LIL PRINCE ๐Ÿ‘‘

Free page 10 to 15

by @anish


Mamaki a fuskar mamie da Abbie har sun kasa magana 
Murmushi baquwar ta saki tare da qarasawa ta zauna a saman wata 3 seater sannan ta ce " tun da ba za ku ce na zauna ba bari na yi zamana "
Mamie ta saki dariya tare da fadin " wallahi aunty Ameerah ba kyada kirki shine sai yau ko ,to ya Abroad din fatan komai lafiya "
" Humm " ta fada tare da ce wa " wallahi Alhamdulillah ai da ya ke ni dai na dawo Nigeria da zama shikuma sai yana zowa ya hutawa sannan ya koma wurin aikin shi "
Abbie ya ce " Barka da zuwa hajiya Ameerah ya kike ya mai gidan da iyali fatan komai lafiya, Amma fa muna fushi gaskiya " 
Dariya tayi sannan ta ce " wallahi duka Alhamdulillah, Ayimana haquri dan Allah tun da yanzu ga shi na zo sai naje har gidan daughter dina sannan na koma abuja " ta fada Ta na dariya 
" Ay yanzu Chan za mu je amma ni na fasa sai ku je keda follows " ya fada yana mai kallon mamie sukayi dariya su duka 
" Amma wani hanzari ba gudu ba mamien Amnah, gajiya ku ka yi da ita da har zaku aurar da yarinya kamar Amnah wacce ko secondary school bata gama ba fa "
" Wallahi aunty Ameera gwara ace Amnah Tana gidan mijin ta , duk family dinmu babu mai kyawunta kuma tun kafin iyayenshi suzo maganar auren nan ko ,maza nata kawo mata farmaki a cikin rayuwa , Hakanan na ji a jikina zan iya Bayarda auren Amnah a gareshi sannan kuma iyayenshi mutanen kirki ne sosai duk da dai ba mu taba ganin Angon ba ma " 
Aunty ameerah Baki ta bude Ta na kallon mamie da Abbie sannan ta ce " idan iyayenshi mutanen kirki ne shi kunsan halinshi ,kunsan ya na sonta ko baya so Amma Allah yasa hakan yafi zama Alkairi "

A taqaice
Aunty Ameerah itace babbar gidansu mamie , fulani ne sudukansu irin fulanin asali dinnan masu mugun kyau ,iyayensu su hudu suka Haifa daga Ameerah sai wani namiji sai mace sannan Mamie Wanda takasance itace auta , Cikin ikon Allah sai Duka biyun suka Rasu yarage saura Ameerah da Mamie , Sai da su ka gama aurar da yayansu mata guda biyu Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa sanadiyar ciwon Cancer , Su Ameerah da mamie sun sha kuka sosai ,sai da suka dade kafin suka koma birni gidajen mazajensu sunyi sunyi sutafi da Dada watakam mahaifiyarsu amma taqi yarda ita ba za ta je ko ina ba tabar Asalinta , Bayan rasuwar baffan su mamie da wata daya Arziqin mijin Ameerah yanata qara habbaka hakan yasa babban yaronta tunda ta yayeshi suka koma qasar Istanbul da zama , Har Allah yasa itama tahaifi santalelen yaronta yaci Suna Abdul maleek bayan haihuwarshi da kwanaki kadan DaDa tarasu, hakan ba qaramin ciwo yayiwa mamie ba ga shi mijinta ba wani hali gareshi, Ameerah ma tun da su ka ji rasuwar su ka zo Nigeria ,sun dade kafin su koma Istanbul sannan ta budewa mamie wani madaidaicin restaurant a kusa da anguwarsu saboda ba qaramin iya girki tayi ba , Gida ma saida suka gyara masu sukayi masu duk abunda ya kamata sannan suka koma Istanbul ,Abbie dama maraya ne iyayensa duk Allah yayi masu rasuwa sannan kuma shi kadai suka haifa 
Wannan shine taqaitaccen labarinsu 
_____________๐ŸŒน๐ŸŒน_________๐ŸŒน๐ŸŒน___________________

Back to story 

Abbie ne ya ce " to yanzu a yi haquri tun da mai faruwa ya faru ameerah duk da dai ba mu san Al,amarin Allah ba "
" Shikenan yanzu mamie bani ruwa masha sai mu wuce " ta fada Ta na gyara wani hadadden veil dinta mai kyau da tsada 
Snacks da drinks kala-kala aka kawoma Auntie Ameerah, sai da ta ci ta sha Ta cika cikinta su ka dan yi fira sannan su ka tafi yayinda driver din Aunty Ameerah ya tuqasu har suka isa katafariyar masarautar , Sai da su ka shiga ga fadawa nan iri iri,basu shiga ba sai da a ka yo masu iso wurin Mommy ta yarda sannan su ka shiga , Ai kam tarba mai kyau su ka samu da ga wurin mommy din yayinda Amnah Ta na toilet Ta na wanka , Ba dadewa da isowar su Mamie ita kuma ta fito da ga toilet, Amnah ba qaramin kyau da girman jiki ta qara ba ,idan bakasan shekarunta ba sai ka rantse tayi 18years , Wani irin lotions masu kyau ta ke shafawa ga skin dinta sai mugun qyalli ya ke yi , Rahama sai da ta gama gaisawa da iyayen Amnah cikin mutunci sannan ta shigo dakin Bakinta daukeda sallama ta qarasa wurinda Amnah take zaune Ta na shafe shafe a gaban mirror 
" Princess " Rahama tafada Ta na saka hannunta a gashin Amnah tare da taje mata kan sannan tasaka ribbon ta yi mata parking gashin tare da bazo shi har baya gwanin burgewa 
" Kashh rahama Wai dan Allah miye" ta fada cikin yar shaqwaaba 
Dariya rahama tayi tare da fadin " Albishirinki "
" Goro " ta fada a taqaice 
" Gaskiya princess ba zan fada maki ba sai kin ba ni Tukwici sannan na fara kuma za ki ji dadi "
" Toh fara fada min dai yanzu " 
" Kai Amaryar lil Prince na san ki da mugun Wayo sai kin fara ba ni sannan dai "
Wani irin hade rai tayi sannan ta ce " Ba na so na ji baki daya ma " ta fada Ta na miqewa tare da nufar inda kayanta suke , Ita kam Rahama sosai Amnah ta shiga cikin ranta hakan yasa kullum burgeta takeyi hadida fatar Allah ya hada kawunansu ita da yayanta , Wata maroon Abaya ta saka wacce ta ji adon wasu beads black and red color sanna ta dan yi rolling veil tare da saka maroon shoes fish shape , Kasancewar akwaita da iya daukar wanka ga tafiyarta mai tafiya da zuciya , Saida taje gaba mirror ta kalli kanta sannan ta saka dan kunne shina maroon and silver color ta fesa perfume mai qamshi, dan murmushi ta saki tare da kama hannun rahama wacce ta kasance Aminiyarta sannan su ka bar part din baki daya , Saida suka fara saukowa daga stairs ta ke jin wasu voice dinda kamar ta san su , Sauri ta qara yi suka sauka qasa , abun da ta yi tozali da shi ne ya sa ta saki wani malalacin murmushi tare da Rugawa da gudu tafada kan Mamie 
Wani marayan kuka tasaki mai tafiya da zuciyar mai karatu, Rungume junansu su ka qara yi Wanda ya sa sai da Mamie ta dan yi hawaye hadi da murmushi 
Kowa na cikin parlorn sai da hakan ya sa sukayi hawaye ba mommy ba ,ba Aunty Ameerah ba ,Ba Rahama ba 
Mommy ta miqe hadi da nufar part din ta zuciyarta na wani irin bugawa 
Sundade a haka sannan su ka saki junansu, Aunty Ameerah ta nufa hadi da rungume ta ta yi zamanta a cinyarta 
Nan suka fara Fira kadan kadan, Aunty Ameera ta ce " Amnah fatan komai ya na tafiya lafiya ko ? "
Shuru ta yi ba tare da ta ce mata komai ba sannan tayi qasa da kanta Ta na wasa da yatsun hannunta 
" Amnah magana da nake maki kina jina ,ina mijinki da fatan shima komai yana tafiya lafiya kuma ya na kula dake yanda ya kamata ko "
Wani irin kuka ta saki tare da saka hannunta Ta na rufe fuskarta ,kukan ma kubce mata yayi saboda tasaka a ranta bazaar fadawa kowa ba 
Duk da Amnah yarinya ce Amma ta na da hankali da tunani sosai tun da har zata iya Adana sirrin mijinta 
" Subhanallah " ta fada Ta na kallon Mamie irin kallon nan mai nuni da kin ga abun da na guda ko , Amma a fili sai ta ce wa Amnah " ke ba na son sakarci mi ye na kuka to daga tambaya,ko bakya jin dadin zaman gidan "
Cikin kuka ta ce " Ni dai Ummu please ku tafi da ni gida na gaji dan Allah kuma bawai dan basu kula da ni,Su na kula da ni tamkar yar da suka Haifa a cikinsu "
" To kuma miye na kuka tun da Su na kula da ke Amnah,ban son rashin godiyar Allah , Sannan kuma shi mijin naki babu wata matsala a tsakaninku ko ? ,sannan kina mashi biyayya yanda ki ka ga mahaifiyarki na yi ma babanki "
Still dai ba ta ce komai ba ta yi qasa da kanta Ta na goge hawaye 
" Ke ba ni son wulaqanci fah "
" To ummu Ni ma sau daya nataba ganinshi fa "
Cikin sauri mamie ta dago da kanta Ta na kallonta 


*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , โ‚ฆ200 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP DIN*
 DM : +22798999753


๐Ÿ‘‘ LIL PRINCE ๐Ÿ‘‘ 


{The story is all about love โค๏ธ Romantic ๐Ÿ’˜ heart break and dramatic}

By 

AID WALEE 

The writer of 
๐ŸŒนSAYYID RAJAT ๐ŸŒน
And now 
๐Ÿ‘‘LIL PRINCE ๐Ÿ‘‘


TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANEL 
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
***


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… 




๐Ÿ…ฟ๏ธโ€ฆโ€ฆโ€ฆโ€ฆโ€ฆ12 ๐Ÿฅ€




Cikin sauri mamie ta dago da kanta Ta na kallonta , Dai dai lokacin da Mommy tadawo a cikin parlorn 
Aunty Ameera ta ce " princess Ba ki qara ganinshi ba, ? miye ya faru ? "
Kuka ta qara fashewa dashi mai qarfi,Aunty Ameerah tayi saurin mayar da ita a qirjinta Ta na rarrashinta 
Mommy tazauna a wata 2 seater ranta ba dadi sannan ta yi gyara murya tare da fadin " Dan Allah ku gafarcemu, tafiya ta taso masa ta gaggawa a lokacin shiyasa yatafi amma ya kusa dawowa insha Allah "
A hankali Mamie tadan sauke ajiyar zuciya sannan ta ce " babu komai Allah ya maidoshi lafiya "
Ameen mommy da Aunty Ameera su ka fada a tare 
Alhamdulillah mommy ta fada cikin ranta tareda cewa Allah na gode maka da ba ta fadi aika aikar da yaron nan ya yi ba 
Sun dade Su na fira sai bayan sallar la,asar suka tafi, an yi musu shatara ta arziqi kam tareda kaisu suka gaishe da mai martaba 

 ____๐ŸŒน_____ PARIS ๐Ÿ•Š๏ธ ____๐ŸŒน_____

11 pm

Iska mai dadi ta ke kadawa Wanda ba qaramin jin dadin yanayin yakeyi ba ,A hankali yake tsotse lip dinshi na qasa hadida lumshe idanunshi 
A saman wata table chair yake zaune hannunshi riqeda qatuwar chocolate da Alamu ya na shan chocolate din ne, a saman table din kam daukeda wata yar qaramar buta ta glass ga cups nan qanana sai uwayen chocolate da biscuit a saman wani heart plate 
Slowly ya miqe tare da nufar window din da ya ke fessing ya bude ta hakan ya sa labulayen dake wurin suke kadawa gwanin burgewa ,daga waje kam flowers ne masu kyau suma sai kadawa su ke 
Dawowa ya yi ya zauna ya sha wasu sleeping dress blue color, bedroom din babu haske sosai sai blue light da ke haska in da ya ke 
A hankali ya ke rufe idanunshi ya na budewa kamar mai dan ya tuna wani abu, Amma ya kasa haka kullum yake fama ya zama kamar marar lafiya , Kullum da ya fara qoqarin tuna wani Abu mai mahimmanci a rayuwarshi amma sai kanshi yafara ciwo hadida jin juwa 
Gently ya miqe ya mayar da chocolates din a fridge sannan yakoma ya zauna, ya dauki good minutes a haka sannan yasake miqewa idanunshi a rufe 
Haka ya yi ta kai kawo a tsakar dakin ya rasa mike mashi dadi a duniyar ,qoqarin yin addu,a yake amma yakasa ,fuskarsa ce tayi jawurr sosai 
Cikin sauri ya dafe kanshi tareda fadawa saman bed kanshi na wani irin ciwo , Ya na a haka har bacci ya yi gaba dashi 
Mu dai sai muce Allah ya kyauta, Asuba ta gari Lil Prince 

๐Ÿ•Š๏ธNIGERIA ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ 

11:45 pm

Dariyarsu su ke ta faman yi sannan bahijja ta ce " mama gaskiya komai na tafiya dai dai ,yanzu fa Saura 2 weeks ya cika 4 month da yin auren nan kin ga da mun gama da wannan sai mukoma kan waccen shegiyar kuma yaya zai yi wannan aikin kanta "
Hahahaโ€ฆ.hahaha mama ke wannan dariyar tare da fadin " Tabbas aikin nan ya na yi, kin ga fa yanda shegiyar take kullum cikin damuwa ta ke har ta rame " ta fada Tana qara wata dariyar 
Ita ma bahijja dariyar ta ke sannan ta ce " kuma kinga idan har yaji muryarta to komai fa ya lalace ,Amma ba zai taba Nina saboda ko phone bata dashi kuma baya magana da kowa nashi, gaskiya mama a taba maki ke ba qaramar muguwa ba ce "
" Zan ci tsohon matsiyacin ubanki fa ,ina daura ki kan dai dai kina fadin ni muguwa ce ,to wannan shi ne hanyar dai dai ki bi boka ki samu biyan buqatarki dawuri "
Hummm kawai bahijja ta fada sannan ta miqe ta nufi dakinta 

Misalin qarfe 3 na dare 

Mommy 

Sallah ta ke Ta faman yi ,idan tayi sujjada sai tafi 6 minutes bata dagoba, " ya ubangijin rahama kai ne kadai masanin gaibi kai ne kasan halin da ya ke a ciki ya Allah ka warware mashi matsalarshi ka tsareshi daga sharrin mugun ko Aljan ka maido shi lafiya a cikin Ahalinshi "
Haka ta cigaba da adduโ€™oi kala -kala, bata daina sallar ba saida aka gama sallar Asuba har rana ta fara fitowa sannan tayi sallar walha
Sai da ta gama tsaf sannan ta miqe hadi da fadawa toilet tayi wanka tayi brush sannan ta fito ta shirya cikin shigar Alfarma , Lokacin da ta ke saukowa da ga stairs ta hangi Amnah Ta na faman shirya abinci a dining area , Ita kuma Rahama ta na ta faman saka turaren wuta a parlorn ,ko ina tsaf gwanin burgewa 
Aranta ta ce " ikon Allah ,yarinya qarama duk ta iya aiki har haka ga girki idan tayi ba,a magana Prince kayiwa kanka ,ina tsoron time ya ida dolene a raba auren nan nasani saboda ko musulunci ya fitar da lokacin da za,a raba aure muddin ma,auratan basu tare da junansu kuma akwai aure tsakani "
Innalillah ta fada Ta na qarasawa in da su ke sannan ta ce " sannunku da aiki yaran kirki, Allah ya yi ma rayuwarku Albarka "
Ameen ya Allah suka fada a tare, sai da mommy ta fiddawa mai martaba Wanda zai ci ta kai masa har part dinshi sannan ta dawo suka fara breakfast din A tare 
Sai da su ka gama tsaf sannan mommy ta ce " Amnah idan kin gama ki je dakina a kwai waya da sim dakina sai ki dauka, Rahama sai ta tayaki settings apps ko "
Murmushi ta saki tare da fadin " Nagode sosai mommy Allah ya saka maki da Alkhairi "
" Ameen ya Allah " ta fada Ta na miqewa ta bar part din 
Dariyar murna su ka saki ita da Rahama sannan su ka bar dining room din tare da nufa part din mommy 

  Walee โœŒ๏ธ 


Muhadu a page nagaba ๐Ÿ™Œโœจ


*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , โ‚ฆ200 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP DIN*
 DM : +22798999753

๐Ÿ‘‘ LIL PRINCE ๐Ÿ‘‘ 


{The story is all about love โค๏ธ Romantic ๐Ÿ’˜ heart break and dramatic}

By 

AID WALEE 

The writer of 
๐ŸŒนSAYYID RAJAT ๐ŸŒน
And now 
๐Ÿ‘‘LIL PRINCE ๐Ÿ‘‘


TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANEL 
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
***


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… 



BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM


๐Ÿ…ฟ๏ธโ€ฆโ€ฆ13 ๐ŸŽ€


__________๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท__________๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท


Dariyar murna su ka saki ita da Rahama sannan su ka bar dining room din tare da nufa part din mommy 
Waya ce lafiyayya qirar IPhone 14pro max purple color, ga punch guda ukku daya pink daya white daya blue sai Bluetooth da charger abun gwanin burgewa 
Murna kam bata musaltuwa wajen Amnah hakan ya sa tarungume Rahama Suna murna , Nan suka zauna su ka yi ta setting komai tare da dakko apps WhatsApp, instagram, TikTok da sauransu , Haka su ka yini kowace na latsar wayarta 

AFTER 2 WEEKS 

Zaune ya ke a office ya kifa kanshi a table din , wayarshi ce keta faman ringing yafi sau 5 sai na six din ne ya duba ,dan tabe Baki yayi ganin number din daga Nigeria ne , Picking call din ya yi tare da karawa a kunne
 Cikin kuka a ke fadin " ka cuce ni ka lalata min rayuwa tin ina qaramata , na tsane ka ba ni qaunarka har Abada Allah ya saka min abun da ka min " ta qarashe maganar Ta na kuka mai qarfi 
Sai a lokacin abubuwa suka fara dawo mashi cikin kai ",Innalillahi waโ€™inna ilaihirrajiโ€™un " ya fada ya na dafe kanshi , Fuskarsa ce ta yi red sosai sai a lokacin kamanninshi su ka dawo na jinin sarauta 

NIGERIA 

Fadar mai martaba 

Zaune su ke a fada da ka kalli fuskarsu ka san babu farinciki a ciki 
Nan mai Martaba ya juya kallonshi yana kallon mahaifin Amnah sannan ya fara da fadin " ina mai Baku haquri Akan abunda yafaru nasan bakuji dadi ba , Ni ma ko da diyata ce bazan ji dadi ba Amma dan Allah ina mai baku haquri , Sannan kuma Kun yi gaskiya ,Aure kam dole za,a rabashi kamar yanda kuka fada dukda dama fadi ne na addinin musulunci , Akwai watannin da ya gida Wanda dole zaโ€™a raba aure muddin akwai aure tsakani kuma basu a tare ba tare da wani dalili mai qarfi ba "
Mommy hawaye ke ta zuba a fuskarta haka ita ma mamie da ke zaune a gefenta ,mai martaba shi ma daka kalli fuskarsa kasan baya jin dadi ga shi su damuwa biyu tahade masu 
Da ga liman sai qanen sarki watakam mahaifin zully, wakilan Ango Dana amarya duk suna nan ,babu yanda su ka iya haka a ka raba auren 
Zaune ta ke ita da rahama suma duk sun damu dukda ba su san mi ke faruwa ba 
Wani irin bugu qirjinta ya yi hakan yasa ta dafe shi da qarfi sannan ta fadi innalillahi.. bata qarasa ba kuka mai qarfi ya kubce mata 
                    
 PARIS ๐ŸŒท๐Ÿ•Š๏ธ

Miqewa ya zoyi da sauri ya koma ya zauna sanadin wani irin bugu da qirjinshi ke yi 
" Ya Rabbi make everything easy for me ,innalillahi waโ€™inna ilaihirrajiโ€™un " ya ke ta maimaitawa har sai da ya samu sauki
A hankali voice dinta ke dawo mashi cikin kai ,take wata muguwar soyayyarta tafara mashi yawo a ko wane sashen jikinshi 
Murmushi ya saki Wanda ya bayyana kyawun shi ,tunda ya dawo bai taba murmushi irin wannan ba , Idanunshi yarufe take ta fara fado mashi a ido ranar da mommy ta ce ya zo ya dauke ta 
Gashinta mai tsawo da qyalli yake hangs da kuma tsantsar yarintar da ke gare ta ,cikin sauri ya bude idonshi tare da fadin " Astagfirullah ,why na aikata haka a gareta sheโ€™s so small " ya fada cikin wata muryar shagwaba 
" But Iโ€™m falling in love with that small girl " smiling on his face gently ya miqe ya bar office din 
Sai da ya isa katafaren gidanshi mai mugun kyawu, sai da yayi wanka yay sallah sannan yasa a ka mashi order din abinci ya ci Wanda rabonshi da abinci har ya mance 
Sai da a ka kawo mashi wata biryani rice yaci ya hada da drinks sannan ya dauko wayarshi yanata murmushi 
Mommyna na ga ya danna wa kira ,yayimata missed call yafi 20 Amma bata daga 
" Ya Allah ,ni raban da na ji muryarki har na manta " ya fada a cikin damuwa 
Daddy ya kira shima bai daga ba ,to lafiya ya fada cikin damuwa , Nan ya fara duba missed call din wayar shi nan ya ga uban kiran da mommy tamishi 
Subhanallah ya fada tare da miqewa ya fita harabar gidan har yana wata zufa , Ya na tafiya waya kange a kunnenshi, kamin ya qarasa wani bature ya iso wurin 
Cikin harshen turanci su ke maganarsu har su ka gama 


      WASHEGARI ๐Ÿ’๐Ÿ•Š๏ธ

7:30 ya bi private jet su kayo Nigeria, 10:00 ya isa katsina har cikin masarautar su 
Fadawa sai faman baza mashi gaisuwa su ke ta ko ina sai dai burinshi ya qarasa ciki 
Babban parlorn gidan ya nufa Baki daya Wanda zai iya samun duka A halinshi a ciki 
Baki daukeda sallama ya shigo cikin parlorn ,kowanensu ba ki a sake ya juyo ya na kallonshi 
Fuskarsa ba yabo babu fallasa yashiga ya zauna a gefen mai martaba 

Wani irin lafiyayyen Mari ya daukeshi dashi tareda fadin " idan ba ka bar nan ba duk abun da na maka kai ka so mutanen banza har ni za ka wulaqanta cikin qasar nan AbdulHafeez ,Duka nawa ka ke da zan ba ka umarni ka qi yi "
Cikin lokaci kadan fuskarsa tayi jawurr idanunshi sunyi wani irin red, kanshi a qasa ba tare da ya ce komai ba 
" Tashi ka ba ni wuri tun da har za ka watsar da umarnin Da na ba ka ,mu na ta faman kiran wayarka amma sai yau kaga damar kiranmu Qila ka saka a duba maka randa zan war ware auren shi ne sai ka dawo ko , to hankalinka ya kwanta aure ni Da na daura na warwareshi "
Wata razana yayi yadaga kai yana kallon daddy ,idanunshi sun qara yin jawurr bakinshi na kyarma ya ce " daddy why? "


By Walee 
*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , โ‚ฆ200 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP DIN*
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
A tura Receipt ta wannan number
 DM : +22798999753

๐Ÿ‘‘ LIL PRINCE ๐Ÿ‘‘ 


{The story is all about love โค๏ธ Romantic ๐Ÿ’˜ heart break and dramatic}

By 

AID WALEE 

The writer of 
๐ŸŒนSAYYID RAJAT ๐ŸŒน
And now 
๐Ÿ‘‘LIL PRINCE ๐Ÿ‘‘


TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANEL 
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
***


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… 



BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM



๐Ÿ…ฟ๏ธโ€ฆ..14โ™ฅ๏ธ


Wata razana yayi yadaga kai yana kallon daddy ,idanunshi sun qara yin jawurr bakinshi na kyarma ya ce " daddy why? "
" Aw rashin kunyar naka ya kai har ka tambaye ni mi ya sa ko ,idan kai baka da hankali sai a ka ce Ni ma ba ni da shi "
Mommy ta ce " dan Allah ka mishi huquri mu ji mi ya same shi ka ga fa duk ya rame "
Tsoki daddy ya yi tare da kauda kanshi 
Bahijja da Mamah sun riga da sunsha jinin jikinsu ga AC amma sai faman zufa su ke yi 

AMNAH POV: ๐ŸŒท๐Ÿ•Š๏ธ

Kuka Tasha sosai har idanunta sunyi qato, Ita ta rasa mike mata dadi, prince kam ta riga da Ta tsane shi 
Auntie Ameerah ita ce keta bata baki ,Dan kowa na gidan ranshi babu dadi , Yay maleek ma da ya ji ,flight ya biyo ya taho Nigeria 
Kowa kam ba qaramin tausayi Amnah take bashi ba 

PRINCE POV:๐Ÿ’•๐Ÿ‘‘

" Daddy wallahi tun da na je na rasa gane mi ke min dadi ,kamar anyi formatting brain dina haka na ke jin komai, Da na fara qoqarin tuna abu sai kaina yayita min ciwo Kuma Allah ina sonta daddy , Daddy wallahi I Donโ€™t want to loosing her, daddy I canโ€™t live without her, I really love her daddy! The first time Da na fara ganinta ta taimake ni kuma tun a lokacin na kamu da sonta daddy , Mi ya sa a ka raba aurennan daddy ? " ,ya qarashe maganar voice dinshi na rawa 
Kowa kallinshi ya ke suna mamakin wadannan maganganun da ga bakinshi , Lallai so Ba qaramin abu ba ne 
A hankali ya miqe ya bar part din tare da nufar nashi 
Ko daya shiga part dinshi bedroom kawai ya nufa tare da fadawa saman bed ko takalmi Bai cireba, wani irin gumi yake fiddawa , Ita kawai yake tunani ya na hasashen ya zai yi ya gan ta a yau , Da sauri ya fiddo waya ya dannanma jawwad kira, Cikin saโ€™a kam yayi picking call din
" Lil prince " jawwad ya fada ya na dariya
" Malam dan Allah turomin adress din gidansu yarinyar nan "
" Wacce yarinya kenan "
" Dan Allah Amaryata "
Dariya ya kece da ita tareda fadin " A masha Allah Harda wani cewa Amaryata but ba za ka tambayeta ba "
Cikin damuwa ya soma fada mashi duk abunda ya faru 
Shima cikin damuwa ya ce " Prince why ka aikata mata haka kuma ka na ganin yarinya ce sosai fa sannan kuma ka yi mata haka sai ka bar qasar baki daya ma, gaskiya ba ka kyauta ba "
" Wallahi sai da ga baya duk na ke jin ban kyauta ba, wallahi Allah kamar an yi min wankin brain ko iyayena bani iya tunawa ,kai Azkhar ma bana iya yi , Tun da na koma na ke cikin damuwa jawwad, wallahi zan iya rasa raina Idan har narasa Amnah saboda ita din farincikna ce da kwanciyar hankalina kai ita din rayuwata ce baki daya , Tun ranar da na fara ganinta na fara qaunar ta jawwad, yanxu daddy ya ce ba zai yi komai ba sai dai ni da kaina na yi , Zan je na roqi iyayenta da su yafe min su ba ni ita " 
Ajiyar zuciya jawwad ya saki sannan ya ce " na sani Dama ka na sonta do ne kawai dai taurin kaine irin naka ya hana ka , Sannan kuma ka dage da adduโ€™a muma zamu taya ka insha Allah Bari na turo maka address din " , Bankwana sukayi sannan suka ajiye phones din 
Ba dadewa yay jawwad ya turawa address din gidansu Amnah 
Yana gani ya miqe ya fada toilet ya yi wanka cikin sauri ya fito ya shirya cikin wata farar shadda wanda lokacin ne kari na biyi da ya taba saka manyan kaya 
Wannan fitinanne turaren ya shafa sosai sannan ya saka black cover shoes ,Wani mugun kyawu ya yi wanda baya musaltuwa abun sai wanda ya gani , Bedside drawer ya bude tare da daukar keys din sabuwar motarshi sannan ya dauki phones dinshi ya fita ya nata sauri 
Misalin qarfe 12:39 ya isa kofar gidansu dai dai fitar motar aunty ameerah wacce zasu tafi Abuja ita da Amnah .

By walee โœŒ๏ธ๐Ÿ˜

*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , โ‚ฆ200 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP DIN*
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
 DM : +22798999753 ku tura shaida ta wannan number 

๐Ÿ‘‘ LIL PRINCE ๐Ÿ‘‘ 


{The story is all about love โค๏ธ Romantic ๐Ÿ’˜ heart break and dramatic}

By 

AID WALEE 

The writer of 
๐ŸŒนSAYYID RAJAT ๐ŸŒน
And now 
๐Ÿ‘‘LIL PRINCE ๐Ÿ‘‘


TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANEL 
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
***


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… 



BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM


๐Ÿ…ฟ๏ธ......15 ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’”



Gate keeper Bai rufe gate ba hakan ya ba shi damar antayawa cikin gidan 
Wani irin qamshin turare ta ji wanda ta rasa ina tasan turaren ,hakan yasa ta lumshe idanu tana shaqar qamshin 
Aunty Ameerah ta ce ko " waye ya shiga da motar nan mai mugun kyau " ,baโ€™a dade da fitowa da ita ba har ta zo Nigeria ko waye wannan ba qaramin shege ba ne 
Ita dai ta na Jin aunty Ameerah amma ba ta ce komai ba 
Su na isa Airport drivern aunty Ameerah shi ma ya iso ,kayan su ya kwashe masu tsaff tareda kai wa idan da,a saka kayan cikin jirgi 
Key ta ba shi ya hau hanya su kuma su ka shige jirgi, dukda cewa wannan shine kari na farko da ta fara shiga 

PRINCE ๐Ÿ‘‘ POV: 

Sai da a ka mashi iso sannan ya shiga directly parlorn da suke cen yashiga baki dauke da sallama 
Mamie da Abbie ne a parlorn haka suka amsa gaisuwarsa fuskarsu a sake 
Abbie ya ce " ka zauna mana a kujera za ka gaji da zuqunni " ,a yar kunyace ya miqe ya hau kujerar sannan ya ce " Abbie mamie na zo ne dan in nemi yafiyarku A kan abun da ya faru "
Cikin damuwa ya ce " wallahi tin da na koma Paris na daina samun kwanciyar hankali komai nawa namance Narasa miyafaru hatta iyayena wlh namance , Sai rannan kawai aka kirani da new number daga Nigeria duk ina cikin yanayin, Tunda naji muryarta wallahi sai na ji kamar Ana mayarmin da abubuwa ,washegarin ranar tun safe nadawo Nigeria , Ina zuwa gida mai martaba ya fara min fada sai daga qarshe yacemin Wai an raba auren kuma wallahi mamie ina sonta " 
Saukowa yayi ya koma saitin Abbie, gwiwowinshi a qasa tare da hada hannunshi sannan ya ce " dan Allah Abbie a mayar da aurenan wallahi ina sonta zan fada raina idan har narasata , Abbie mamie Amnah tawa ce ni kadai nima natane ita kadai ,ita ce raunina A rayuwa " ya qarashe maganar fuskarsa ta yi jawurr 

Mamie kam wani irin tausayin shi ya kama ta ," Allah ya yi mana jagora " ta fada kawai 
Abbie ya ce " a wancen karin munyi mata aure da kai ba dan ranta ya na so ba kuma ta yarda ta bi umarnin mu, Amma yanzu ka je da kanka ka neme ta duk yanda ku ka yi to Alhamdulillah a yanxu ma bata nan , shigowarka da mota su ma su ka fita qilama ka gan su "
" Innalillahi waโ€™inna ilaihirrajiโ€™un ya fada tare da fadin " yanzu ta ina zanje "
" Ka yi haquri ta qara hucewa sai ka neme ta ko " cewar mamie 
" Tohm amma yanxu ta na ina ? "
Mamie ta ce " wallahi ba zan iya sanin ta qaita ccen wurin da suka tafiba ahalin yanxu sai dai idan munyi waya sai in ji su "
Ya salam ya furta cikin ranshi tare da miqewa jiki a sanyaye ya yi masu bankwana ya fice 
Yafi 40 minutes a cikin motar ba tare da ya tayar da ita ba kanshi ya kifa zuciyarshi ba dadi , A hankali ya tayar da motar ya fice daga gidan cikin wani mugun gudu , Bai tsaya ko ina ba sai katsina guess in wata hotel dake cikin garin katsina , Room ya kama ya shige tare da sakawa dakin key , Bed ya fada yayi hugging pillow fuskarsa tayi jawurr ,idanunshi sun cenza kamanni 
Wayarshi ya dauka tare da latsa power dinta ,wani picture dinta wallpaper din wayar , Ranar da yatafi da ita daga dakin mommy, a time din da zata shiga wanka Tana warware gashinta 
Picture din ba qaramin kyau yayi ba ,ga gashin ya wani bazo gwanin burgewa 
             
 Abuja Nigeria ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ 

AMNAH POV โค๏ธ
misalin qarfe 2:00 suka shiga cikin state dinsu Aunty Ameera , Gate man ya shigar da akwatin kayan har cikin wani katafaren parlor da ke gidan , Su ma shiga su ka yi bakinsu dauke da sallama ,wasu yan mata ne guda biyu zaune a saman sofa da ka gan su ka san rainon madara ne da ice cream 
Wacce ke zaune da ga ita sai pink din Riga da wando ta ba zo gashin kanta tubarkallah Ta na da kyau sosai 
" Laa ummu you are welcome " ta fada ta na miqewa ta rigo ta rungume ta, ummu " ta ce me too my zarah hope you are fine "
Ita ma dayar tashi ta yi ta na turo baki cikin sigar shaqwaba ta ce " ummu ni ba ki yi kewana ba ko ? "
Dariya ta yi ta rungume su su biyun sannan ta ce " na yi kewar ku mana ku dukan ku "
Dukan su kansu daya da ga ganin yanda su ke muguwar kama twins ne zarah da Sarah ba za su wuce 19 years ba su duka 
" Tohm Allah yayi ma ku Albarka my twinโ€™s, " 
Ameen suka amsa a tare 
Juyawa ta yi tana kallon Amnah da ta riga da ta fada cikin zurfin tinanin da ta saba 
" Ummu kamar Amnah ko , ita ce Amaryar ko ummu " cewar sarah 
Wani irin Abu ta ji ya soke ta a ranta sai dai ta dan saki murmushin qarfin hali 
Ummu ta ce " yanzu dai duk ba wannan ba mu je mu zauna please "
Sarah da zarah su ka kama hannunta su ka ida shiga har cikin parlorn tare da zama saman sofa , Ma su aiki a ka saka su ka kawo masu girki mai rai da lafiya ,sai da a ka jera komai a dining room sannan su ka koma chan
Sultan chips ne da macaroni salad sai Pepper chicken da cucumber juice 
Amnah kam Abinci yanzu ya daina mata dadin ci ,ji ta ke tamkar an canza mata rayuwa komai ba ya mata dadi ,qarama da ita an sake ta innalillahi waโ€™inna ilaihirrajiโ€™un ta fada cikin ranta ta na ta juya spoon 
Sarah ta kalle ta sannan ta ce ummu " ko dai ba ta da lafiya ne na ga ba ta cikin wal-wala hope dai everything is fine "
" Mu gama sannan mun yi magana " Ummu ta ce " please Amnah forget about everything please I donโ€™t want to see you in this bad mood "
A hankali ta dago idanunta ta kalle ta sannan ta ce " insha allah ummu "
" Yawwa my daughter Allah ya yi maki Albarka "
Haka har kowa ya gama ita kam bai wuci tayi 3 spoon na Abincin ba 

   KATSINA GUESS IN

            HOTEL 

Tun da ya tsirawa picture din ido ya ke ta kallo saidai idan lokacin sallah ya yi ya tashi ,ya kasa cin komai picture dinta ne abincin shi 
" Ya rabbi na san a duk in da ta ke ba ta cikin yanayi mai kyau " Ya fada cikin damuwa 
Wayarshi dake flight mode ya fidda tare da shiga call history ya gano number din data kirashi 
Saving yayi da my pinky ๐Ÿ’•๐Ÿฉท
Misalin qarfe 10 na dare bumber dinta ya soma kira,cikin sa,a tayi pickig call din 
Shuru ba tare da da ta ce komai ba ,haka shi ma bai ce komai ba 
Dukkaninsu Su na jin fitar numfashin juna, a tare zuciyoyinsu su ka yi wani irin bugawa kowane ya dafe saitin zuciyarshi 

By WALEE โœŒ๏ธ


*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , โ‚ฆ200 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP DIN*
 Via 
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
 DM : +22798999753 for evidence