KARAGAR MULKI

Page 1 Book 2

by @cwtsumiey19988

*KARAGAR MULKI*

STORY & WRITTEN BY 
(*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin 
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH

   And now...*KARAGAR MULKI*

*YOTA*

Book 2

Page 1
"Ranki ya dad`e kar ki so ki ga irin kisan gilla,kisan rashin imani da rashin mutunci da wannan tambad`ad`en yaron  ya yi ma Dakarunmu,sai da ya kashe mutun Ashirin da shidda ya raunata mutum talatin da biyar,Idan ki kai duba ya zuwa wad`anda ya kashe za ki iya firgita,ki razana sannan ki d`imauce domin irin munmunan kisan da ya yi ma su,daga wanda ya sokawa wuk`a a mak`oshi ta fito ta tsakiyar kwakwalwar kansa sai wanda ya caka ma wuk`a a Ido ko ya fillewa wasu daga ciki kai d`ungurungum"....da sauri Sarauniya Junayyah ta dakatar da Sarkin Yak`i ta na mai cewa" A'a bazai yiwu ba,ban yarda ba, ta ya mutum d`aya zai shigo har cikin wannan Masarautar ya illata mutane masu tarin yawa har haka,kai ba za ta ta`ba sa`buba wankan kuturu da sabulu,mutun d`aya ne fa ba wai mutane Goma ko Ashirin ba,muje in ga ni da idona ,don abun da kamar wuya gid`an ganga da lauje".
      Malikat Juwairiyya ce ta matso kusa da ita ta na mai dafa kafad`unta ta ce da ita ,"Ya Isa haka,wannan tashin hankali da rashin natsuwar ba abinda za su haifar mi ki face sa ke afkawa cikin wani sabon ramin mai d`auke da zurfi kuma da tsananin duhu a cikinsa,na riga da na je na ga duk irin `barnar da ya aikata,don haka ki sawa Ranki dangana kar ki he ki ga abinda zai tsaya mi ki a rai ko ya tada ma ki hankali","Ya ke maihaifiyata zuciyata rawa ta ke na kasa gasgata ko yarda da abinda su ke fad`a, Anya kuwa wannan yaron mutum ne,ji bi yanda ya maida mana Masarauta tamkar kango daga inda ya rushe katangun wurin sai inda ya cinna ma su wuta abun akwai d`aure kai da ban mamaki wanda ya ke cike da tarin al'ajabi ".
           " Hmmmmm wannan shine abinda tun farko na ke guje ma ki amma kar ki damu komi zai dai-daita yanzu haka na kira taron gaggawa na kuma baza Dakarunmu a ta kowanne `bangare,lungu da sak`o na cikin wannan Garin domin ina da tabbacin bai isa ya kai ga fita ko tsalakewa daga cikin wannan garin ba,abinda ya fi yanzu ki je ki sa a tada katangun da ya zubar sanan runbun da ya cinnawa wuta a kwashe tokar,daganan sai ki zo musan yanda za mu `bullo ma lamarin".daga can k`asan zuciyar Sarauniya Junayyah kuwa sak`e-sak`e ta ke har ta nacewa,"Kamarya kin kira taron gaggawa,kuma kin baza Dakaru a ta ko'ina,me wannan tsohuwar ta ke nufi ne ni fa bana son shigar hanci da k`udundine,ta ya ma haka za ta faru kota ta`ba ganin in da Sarki biyu ya MULKI KARAGA guda d`aya m,ai wannan ayai shishigi ne,amma ba komi zan yi maganinki bari dai wannan rikicin ya lafa ki gani sai na kwantar da ke ba tare da kin iya ko da motsa d`an yatsanki ba".
A fili kuwa sai cewa tai,"Ina Godiya da samun ki da na yi a matsayin Mahaifiya da kuma irin k`ok`arin gami da kulawar da ki ke ba ni tare da Masarauta ta gaba ki d`aya,ina alfahari da ke sannan kuma ina son"......Kasa k`arasawa tai sakamakon fad`owar da Jakadiya Gaje tai inda su ke da matuk`ar gudun tsiya ta na cewa,"Ran ki ya dad`e...Malikat.... an....an....nemi Gimbiya Junainah a kaf fad`in Masarautarnan amma ba ta ba labarinta".
A matuk`ar firgice su duka biyun su ka mik`e tsaye har suna had`a baki wajen cewa,"Me ne,kin san me ki ke cewa kuwa ko baki da hankali ne,koko wata matsalar ki ka samu a cikin kan ki?".
"Na rantse ma ku har da wanda raina ya ke a hannunsa wannan zancen da na zo ma ku da shi gaskiya ne,tun tashinmu da garin Allah ya waye mu ka fahimci hakan amma mu ka k'asa bayyana ma ku har sai da mu ka bincika, iya bincikawa sannan mu ka yarda da bata wannan Masarautar, yanzu  ma haka daga cikin d`akin ta na ke ".
" Ke asararriyar Bawai dakata daga fad`in wannan munmunan zancen domin `yata Gimbiya Junainah ba inda za ta ta tafi ta barni",Cewar Sarauniya Junayyah, ita kam Malikat Juwairiyya zaune ta kai jikinta duk ya mutu,tamkar wacce a ka zarema lakka ba sauran k`arfi ko na sisin kwabo a jikinta,sai da ta d`auki wani lokaci sannan ta ce ,"Maza je ku zo min da Kuyanga Jazila yanzu-yanzu ba tare da `bata lokaci ba ",
Sai da Jakadiya Gaje ta sa ke duk`ar da kanta k`asa sosai ,alamun ta na jin nauyi da tsoran abinda za ta ce da kuma  firgicin abinda ka iya biyo bayan a matsayin tagomashi ko tukwuici a gareta,sai da k`yar ta iya cire kanta kafin ta ce da su" Ki gafarce ni Malikat Juwairiyya amma da alama har da ita Kuyanga Jazila ba a gani ba,da alama dai tare su ka bar cikin Masarautarnan ".
Wani irin rik`o Sarauniya Junayyah ta yi ma ta ta na cewa," Garin ya akai haka ta faru wanne irin sakarkarun ne ku da har za ku bari haka ta faru me ye amfanin ku ,me ye dalilin da ya sa aka aje ku ,ba dan ku yi gadin ta ba kuma ku kula da ita ba ,gami da ba ta kariya ba?",cikin kakarin shak`ar da a kai mata ta ce ki yi hak`uri amma wallahi na rantse mi ki ba mu san sanda ta fita ba kuma ko da wasa ba mu runtsa ba har sanda aka fara wannan tashin hankalin na cikin  wannan Masarautar wata k`ila ta yi amfani da wannan damar ne ta fita" .
Jikinsu su duka sanyi yai, sai tunaninnika da dama ne ke kai kawo a Zukatansu,"Ko dai wannan ja'irin yaron da ita ya tafi ne ba mu sa ni ba?",cewar Sarauniya Junayyah.
Sarkin Yak`i ne ya ce da ita "Ba na tunanin haka ya shugabata amma ina da tabbacin ba tare da ita ya fita ba,domin a kan idona,duk da bishi-bishi na ke ganinsa har ya bar cikin wannan Masarautar bayan ya jimin ciwo a ka ,da wani mugun k`arfe,shi kad`ai ya fita ba Gimbiya Junainah a tare da shi".
" Na shiga uku Ni Malikat Juwairiyya me ya shiga a cikin kaina ko dai na rasa tunani da hankalina ne,ta ya zan yanke irin wannan tsatsauran hukuncin a kan Jikata guda d`aya da na mallaka kuma na ke da ita?".
   "Me ki ke son cewa ya ke Mahaifiyata Malikat Juwairiyya ta ya za ki d`ora laifi ko nauyin wannan abun da ya faru a kan ki ?".
"Ba dole in d`ora laifin a kaina ba, ni ce fa na jajurce gami da tsayawa tsayin daka akan sai ta amince da abinda Bokanya Azizah ta zo da shi,kin san ta fa, kafiya ce da ita ga naci akan duk abinda ta sa kanta ko ta sa shi a ranta,wata k`ila hakan ne ya sa ta za`bi da ta gudu ta barmu akan ta amince da abinda mu ke so".
"Ki kwantar da hankalin ki na yi ma ki alk`awari a duk inda ta ke a kaf fad`in duniyarnan sai na dawo ma ki da ita,walau a hannun mutum ko a hannun aljan",cewar Bokanya Azizah da k`arasowarta wurin kenan ita da Boka Dürsäås.
"Tabbas nima ina tare da Bokanya Azizah a cikin wannan tafiyar zan sadaukar da lokacina da duk abinda na ke da shi wajen ganin na dawo da Gimbiya Junainah har cikin wannan Masarautar ta BAIBAH ba tare da ko kwarzane ya same ta ba".
"Da kuwa na ji dad`in idan har ku ka aikata hakan a gare ni,ku ka manta da gabar da ta ke tsakanin ku da kuma rashin jituwarku tabbas zan yi ma ku kyautar ban mamaki, kyautar da za ta azirta dukkanin ahali da tsatsanku ba za ku k`ara talauci ba har k`arshen rayuwar ku".
Wata irin muguwar dariya Boka Dürsäås ya sa ki,ita kuwa Bokanya Azizah ihu ta sa ki har ta na cangala k`afarta d`aya da dama ba ta kaiwa k`asa saboda murnar abinda su ka ji daga bakin Malikat Juwairiyya.
~~~~~
     "Me na ke yi anan,wa ya kawo ni nan, ya na ga jikina duk jini,me na aikata ,suwa kuma na kashe,waye ni a yanzu ,me ya ke faruwa da ni?", ya d`an tsagaita ba wai don tunanin wani zai ba shi amsa tarin tambayoyin da ya ke yi ma kan shi  ba.
"Wa ye ni a yanzu?!!!!,ya sa ke fad`a ya na mai sakin k`araji gami da k`ank`ame jikinsa wuri guda,sai faman tura hannayensa cikin gashin kansa ya ke,sosai jikinsa ke mak`yark`atar sanyi domin duk kayan jikinsa sun yage ko rigar kirki babu a jikinsa ,k`afar shi guda da ta bugu tun ya na cikin kurkuku sai faman rad`ad`i zugi da zafi da ta ke ma sa, jin motsin ko alamun tafiyar wani kusa da inda ya ke yasa shi sa ke lafewa a jikin bangon da ya ke,lokaci guda yanayin sanyi da zafi su ka riski gangar jikinsa wanda hakan ya k`ara sawa ya k`ank`ame jikinsa wuri guda, bakinsa sai rawa ya ke zuciyarsa ta cunkushe gami da curewa guri guda gaba ki d`aya tunaninsa da hankalinsa sun bar gangar jikinsa, ji da ganinsa sun fara d`aukewa dishi-dishi ya ke gani duhu ya fara mamaye dukkanin idanuwansa,lalube ya fara yi da hannayensa,ji ya ke ya fara rasa komi na sa da ya mallaka, jijiyoyin kansa sun fara fitowa rud`u-rud`u idanuwansa sun rikid`e sun yi ja,sannu-sannu a hankali komi ya fara lafawa ,jijiyoyin jikinsa sun fara komawa sun kwanta,idanuwansa sun koma dai-dai yanda su ke sai dai wannan karan tamkar a shafa nasa kwalli ya ji rambad`ad`au,tamkar ba shi ba haka ya mik`e tsaye tare da sa hannayensa a saman kansa ya kwance tarin himilin gashin da ke kansa ya barbaza shi ya na mai rufe ilahirin fuskarsa wata mik`a ya fara yi ya na mai cewa, "Oh sabuwar duniya,ina ne nan,kuma wannan wanne irin gari ne mai d`aukar hankali da sanya zuciya nishad`i ?,za ka shana NARSHAD da alama ka zo wani sabon wuri ne,fatana dai da akwai abun d`ebe kewa a cikinsa",ya k`are zancen cikin jin shauk`i da annashuwa rai ,fitowa yai ya na tafiya gami da had`awa da waige-waige da gani kasan bai san inda ya ke ba ,ko kuma bai san garin ba jefa k'afafunsa kawai ya ke, idanuwansa ya sauke kan wani gida mai danni gefe da shi kai tsaye can ya nufa ba tare da jin tsoro ko tunanin wani abu ba ya danna Kai ciki,cinkaro da tulunan ruwansu yai ba tare da ya tsaya dogon tunani ba ya za`bi guda d`aya daga ciki ya shek`a ma kansa shi ya na mai cud`awa don ya fidda jinin da ke jikinsa.
Motsin da mutanen Gidan su ka ji ne ya jawo hankalin su su ka fito da nufin ganin me ke faruwa,d`an tsohon da ya fara fitowa da k`ok`o a hannunsa ne ya ce," Uban waye a nan kuma me ka ke aikatawa ?".
Cikin Isa da da tunk`aho ya ba shi amsa da cewa,"Tsohon ka ne,na ce ma ka Baban ka ne".
Sai da tsohon ya d`an ja baya sakamakon jin abinda ya ce da shi,kafin ya ce da shi ,"Kai tsageran yaro nan da ka ke ji da gani na ba k`aramin d`an tasha ba ne ba nima,duk tujara da d`ibar albarkar ka sawun wasu ka tarar dan haka ka iya bakin ka kuma rik`e a kan ka nan k`asar BAIBAH ce k`asar da ke koyama dabba hankali ba ma mutum ba".
"Au haba,da gaske ka ke ?,amma ba na tunanin ka ta`ba cin karo da mutum mai kama da aljani kamar ni,ni d`in tamkar jirkitaccen yanayin mai saurin sauyawa a duk sanda ya so ni ke,ni d`in tamkar hawainiya na ke mai rikid`a zuwa launi-launi kuma a sanda na so!",ya k`are zancen cikin hargagi gami da sakin tulun ya fad`i k`asa ya tarwatse.
Matarsa ce ta fito tana mai cewa,"Haba kai ko wannan matashin saurayin mene ne ya ribace ka har ka jefa kan ka cikin irin wannan rayuwar kalli jikinka duk ciwuka ga jini duk ya bushe a wasu `bangarori na jikin ka,ba fa za ka ta`ba cin ribar rayuwa ba har sai ka iya tafiyar da rayuwa bisa sirad`i ko k`adamin rayuwa yanda ya kamata ya kuma dace da kai,zo d`ana matso kusa da ni".
    Idanuwan sa ya k`ara fiddo su waje sakamakon jin ta ambaci kalmar d`ana,har gefan kan shi ya kama ya rik`e alamun wani abu na yi mishi yawo ko kai kawo a cikin sa, da wani irin sauri ya matsa inda ta ke ba tare da ya sa ni ba ,sai dai ya na kusantar inda su ke ya fara shinshine-shinshine da alama dai hancin sa ya jiyo ma sa wani abu,wanda hakan ne ya d`auke hankalinsa game da abinda ya je yi kusa da ita.
     "Kamar da akwai burkutu a cikin Gidannan ?",ita ce tambayar da ya jefo,"Giya wai ka ke tambaya to aini d`in sana'ata kenan saida Burkutu,ko na d`auko ma  , ka na so ne za ka sha ?,amma fa ta saidawa ce ",ya na mai nuna d`akin da su ka fito da hannu alamun ta na ciki.
     Ko ta kansa Narshad bai tsaya ba ya bangaje shi ya shiga cikin d`akin ba tare da ya tsaya jiran komi ba ya kafa bakinsa a d`aya daga cikin tulunan da su ke a ciki,shan fitar hankali ya ke ma ta,in ya sha wannan sai ya ajiye ya d`auki wata duk a zatonsa da tunaninsa d`and`anonsu daban-daban ne,wani irin ihu yai yana wurgar da ta hannunsa alamun har yanzu bai sami wacce ta yi masa yanda ya je so ba.
     Da sauri  wannan d`an tsohon ya matso kusa da shi ya na cewa,"Ya ya dai ka ji zan-zan ko,ta kai ma ka karo,ka fara jin ka a sama ka na yawo?,".
"Ina ko kusa ko alama wannan ko marisa ba ta Isa ta sa ni ba balle har ta kai ni ga samun sanyi da salama kamar yanda na ke so".
"Ka biyo ni zan kai ka mashayarmu na rantse ma ka har da gemun kakana da akwai barasar da in ka shata baza ka iya gane ko Uwar da tai silar kawo ka duniya ba".
Da wani irin sauri ya nufe sa gami da had`a shi da jikin bangon d`akin ya ce da shi,"Kai k`azamin tsoho kar ka sa ke sanya  Uwata a duk cikin wani lamarin da zai shiga tsakanin mu in ba haka ba tabbas sai na shayar da kai ruwan mamaki".
"Na tuba ka gafarce ni ba zan k`ara aikata irin wannan kuskuren ba","Da dai ya fi ma ka,ma za mu je zuwa mashayar ta ku domin har na k`agara in ganni a cikinta",da haka su ka nufi hanyar da zata sada su da mashayar d`an tsohon ya na d`auke ko sanda wacce ya sagala tulunan Burkutun sa kamar yanda ya saba