LIL PRINCE 👑

Free page 1

by @anish

LIL PRINCE 👑 


[The story is All about Love 💗 Romantic 💘 heartbreak 💔 funny and dramatic]


By : Walee 🦋🦋


 The writer ✍🏻 of 
💐SAYYID RAJAT 💐
And Now 
LIL PRINCE 👑 



 DRÊÄM PÊÑ 🖊️ŠQUÄDŠ 

 ŸOUNG 🌱WRITTERS ✍🏻ASSOCIATION 


بِسْمِ الَّلهِ الْرَّحْمَنُ الرَّحِيمْ
Da sunan Allah mai rahma maijin qai, ina roqon Allah yanda nafara lafiya kasa ingama lafiya 
Ameen 



🫧🅿️………1



Wannan page naki ne aunty Meerah [Anish] marubuciya kuma ❤️❤️



 “Amnah Amnah ! " yarinyar da a ka kira da Amnah ta juyo smiling on her face sannan ta ce " yes Mah I’m coming " ta fada ta na daga yatsun hannunta qwara biyu
       Da dan gudu ta qarasa cikin dan kitchen din restaurant din ta na waqa kadan kadan 
" Ya rabbi Amnah ba na ce ki daina guje gujen nan ba , ba ki ganin kinfara girma ne ? “
         A shaqwabe ta na dira qafanta sannan tace " wayyo Mah ni ban wani girman da na yi " ta fadi tana turo cute mouth dinta mai kyawun kallo 
" Dauki tray ki jera moctail guda ukku sai burger ma guda 3 kikai ma wadan can da su ke a wancan table din “ Mah ta faɗa 
     Tsalle ta daka ta sake wani tsallen sannan tanufi tray din ta shirya komai kamar yanda a kace mata 
Bakinta dauke da murmushin da ya zame mata jiki take ta faman yi ta nufi wurinda suke 
         “Hello rich kids " ta fada ta na ajiye masu abunda sukayi order 
 Dariya su ka kwashe da ita su duka ukkun sannan wani acikin su yace " how are you cute girl ? “
    Murmushin ta sake saki sannan tace " I’m not a cute girl " ta fada ko a jinkinta 
Wani acikin su yace " why are you saying that? " ya fada yana tsare ta da ido 
     " Forget about that Sir " ta fadi hakan tana sara mashi da hannu irin taga police man din nan
Dariya suka saka su dukansu sai faman yi suke, dayan yaciro wayarshi tareda daga masu selfie su dukansu ,itama tashiga tana washe haqora wanda hakan yasa baqaramin kyau tayi ba 
    “Girkin Mah dina akwai dadi ko ? " ta fada ta na tsare su da ido 
“Sosaima kamar a qasar waje " , jin an yaba girkin mamanta yasa tayita murna tana tsalle 
Haka mutane ke ta kallonta suna murmushi,dan wasu saboda ita suke zuwa siyan abinci wurin 
“Hey little girl," wani daya iso yanzu yafada
    Smiling on her face ta juya ta na kallon shi sannan tace " I’m coming uncle “
Cikin muryarta mai dadi tacema wadannan " hope dai kullum zaku na zuwa ko ? ”
     “Yeah " su ka ba ta amsa a taqaice , su ma su na murmushin 

Menu tamiqa mashi yagama dubawa sannan yafada mata abunda yakeso 
Ba dadewa ta dawo hannunta dauke da gasassar kaza 🍗 

" Little girl " ya faɗa ya na kallon ta
" Yes sir " ta amsa mishi 
" How old are you ? "
“ 14 years old " ta fada ta na murmushi 
  Shikam ya bi ta da kallo sannan ya cigaba da cin abincinshi        

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
 *****************
  KINGDOM OF KATSINA 

Kasancewar kowa yasan masarautar katsina ta nada kyau basai an tsaya musaltawa ba 
Tun da na shigo masarautar na ke ta ganin fadawa ahaka dai nasamu muka shiga muda fans 
Wata matashiyar hajiya ce zaune a saman wata katafariyar sofa ta alfarma ga sarqar gold doguwa a wuyanta , fuskarta babu ko annuri 
“Bahijja dan ubanki kisan yanda zakiyi kijawo hankalin Prince a kanki ki samu ki aureshi kinga haka da ta faru zamu gaje masarauta , Idan kuma ya qiya zamu kawar dashi dan uwanki ya hau karagar mulki " tafada cikin tsabar mugunta hadi da dariyar shu’umanci 
Hannu bahijja ta ba ta suka tafa sannan tace " gaskiya Mama kin iya shirya makirci har kinfini, yo ay daman Mama idan na sace zuciyar LIL PRINCE to ay kaina na qara jawoma girma mutane za su so su ga wace ce matar shi , Kin kau ga mun qara matsayi " ta fada Ta na dariyar shu’umanci hadida qara tafawa itada Mamanta 
Ahankali take safkowa cikin isa da kissa fuskarta daukeda murmushi ga ta fara mai kyawu sai baza qamshi take tasha wasu irin manyan gold 
Qarasowa tayi cikin parlon tareda zaunawa a saman wata sofa dake facing nasu
Masu yimata hidima ne suka shigo wajen su biyar kowace hannunta dauke da tray dayaji kayan marmari kala kala 
Apple tadauka Tanaci har sai da taci rabi sannan tace " barka da hutawa " ta fada tana kallon gimbiya Maryamah 
“Barka " ta fadi tana yatsine fuska kamar wacce aka daka 
“Gobe insha allah Abdul hafeez na hanyar dawowa kinsan yadade rabonshi da Nigeria “
“Adawo lafiya " ta fada a yatsine tareda cewa ke bahijja tashi muwuce ciki 
Har sun nufi part dinsu sannan Bahijja ta ce " Mommy Allah ya maidoshi lapiya”
“Ameen bahijja “

   WASHE GARI🌤️⛅️

🌹🫧🫧🫧🫧🫧🫧 🌹
       Amnah :

Kamar kullum yanda ta saba zowa taya Mah dinta aiki a dan qaramin restaurant dinta na sayar da abinci na gargajiya dana qasashen qetare 
“My Amnah " haka wani matashin saurayi kuma kyakykyawa yake fadi yana sakar mata murmushi 
     “Oyoyo babban yaya kana lafiya ina Abbi yake?" 
“Yana gida shine ma yace nazo naduba ku”
“Yauwa muna lafiya yaya maleek yau dawuri zandawo gida sarauta nakeji “
“Onhi kedai bakida lafiya kindaura ma kanki san dan sarki, ke ina zakiga dan sarki balle yace har yana wani sanki “
“To yaya kana iya ganin hakan yafaru fa “
“Hum Allahu yahadiki yarinyar nan,13years da maganar aure dan bakida kunya “
Hannunta tasa tarufe face dinta sanna tace " ay yaya dan sarki zan aura”
Mtwss yaja tsoki yawuce 
Dariya ta tuntsure da ita sannan tabi bayanshi 

🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋

  PARIS 

🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋

Allahu Akhbar Allahu Akhbar,tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin da yayi halitta 
Ni dai walee na zauce bareku fans 
To muhadu a kashi nagaba domin jin qarashin labarin 

Ranakun posting 
Litinin da Alhamis insha allah 
Dan Allah ariqa sharhi yana qaramani qwarin gwiwa ❤️❤️
Love you all my dearest fans ❤️🌹💗😁