JADEEDA

Page 45

by @cwtsumiey19988

Part 45

Jiki a sanyaye Ummu Nurain ta iso kusa da inda ya ke zaune ta aje masa Abincin da ta kawo masa tana yi tana satar kallon shi,har ta miƙe za ta bar wurin ta dawo ta zauna ta fuskance shi da cewa,"Dan Allah ba dan halina ba ko yaya ne ka ci wani abu daga cikin abinda na kawo maka,ba zan iya jure ganin ka a cikin irin wannan yanayin,kuma ga shi tafiya za kai mai nisa ya kamata ka ci wani abun,dan Allah".
   Shima gyara zaman shi yai tare da cewa da ita,"Ki yi haƙuri,na yi maki tsawa,na horar da ke ba bisa laifin ki ba,ki yafe ni kinji Mata ta".
    Wata ajiyar Zuciya Ummu Nurain ta saki mai ƙarfi,kafin hawaye su biyo bayan ta,ba ta ce komi ba kan abinda ya ce sai cewa tai,"Me zan zuba ma ka,ko Black bhazar Coffee zan fara haɗa maka",ta kai zancen tana mai ƙoƙarin buɗe plaks ɗin,hannunsa yasa ya riƙe na ta tare da cewa,"Ba abinda zan sha matuƙar ba ki furta kalmar yafiya a gare ni ba,zan zauna da da yunwa har in tafi Bazan ci komi ba".
    "Ka bari in haɗa maka,domin Ni ban ji zafin ka ba,kawai dai na ji ba daɗi da dana ga laifin wata ya shafe ni,kuma nasan kaima hakan ya faru ba don son ranka ba","Na gode da wannan karamcin na ki,amma ina gani kamar Babban Gida ya kamata ki koma har zuwa san da zan dawo bai kamata kina ɗauke da irin wannan Cikin a ce ,ki zauna ke kaɗai duk faɗin shi","Hmmmmm in ka ce in tafi zan tafi,haka ma in ka ce in zauna zan zauna domin ni gareni wannan Gidan ya fiye min ko'ina,na fi son in zauna a cikin sa kamar Sarauniya","Haka ne amma saboda tsaran lafiyar ki zai fi kyau ki tafi can","To zan tafi Abu Nurain amma dan Allah in ka dawo ka rage wannan yawan tafiye-tafiye mu  Ahalin ka muna buƙatar ka,mu na san ganin muna samun lokacin ka ko yaya ya ke",.
     "Zan duba hakan Ummu Nurain amma ban miki alƙawarin a kan hakan ba,domin duk ɓangarorin guda biyu duk sun zame min kusan dan dole,daga ɓangaren yaɗa Addini sai kuma ɓangaren Ceton rayukan muta ne,to kin ga a cikin su ba wani na bari","Ya kamata ko yaya ne a duba magabana,ko ba yanzu ba","To shikenan zan duba in Sha Allah","Yauwa Abu Nurain bari in je in haɗa maka sauran kayan da za ka tafi da su,domin na fara ɗazu na aje gaba ɗaya hankalina na kan ka saboda ba ka ci komi ba","To bari in zo in taya ki ,in muka gama da nawa sai mu haɗa naki ke da Nurain","A'a zauna ka ci Abinci ka na hutashshe ka yanzu zan gama".

√√√√√√√√√√


“Sister Zahara Komi ya kammala ko?", Jadeeda ta tambaye ta a hankali.
"Komi ya kammala Jadeeda kamar yanda ki ka so,amma dai...",ta ɗan dakata ta na maida hankalin ta akan Jadeedar.
"Kai na gode Allah,na samu natsuwar ruhi da jin haka"."Amma Jadeeda ba ki ganin hakan a matsayin babban kuskure ta ya za ki ce za ki bar gida, Revered Anderson ya dawo ya tsawatar game da lamarinnan,kuma jikin Madan Gloria yayi sauƙi komi fa a hankali ake samun sa" .
"Sister Zarah kiyi haƙuri amma ba zan iya janyewa daga wannan tafiyar ba,nasan kin girme ni,mun zauna a tare cike da amana da kuma mutunta juna,ba za ki bani shawara wacce za ta cutar da ni ba,ina baki haƙuri akan ƙin ɗaukar shawarar ki a wannan karon".
Sister Zahara ta kalle ta na ɗan lokaci kafin ta ce da ita da cikin taushin murya da son shawo kanta, "Ke kin san, akwai bambanci tsakanin guje wa matsala da kuma fuskantar ta da zuciyar da ba ta jin tsoro,shin dan me zai sa ki yanke wannan hukuncin?,wanda zai iya jefa ki a cikin halaka".
Jadeeda ta yi shiru. Idonta ya cika da hawaye, zuciyarta kuma na bugawa.ta dubi Sister Zahara tare da cewa,"Bazan iya ba....ba zan iya janyewa daga wannan tafiyar ba,ina jin acan ne kawai zan samu salama da kwanciyar hankali,komi zai koma Normal idan ya kasance bani nan,domin kumi ya faru a sanadina ne,Ni ce silar komi,domin Ni sheɗan ya samu mafaka a cikin Zuciyoyinsu,za su dawo cikin hankalinsu, natsuwa da kuma tunanin su,idan komi ya lafa zan dawo".

Sister Zahara ta bude Jakar da ta zo da ita ta ciro,Biza ta miƙa mata tana yi tana waige-waige don kar wani ya ganta kafin ta ce da ita,"Kafin ki tashi, ki tabbatar kin gama da dukan sirrin zuciyarki. Kasar da za ki je ba za ta share maki hawaye ba sai zuciyar ki ta yarda da ita ce take da ikon yin hakan."

Jadeeda ta kalle ta da idanunta a waje da son fahimtar me ta ke son cewa,ganin kamar abun zai ja ta ta da nisa yasa ta amsa kawai gami da yi mata godiya tare da cewa,"Na roƙe ki ki riƙe min wannan a matsayin sirri kar wanda ya sani,ba na son kowa yasan ina zani komi rintsi ko wuya zan dawo da lokacin hakan yayi,na roƙe ki kin ji Sister Zahara"."Indai don ta ni ne kar ki damu,babu wanda zai ji,amma na roƙe ki da ki sake duba wannan lamari Jirgin Ak Peace shi za ki bi zai tashi ƙarfe 4pm amma sai dai ki yi haƙuri domin Jirgin ki Transcit Flight ne za ki iya samun delay na wucin gadi,amma dai by the grace of God za ki isa lafiya , sannan zai fi miki ki sauka a garin Quebec ko kuma Montreal zai fi miki daɗin zama, sannan ki kula da matakin lafiyar ki".
"For the sake of father lord ba abinda zai same ni,tamkar zan yi hijira ne, Jesus Christ zai bani kariya,ya sani zan aikata hakan domin guje ma faɗawa daga halaka ko kuma sauka daga kan littafin shi littafin tsira Bible","Amen Jadeeda zan taya ki da addu'a kin ji",ta kai zancen ta na mai dafa kafaɗar ta haka dai su kai bankwana kafin Sister Zahara ta tafi da sauri ta na yi tana waige-waige,sai da Jadeeda ta tabbatar da wucewar Sister Zahara kafin ita tama ta tafi bayan tabbata babu wanda ya gan su.
     "Aunty Jeeyyyy lafiya me ya faru daga ina ki ke tunda safiyar nan,na shiga Bedroom ɗin ki na iske ba ki nan ?",Nora ta tambaye ta"Ba ko ina na ɗan fita waje ne na shawo iska",ta ba ta amsa ba tare da ta yarda sun haɗa ido ba kuma ta na magana ta na tafiya.
   Da kallo Nora ta bi bayanta da shi,kafin ta gyaɗa kai ta cigaba da tafiya zuwa inda ta nufa.
Jadeeda tunda ta shiga ɗakin ta ke daman kai kawo,"Yanzu ya zan yi, Flight ɗina zai tashi around Four ya kamata ace before time ɗin na bar Gida,kuma in bar Gida ba tare da wani ya farga ba ,domin in hakan ya faru zai iya zama tsaiko ko dalilin da zai hana ni tafiya,to yanzu ya zan yi,gashi yanzu Past Eleven ya zan yi,dole ina buƙatar tafiya da wasu kayan tunda ban san kowa a can ba,to ya zan yi?", shiru ta yi na wani lokaci kafin ta ce," Yes na samo mafita".
     Wurin Momy ta nufa ta iske ta kishin giɗe tamkar wacce ta lula wata sabuwar duniyar ta tunani,"Mommy kina lafiya kuwa?", Murmushin yaƙe ta yi mata kafin ta gyara zama ta ce da ita ,"Me ki ka gani ne Sweathert?","Mommy duk wanda ya kalle ki yasan You are not in the mood ba haka ki ka saba zama ba ,komi na ki ya sauya kuma duk a saboda ni....","A'a Jadeeda ba laifin ki bane wadancan shashan ne da su ka ja komi sune ke da laifi ba ke ba".
    Rausayar da kanta gefe tai gami da saurin kawo maganar da ta kawowa kar ta bari damar ta suɓuce mata,"Am Mommy wai Ezekeal ne ya kira wai da buƙatar in zo yana son gani na,wai wani case ya taso a ɗaya daga cikin ƙauyukan da mu ke zuwa Bushara ,to na ce masa ba zan sami damar zuwa ba shine ya matsa na ce bari in zo in sanar da ke".
    "To mene ne a ciki Dear ki tafi mana ko ba komi za ki ɗan rage abinda ki ke ji in ki ka shiga cikin mutane biside ma aikin lada zaki don haka ba ni da ja ki tafi sai kin dawo ,Yesu Almasihu ya albarkace ki a tafiyar da za ki ki je ki dawo lafiya",sai da fuskar Jadeeda ta faɗa ta rungume ta gami da cewa,"That's My Sweat Mom na Gode da samun ki da nai a ciki rayuwata".
    "Nima na Gode ma Jesus da ya sanya ki ka kasance ɗaya daga cikin tsatsona,amma dakata ba zaki kai 4pm a waje ba ko".
    Sai da Jadeeda ta yi jim kafin ta ce"Ehhhhh to ba lalle ba,domin case ɗin na wata ƙaramar yarinya da ke fama da ciwon zuciya to muna son foundation ɗin mu yaɗauki nauyin aikin da za ai mata ne, da zaran mun yi solving ɗin sa zan dawo buy the grace of God".
    "Okay ki kula ki kira ni ki sanar da ni komi ke faruwa kin ji,in ma da buƙatar mu sa hannu a cikin lamarin sai ki sanar da ni","Wai da na ce ina Martin ya ke ko shine sai mu tafi tare ban san tafiyar ni kaɗai",ta ƙare maganar zuciyar ta na bugawa da ƙarfi da addu'ar Allah ya sa baya Gidan,"Sun fita shi da Papa ɗin ku,ita kuma Nora Unexpected test ce ta taso ma ta tafi school sai dai ko kusa Driver ya kai ki","A indai haka ne Gara in tafi ni kaɗai ,na yi driving ɗin da kaina amma kafinnan in wuce zan shiga Church ɗin Our Lady Queen of Nigeria Pro‑Cathedral","Kina ganin ba zaki sanya su ta jiran ki ba","A'a Bazan jima ba zan wuce,ina so in ɗan yi addu'o'in ne kafinnan","okay ba matsala ina maki fatan alkairi sai kin dawo".
    Da wannan damar ta samu ta haɗa duk abinda zata buƙata tasa a cikin troly ta saɓa ta fitowa ta ci karo da Ester wanda har sai da gabanta ya faɗi,"Aunty ina za ki haka na ga kin fito da sauri irin haka?",sai da Jadeeda ta haɗiye yawun da ya tarar mata a baki kafin ta ce da ita,"Wanki zan bada na","Wanki kuma Aunty ba akwai Machine ba?",Cigaba da tafiya tai kafin ta ce da ita,"Bana da buƙatar shi ",idanu Ester ta zaro waje ta na mai cewa a cikin Zuciyar ta,"Anya kuwa lafiya,Aunty Jadeeda ba haka ta ke ba,ba ta magana da mutun a irin wannan yanayin kuma na ga kamar unguwa za ta ,Uhmmmm ba ruwana",ta ƙare zancen ta na mai tafiyarta abinta.
    Kai tsaye Church ɗin ta nufa acan ta kwashe tsawon lokaci acan sai da taga gabatowar 4pm sannan ta baro cikin Church ɗin ta samu wani ɗaya daga cikin masu aikin Cleaning a cikin Church ɗin ta kira shi gefe guda ta ce da shi,"Ina son za ka yi min wani aiki zan biya anan take shin kana da interest akan shi?,zan biya ka 50k anan take just delevering ɗin saƙo za kai min zuwa wani address da zan baka",zaro idanu waje yai alamun zuciyar shi na son kuɗin kafin ya ce,"Anya ba akwai wani abu a cikin wannan aikin da ki ke son sanya Ni acikin da ba,ma'ana akwai lauje cikin naɗi akan shi ba","Ba wata manufa a bayan haka,tafiya ce ta gaggawa ta ka mani zan baka keyn Mota ta ka kai min ita,zuwa Gidan mu,da takarda da zaka ba su in ka isa, simple shine kawai,na faɗa maka haka da iya gaskiyata ba zan cutar da kai ba,nan guri mai tsarki mu ke,ba zan faɗa maka akasin gaskiya".
    "To shikenan na yarda da ke","Amma ina so sai nan da  6pm za ka kai sauƙin",da to kawai ya amsa mata ta je farking space ta nuna masa Motar tafidda trolynta ta ba shi keyn sannan ta tafi ta tari tacxi ta nufi Airport kai tsaye.
Bayan awannin biyu da tafiyar Jadeeda a kai sallama a bakin gare ɗin Gare Akan ɗin Gidan ya leƙa ya ga wani Magidanci tsaye da takarda a hannunsa ga kuma Motar Jadeeda tare da shi,"Lafiya Malam na gan ka anan ko wani ka ke nema ne?",Gate Man ɗin ya tambaya.
    "Eh wani daga cikin Halin Gidan na ke nema domin in isar da saƙon da na zo da shi","Kamarya wani daga cikin Gidan kana da alaƙa da su ne","A'a kawai dai an bani saƙo ne,wanda zan fi son in ba wani ahali na Gidan",Shiru Gate Man ɗin yayi kafin kuma ya ce da shi,"A'a ka dai fara sanar da ni abinda ke tafe da kai sai in ji daɗin sanar da mutanen Gidan abinda ya kawo ka ba hakanan in tunkare su da labarin da ba ni da wata masaniya akan sa ba","Zan dai fi son ka kiramin wani a Gidan sai a yi komi a gaban ja domin Ni ban zo da wata cuta ba".....Isowar Nora wurin ya dakatar da musayar yawun da suke ,ta dakatar da gami da tambayar Gate Man ɗin da cewa,"Baba Joshua lafiya na ga Motar Aunty Jeeyyyy a waje ?","Nima yanzu na fito na iske ta anan da alama dai wannan mutumin ne ya zo da ita",da sauri Nora ta maida hankalin ta akan mutumin da aka nuna da sunan shine ya zo da Motar,"Ina ka sami wannan Motar,Ina mai Motar ta ke,meye haɗin ka da ita", wannan sune jerin tambayoyin da Nora tai mi shi a ƙagauce da son jin amsar su.
    "Kwantar da hankalin ki me motar da kanta ta bani ita gami da bani address ɗin wannan Gidan ta ce in kawo ,in sanar maku tafiyar gaggawa ce ta risketa,ga wannan takardar da ta bani don ku tabbatar da abinda na ce da gaske na ke",ya kai zancen ya na mai miƙa mata ,tana amsa ya juya yai tafiyarsa ba tare da ya tsaya ba.
    Ita kuwa Nora a hargitse ta shiga cikin Gidan kamar wacce aka biyo,tun kafin ta shiga ta ke kwalama Momy kira,"Lafiya Nora me yake damun ki za ki shigo Gida a cikin irin wannan yanayin,sai kace makauniya".
    "Momy ina Aunty Jadeeda,ina ta tafi?","Nima abinda na ke tambaya kenan ki ka shigo",cewar Papa da ke zaune a kan dinning suna cin abinci".
    "Ohhh,ta tafi duba wata Yarinya mai ciwon zuciya ƙarƙashin Foundation ɗin su, Shikenan ko sai ki samu wuri ki zauna kin shigo kina ƙoƙarin tada ma mutanen Gida hankali".....,"Kin kirata ko kuma ita ta Kirani tun bayan tafiyar ta?",Papa ya tambaya.
    "A'a na yi ta trying number na ta amma a kashe ba ta tafiya wani lokacin ma sai ace min not reacherble".
    "To ga Motar can wani ya kawo ya ce,wai a gaya maku tafiyar gaggawa ce ta kamata,da kuma wannan takardar",ta kai zancen ta na mai miƙa masu Papertun kafin wani ya motsa Papa yace,“Ina ita Jadeedar? Me yasa wani ya kawo Mota da wannan takardar?!” Papa ya buge da tambaya, yana ƙoƙarin ɗaukar takardar.

Gidan kowa ya firgita, Zuciyoyinsu sai faman kai komo take da son sani ne takardar ta ƙunsa Granny tana zaune dafe da ƙirjinta, Papa har ya fara fitar da ɗigon zufa . Momyn Jadeeda kuwa ba ta iya ɗaga kai ba.
Papa ya buɗe takardar cikin sauri, zuciyarsa na dukan bugun tashin hankali. Granny ta daga hannu tana karanto addu’a a cikin ranta, kamar zata faɗi,Papa ya fara karantawa kamar haka
“Ina roƙon gafararku…
Ba don na tsane ku ba ne na tafi, sai don na rasa inda zan nufa,Zuciyar ta kasa iya ɗaukar abinda ya tunkaro ni.
Kowane numfashi a cikinsa akwai ruɗani, tsoro da ɓacin rai. Idan ni ce kuskure, sai na zauna kuma na rayu da shi
Ban san inda nake nufa ba, amma ba zan iya komawa inda ku ke ba.
Ina mai tabbatar maku da zan dawo amma sai Sheɗanin da ya ƙawata Zukatan Ƴan'uwana kuma makusanta na ya bar gangar jikinsu,to a sannan zan dawo,ina kewan dukkanin kulawa da soyayyar da ku ke nuna min,zan yi rayuwa a inda na ke cike da kewar ku.
Uncle Miey har yanzu matsayin ka yanan a cikin raina bai sauya ba,haka kaima Bro Edwin,Nora da Martin zan yi kewar ku,ku kula min da Mommy da kuma Papa har zuwa sanda zan dawo.”
Jadeeda
Uncle Miey ya dafe bango, yana kallon Edwin,“Mun cuce ta...!” Granny ta faɗi da hawaye.
"Kai ne dai ka cuceta,kaine mabuɗi kuma sular faruwar komi,kai ne ka cuceta", Uncle Richal ya faɗa cikin hargowa yana nuna Edwin da ya yatsa  
Papa ya jefar da takardar, ya nufi inda Madam Gloria ta zube ƙasa tana kuka mai cike da raɗaɗi ba kuka irin na ɓacin rai kawai ba, amma kuka mai tambayar "me ya faru da ƴata Jadee?,ina take a halin yanzu wacce irin rayuwa za ta riska a duk inda ta ke,shin sake jefa kanta cikin wata rayuwar mai cike da hatsari tai ko ko hanyar mafita ta samar kanta a sanadin barin Gida"
Amma tabbas barin Jadeeda ya bar ƙura, damuwa, da abin da babu mai iya warwarewa,face sai lokaci domin shine alƙalin da baya ƙaryata,kuma baya cuta ko kaɗan.