SHAFI NA HUƊU
by @ummishatu
©️Love story 2025
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA....!
NA
*UMMI A'ISHA*
Wattpad:ummishatu
Arewabooks:ummishatu
4
***Mommy ba dan ta so ba ta hakura da maganar tura shi gidan kangararrun yara sai dan yadda taga Imaan ta dage, ko babu komai yarinya ce mai nutsuwa da hankali da kuma sanin ya kamata shiyasa ta ɗauki shawararta ta rabu dashi dama kuma tunda hakan ta faru da ya fita ya bar gidan bai dawo ba yanzu tsawon kwana shida kenan idan da sabo an saba idan ya kwana a gida yau to gobe ba lallai ba kai zai iya ma share sati guda bai waiwayi gida ba haka rayuwarsa take kullum yana hotel, kamar koda yaushe Imaan ke bawa mommy baki tana kwantar mata da hankali da kuma sake karfafa mata gwiwa akan taci gaba da yi masa addu'a karta ƙosa haka kuma kar ta gajiya domin Allah maji roƙon bawansa ne cikin kowanne lokaci, a duk lokacin da mommy taji Imaan din ta faɗi haka shuru take yi kawai tayi murmushi bata cewa komai saboda babu irin addu'ar da bata yiwa Anaam amma kamar sake tirawa ake maimakon lamarinsa yayi sauki ma a'a sai karuwa da yake sake yi,
A daren ranar ya baro hotel din da yake wanda ya mayar tamkar dakinsa na gida ya taho gida lokacin misalin ƙarfe 2:30 na dare, kasancewar cikin maye yake sama sama da ya hango motar jami'an tsaro masu patrol baiyi niyyar ya tsaya ba amma dan dole sai da suka tsayar dashi saboda wani babban karfe da suka yi amfani wurin ajiyewa akan hanyar wanda muddin idan mutum bai tsaya ba ya taka to tabbas zai yi masa ɓarna dan sai ya fasa masa tayoyin mota,
Tsayawa yayi sai dai sam bashi da niyyar fitowa hakan yasa su suka karaso inda yake suna tambayar sa daga ina zuwa ina cikin wannan daren, da yake koda yaushe cikin high temper yake kuma abu kadan ke fusatashi yanzu take ya soma fada da jami'an tsaron harda kokarin dambe nan suka kama shi suka saka a mota basu tsaya dashi ako ina ba sai office kuma suna zuwa suka saka shi cikin cell sai dai har lokacin bai yi shuru ba yana mayar musu da martani dan cewa yake idan wani abu ya samu motar shi wallahi ba zai yarda ba, dan bai so wani ya shigar masa mota ba ya tukota har zuwa station din,
Ba a kira mommy ba sai da gari ya waye misalin karfe 10 da wani abu ta gama yin breakfast kenan tana shirin barin gidan, ranta a bace tace ba zata je ba suje suyi ta rike shi a police station din har sai ranar da suka gaji sai su sako shi,
Malam bala driver da komai ya faru cikin kunnuwansa a ransa fadi yake "Assha.. Assha albasa bata yi halin ruwa ba" amma a fili sai ya kwantar da murya yace,
"Ranki ya dade hakurin nan dai da aka saba shi za ayi, yanzun ma kar a kasa ko kuma kar a gaji a daure aje a karbo belinsa, shi ɗan yau ne ka haife shi amma baka haifi halinsa ba...."
Fasa fitar da zata yi da farko tayi ta juya ta koma ciki ranta na yi mata wani irin zafi da kuma suya, Imaan dake tsaye tsakiyar falon tana yin mopping ganin mommy din ta shigo tayi saurin ajiye mopper din hannunta ta rissina,
" mommy ko kinyi mantuwa ne?"
Girgiza kai mommy tayi kawai ta shige cikin bedroom dinta ba sake fitowa ba har Imaan din ta kammala gyaran da take yi ta fita saboda ta fara jiyo hayaniya daga waje dama duk ranar Juma'a haka kofar gidan yake kasancewa saboda abincin sadakar da ake yi ana fitar dashi waje ana rabawa almajirai da sauran mabuƙata kuma duk yawan sa baya isa wasu haka suke tafiya basu samu ba dan daga wurare daban daban ake zuwa karɓa, hakika mutane na cikin wani hali na talauci da kuma babu gefe guda kuma ga tsadar rayuwa da ta sako bayin Allah a gaba shiyasa kowa ka gani a ruɗe yake kuma a rikice sai wanda Allah ya taimaka yafi karfin bukatunsa, wannan kadai ni'ima ce babba da bawa idan ya kalla ya kamata ya godewa mahaliccinsa, anan wurin masu dafe dafen abincin tsakar gida ta jiyo labarin dake ta kai komo cikin gidan cewar Anaam yana hannun jami'an tsaro sai dai wannan Karon mommy tace ta gaji dan haka babu inda zata je domin duk tsuntsun da yaja ruwa tofa shi ruwa kan doka, tabbas ta san mommy tayi hakuri kuma tayi kokari wanda har gobe tana kan yi to amma yaya zata yi? Ita tata kalar jarrabawar kenan, dole ita dince zata tsaya masa duk lokacin da yaje ya jajibo rigimarsa ko tashin hankali,
Ciki ta koma wurin mommy duk da bata da kalamai ko bakin da zata rarrashi mommyn har ta ja ra'ayin ta taje ta fito da Anaam, abin tabbas akwai gajiya da kuma ƙosawa, sai da ta jima zaune a falo ganin har lokacin mommy bata da niyyar fitowa yasa ta tashi ta nufi cikin bedroom din mommy din, kamar yadda ta saba zama tana rubuce rubuce cikin babban diary dinta yanzunma zaune take tana yan rubuce rubucenta,
"mommy sannu da aiki......."
"yawwa Imaan..... Akwai wani abu ne?"
"mommy yanzu ne nake jin wai Anaam yana hannun jami'an tsaro...."
"ehh hakane...."
"kuma mommy baza aje aji ba'asi ba?"
Sai lokacin mommy ta dakata daga abinda take yi ta kalli Imaan din kafin tace "wanne ba'asi za aje aji? Ko mu tambaya ko kar mu tambaya kowa yasan shine mai laifi domin halinsa ne..... Dauko rigima da rashin son zaman lafiya a jinin sa yake, wannan halayyarsa ce kuma dabi'arsa ce ta yau da kullum, every single day sai kaji wata rigima sabuwa da ya dauko, bai taba yin cikakken 1 week batare da jami'an tsaro sun kama shi ba, idan yan sanda basu kama shi ba to yan drugs sai sun kama shi, kullum ahaka fa ake..... Yanzun abarshi acan ya zauna yaji idan zaman cell din dadi gareshi, na gaji da bata kudi na da lokaci na wurin iyo belinsa...... "
" mommy wallahi kowa ya san kina namijin kokari amma haka zaki cigaba da jajircewa domin hannunka baya rubewa ka yanke ka yar...... Dan Allah kiyi hakuri"
"Imaan idan ma naje na fito dashi a gobe yana iya sake taro rigimar da zata mayar dashi cell....."
"duk da haka mommy ki daure kiyi hakuri kuma kije ki taho dashi...."
"Imaan bani da wannan lokacin.... Idan wannan ne kadai abinda ya kawo ki, you can go please...."
Kasa tafiya tayi taci gaba da zama awurin tana bawa mommy haƙuri, jin magiyar tayi yawa ya sanya mommy rufe diary din dake hannunta ta kalli imaan tace,
"Imaan zan je na taho dashi kamar yadda kike ta rokata amma ki sani zanyi hakane a bisa sharadi guda daya.... Sharadin shine idan har Anaam ya sake zuwa ya aikata laifi ko wani abu wanda hukuma ta kama shi ba zan sake zuwa karbo shi ba koda kuwa zai shekara a hannun su....... "
" mommy insha Allah ma haka ba zata sake faruwa ba.... "
Tashi mommy tayi ta fita saboda ta san wannan shi yafi komai sauki awurinsa. Bayan fitar mommy da kamar awa 1 sai gashi ya dawo gidan ya tuko motarshi a zuciye kuma a hasale, babu wanda ya kula ya wuce part dinsa ransa a ɓace,
" sarkin kunci ai fa Allah ya dawo da kai kuma....." imaan ta fada cikin zuciyar ta bayan ta ga shigowarsa da shigarsa cikin part dinsa, falon mommy ta koma ta fara kokarin sake goge shi bayan ta kunna turaren wuta, zuciyar ta ɗaya sannan hankalinta kwance take yin goge gogenta tana magana ita ɗaya,
" Ace mutum sam baya jin magana.... Bashi da aiki sai faɗace faɗace da ɗauko magana...... Kawai dan ka samu kuɗi a banza an tara maka ba tare da kai kasan zafin nemansu ba shine zaka zauna kana hauka a gari tamkar......"
"ke...." tsawar da ta jiyo ya sanya ta saurin juyawa hankalinta a mutukar tashe dan ta san wanda take gulmar zai yi wahala idan bai ji ba,
"Meyasa ba a gyara min part ɗina ba ko ina datti?"
"Ehmmm... Ehhmmmm...."
"kibar duk abinda kike yi ki zo ki gyara min bedroom dina malama.... Bazan iya zama cikin waccar kazantar ba"
Juyawa yayi ya fita ta bishi cikin sauri, tana gyara masa falo yana cikin bedroom babu jimawa sai gashi ya fito da alama wanka yayi dan gashi nan har ya canja kaya zuwa farar t shirt da blue din jeans wanda suka yi mutukar amsar jikinsa sai kamshi mai dadi da sanyi dake tashi daga jikinsa,ganin ya dauki key din mota zai fita ya sata saurin faɗin,
"Ranka ya dade zaka fita ne?"
Banza taji yayi da ita kamar yadda dama ta tsammata dan zai yi wahala ya amsa mata,
"Dan Allah kar ka fita..... Ka zauna a gida kar ka je ka sake dauko wata rigimar da za a kulle ka....." ta fada cikin karfin halin da ita kanta mamakin kanta take yi dan wannan shi ake kira da karfin hali wato ɓarawo da sallama banda haka ina ita ina shiga sha'aninsa?
Juyowa taga yayi yana kallonta " wai dani kike? " ya fada tare da nuna kansa da yatsansa guda daya,
"da kai nake, dan Allah kar ka fita.... Saboda duk lokacin da ka fita sai....." bai sake sauraren ta ba taga yayi ficewarsa, ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta cike da tsanarsa da haka tayi aikin ta kammala ta koma part din mommy ta ɗora mata abincin rana dan ta san duk inda take kafin azahar zata dawo gida, ai kuwa tana dab da gama dafa abincin mommy ta dawo, sannu da zuwa taje tayi mata kafin tace,
"mommy yanzu zan shirya table na kusa gama abincin...."
"Imaan bakina babu dandano nayi loosing apatite ba zan iya cin abincin nan ba..."
"zaki ci insha Allah mommy, ba zan taba bari ki zauna baki ci abinci ba saboda likita yace ki rinka shan maganin ki...."
"Rabu dashi ko na sha ko ban sha ba ai ba sani zai yi ba...."
"zai sani mana mommy...."
"sai idan ke zaki fada masa" mommy ta fada cikin murmushi, Itama murmushin tayi kafin tace,
"to amma ai mommy zaki iya bani cin hanci ta yadda ba zan fada masa ba..."
"yawwa to ko ke fa.... Fada min abinda kike so...."
"to shikenan ina zuwa..." daga haka ta fita fuskar ta dauke da murmushi, kai gaskiya mommy duniya ce shiyasa take kaunarta, table din ta shirya inda ta dafa shinkafa da miya da chicken salad, cikin barkwanci suka kasance tare da mommy har taci abincin ta gama ta sha maganin ta............. ✍️
Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,
FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.
. Ummi Shatu👌🏻