa kunne. An riga an gama addu'ar dare, an kashe fitilu. Dukkan gidan ya yi tsit kamar kabari. Sai dai Jadeeda ba ta iya barci ba. Kamar kullum, zuciyarta cike da damuwa da tambayoyin da ba su da amsa.
     A yau, wani abu daban ya faru,ta kasa iya mantawa da duk abinda ya faru tsakanin ta Bro Edwin,yanayin bugun zuciyar ta har yanzu ya ƙi komawa dai-dai,idan ta runtse idanunta,sai ta ji inama da ace komi zai gushe a cikin su,inama da komi zai gushe kamar bai taɓa wanzuwa ba,taya hankali da tunanin ta zai iya ɗaukar wannan lamarin,tsawon yaushe zata iya mantawa da abinda ya faru,wasu zafafan hawaye ne suka sake kwaranyowa da ga idaniyarta

Motsin shigowa ta ji ya sa ta ɗan waiga,Uncle Miey,ya kama hannun ta ya yi, ya zauna da ita a ɗaya daga cikin kujerun da su ka yi ma Parlon ƙawanya. Akwai nutsuwa a fuskarsa kamar koyaushe, sai dai idonsa yau sun bambanta. Yana kallonta tamkar ba mutum ba ne.

"Jadeeda," ya fara da murya mai laushi,"wannan yanayin bai kama ce ki ba,ki manta da da duk abinda ya faru ki ɗauka duk zancen da Edwin yai mi ki tamkar sun gudana a mafarki ne,kar ki bar su su zama wani dalili da zai lalata miki rayuwa ko ya jefa ki a cikin,ki manta da shi"......"A'a Uncle Miey wannan lamarin mai girma ne,ya fi ƙarfin in manta da shi haka da sauri, babban lamarine,a ce ɗan'uwana na jini ya bijiro min da batun soyayya ta ya hankali zai iya ɗaukar hakan da sauƙi?".
      "Shakka babu nasan maganganunsa suna da girma da saka nauyi a cikin zuciya amma bai kai ki bar sa ba,domin hakan zai iya yi miki illah",......."Illah kuma ta nawa Uncle Miey ai sai dai kar a kuma amma Bro Edwin ya dasa miki mai zafi da zurfi a cikin Zuciyata wanda ban san dare ko ranar da zan warke ba".
"Zan cutu matuƙa idan har ki ka ce za ki cigaba da rayuwa a haka,cikin tunani da damu,ki sani kwata-kwata hakan bai dace da ke ba,na ji baƙin cikin faruwar wannan lamarin,ina so ki sani,ba zan iya jurar ganin ki a cikin wannan tashin hankalin ba,ki sani ba abinda ke damun Edwin sai hauka da kuma ƙuruciya da ke damunsa,in Banda haka ta ya zai iya fuskantar ki da irin wannan kalamin mai girma,tabbas ya aikata kuskure,ki manta da komi I'll handle everything kin ji".
"Ba ni tunanin zan iya fita waje in haɗa ido da ɗaya daga cikin mutanen Gidannan,nauyin su na ke ji ina tsoran jin wani labari da baza iya ɗauka ba,bana son jin wani sabon labari wanda zai sake tada min da hankali,don haka ka bar ni na fi son kaɗaici a yanzu"
"A'a a duk sanda na ke cikin damuwa ko tashin hankali ki na tsayawa tare da ni har sai na koma dai-dai don haka ba zan bar ki ba,zai fi kyau mu fita wurin ƴan'uwa, su kan su suna cikin damuwa da tashin hankali akan wannan lamarin".
Cikin ƙarin tashin hankali ta fashe da kuka tare dacewa,"Uncle Miey ka bar ni,na fi son zama ni kaɗai,Mommy ta saka ni tsaka me wuya,ta kawo jerin sunayen samari wai dole sai na zaɓi ɗaya daga cikin su ,a matsayin wanda zan aura,ga Bro Edwin ya zo da wata sabuwa a cikin rayuwata,don haka zai fi Min kyau in samu wuri in keɓe ko na samu damar da zan sama ma kaina mafita"..….
A firgice Uncle Miey ya kusanto ta tare da cewa,"No....no..no ...kar ki ce dani Sister Gloria na neman haɗa ki Aure da wani ba tare da na sani ba,don me ya sa zata aikata hakan ?."
Ya sake ta gami da fara kai kawo a cikin Parlon,zuciyarsa sai aiyana masa abubuwa kala daban-daban ta ke,tabbas gab ya ke da yin sake,me yasa ya cika zurfin ciki,me yasa ya ke son ɓoye gaskiya gami da son tauye kan shi,don me yasa Sister Gloria za tai yunƙurin kawo wani ko wasu da nufin son zaɓama Jadeeda Mijin Aure bayan dakon sonta da yake ɗawainiya da shi tun shekaru Ashirin da suka wuce.
Ganin yanda hankalin shi ya tashi yasa Jadeeda tsura mashi idanunta,ganin tamkar ya na shirin zaucewa ya sa ta nufe shi gami da kamo hannunsa ta ce,"Uncle Miey kana lafiya wannan sauyin na mene ne,na ga duk ka rikice da ga jin wannan zancen nawa duk ka ruɗe har ma kafi ni shiga tashin hankali me yake faruwa?."
Kasa ce mata komi yai sai jan hannunta yai ya zaunar da ita akan seater ya tsura mata idanu,zuciyar shi na tsananta bugu wani ɓangaren kuma na ingiza shi akan ya sanar da ita sirrin da ke binne a cikin Zuciyar sa tun da daɗewa kar ya bari ayi mishi Sakiyar Ciki,wani ɓangaren kuma na cewa da shi a'a kar ka aikata hakan domin za ka sake cilla rayuwar ta cikin wata sabuwa kuma ruɗaɗɗiyar ƙaddara,za ka ɓalle wani sirri mai girma na cikin rayuwarta,hakan kuma ba ƙaramin illah zai mata ba,to idan har ka ɓoye ka kasa faɗa mata ya zaka yi a randa ka wayi gari wani daban wani bare ya Aure ta ya bar ka da dakon sonta da ya ginu a cikin rai da rayuwar sa?, wannan lafazin da ya zo mi shi a raine ya ƙara hargitsa shi gami da sake lulawa cikin dogon tunani.....
"Uncle Miey say something mana,shirun ka ya fara tsorata ni,ka sanar da Ni abinda ya ke faruwa ka sanar da ni,na roƙe ka"....ta kai zancen muryarta na rawa.
"Kar ki yi kuka Jadeeda,ba zan so ganin zubar hawayen ki ba zan faɗa mi ki komi sai dai na roƙe ki kar ki ce zaki guje Ni no meter how,za ki tsaya tare da Ni"......"Ka sanar da ni koma meye domin Zuciyata ta ƙarfi da yasan mene ne dalilin da ya  sauya ka kuma ya jefaka cikin irin wannan yanayin".
"Za ki iya tuna ranar da na ce ki shirya zamu fita zan yi Surprise ɗin ki sai rashin lafiyar Sister Gloria ya tashi wanda hakan ya sa mu ka fasa fitar ?","Eh na tuna",ta bashi amsa ta na mai ɗaya kanta alamun ta tuna ɗin
"Jadeeda ina son ki, I mean I love you,I love you since day one da na fara ganin ki,na ji Muryar ki,na ji kukan ki ya ratsa kunnuwan,tun rana ta farko da na fara ɗaukar ki na danganta ki a jikina,ina son ki da gaskiyata", wannan shine abinda na ke so in sanar dake a ranar".
     Jadeeda ta yi murmushi mai cike da ladabi, amma jikinta ya fara rawa ba tare da ta san dalili ba. Sai kawai ta ce, "Na gode Uncle Miey."
   "Ban ce hakan don yabawa ba kawai Jadeeda....." Ya tashi daga kujerarsa, ya matso kusa da ita. "A'a...Jadeeda... ina son ki ne. A zahiri, ni dai ina sonki dakuma dukkan gaskiya ta,ina nufin ina son ki da Aure."
  Kamar an zuba mata ruwan sanyi haɗe da zafi haka taki sanyi da zafi na keto mata ta rako 'ina . Gaban ta ya fadi. Idonta ya lumshe, zuciyarta ta fara dukan uku-uku,ta fara jin wata hayani da kuma ƙara na zagaye saman kanta, ƙafafuwan ta suka fara raurawa tamkar suna ƙoƙarin kayar da ita.
   "Uncle Miey… ka ce me?"
      Ya sa hannunsa kan kafadarta. "Ki fahimce ni, wannan ba laifi bane. Mun riga mun san halayyar juna,na fahince ki kin fahimce ni. Ba na kallonki a matsayin ‘yar ƙanwata. Ina son ki a matsayin matar da nake so in aura."
Duhu ya ƙara yin duhu. Sanyi ya fara ratsawa cikin kasan ƙafarta. Tana jin numfashinta ya yi nauyi. Idanun Uncle Miey sun dushe da wani irin ƙiyayya da rudani. Bai kama da mai gaskiya ba. Bai kama da Kirista ba.,"Ni ba zan iya ba!" Ta miƙe da hanzari, tana jin kamar ta fara zufa. "Kai… kai ƙanin mamana ne. Wannan zunubi ne!"

Yai dariya da wata murya da ba ta saba jin sa ba. "Zunubi? Menene zunubi, Jadeeda? Ko kina nufin addini zai hana mu soyayya?, to idan kina wannan tunani ki bari don Aure na da ke halattaccen Aure ne kamar ma anyi anga domin har na fara gano ki sanye da wedding gwon sanye a jikin ki an kai Gidana a matsayin Mata ta"
     Da wani irin gudu ta tafi zuwa cikin bedroom ɗin ta tana kuka. Tana jin ana kiranta da murya, amma ba ta waiga ba. Ranar nan ba ta runtsa ba. Tana jin tamkar duhu ya shige mata rai. Ta fara shakku shin anya ba duka Gidan ne shaiɗan ya shafa ba kuwa ?.
   Kasa haƙuri Uncle Miey yai ya bi bayanta har cikin Bedroom ɗin na ta yana mai cewa,"Me hakan ke nufi,kar dai ki ce za ki bari ko ki guje Ni,kar ki ce ba zaki amshi tayin soyayya ta domin hakan babban kuskure ne da bazan iya jurar faruwar hakan ba,ki sani My Angel zan iya aikata komi in har akan ki ne ciki har da kisa,ki sa hakan a ranki da gaske na je ina son ki na shirya in rayu ko in mutu duk akan ki",ya kai zance a matuƙar tsawace wanda har sai da Jadeeda ta tsorata gami da dunƙule kanta a jikin gwuiwowinta.

Momy ta shigo a hargitse, ruwan zufa na gangarowa daga goshinta, hannunta na rawa, idonta sun yi ja tamkar wacce ta fito daga mafarki mai muni.

Ba ta iya furta kalma ko ɗaya ba. Sai dai bakinta yana motsi, zuciyarta na bugawa da ƙarfin da har ana iya jin sa daga waje. Kamar ta faɗi. Sai da ta dafa bango tana neman numfashints,Richal ƙaninta wanda ƴarta Jadeeda ta ke kira da Uncle Miey, yana tsaye a gabanta cikin kwanciyar hankali, kamar wanda ya gama cin nasara akan wani yaƙi.

Momy ta ɗaga idonta, ta kalle shi da wani irin yanayi da ya haɗa ƙiyayya, firgici, da bacin rai.

"Kana cikin hankalinka kuwa?! Ka san me ka ke faɗa?!”,Tayi ƙoƙari ta doshi gabansa, hannunta na girgiza kamar za ta watsa masa mari.
   Uncle Miey ya zuba mata ido yayi,sai ya saki murya mai sanyi da kasaita,"Ina cikin hankalina sosai, Gloria. Kuma duk abin da na faɗa, na faɗa ne da zuciyata duka. Ina son Jadeeda. Ina son ta fiye da komi. Kuma babu wani mutum ko wani dalili da zai hanani Aurenta."
Momy ta girgiza kai da hawaye a idonta, "Ta yaya za ka faɗi haka? Kai fa ƙanina ne! Kai ka sani da kyau ita ‘yar cikin da ba za ka iya kallon ta da ido mai tsarki ba ce! Kana kallon kanka  a mata Krista na gari kuwa?,idan har haka ne ta ya zaka riƙa irin wannan tunani mafi muni fiye da na wulakantaccen mutum?".
   "Da gaske Ni mabiyan Yesu Almasihu ne,na gaskiya da gaskiya amma hakan ba yana nufin zan bar soyayya ta ta farko ba".
      Ya ɗan dakata kafin ya ɗora da cewa,"Wai ke duk a tunanin ki kulawar da na ke bama Jadeeda don ta kasance ɗiyar da ki ka haifa ne,na liar wannan ƙarya ne,ki sani son ta na ke Aurenta na ke buri ko da kuwa zai sa ki rasa hankali ki shiga hauka ne wannan bai dame ni ba."
     Ba Mommy ba hatta da Jadeeda duƙe riƙe tana daman gursheƙen kuka sai da tai saurin ɗagowa gami da dakatar da kukan nata,daga ina Uncle Miey ya samo wannan sabbin halaye,shine tsayar da ta tsaya masu ai su duka biyu,sai daga baya Momy ta iya motsawa gami da cije leɓenta har ya fara zubar da jini. Sai ta juya kamar za ta bar falon, amma sai ta dawo da karfi.
"Tabbas ka zo da wani sabon batu Richal wanda ko a cikin jerin mahaukata ban taɓa jin wanda ya aikata irinsa ba,ina so ka sani daga yanzu na shirya ma duk irin haukan da ka zo da shi,ba kai ba ba Edwin ɗin ba dukkan ku a tafin hannuna ku ke,mu zuba mu gani,na yi maka alƙawarin sai na dakatar dakai na kuma ƙaryata duk wasu kalaman ka,zan aikata haka in har na cika kuma ina amsa suna na Gloria"

"To Ni kuma ina mai tabbatar mi ki da sai na  fallasa ki!,domin a gare ni ba ki da wata daraja tun lokacin da kika boye gaskiya. Ni zan nemi farin cikin rayuwa ta ,a tare da Jadeeda ta kasance,don haka ba makawa Aurena da ita zai kasance!",ya ɗan dakata ,kafin Uncle Miey ya ce da rawar murya, "Na fi kowa sanin wanene ni! Na fi kowa sanin irin wutar da ke ci a zuciyata. Ba zan bari wani ya hana ni son da ya wuce duk wata doka a gare ni ba!"
     Momy ta tsaya cak. Hannunta na rawa. Idonta ya rine da shudi. Zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi da ƙarfi fiye da da. Sai kawai ta dafe ƙirjinta, ta ce da karamin murya

"Ya kamata Richal ka gane kuskure ka ke aikatawa,bai kamata ka ce" .......Kafin ta kammala, ta fadi kasa da wani ƙara mai tsuma zuciya.

“Momy!!”,“Gloria!!”,a tare Jadeeda da ta ke cikin mugun halin da ya faskara kuma ya fi ƙarfin Zuciyarta da ita  da Richal suka fara kiran sunanta
Suna fadan haka su ka nufe ta domin kai mata agaji. Sai faman jijjigata suke a rikice. Amma ina ba ta iya magana ba,bata motsi. Idonta ya cika da hawaye amma kuma ba kalma ko guda da ke iya fita daga bakinta ., “Call an ambulance!!”, Richal ya faɗa a kiɗime da ƙarfin muryarsa, wannan ƙarar da ya yi ce ta jawo hankalin mutanen gidan,ana duk hankalin su ya tashi ciki da ruɗu da kuma gaggawa,Aka fito da mota. Gami da nufar asibiti da ita, zuciya cike da firgici da tambayoyi masu ɗaci.